Katafaren Jirgin Daukar Jiragen Yaki Na Kasar Amurka Harry Truman Zai Fice Daga Tekun Maliya
Published: 30th, April 2025 GMT
Rahotannin da suke fitowa daga kasar Yemen na cewa katafaren jirgin ruwa mai daukar jiragen saman yaki malakar klasarAmurka wato USS Harry Truman zai fice daga tekun red sea da nan kusa saboda makaman kasar Yemen da suka fada mata.
Tashar talabijin ta Almasirah ta kasar Yemen ta nakalto wani jami’in ma’aikatar tsaron kasar wanda baya son a bayyana sunansa yana cewa, saboda yawan hare haren da sojojin Yemen suka kaiwa jirgin, wadanda suka hada da amfani da makamai masu linzami samfurin Crusse da kuma Balistic, har ila yau da jiragen yaki masu kunan bakin waken da suka fada a kansa.
Tun cikin watan Maris da ya gabata ne gwamnatin shugaba Trump ta fara kaiwa kasar yemen hare-hare da jiragen sama wadanda suke tashi daga sansanin jiragen yaki da ke kan wannan jirgin. Saboda tilastawa kasar Yemen dakatar da kai hare-hare a kan HKI, don ta kawo karshen tallafawa Falasdinawa a Gaza.
Amma ya zuwa yanzu hare-haren na Amurka sun kasa kaiwa ga bukata, majiyar gwamnatin kasar ta yemen ta ce hare-haren Amurka a kasar ba zasu sa ta dakatar da tallafawa Falasdinawa, da kuma hanata kai hare hare kan jiragen kasuwanci na HKI masu wucewa ta tekun red sea ba.
A wani labarin kuma hare haren na sojojin yemen sun sa wani jiegin yakin Amurka samfurin F-18 ya fada cikin ruwa a tekun na Red Sea a kokarin kaucewa makaman sojojin Yemen.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Yemen
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Yana Maraba Da Masu Zuba Hannun Jari A Kasarsa Daga Kasashen Waje
Shugaban kasar Iran ya nuna murnarsa da yin maraba lalai da masu zuba hannun jari daga kasashen waje a Iran
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana Iran a matsayin dandalin da ta dace wajen zuba hannun jari da gudanar da harkar kasuwanci, yana maraba da masu zuba hannun jari na kasashen waje da ‘yan kasuwa na duniya da su shiga harkokin tattalin arziki da zuba hannun jari a Iran.
A yayin bikin bude baje koli karo na bakwai na baje kolin kayayyakin da Iran ke fitarwa zuwa kasashen ketare (Iran Expo 2025) a safiyar yau Litinin, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi maraba da baki na kasashen waje da suka halarci wannan baje kolin, yana mai cewa, “Ko da yake ana gabatar musu da wani hoto na daban da ya yi hannun riga da hakikanin Iran da al’ummar kasarta a ketare, amma Iran kasa ce mai karbar baki, kuma al’ummarta masu tausayi da nuna jin kai.”
Yana mai jaddada cewa: Iran wata kafa ce da ta dace da zuba hannun jarin kasuwanci da yawon bude ido na ketare, Pezeshkian ya bayyana cewa da wannan karfin, kuma ta hanyar ciniki, zuba hannun jari, da hadin gwiwa, za a iya samar da makoma mai haske ga duniya, mai cike da tsaro da zaman lafiya.
Ya kuma yi nuni da cewa: Yake-yaken da suka gani a duniya sun samo asali ne sakamakon rashin mutunta hakkokin bil’adama da na kasashe, Pezeshkian ya jaddada mutunta yankin kasar Iran da hakkokin kasashe, yana mai bayyana Shirin Iran na gudanar da duk wani hadin gwiwa a fannin kimiyya, tattalin arziki, siyasa, da zamantakewa da duniya, da kuma mika ilimi ga sauran kasashe ba tare da iyakancewa ba.