Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Atisayen soji na “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara

Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Admiral Ali Reza Tangsiri ya sanar da cewa: Atisayen soji mai take “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara da burin da ake son kai wa bayan samun nasarar gwada sabbin na’urori da gudanar da ayyuka daban-daban, tare da samun nasarar gwajin kai hari kan wuraren abokan gaba.

A wata hira da ya yi da manema labarai a yau Lahadi, Admiral Tangsiri ya bayyana cewa: A rana ta biyu ta atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19” da aka gudanar na gwada karfin soji, wanda ke dauke da sunan shahidi Manjezi, makamai masu linzami daga kasa zuwa teku da kuma daga kasa zuwa masu cin dogon zango, matsakaici da gajere.

Ya kara da cewa: A cikin wannan atisaye a karon farko an harba makami mai linzami na Nawab da ke goyon bayan shamakin jirgin sama da jirgin ruwan shahidi Qassim Suleimani kuma sun samun nasarar cimma wurin da aka harba su.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Alhassan (a) 112

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissiso da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin dastane rastan, ko kum littafin mathnawi na maulana Jalaluddeen rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///… Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-hassan limami na biyu daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s), kuma da na farko ga Fatimah diyar manzon All..(s), sannan jikansa na farko.

A cikin shirimmu da ya gabata mun kawo maku yadda Abuzar a Alghifari babban sahabin manzon All..(s) wanda ya kasance daga cikin mutane na farko da suka musulunta a Makka, sannan ya kuma garinsu giffar yana kiran mutane zuwa ga addinin musulunci har zuwa lokacinda manzon All..(s) yayi hijira, zuwa Madina sai shi ma yayi hijira. Banda haka, manzon All..(s) ya yabeshi a cikin hadisai da dama saboda tsoron All..ta zuhudu da kuma sanin addini.

Amma a lokacinda Uthman bin Affan ya  zama khalifa ya kuma dora danginsa Banu Umayya a kan al-ummar musulmi suna azabtar da shi suna kuma kwasar kudaden jama’a suna kashewa kansu, ya fuskanci matsaloli da sahabban manzon All..(s) da dama daga ciki har da Abuzar Alghiffari, wanda ya ci gaba da sukar khalifa da kuma danginsa, har sai da ya kore shi daga madina zuwa Sham da farko, sannan ya sake dawo da shi Madina a cikin mummunan hali, amma Abuzar bai dandara ba, ya ci gaba da sukansu har sai da wata rana, Khalifa yayi tambaya a kan al-amuran addini sai wani bayahude wanda bai dade da musulunct ba, ya bada amsa kuma ba dai dai ba, sai Abuzar ya tashi a kasansa, sai Khalifa kuma ya tashi a kan Abuzar yana masa tsawa, daga karshe ya sake korarsa daga Madina karo na biyu, amma a wannan karon ya kore shi zuwa wani daji inda babu mutane, kuma yace zai zauna a wurin har sai ya mutunu.

Munji yadda ya umurci Marwan dan hakam, ya bashi guzuri ya koma can inda ba zai ga wani ba, kuma ba wanda zai ganshi. Sai Marwan ya ajiye shi a wani wuri kafin ya kammala hada masa guzuri, sannan khalifa ya fadawa Marwan ya fitar da shi cikin kaskanci daga Madina sannan kada ya bar wani ya yi magana da shi ko y ace za iyi bankwana da shi.

Sai mutanen madina da dama, a lokacinda suka ji abinda ya faru da Abuzar sun sabawa Khalifa Uthman sun zo suna bankwana da Abuzar suna kuma Magana da shi suna bashi hakuri, suna masa naisiha kan ya yi hakari da abinda ya sameshi.

Daga cikin wadanda suka sabawa Khalifan Uthman, akwai Amirul Muminina Aliyu dan Abu talib (a). Ya fito tare da yayansa Alhassan da Alhussan (a) da Akilu dan Abitalib, da Abdullahi dan Jaafar, sun nufi Abuzar a inda suka ajiye shi.

A lokacinda Marwan dan ya ga haka, sai ya yi yaje wajen Imam Hassan (a) yana cewa: Ya kai Alhassan baka san cewa khalifa yah ana a yi Magana da wannan mutum ba? Idan baka sani ba to ka sani!.

Sai Imam Ali (a) ya shi da dokinsa ya kuma bugi kunnen dokinsa da bulala da ke hannunsa, ya na cewa: Kauce ! All..ya kaudakai zuwa wuta, sai Marwan ya ji tsoro, sannan ya yi sauri ya je ya fadawa Uthman abinda ya faru.

