Bayan tsawon shekaru 40 a tsare, shugaban fursunonin Falasdinawa, Mohammed Al-Tous, ya samu ‘yancinsa

Kungiyar kula fursunonin Falasdinawa da suke tsare a gidan yarin haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta saki Muhammad al-Tous, wanda shi ne fursuna mafi tsufa a hannunta, tare da tasa keyar shi tare da wasu fursunoni 69 zuwa kasar Masar, a wani bangare na yarjejeniyar musayar fursunoni tsakaninta da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas.

A ranar Asabar din da ta gabata ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta saki fursunonin Falasdinawa 200 a madadin wasu mata sojoji hudu da kungiyar Hamas ke tsare da su a Zirin Gaza.

Al-Tous (mai shekaru 69) yana tsare tun 1985 kuma yana cikin kungiyar Fatah an yanke masa hukuncin daurin rai da rai kuma ya shafe shekaru 40 a jere a gidajen yarin haramtacciyar kasar Isra’ila.

An kama Al-Tous ne bayan an fafare shi a lokacin da yake cikin wata mota ta kungiyar Fatah da ta kai hare-hare da dama kan wasu wurare da dama a haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin Beit Laham.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Siriya : Ofishin jakadancin Amurka ya yi gargadi game da yiyuwar hare-hare a yayin bikin sallah

Ofishin jakadancin Amurka da ke Damascus ya fitar da wata sanarwar gaggawa, inda ya yi kira ga daukacin Amurkawa da su gaggauta ficewa daga kasar Syria, sakamakon karuwar hare-haren da ake kai wa a lokacin bukukuwan sallar Idi, wanda ke kawo karshen azumin watan Ramadan mai alfarma.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta daukaka tafiye-tafiye zuwa Syria zuwa mataki na 4 mafi girman inda aka gargadi, Amurkawa da kada su je kasar Siriya bisa kowane dalili.

Ofishin jakadancin ya gargadi ‘yan kasar game da yiwuwar kai hari kan “ofisoshin jakadanci, kungiyoyin kasa da kasa da cibiyoyin jama’a na Syria” a Damascus.

Halin tsaro a Syria ya tabarbare bayan da kungiyoyin ‘yan ta’adda, karkashin jagorancin Hay’at Tahrir al-Sham, suka hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad a ranar 8 ga Disamba, 2024.

Tun bayan rugujewar gwamnatin Assad, sojojin Isra’ila ke kai hare-hare ta sama a kan cibiyoyin soji, da kuma rumbun adana kayan yaki na sojojin Siriya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dan shekara 4 ya kira wa mahaifiyarsa ’yan sanda
  • Iran: Amurka ta hada kai da Isra’ila wajen kawo cikas ga harkar tsaro a gabas ta tsakiya
  • Somalia: Harin Amurka a kan kungiyar IS ya kashe wasu mambobin kungiyar
  • Gwamnatin Kasar Guinea Ta Yi Wa Musa Dadis  Camara Afuwa
  • Hamas A Gaza Ta Amince Da Kafa Gwamnatin Hadin Kan Falasdinawa, Amma Makamanta Jan Layi Ne
  • Siriya : Ofishin jakadancin Amurka ya yi gargadi game da yiyuwar hare-hare a yayin bikin sallah
  • Kungiyar “White Helmets Ta” A Kasar Siriya Ta Rasha Tallafin Da Take Samu Daga USAID
  • Gwamnatin Kaduna za ta ɗauki ma’aikatan lafiya 1,800 aiki
  • Gwamnatin Kaduna Ta Jadadda Kudurin Ta Wajen Samarda Tsaftatacen Ruwan Sha Ga Al’umma 
  • Ɓarayin kekunan ɗinki sun shiga hannu a Borno