Leadership News Hausa:
2025-04-28@19:49:49 GMT

Xi Jinping Ya Bukaci A Hada Karfi Wajen Farfado Da Kasar Sin

Published: 28th, April 2025 GMT

Xi Jinping Ya Bukaci A Hada Karfi Wajen Farfado Da Kasar Sin

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda Cazar Kudade Da Yawa Ke Haifar Da Raguwar Fitar Da Kaya A Tashoshin Jiragen Ruwa – NPA

“Rashin samar da daidaito a hada-ahadar kasuwanci, ya kasance abinda ya sanya Hukumar ta NPA ke cazar kudaden gudanar da aiki da yawa,” Inji Dantsoho.

 

Dantsoho wanda Janar Manaja na sashen hudda da jama’a da gudanar da tsare-tsare na Hukumar NPA Miista Seyi Iyawe Akinyemi ya wakilce shi a wajen taron, ya ce, NPA ta bai wa kamfanini biyar Lasisi a jihar Legas, bisa kokarin da take yi, na bunkasa fitar da kaya zuwa waje ta hanyar amfani da Tashoshin ta.

 

Sai dai, ya sanar da cewa, Hukumar na duba yuwuwar samar da rangwamen cazar kudaden, musamman domin ta kara inganta ayyukanta.

 

Ya yi nuni da cewa, Tashoshin Jiragen Ruwa waje ne da ke taimaka wa wajen kara habaka tattalin arzikin kasa, musamman saboda shigowar kasuwanci cikin kasar.

 

Dantsoho ya kara da cewa, yin ragin, zai bayar da dama wajen kara karfafa gasa a kasashen da ke Afiraka.

 

Shi ma a na sa sakon a wajen taron Babban Sakatare kuma Shugaban Majalisar Masu Fiton Kaya zuwa Ketare NSC, Dakta Akutah Pius Ukeyima, ya sanar da cewa, tabbatar da inganci a Tashar Jiragen Ruwa, abu da ya wuce, batun jigar kaya a Tashar, amma ana da bukatar komi ya tafi yadda ya kamata.

 

Ukeyima, ya bayyana haka ne, ta bakin Madam Margaret Ogbonna, Daraktar Sashen Kula da Ayyuka a NSC, ya kara da cewa, Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar nan, na fuslantar cazar kudade da yawa a yankin Afirka, musamman duba da yadda cazar kudaden, suka kai daga kashi 30 zuwa 40, wanda ya dara na Afirka ta Yamma.

 

A cewarsa, a yanzu, Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar nan, rashin inganci, wanda hakan ke ci gaba da shafar gudanar da hada-gadar kasuwanci.

 

Ya ci gaba da cewa, a yayin da Nijeriya ke ta kokarin tara sama da kashi 85 a cikin dari na fannin hada-hahadar kasuwancinta, musamman ta hanyar yin amfani da Tashoshin Jiragen Ruwanta, sai dai, cazar kudade da yawa a Tashohin Jiragen Ruwan Kasar, akalla a cikin kwana 18 zuwa 20, na ci gaba da zama kalubale, musamman duba da yadda cazar kudaden, daga kwana 3 uwa 5 suka dara na duniya.

 

“Wannan matsalar na janyo jinkiri da kuma shafar shiga da fitar da kaya.” Inji Ukeyima.

 

Ya bayyana cewa, domin a lalubo da mafita kan wannan matsalar, NSC ta mayar da hankali wajen ganin an wanzar da matakan da suka dace, musamman na bunkasa kundin farashi a Tashar Jiragen Ruwan Kasar.

 

Shi kuwa a na sa jawabin na maraba, Shugaban LCCI, Mista Gabriel Idahosa, ya alakanta Tashoshin Jiragen Ruwa na Kasar, a matsayin fannin da ke kara bunakasa gasar gudanar da hada-hadar kasuwanci da kuma kara habaka tattalin arzikin kasa.

 

“Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar sun kasance wata mahada ce ta gudanar da hada-hadar kasuwanci ta kasa da kasa, musamman duba da yadda ake fhigar da kaya da kuma fitar da su waje,” Inji Idahosa.

 

“Tabbabar da ingancin gudanar da ayyuka a Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar, ta hanyar rage cazar kudade masu yawa, tabbatar da ana tura kaya kan lokaci, karfafa gasar hada-hadar kasuwanci, na kara taimakawa Tashoshin,” A cewar Idahosa.

 

Ya kara da cewa, amma rashin tabbatar da ingancin, kara yawan cazar kudade, na rage yawan adadin hada-hadar kasuwancin da ake bukatar gudanar wa, wanda kuma hakan, ke janyo tattalin azriki nakasau.

 

A cewarsa, Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar nan, sun jima suna fuskanatar matsaloli, wanda hakan ya janyo rashin samar da inganci da kuma bayar da gudunmawarsu, kan habaka tattalin arzikin kasar.

 

“Daya daga cikin manyan kalubalen da Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar ke fuskanta sun hada da samun cunkoso a Tashoshin da kuma samun jinkiri, musamman a Tashar Apapa da ta Tin Can Island da ke a jihar Legos, “ Inji Idahosa.

 

“Kayan aikin a Tashoshin, an jima ana yin amfani da su, wanda hakan ke haira da samun jinkirin gudanar da aiki, cazar kudade da yawa na tura kaya, wanda hakan ke sanya ba a samun damar gudanar da gasar hada-hadar kasuwanci, kamar yadda ta dace,” A cewar Idahosa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Na Maraba Da Karin Abokai Daga Kasa Da Kasa Su Ziyarci Kasar
  • Bai Dace A Mika Wuya Ga Wanda Ya Nuna Fin Karfi Da Matakan Haraji Ba
  • Kasar Sin Za Ta Samar Da Dokar Da Ta Shafi Raya Kasa
  • Daidaikun Kasashe Za Su Kara Karfi Idan Suka Hada Hannu Tare
  • Iran Ta Bukaci Kasashen Indiya Da Pakistan Da Hada Kai Don Yakar Ta’addanci
  • Xi Jinping Ya Yi Kiran Samar Da Kyakkyawan Tsari Na Sarrafa Fasahar AI
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Siriya Ya Bukaci MDD Ta Dagewa Kasarsa Takunkuman Tattalin Arziki
  • Yadda Cazar Kudade Da Yawa Ke Haifar Da Raguwar Fitar Da Kaya A Tashoshin Jiragen Ruwa – NPA
  • Kasar Sin Ta Goyi Bayan Rawar Da Hukumar IAEA Ke Takawa Wajen Warware Batun Nukiliyar Iran Ta Hanyar Diflomasiyya