Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ya Bayyana Cewa: Atisayen Sojojin Iran Ya Fayyace Karfinsu
Published: 26th, January 2025 GMT
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta kasar Iran ya bayyana cewa: Atisayen sojin mai take “‘Manzon Allah Mai Girma na 19” ya bayyana ƙarfin sojojin Iran
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran, Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19” a cikin ruwan Tekun Fasha ya bayyana Alamar da ƙarfin sojojin Iran suke da shi.
Mohammad Baqir Qalibaf ya bayyana haka ne a yayin zaman majalisar shawarar Musulunci a yau Lahadi: Atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19″ na sojojin ruwa da ke karkashin dakarun kare juyin juya halin Musulunci suka yi a cikin ruwan tekun Fasha, da kuma makaman tsaro da aka mika wa sojojin kasa na sojojin Iran, wanda a lokacin aka yaye shamakin wasu sabbin gagaruman nasarori na tsaro da aka samu a Iran, da suke bayyana wasu sabbin nasarorin da Iran ta samu a fagen kere-kere, a bangare na karfin sojojin Iran.
Qalibaf ya jaddada cewa: Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta sanar da bin diddigin matsayar Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan manufofin harkokin wajen kasar bisa tsarin manufofin da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya tsara, kuma nauyi na karshe yana kan ministan harkokin wajen kasar, kuma dole ne ya kasance mai bin diddigin ayyukan da ya yi a gaban Majalisar Shawarar Musulunci da kuma al’ummar kasa, karkashin tsarin dabarun aiki da ya ba da tabbacin aiwatar da tattalin arziki da yin watsi da ayyukan da suke hatsari na zahiri.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Mai Ba Da Shawara Ga Jagora Ya Bayyana Cikakken Ikon Tawagar Masu Tattaunawan Iran A Zaman Shawarwari Da Amurka
Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Masu sasantawa Iran a birnin Roma suna da cikakken ikon gabatar da shawara kan matsayin kasarsu
Ali Shamkhani mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi nuni da cewa: Masu gudanar da shawarwari na Iran sun tafi birnin Roma ne domin yin shawarwari karo na biyu da Amurka kan batun makamashin nukiliyar kasar Iran. Ya ce masu yin shawarwari na Iran suna da cikakken ikon gabatar da shawara kan matsayin kasarsu.
Shamkhani ya yi nuni da cewa: Masu shiga tsakani na Iran suna neman cimma cikakkiyar yarjejeniya bisa ka’idoji guda tara: tsanani, samar da lamuni, dage takunkumi, yin watsi da tsarin Libya/UAE, kaucewa barazana, gaggauta yin shawarwari, dakile masu shirga karya kan Shirin makaman nukiliyar Iran -irin haramtacciyar kasar Isra’ila- da saukaka zuba jari. Iran ta zo ne domin cimma daidaiton yarjejeniya, ba ta mika wuya ga bakaken manufofin Amurka ba.