Shugaban  kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’imKasim ya bayyana cewa, kungiyarsa tare da Sojojin kasar da kuma mutanen kasar ne zasu tabbatar da ci gaban kasar Lebanon a wannan halin da ake ciki.

Tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta nakalto sheikh Na’im kasim yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a jiya Litinin, jawabinda kafafen yada labarai da damaa suka watsa kai tsaye.

Sheikh Qasim kasar Lebanon zata ci gaba da zama mai karfi idan gwamnatin kasar ta dakatar da hare-haren da HKI take  ci gaba da kawowa a kan kasar, da kwato dukkan yankunan kasar da aka mamaye, har’ila yau da kuma ci gaba da hadin kai tsakanin masu gwagwarmaya, sojoji da kuma mutanen kasar.

Shugaban kungiyar ya jadda bukatar sake gina wuraren da HKI ta rusa a yankunan daban daban a kasar, ya ce gwamnatin kasar ta yi alkawalin zata sake gina wuraren da HKI ta rusa a yakin da hizbullah a baya-bayan nan.

Kuma ya ce rashin yin haka nuna bambanci ne a tsakanin mutanen kasar. Ya ce dangane da wadanda aka rusa gidajensu kungiyar ta bada kudaden haya ga 50,755 , sannan ta gyura wasu 332 da aka lalata, wanda duk aikin gwamnati ne ta yi hakan. Don haka akwai bukatar gwamnati ta aikata wajibin da ya hau kanta.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Wajabcin Kawo Karshen Ayyukan Ta’addanci A Kasashen Yanki

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dole ne a kawar da ta’addanci ta hanyar hadin kan kasashen yanki

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin ta’addancin da aka kai a birnin Pahalgam na kasar Indiya, tare da nuna alhini da juyayinsa ga gwamnati da al’ummar kasar Indiya, yana mai jaddada bukatar hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin domin yakar ta’addanci da kuma tsayawa tsayin daka kan wannan barazana ta bai daya.

Pezeshkian ya zanta ta wayar tarho a yammacin jiya Asabar da fira ministan kasar Indiya Narendra Modi, inda suka tattauna kan sabbin al’amuran da suke faruwa a yankin na Indiya, da kuma alakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasar Indiya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mutanen da talauci ya yi wa katutu zai ƙaru a Nijeriya — Bankin Duniya
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauana Da Shugaban Hukumar IAEA
  • Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Wajabcin Kawo Karshen Ayyukan Ta’addanci A Kasashen Yanki
  •  Adadin Wadanda Su ka Kwanta Dama A Gobarar Tashar Jirgin Ruwan Shahid Raja’i Sun Kai 21
  • Daga Kaina An Gama Harkar Fim A Zuri’ata – Moda
  • Kasashen Duniya Sun Yi Ta AiIka Tallafi Bayan Fashewar Bandar Abbas
  • Hamas Ta Yi Allawadai Da Dage Rigar Kariya Na Ma’aikatar Hukumar UNRWA
  • Shugaban Kasar Azerbaijan Ya Tattauna Da Wakiliyar CMG
  • Wace Kungiya Ce Za Ta Lashe Kofin Zakarun Turai?