Sai Imam Ali (a) ya sauka ya zo kusa da Abuzar ya kuma ya masa bankwana, ya kuma yi masa Jababi wanda ya zabe masa salwa, (tsuntsun da All..ya saukarwa banu Isra’ila a lokacinda suke dimwa a yankin Sina). Kalmomi wadanda suka kasance hakan a tsawon zamansa a Rabazah.

Ya na cewa: 

Ya Abazar lalle kai ka yi fushi don All.., ka yi kaunar samun lada daga wanda kayi fushi dauminsa, Lalle mutanen nan sun ji tsoranka, saboda duniyarsu, kai kuma ka ji tsoronsu saboda addininka, ka barsu da abinda suka ji tsoronka sabo da shi, ka gudu da abinda ka ji tsoronsu saboda shi, ai su suka fi bukatar abinda ka hanasu, sannan ka wadatu daga abinda suka hanaka, da sannu zaka sani waye mai riba a gobe kiyama. Kuma wanda yafi yawan hasada.

Da ace sammai da kassai sun fada a kan a kan bawa, sannan ya ji tsoron All…da lalle sai All..ya yi masa mafita daga garesu! Lalle kada wani abu ya shagaltaka sai gaskiya. Kuma kada kayi kewan bata, da ka karbi duniyarsu da sai sun so ka, da kayi aron wani abu daga cikinta da sun amintar da kai. (khuduba 129 cikin Nahjul Balagha).  

Tare da wadannan kalmomi masu muhimmanci Imam Ali(a), ya dauki iyakance matsayin Abuzar da halin da ya fada ciki, da kuma abinda ya sa sarakunan Banu umayya suka ki shi. Yau tashi a kansu ne don ya tsira da addininsa, su kuma sun tashi a kansa ne don suna jin zai bata masu duniyarsu. Don tashi a kansu ne don ya farkar da mutane hatsarin wadannan shuwagabannin ga akidun musulunci musamman kan abinda zai zo nan gaba.

Daga nan sai Imam Alhassan (a) ya yi sauri yak ama hannun Abuzar ya yi musafaha da shi, ya kuma yi masa bankwana, ya kuma yi masa Magana wadanda zasu kwantar da hankalinsa. Yana cewa:

Ya ammina ! Ba don yakamata ga wanda akewa bankwana ya yi shiru, sannan wanda yake bankwana ya juya ya dawo ba, da zance yayi kadan, ko da kuwa bakinciki mai tsawo ne. Wadanan mutane, sun dora maka, abinda muke gani, ka yi bankwana da duniya tare da tunanin rabuwa da ita watarana, Ka kuma manta da tsananin da ya tsananta a cikinta da fatan abinda ke bayanta., ka yi hakuri har sai ka hadu da annabinka (s) ya na mai yarda da kai.

Don haka Imam Hassan (a) ya yi masa wasiyya da hakuri kan abinda ya sameshi har zuwa haduwarsa da ubangiji, da kuma manzon All..(a).

Sai Abuzar alghiffari yad aga kansa ya kalli iyalan gidan manzon All..(s) yana mai matukar bakin cika da rabuwa da su, sannan ya bude bakinsa yana cewa:

All,,yayi maku rahama , ya ku iyalan gidan rahama, kuna tunatar da ni manzon All..(s) a duk lokacinda na kalleku, bani da wani masu zama a Madina wadanda ne shaukinsu banda ku. Lalle na yi nauyi ga Uthman a Hijazi kamar yadda na yi nauyi da Mu’awiya a Sham, banda haka Uthman ya ki in kasance tare da dan’uwansa da kuma dan yar uwansa, a birane guda biyu (kufa da Basra) don kada in bata masu al-amarinsu a cikin mutanen wadan nan birane.

Don haka ne suka koreni zuwa wurinda bani da mataimaki, da kuma mai kare ni sai All… Na rantse da All..bana bukatar wanda zai kasance tare da ni sai All.., sannan bana jin kewar wani abu matukar ina tare da All….).

Daga nan sai aka kori Abuzar daga madinan manzon All..(s), aka nisantar da shi daga iyalan gidan manzon All…, aka nisantar da Abuzar daga Madina duk tare da cewa manzon All..(s) ya fadi matsayinsa a cikin sahabbansa, daga cikin yace wanda yake son ganin annabi Isa a cikin zuhudunsa da Rashin yawan maganarsa da kuma shiriyasa. Manzon All..(s) ya yabe shi da fadin gaskiyarsa.

Uthman ya koreshi daga madina manzon All….(s) don yaje ya mutu a can, shi kadai. Shi kuma shi kuma da danginsa su ci gaba da cin duniyar al-umma. Suna yin abinda suka ga dama.

