Sabbin Bayanai Kan Fashe-Fashe Wasu Abubuwa A Tashar Jiragen Ruwan Kasar Iran
Published: 29th, April 2025 GMT
Gwamnan lardin Hormozgan (mai hedikwata a Bandar Abbas), Mohammad Ashouri, ya ce wani bangare na lamarin tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’i ya faru ne sakamakon keta sanarwar adana kayayyaki ne, wani bangaren kuma na da alaka da sakaci da rashin kulawa (a wajen ajiya).
AShouri, wanda ya bayyana ta hanyar faifan bidiyo a wata hira da aka watsa ta talabijin a yammacin jiya Litinin, ya bayyana sabbin alkaluman wadanda suka bata: Akwai mutanekusan 22 da suka bace, kamar yadda wasu gawarwakin mutane 22 ba a iya tantace su ba ko su waye ba.
Ya ce: “Wasu daga cikin wadanda suka jikkata an hanzarta jigilar su ta jirgin saman soja zuwa asibitin birnin Shiraz.”
Gwamnan lardin Hormozgan na Iran ya ce: An cimma wasu bincike na farko dangane da yiyuwar yin sakaci a wannan fanni, kuma ana gudanar da bincike sosai kan dukkan al’amuran da suka faru. Kuma babu wata daga kafa da za a yi ga duk wanda aka samu da yin sakaci a kan haka za a tuhume shi kamar yadda shari’a ta tanada.
Ya ci gaba da cewa, “Ta hanyar nazarin faifan bidiyo daban-daban na aukuwar lamarin tashar jirgin ruwa ta Shahid Raja’i, an lura da cewa, an yi jigilar kaya a lokacin da lamarin ya faru, inda hayaki ke tashi, sai kuma fashewar wani abu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jiragen Yakin Amurka Sun Kashe Mutane Da Dama A lardin Sa’ada Na Kasar Yemen
Mutane da dama daga nahiyar Afirka ne suke cikin mutane kimani 50 wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan wani gidan kaso a lardin Sa’ada na kasar Yemen.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Al-Masirah yana cewa makaman Amurka sun fada kan wani gidan yarin da aka kebewa yan Afrika, kuma yawansu ya kai 115, amma har yanzun ba’a san yawan wadanda suka rasa rayukansu a gidan yari.
Labarin ya kara da cewa har yanzun ma’aikatan agaji suna aikin ceto a wurin, sannan hotunan da suka fara bayyana sun nuna gawaki da dama. Amma Al-Masirah ta bayyana cewa akalla mutane 68 sun rasa rayukansu.