HausaTv:
2025-04-28@10:19:20 GMT

Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 115

Published: 28th, April 2025 GMT

115-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissiso da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin dastane rastan, ko kum littafin mathnawi na maulana Jalaluddeen rumi.

Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///… Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-hassan limami na biyu daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s), kuma da na farko ga Fatimah(s) diyar manzon All..(s), sannan jikansa na farko.

A cikin shirimmu da ya gabata, mun ji yadda wasu malaman tarihi suka kawo wasu hadisai wadanda basu inganta ba suka jinginawa Imam Alhassan Almujtaba (a) dangane da son da yakewa khalifa na ukku wasu Uthman bin Affan, mun gudanar da bincike cikin daya daga cikin hadisan a sanadi da kuma mataninsa inda muka tabbatar da cewa , Mada’ini wanda aka ruwaito wannan hadisin, nasibi ne, wato wata jama’a wacce ta ke addini da kiyayya ga iyalan gidan manzon All..(s), har’ila yau yana kirkiro hadisan na kariya ya jinganawa manzon All..(s) na muzantasu da kuma kirkiro wasu hadisan daga manzon All..(s) na yabon banu umayya.

Sannan a matanin hadisin mun bayyana kariyar zance mai cewa Imam Hassan yana zargin babansa Imam Ali (a) da hannu a kashe Uthman dan Affan, sannan yana tare da mahaifinsa, manya-manyan yake-yake guda biyu da yayi a lokacin khalifancinsa, da wadanda  suke tuhumarsa da zubar da jinin Khalifa Uthman.

Wato yake-yaken Jamal da Siffin. Imam Hassan (a) ya yaki wadannan makiyan mahaifinsa wadanda suke zarginsa da hannu a kissan Uthman. Kuma bamu taba sanin akwai sabani tsakanin Imam Ali (a) da yayansa Alhassan da Alhussain (a).

Daga karshen mun kawo maku yadda manyamanayn sahabban manzon All..(s) da suka rage a Madina suka rubuta wasi ku zuwa sauran sahabbansa a sauran yankuna na daular musulunci suna neman taimakonsu don kauda Khalifa uthman daga khalifanci, saboda ya sabawa littafin All..da sunnar manzon All..da kuma siran khalifofin da suka gabata. Sun koka kan yadda ya mika al-amuran daular musulunci ga danginsa banu Umayya suna satar dukiyar al-umma sannan sun barsu da talauci.

Mun bayyana cewa akwai abubun lura a cikin wannan wasikar kamar haka,

1-Sunan zarginsa na kin amfani da littafin All..

02-Sauya sunnan manzon All..(s) da kuma, yayi watsi da ita,

03-yayi watsi ga hanyar khalifofin biyu da suka gabace shi wato Abubakar da Umar

04- Ya kauda ma’anar khalifancin manzon All..(s) daga yadda yakamata ta kasance,

5-Kwace dukkan duniyar Al-ammu da kuka sarrafata a wasu wurare kebantattu, wato kashe ta kan dangin khalifa wato Banu Umayya.

Malaman tarihi sun bayyana cewa, wadannan al-amura sun girgiza daular musulunci, kuma sun kusan su rusata.

Sannan mun bayyana cewa wadanda suke sukan shugabancin Khalifa Uthman sun rubuta wata wasika ga murabiduna, wato wadanda suke kula da kan iyakokin daular musulunci daga cikin sahabbai, sun bukacesu su dawo madina don tsada khalifancin manzon All..(a), don tabbatar da khaifancin ya dawo kan yadda yakamata ya kasanci.

Ga kuma matanin wasikar kamar haka.

{Lalle ku, kun fita ne don ku yi jihadi a kan tafarkin All..mai girma da daukaka, kuna neman kare addinin Muhammad (s) to lalle khalifanku ya lalata addnin Muhammadu, ku dawo ku tsaida shi,…}.

Banda haka a lokacinda wasikun nan suka isa yankuna da dama na daular musulunci sun yi ta aika tawaga don ganin abinda yake faruwa a Madina, sannan tawagogi da suka isa Madina don ganewa idanunsu abubuwan da suke faruwa, da kuma tattauna matsalolin da kuma yadda za’a magance su, sun hada da.

Tawaga daga kasar Masar, kafin haka akwai mutane 700 da suka tura tun farko bayan da suka kama wani bawan Khalifa Uthman wanda ake kira warsh dauke da wasikar Khalifa zuwa dan uwansa gwamnan Masar Abdullahi ibn Abisharkh, na ya kashe sui dan sun isa da sabon kwamna Muhammad dan Abubakar.

