HausaTv:
2025-04-28@09:58:27 GMT

Lebanon:  Isra’ila Ta Kai Hari Akan Unguwar Dhahiya A Birnin Beirut

Published: 28th, April 2025 GMT

Jiragen yakin HKI sun kai hari a yankin Hangara dake unguwar “Dhahiya” a cikin birnin Beirut. Yankin da jiragen yakin na ‘yan sahayoniya su ka kai wa harin, yana cike da mutane da kuma makarantu biyu.

Jiragen yakin na HKI sun harba makamai masu linzami 3, da hakan ya haddasa tashin gobara.

A sanadiyyar wannan harin, an sami shahidi daya,yayin da wasu da dama su ka jikkata.

A ranar 1 ga watan Aprilu ma dai sojojin HKI sun kai wani harin a unguwar Dhahiya wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane 4 da kuma jikkata wasu da dama.

Tun bayan tsagaita wutar yaki a ranar 27 ga watan Aprilu 2025, HKI ta keta wutar yakin fiye da 2000.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Ƴan Ta’adda Sun Kashe Maharba 10 A Adamawa

Ƴan ta’adda da ake zargin Boko Haram ne sun kashe mutane 10 na yawucin dabbobi da kuma mambobin jami’an tsaron sa kai (CJTF) a garin Kwapre, dake cikin ƙaramar hukuma ta Hong a Jihar Adamawa.

Shugaban ƙaramar hukuma, Hon Usman Wa’aganda, ya tabbatar da wannan lamarin ga LEADERSHIP ta waya a ranar Lahadi a Yola, inda ya bayyana cewa wani mutum da ya samu raunuka daga harin ‘yan ta’addan yana samun kulawar likita a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba.

Daidaikun Kasashe Za Su Kara Karfi Idan Suka Hada Hannu Tare ‘Yansanda Sun Kama Wani Kato Bisa Zargin Cin Zarafin Wata Mata A Adamawa

Wa’aganda ya ce ‘yan ta’addan sun ƙone gidaje da dama da kuma amfanin gona, yana mai cewa wannan harin ba na farko bane, domin garin ya sha hare-hare sau da dama wanda ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.

Ya nemi hukumomin tsaro su ƙara tura jami’ai a yankin domin taimakawa wajen kare al’umma da kuma tabbatar da tsaro.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ƴan Ta’adda Sun Kashe Maharba 10 A Adamawa
  •  Dakarun Kai Daukin Gaggawa Na Sudan Sun kashe ‘Yan Hijira Da Dama A Yankin Tekun Maliya
  • Sojojin Yemen Sun Sanar Da Kai Wa Cibiyar Sojan Sama Ta “Nivatim” Hari Sau Biyu A Cikin Sa’o’i 24
  • An Kammala Jana’izar Paparoma Farancis A Birnin Vatican
  • Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Sansanin Nevatim Na Harahtacciyar Kasar Isra’ila Da Makami Mai Linzami
  • Sojojin Mamaya Sun Yi Kasan Kiyashi A Zirin Gaza Da Kuma Ci Gaba Da Killace Falasdina  Cikin Masifar Yunwa
  • Gaza: Falasdinawa Da Dama Sun Yi Shahada A  Yau Asabar
  • Sojonin Yemen Ta Kakkabo Jiragen Yakin Amurka Wadanda Kimarsu Ya Dalar Amurka Miliyon $200 A Makonni 6
  • Jiragen Yakin Amurka Sun Kai Sabbin Hare Hare Kan Yakuna 4 A Kasar Yamen