Imam Aliyu (a) da yayansa suna komawa gida sai ga wata Jama’a tazo daga wajen Khalifa sun fada masa cewa, khalifa Uthman yayi fushi da shi, kuma yana kiransa kan ya sabawa umurninsa na hana mutane yin bankwana da Abuzar Alghiffari makiyinsa.

Sai Imam(a) yace masu : Fushin dawaki ga linzami kenan.  Yana nufin don dawaki na fushi da lanzami sai a bar Sanya masu linzami ne?

Sai Imam (a) ya je wajen Khalifa ya shiga wajensa., sai Khalifa yayi sauri ya fara fada masa, kan cewa: Me yasa ka maida dan aike na?

Sai Imam Yace: Amma Marwan ya zo mani yana son ya maidani sai na maida shi daga hanani zuwa wajen Abuzar, amma umurninka bai saba masa ba.

Sai Uthman ya ce: Shin umurnina bai kai gareka ba, kan cewa na hana mutane su yi bankwana da Abuzar ba?

Sai Imam (a) yace: shin duk wani umurnin da ka bayar, sannan ana ganin sabon All..a ciki, a yi biyya ga umurninka?

Sai Uthman yace: Ka daki Marwan, sai Imam Yace: Ban dake shi ba, sai dai na daki kunnen abin hawansa ne, sannan ga abin hawa na, idan ya na son ya rama kamar yadda na daki tasa ya yi hakan. Amma dangane da ni, na rantse da All.. idan ka zageni, sai na zageka da zagi irinsa. Ba zan yi kariya cikinsa ba kuma ba zan fada bas ai gaskiya.

Sai Uthman yace: Me yasa Marwan ba zai zageka bai dan ka zage shi? Kuma na rantse da All.. a wajene ba abinda ka fishi da shi.

Sai Imam (a) yayi Fushi, da uthman saboda ya daidai da Marwan, (alhali ya sani)  manzon All..(s) ya fada dangane da shi, :Matsayinka da ni kamar matsayin Haruna da Musa ne, a yayinda yake fada dangane da Marwan  Hakam: Tsaka dan tsaka, kuma wanda manzon All..(s) ya la’aneshi tun yana cikin tsotson mahaifinsa; Sai Imam (a) yace: Ni kake fadawa wannan zancen? Kana daidaita ne da Marwan? Na rantse da All..ya fika, kuma babana ya fika, babanka, kuma mahaifiyata ta fi mahaifiyarka, kuma ga wannan kori ne ya zare su.

Sau Uthman yayi shiri, sanna Imam (a) ya juya ya tafi ya na fushi da Uthman, saboda dai-datashi da Marwan Dan hakam, bai bashi matsayin da All..da manzonsa (s) suka bashi ba. Bai bashi hatta matsayin da sahabanna manzon All..(s) suke bashi ba. Kuma idan ba don Aliyu (a) baya khainci ba, da yah ana Uthman zama Khalifa a lokacinda Abdurraman dan Auf ya bijiro basa Khalifanci tare da shardanta masa da bin Abubakar da Umar.  Amma yaki amincewa, a sannan ne ya bijirowa Uthman ya yarda da dukkan sharuddan da suke cikinta, ya kuma saba masu gaba daya. Bai bi littafin All..ba bai bi sunnan manzon All..ba, bai kuma bi hatta sunnar Abubakar da Umar ba.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Manufar Kasarsa Da Shirin Kare Muradunta A Duk Wata Yarjejeniya
  • Iran Ba Ta Da Niyyar Tattaunawa Da Amurka A Fili Bainar Jama’a Kan Shirinta Na Makamashin Nukiliya
  • Burnley Da Leeds United Sun Dawo Gasar Firimiya Lig 
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Alhassan (a) 112
  • Kakakin Ma’aikatar Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Babban Abin Da Suke Bukata Shi Ne Daga Takunkumi
  • Gharibabadi : inganta sinadarin uranium jan layi ne a tattaunawar Iran da Amurka
  • Zaɓen 2027: Babu ɗan takarar da zai yi nasara ba tare da goyon bayan Arewa ba — Hakeem
  • Faransa : An kama wata ‘yar Iran mai goyon bayan Falasdinu
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yaba Da Zaman Tattaunawan Iran Da Amurka Zagaye Na Biyu A Birnin Roma
  • Mai Ba Da Shawara Ga Jagora Ya Bayyana Cikakken Ikon Tawagar Masu Tattaunawan Iran A Zaman Shawarwari Da Amurka