Sama Da Masu Sayayya Daga Ketare 220,000 Ne Suka Halarci Bikin Baje Kolin Canton Karo Na 137
Published: 28th, April 2025 GMT
Bikin baje kolin na wannan karo da ake gudanarwa a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin daga ranar 15 ga watan Afrilu zuwa ranar 5 ga watan Mayu, an shirya shi ne cikin matakai uku. Matakin farko ya mayar da hankali ne kan masana’antu masu ci gaba, na biyu a kan ingantattun kayayyakin gida, na uku kuma a kan kayayyakin dake sa kaimi ga inganta rayuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Falasdinawa 39 Sun Yi Shahada A Cikin Sa’o’I 24
A cikin sa’o’i 24 da su ka gabata an sami shahidai 39 sanadiyyar hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamaya su ka kai a sassa mabanbanta na zirin Gaza.
A birnin Khan-Yunsu Falasdinawa 3 sun yi shahada, daga cikinsu da akwai karamin yaro, yayin da wasu da dama su ka jikkata.
Majiyar kiwon lafiya ta Falasdinawa ta ambaci cewa, wani masunci ya yi shahada saboda harin da ‘yan sahayoniya su ka kai masa a gabar ruwan garin Khan-Yunus.
A wani labarin daga yankin na Gaza, sojojin HKI suna ci gaba da rusa gidajen fararen hula a arewacin birnin Rafah dake kudancin zirin Gaza.
Tun da HKI ta sake komawa yaki gadan-gadan akan al’ummar Falasdinu a ranar 18 ga watan Maris, Falasdinawa 2,111 ne su ka yi shahada, yayin da wasu 5,483 su ka jikkata.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza da ta fitar da wannan kididdigar ta kuma bayyana cewa; tun daga 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu jumillar Falasdinawan da su ka yi shahada, sun kai 51,495 wadanda kuma su ka jikkata sun kai 117,524.