Falasdinu: Mahmud Abbas Ya Nada Magaji Da Kuma Mataimakasa
Published: 28th, April 2025 GMT
Shugaban Palasdinu da kuma kungiyar kwatar yencin falasdinawa PLO Mahmud Abbas ya nada magajinsa da kuma wasu mataimaka.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran, ta bayyana cewa Abbas dan shekara 89 ya nada mataimakinsa ne bayan taron majalisar gudanarwa ta gwamnatinsa a makon da ya gabata.
Labarin ya kara da cewa kasashen yamma da yankin sun dade suna takurawa Abbas kan ya nada mataimaki da kuma wasu mataimaka sabuda rawar da gwamnatinsa zata taka bayan yakin gaza.
A yau ne majalisar zartarwa ta amince da nada Hussein Al Sheikh a matsayin mataimakin shugaban majalisar da kuma mataimakin shugaban kasa a lokaci guda.
Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Falasdinawan WAFA, ya bayyana cewa gwamnatin Abbas ce da hakkin sa hannu a kan yarjeniyoyi da suka shafi Falasdinu, a madadin dukkan kungiyoyin Falasdinawa, banda wadanda su ka dauke da makamai suna yakar HKI, wato Hamas da kuma Jihadul Islami a Gaza.
Mr Al Sheikh, dan shekara 64 a duniya na hannun daman Abbas ne a kungiyarsa ta fatah.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Siriya Zata Samar Da Huldar Jakadanci Da HKI A Dai-Dai Lokacinda Ya Dace
Shugaban rikon kwarya na kasar Siriya Ahmed Al-sharaa ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take ta samar da hulda da HKI a dai-dai lokacinda ya dace.
Jaridar Middle East Eye ta kasar Burtaniya ta nakalto Ahmed Sharaa yana fadar haka a wata wasikar da ya rubutawa shugaba Donal Trump
Har’ila yau shugaba Al-sharaa ya fadawa wani dan majalisar dokokin kasar Amurka kan cewa gwamnatinsa zata samar da huldar jakadanci da HKI a lokacinda ya dace, sannan a bangaren kasar Siriya kuma tana bukatar da farko a dagewa kasar takunkuman da aka dora mata, sannan yana son a yi maganar yankunan kasar Siriya wadanda HKI ta mamaye bayan juyin mulkin da aka yi a kasar.
Dan majalisar dokokin kasar ta Amurka Cory Mills na hannun daman Trump ya ziyarci kasar Siriya a makon da ya gabata inda ya gana da shugaban, na kimani minti 90, don tattaunawa wadannan al-amura
Mill dai wanda ziyarci kasar ta tare naukar nauyin yan kasar Siriya a Amurka ya bayyana kamfanin dillancin labaran Bloomberg kan cewa ya fadawa shugaban matakan da yakamata ya dauka don ganin an daukewa kasar takunkuman tattalin arziki.
Ya kuba bukaci shugaban wargaza sauran masana’antun makaman guba a kasar, ya shiga cikin kasashen yankin masu yaki da ayyukan ta’addanci, ya kuma san yadda zai yi da yan kasashen waje wadanda suke cikin HTS, wanda suka taimaka masa ya sami damar kifar da gwamnatin Bashar al-asad. Sannan dole ne ya amintar da HKI kan cewa ba zai kai mata hari ba.