Jiragen Yakin Amurka Sun Kashe Mutane Da Dama A lardin Sa’ada Na Kasar Yemen
Published: 28th, April 2025 GMT
Mutane da dama daga nahiyar Afirka ne suke cikin mutane kimani 50 wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan wani gidan kaso a lardin Sa’ada na kasar Yemen.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Al-Masirah yana cewa makaman Amurka sun fada kan wani gidan yarin da aka kebewa yan Afrika, kuma yawansu ya kai 115, amma har yanzun ba’a san yawan wadanda suka rasa rayukansu a gidan yari.
Labarin ya kara da cewa har yanzun ma’aikatan agaji suna aikin ceto a wurin, sannan hotunan da suka fara bayyana sun nuna gawaki da dama. Amma Al-Masirah ta bayyana cewa akalla mutane 68 sun rasa rayukansu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Yemen Suna Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Babban Filin Jirgin Ben Gurion Na Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Rundunar sojin Yemen sun kai hari kan filin jirgin saman Ben Gurion da makami mai linzami
Rundunar sojin Yemen ta sanar da kaddamar da farmakin soji kan babban filin tashin jiragen saman Ben Gurion da ke yankin Jaffa da aka mamaye, domin jaddada goyon baya ga al’ummar Falastinu da ake zalunta da kuma yin nuna kiyayya ga kisan kiyashin da makiya ‘yan sahayoniyya suke yi wa ‘yan uwansu a Zirin Gaza.
Kakakin rundunar sojin Yemen Birgediya Janar Yahya Sari’e ya bayyana cewa: Don goyon bayan al’ummar Falastinu da ake zalunta da ‘yan gwagwarmaya da kuma nuna rashin amincewa da kisan kiyashin da makiya ‘yan sahayoniyya suke yi kan ‘yan uwansu a yankin Zirin Gaza, sojojin Yemen suna ci gaba da kai hare-hare da makamai masu linzami kan babban filin jirgin sama na Lod, wanda haramtacciyar kasar Isr’ila ke kira da filin jirgin saman Ben Gurion, a yankin Jaffa da suka mamaye.
Janar Yahya Sari’e ya kara da cewa: Suna kai hare-haren da makamai masu linzami masu linzami, domin tarwatsa yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida.