Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok
Published: 29th, April 2025 GMT
Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun kashe masu zaman makoki bakwai tare da jikkata wasu a ƙauyen Kopl da ke Ƙaramar Hukumar Chibok ta Jihar Borno.
Shugaban Karamar Hukumar, Honorabul Modu Mustapha, ya ce mayaƙan sun buɗe wa mutanen wuta ne a yammacin ranar Litinin, a yayin da suke shirin gudanar da addu’o’i ga ’yan uwansu da suka rasu.
Ya ce, “Sun taru ne domin yin addu’a lokacin da ’yan ta’addan suka sauka a kansu. Mun kwashe mutane da yawa da suka samu raunukan harsashi zuwa Babban Asibitin Mubi da ke maƙwabtaka da Jihar Adamawa.
“Adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa, saboda wasu sun tsere cikin daji da raunukan harsashi. Ana ci gaba da aikin nemowa da ceto waɗanda ke cikin daji,” in ji shi.
Bom ɗin Boko Haram ya kashe mutane 26 a Borno NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya Shugaban Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya ya rasuSanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya ci gaba da yin Allah wadai da hare-haren, inda ya bayyana halin da ake ciki a matsayin abin da ya wuce tunanin dan Adam.
“Ko jiya ma, na samu kiran gaggawa cewa an kashe sama da ’yan banga 10 a wani yankin da ke tsakanin Karamar Hukumar Hawul ta Jihar Borno da garin Garkida a Jihar Adamawa.
“Al’ummata na fama da munanan asara ba tare da wani faɗa ba. A cikin wata guda da ya gabata kaɗai, an kashe sama da mutum dari a hare-hare da dama yankunan Sabon Gari da Izge da Kirawa da Pulka da Damboada Chibok da Askira Uba da wasu da yawa da ba zan iya lissafawa ba,” in ji Sanata Ndume.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram
এছাড়াও পড়ুন:
Ƴan Fashi Sun Sace Fasinjoji 7, Ƴansanda Sun Ceto 2 A Kwara
Ƴan fashi sun sace fasinjoji guda bakwai a cikin motocin haya biyu a ƙauyen Eleyin da ke cikin ƙaramar hukumar Isin a Jihar Kwara.
A cewar rahoton LEADERSHIP, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:45 na yamma a ranar Juma’ar da ta gabata, lokacin da wasu ƴan fashi su biyar suka toshe hanya, suka tsayar da motoci biyu, sannan suka tilasta ɗaukar dukkanin fasinjojin zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Uwargidan Shugaban Kasar Sin Ta Tattauna Da Takwararta Ta Kasar Kenya Ra’ayin Matasa Kan Kungiyar ‘Yan Ta’adda Mai Suna Lakurawa Da Ta Fito A KebbiWasu majiyoyi sun bayyana cewa, daga cikin fasinjojin motar ɗaya, akwai shugaban sashin shari’a na ƙaramar hukumar Oke Ero, Barr. Elizabeth Arinde, da daraktan gudanar da ma’aikata na wannan ƙaramar hukumar, Alh. Musbau Amuda.
Kakakin Ƴansanda na Jihar Kwara, Toun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa an sami ceto fasinjoji biyu, Ganiyu Ajayi da Kolawole Adeyemi. Ta kuma ƙara da cewa, har yanzu ana ƙoƙarin ceto sauran fasinjojin guda biyar da kuma kama ƴan fashin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp