Talata ce ɗaya ga watan Zhul Qi’ida — Sarkin Musulmi
Published: 28th, April 2025 GMT
Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Muhammad Sa’ad, ya bayyana cewa gobe Talata, 30 ga watan Afrilun 2025, ita ce za ta kasance 1 ga watan Zhul Qi’ida na shekarar 1446 ta Hijiriyya.
Wata sanarwa da shugaban kwamatin ganin wata na fadar, Farfesa Sambo Wali ya fitar ta ce an ɗauki matakin ne saboda ba a ga jinjirin watan ba a ranar Lahadi.
Hakan na nufin yau Litinin, 28 ga watan Afrilu ne 30 ga watan Ƙaramar Sallah na Shawwal.
A ƙa’idar kalandar Musulunci, kowane wata yana yin kwana 29 ne, amma idan ba a ga jaririn watan ba sai a cika shi zuwa kwana 30.
Aminiya ta ruwaito cewa tun a ranar Asabar da ta gabata ce Fadar Sarkin Musulmin ta ba da umarnin duban watan na Zhul Qi’ida.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Sarkin Musulmi Shawwal
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka Ta Ce: Shugaban Rikon Kwarayar Siriya Al-Julani Ya Yi Alkawarin Cewa Ba Zai Cutar Da Tsaron Isra’ila Ba
A ganawarsa da wata jami’ar Amurka, al-Julani ya yi alkawarin ba zai cutar da tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila ba!
Barbara Leaf, tsohuwar mataimakiyar sakatariyar harkokin wajen Amurka mai kula da harkokin gabas ta tsakiya, ta tabbatar da cewa shugaban rikon kwarya a Siriya, Mohammed al-Julani (al-Shara’a), “ya bayyana fahimtar matsalolin tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila,” a cewarta.
Hakan ya zo ne a wata ganawa tsakanin Leaf da al-Julani a birnin Damascus, jim kadan kafin ta bar mukaminta. Leaf ta bayyana taron a matsayin “mai kyau kuma mai amfani.”
Har ila yau Leaf ta yaba da “hanzari da kuma dabarar da Shara’a ke bi wajen tunkarar al’amurran yankin,” tana mai cewa “yana neman kulla kyakkyawar alaka da bangarorin yankin.”