Shugaban Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya ya rasu
Published: 29th, April 2025 GMT
Allah Ya yi wa Shugaban Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Muslunci a Najeriya, Sheikh Abdul Rasheed Hadiyatullah, rasuwa.
Babban Mufti na ƙasar Yarbawa, Sheikh Daood Imran Molaasan, ne ya sanar da rasuwar Sheikh Abdul Rasheed Hadiyatullah a cikin wata sanarwa da ya sanya hannu a kai a daren Litinin.
Sai dai bai bayar da cikakken bayani game da inda Sheikh Hadiyatullah ya rasu ko kuma lokacin da hakan ya faru ba.
Sheikh Molaasan ya bayyana cewa rasuwar marigayi Sheikh Hadiyatullah ta bar giɓi mai wuyar cikewa a shugabancin Musulunci na ƙasar.
Bom ɗin Boko Haram ya kashe mutane 26 a Borno NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya“An haife shi a garin Iwo a Jihar Osun kuma an san shi da dabi’u Musulunci. Sheikh Hadiyatullah ya kasance fitaccen malamin Musulunci kuma masanin shari’a, wanda an san shi da ƙoƙarinsa na neman a aiwatar da Shari’a Musulunci a tsarin mulkin Najeriya, tattaunawa tsakanin addinai, da zaman lafiya a tsakanin al’ummomin Najeriya masu bambancin addini.
“Ya yi aiki a matsayin Shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci na tsawon shekaru, inda ya jagorance ta a lokutan ƙalubalen zamantakewa da ci gaba.
“Sheikh Hadiyatullah ya fara karatun addinin Musulunci a wurin malaman gida kafin ya ci gaba da karatunsa a ƙasashen waje.
“Ya samu girmamawa a faɗin Najeriya da ma wajenta saboda zurfin ilminsa a fannin fiƙihun Musulunci da kuma salon shugabancinsa mai nutsuwa da tsayin daka kan akida,” kamar yadda Molaasan ya bayyana.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya gafarta wa Sheikh Hadiyatullah ya kuma ba shi Aljannatul Firdaus.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Najeriya Shari ar Muslunci Sheikh Abdul Rasheed Hadiyatullah Sheikh Hadiyatullah Sheikh Hadiyatullah ya
এছাড়াও পড়ুন:
HOTUNA: Yadda aka dawo da ’yan Najeriya 203 daga Libya
Kalli yadda aka karɓi ’yan Najeriya guda 203 da aka dawo da su daga ƙasar Libya.
(Hoto: Onyekachukwu Obi).