A wannan karon mutanen masar sun aiki mutane 400. Tare da jagorancin Muhammad dan Abubakar wanda dama yana manina, da Abdrrahman dan Udais Al-balawi.

2-sai tawagar Kufa wanda ya hada da Malik dan Ashtar, Zaidu dan Sauhan Al-Abdi, da Ziyad dan Annadhir Al-harithy. Da abdullahi dan Asam Al-Amuri da shugabansu gaba daya, Amru dan Ah-tham .

03-sai tawagar Basra wacce ta hada da Hakin dan Jibilah, tere da wasu mutane 100. Bayan haka wasu khamsin sun bisu. A cikinsu akwai Zarih dan Abidi Al-Abdi, da bishru dan shuraih Alkaisi, da dan Mahrash, da wasunsu daga cikin fitattun mutane kuma sanannu na Basra.

A lokacinda wadannan tawagogi suka isa Madina an yi maraba da su, kuma nag ode masu da karban kiran da aka yi masu, sannan sun tattauna da sauran sahabbai da kuma musulmai dan al-amuran da suka faru, da kuma irin mummunan halin da musulmi suka shiga ciki saboda yadda Khalifa Uthman ya sauya al-amura da dama, daga cikin ya hanasu dukiyoyinsu, wadanda suka saba samu a zamanin khalifofin da suka gabata. Ko kuma ya fita daga tsarin da manzon All..(s) yake raba dukiya a cikin al-umma.

Bayan yan kwanaki sai mutanen kasar masar sun ga cewa kafin ko me da farko a rubutawa khalifa Usman  wasika, a yi masa nisiha kan ya dawo kan tafarkin da ya dace ga kuma kadan daga cikin abinda wasikar ta kunsa.

Bayan Basmala da salati ga manzon All..(s) da kuma godiya ga All..sai suka ce

(bayan haka, ka sani kan cewa, {Lalle All..baya sauya halin da mutane suke ciki sai sai sun sauya halinsu, muna hadaka da All..kuma muna sake hadaka da All..Lalle kai kana cikin duniya mai gucewa, … .. kuma kada ka manta da rabon a lahira, kada duniya ta rudeka, kuma ka san cewa mu don All..muke yi, kuma don All…muke fushi. Kuma muna neman yardarm All.. ne, kuma lalle ba zamu dauke takubbammu daga wuyoyimmu ba saika tuba daga abubuwan da ka aikata mana, tuba mai tsanani kuma a fili, wannan shi ne maganarmu da kai, sannan bukatarmu a gareka, All..ne mai karban uzurimmu dangane da kai..wassalam…}.

A lokacinda Khalifa Uthman ya karanta sai ya ji tsoro. Sai Mughira ya nemi izininsa yayi Magana da mutane, sai ya bashi izini, a lokacinda suka ganshi sai suka daga murya suna cewa: Ya makaho  koma ya Fajiri koma ya fasiki koma.ya koma ya kasa Magana da su.

Sai Uthman ya kira Amru dan Asi, ya bukaci yayi Magana da su, ya amince, amma a lokacinda suka ganshi, sai yayi masu, sallama ba wanda ya amsa daga cikinsu,  suka daga murya suna cewa: Ko koma ya makiyin All.. ka kuma ya dan Nabigha. Kai ba amintecce ne a wajemmu ba kuma mai aminci ba.

A nan sai Khalifa Uthman ya fahinci cewa babu wanda zai taimaka masa sai Amirulminina Aliyu dan Abitalib (a), sai ya nemi taimakonsa, ya fada masa cewa, yayi kira ga mutane zuwa ga Alkur’ani mai girma da sunnar annabinsa.

Sai Imam ya amince, amma da sharudda kan cewa, ya yi masa alkawali tsakaninsa da All..zai yi aiki da abinda ya fada. Sai ya yi alkawali zai zai cika alkawalinsa, za iyi aiki da abinda ya fada.

Sai Imam (a) ya je wajen mutane, shima a lokacinda suka ganshi suka ce, koma , sai yace a’a na zo maku da cewa, za’a yi aiki da littafin All.., kuma za’a sauya duk abinda kuka yi fushi dominsa. Sai ya fada masu abinda khlifa ya bada.  Sai suka ce: Ka lamunce mana haka zai faru? Sai yace :ee. Sai suka ce mun yarda.   

