Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-04-28@23:11:54 GMT

Hajjin 2025: Gwamna Namadi Ya Nada Sarkin Kazaure Amirul Hajj

Published: 29th, April 2025 GMT

Hajjin 2025: Gwamna Namadi Ya Nada Sarkin Kazaure Amirul Hajj

 

Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya amince da nadin Mai Martaba Sarkin Kazaure, Alhaji Dr Najib Hussaini Adamu, a matsayin Amirul Hajj na Jihar Jigawa, kuma shugaban tawagar Gwamnatin jihar domin gudanar da aikin Hajjin 2025.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai.

Gwamnan ya kuma amince da nadin mambobin tawagar Amirul Hajjin.

Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa, mambobin sun hada da Dr. Yusuf Abdurrahman, Babban Limamin Masarautar Hadejia da Alhaji Lawan Ya’u Roni, Talban Kazaure.

Sauran su ne Dr. Mahmoud Yunusa, Sa’in Dutse da kuma Alhaji Adamu Dauda Zakar, Durbin Hadejia.

Sanarwar ta bayyana cewa an yi wadannan nade-nade ne bisa la’akari da irin kwazon da suka nuna a ayyukansu, sadaukarwa, kishin kasa, amana da kuma tsoron Allah.

A cikin sakon taya murna ga wadanda aka nada, Sakataren Gwamnati ya bukace su da su ci gaba da nuna wadannan dabi’u yayin da za su gudanar da wannan muhimmin aiki da aka dora musu, don kara tabbatar da amanar da gwamnatin da al’ummar Jihar Jigawa suka dora a kansu.

Sanarwar ta kara da cewa, ana sa ran tawagar Amirul Hajjin za ta yi aiki kafada da kafada da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa da kuma sauran hukumomin da suka dace a matakin Jiha, Tarayya da na kasa da kasa domin tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara da inganci.

Sanarwar ta bayyana cewa nade-naden sun fara aiki nan take.

 

Usman Muhammad Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yan Gudun Hijiran Sudan Sun Yi Kira Ga Kungiyoyin Kasa Da Kasa Da Su Ceto Yara Da Tsofaffi Daga Mummunan Kangi A Sudan

‘Yan gudun hijira a Sudan sun yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su ceto yara da tsofaffi daga mummunan kangin da suka shiga

An gwabza kazamin fada a kusa da birnin El Fasher da ke arewacin Darfur tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces, wadanda suka yi ruwan bama-bamai kan birnin da na manyan bindigogi, inda suka kashe fararen hula akalla 35.

Sojojin Sudan sun samu nasarar dakile wadansu daga cikin wadannan hare-hare, amma duk da haka sun janyo hasarar rayukan bil’adama da na dukiya. Sannan  sojojin Sundan sun kuma kwace iko da birnin Bara da ke Arewacin Kordofan, kofar Nyala a Kudancin Darfur.

Dakarun kai daukin gaggawa sun yi wa birnin kawanya da nakiyoyi da ramuka da nufin yiwuwar harin farmakin sojojin Sudan.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jihar Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Aikin Hajjin 2025
  • Hajjin 2025: An Fara Yi Wa Maniyyata Allurar Rigakafi A Jigawa
  • Hajjin 2025: Jihar Kwara Ta Fara Allurar Rigakafi Ga Maniyyata
  • Sarkin Musulmi Ya Ayyana Ranar Talata 1 Ga Watan Zulki’ida
  • Falasdinu: Mahmud Abbas Ya Nada Magaji Da Kuma Mataimakasa
  • Hakimin Kafin Hausa Ya Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Ayyuka Cigaban Al’umma
  • Samarin Arewa sun yaba wa Sarkin Daura kan bai wa Ja’o’ji muƙami
  • Hukumar Alhazan Jihar Kaduna Ta Wajibta Gudanarda Binciken Lafiya Ga Maniyatan 2025
  • ‘Yan Gudun Hijiran Sudan Sun Yi Kira Ga Kungiyoyin Kasa Da Kasa Da Su Ceto Yara Da Tsofaffi Daga Mummunan Kangi A Sudan