Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ƙaddamar da shirin rigakafin mahajjata na shekarar 2025 a yankin Hadejia da ke shiyyar arewa maso gabas ta jihar.

Shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Hadejia.

Alhaji Ahmed Umar Labbo ya jaddada kudirin hukumar na ba da fifiko ga lafiya da kuma tsaron mahajjatan jihar.

Ya ce, kare lafiyar mahajjatan jihar  nauyi ne da ya rataya a wuyan  hukumar.

“Shirin rigakafin da muka fara yana nuna shirinmu na tabbatar da nasarar aikin Hajjin shekarar 2025. Ina ƙarfafa mahajjata su ba da haɗin kai tare da bin ƙa’idojin lafiya yayin wannan tafiya mai albarka.”

“Ina kuma ƙarfafa ku da ku zama masu bin doka da haƙuri yayin aikin Hajji. Da fatan za ku halarci dukkan tarukan bita da kai da aka shirya, domin muhimmanci su Alhazai” In ji shi.

Labbo, wanda ya sa ido a kan shirin rigakafin tare da bai wa wani mahajjaci daga Hadejia allurar farko, ya bayyana cewa aikin rigakafin zai ci gaba har zuwa lokacin tafiyar su zuwa ƙasa mai tsarki.

Haka kuma, Shugaban cibiyar lafiya a matakin farko, Dr. Bala Ismaila, ya bayyana muhimmancin allurar rigakafin da ake bayarwa, wanda ya haɗa da rigakafin cutar sankarau, cutar shan inna, da kuma cutar zazzabin cizon sauro (yellow fever).

Ya kuma yi bayani kan yiwuwar fuskantar rashin lafiya bayan rigakafin, inda ya shawarci mahajjata da su nemi kulawar likita cikin gaggawa idan suka fuskanci hakan ko wata matsala da ta wuce kima.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ana gudanar da aikin rigakafin a dukkan kananan hukumomi 27 na jihar.

 

Usman Muhammad Zaria 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

Amurka Ta Ce: Shugaban Rikon Kwarayar Siriya Al-Julani Ya Yi Alkawarin Cewa Ba Zai Cutar Da Tsaron Isra’ila Ba

A ganawarsa da wata jami’ar Amurka, al-Julani ya yi alkawarin ba zai cutar da tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila ba!

Barbara Leaf, tsohuwar mataimakiyar sakatariyar harkokin wajen Amurka mai kula da harkokin gabas ta tsakiya, ta tabbatar da cewa shugaban rikon kwarya a Siriya, Mohammed al-Julani (al-Shara’a), “ya bayyana fahimtar matsalolin tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila,” a cewarta.

Hakan ya zo ne a wata ganawa tsakanin Leaf da al-Julani a birnin Damascus, jim kadan kafin ta bar mukaminta. Leaf ta bayyana taron a matsayin “mai kyau kuma mai amfani.”

Har ila yau Leaf ta yaba da “hanzari da kuma dabarar da Shara’a ke bi wajen tunkarar al’amurran yankin,” tana mai cewa “yana neman kulla kyakkyawar alaka da bangarorin yankin.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jihar Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Aikin Hajjin 2025
  • Hajjin 2025: Jihar Kwara Ta Fara Allurar Rigakafi Ga Maniyyata
  • Hajjin 2025: Gwamna Namadi Ya Nada Sarkin Kazaure Amirul Hajj
  • Aikin Hajji: Za A Fara Jigilar Alhazan Jihar Kwara A Ranar 12 Ga Watan Mayu
  • Fira Ministan Indiya Ya Bayyana Cewa: Iran Tana Kokari A Fagen Inganta Zaman Lafiya A Yanki Da Duniya Baki Daya
  • Amurka Ta Ce: Shugaban Rikon Kwarayar Siriya Al-Julani Ya Yi Alkawarin Cewa Ba Zai Cutar Da Tsaron Isra’ila Ba
  • Hukumar Alhazan Jihar Kaduna Ta Wajibta Gudanarda Binciken Lafiya Ga Maniyatan 2025
  • Iran ta Bayyana cewa: TattaunawarMuscat Wata Dama Ce Ta Samun Zaman Lafiya Kan Batutuwan Masu Sarkakiya
  • Gidauniyar Dangote Ta Kai Tallafin Abinci Ga Wadanda Iftila’in Gobara Ya Ritsa Da Su A Jigawa