Sai ya shigar da manya manya daga fitattun mutane  wajen Uthman, sai suka yi ta sukansa, sannan suka ce, ya Sanya abinda ya yi alkawali na aiki da littafin All..da kuma sunnar manzon All..(s) da kuma bawa musulmi hakkinsu da ake basu.

Sai ya amince ya rubuta ya basu sannan suka karbi takardan suka kama hanyar masar.

Wannan shi ne nassin abinda ya rubuta ya basu’

{Wannan rubutun daga bawan All..Uthman Amirulmuminina zuwa ga wadanda suke sukansa daga cikin muminai da musulmai, kan cewa hakkinsu ne in yi aiki da littafin All..da sunnar annabinsa a cikinu, za’a bawa talaka hakkinsa, wanda yake cikin tsoro a amintar da shi, wanda aka kora adawo da shi …kuma za’a samar da kudade ga musulmi. Sannan Aliyu dan Abitalib (a) shi ne mai lamuncewa muminai, kuma wajibi ne ga Uthman ya cika alkawalin da ya dauka cikin wannan rubutun}.

Banda haka Zubair dan Awwam, Talha dan Ubaidullahi,Sa’du dan Abi wallas, Abdullahi dan Umar, Zaidu dan Thabit, Sahal dan Hunaif,, Abu ayyuba Khalid dan zaid, kuma anyi wannan rubutun a cikin watan Zulkida shekara ta shekara 35.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu. Wassalau alaikum warahamatullahi wa barakathu.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: daular musulunci wadanda suke masu sauraro

এছাড়াও পড়ুন:

An kama mutane 13 kan zubar da ciki a Bauchi

Wasu mutane 13 sun faɗa a komar ’yan sanda ka zargi da zubar da ciki da kuma mutuwar wata budurwa ’yar shekara 18 a Jihar Bauchi.

Kakakin ’yan sandan jihar, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya ce ana tuhumar huɗu daga cikin mutanen da aikata laifin fyade, zubar da ciki da kuma mutuwar budurwa a garin Misau da ke Ƙaramar Hukumar Misau.

Wakil ya ce, a ranar 4 ga Afrilu, 2025 sun samu bayanai ewa, kimanin watanni hudu da suka gabata, wasu matasa biyu a yankin Lariski da ke Misau, sun kama wata yarinya mai shekaru 18 da suka yi ta yi lalata da ita sau da yawa.

Ya ce a lokacin da suka lura tana ɗauke da juna biyu, sai suka nemi wani mutum suka ba shi naira 40,000 don ya taimaka musu wajen zubar da cikin, amma abin takaici sai aka samu matsala wanda a qarshe ya yi sanadiyyar mutuwarta.

Wakil ya ce, “Bayan an yi mata allurar zubar da ciki saita fita daga hayyacinta, daga baya kuma ta kamu da rashin lafiya. Hakan ya sa danginta suka kai ta Babban Asibitin Misau, daga baya an mika ta zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) da ke Azare, inda hukumomin asibitin suka sanar da cewa ta mutu a lokacin da take jinya.”

Bayan samun rahoton, an kama wadanda ake zargin, inda suka amsa laifin da suka aikata tare da ambaton wasu da ke da hannu a lamarin.  Ya ce sauran wadanda ake zargin da wasu mutum huɗu suna hannun ’yan sanda ana bincike.

Bayan haka kuma za a gurfanar da su a gaban kuliya bisa laifukan da suka aikata.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kissoshin Rayuwa: Imam Al-Hassan 114
  • An kashe sojoji 12 a barikin Nijar
  • Falasdinawa 39 Sun Yi Shahada A Cikin Sa’o’I 24
  •  Adadin Wadanda Su ka Kwanta Dama A Gobarar Tashar Jirgin Ruwan Shahid Raja’i Sun Kai 21
  • Sulhu da ’yan bindigar Katsina: Gaba aka ci ko baya?
  • ‘Yan Gudun Hijiran Sudan Sun Yi Kira Ga Kungiyoyin Kasa Da Kasa Da Su Ceto Yara Da Tsofaffi Daga Mummunan Kangi A Sudan
  • ’Yan kasuwar da suka ɓoye kayan abinci na tafka asara
  • Sayyid Fadhlullahi Ya Jaddada Muhimmanci Samar Da Makamai Ciki Har Da Kare Kasa Daga Dan Mamaya
  • An kama mutane 13 kan zubar da ciki a Bauchi