Kissoshin Rayuwa Imam Hassan (a) 07
Published: 26th, January 2025 GMT
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da war haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na Aya. Shahida Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin rumi.
///..Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a shikin shirimmu da ya gabata, mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Hassan (a) jikan manzon All..(s) kuma limami na biyu daga cikin limamai masu tsarki daga cikin iyalan gidan manzon All..(s), sannan dan Fatimah(a) diyar manzon All..(s) na farko.
A cikin shirimmu da ya gabata mun kawo maku ayoyin akur’ani wadanda suka yi magana dangane da Imam Hassan (s) da kuma iyalan gidan manzon All..(s).
Mun kawo hadisan manzon all..(s) wadanda suka yi magana kan Imam Hassan(a) shi kadai, sannan da wadanda suka yi magana dangane da shi da dan uwansa Imam AlHussain (a).
A cikin hadisan dai, munji yadda ya kasance daga cikin wadanda manzon All..Ya fi so daga cikin iyalan gidansa (s). Mun kuma ji yadda, shi da dan’uwansa Imam Hussain (a) suka kasance karkashin kula na mala’ikun All..a ko ina suke, wato dare da rana wasu mala’ikun All..suna kula da da su. .
Sannan manzon All..(s) ya fadawa al-ummarsa yadda ya ke sonsa da kuma dan’uwansa Imam Alhussain, har’ila yau da yadda All…ya sanyasu cikin shuwagabanni a cikin al-ummar kakansu, manzon All..(s).
-Hadisi na gaba, an karbi shi daga Jabir Dan Abdullahil Ansari (r ) ya na cewa; na shiga wajen manzon All..(s), sai na sami Alhassan da Alhussain (a) suna kan bayansa suna wasa, sai kuma ya na cewa : Madallah da ramuminku, kuma madallah da ku adilai.
-Awani hadisi mai kama da wannan, Umar yace, na ga Alhassan da Alhussain (a) suna kan kafadar manzon All…(s), sai nace: madallah da doki wanda yake karkashinku, sai manzon All..(s) ya ce: Madallah da mahaya su biyu.
An karbo hadisi daga Yaalaa dan murrah, Athaqafi, ya ce: Alhassan da Alhussain (s) sun zo suna sauri, wajen manzon All..(s) sai ya kamasu ya rungumesu….har zuwa karshen hadisin,
-A wani hadisin manzon All..(s) yace: Alhassan da Alhussain jikoki biyu daga jikoki. -A wani hadisin an nuna cewa manzon All..(s) ya na tausaya Alhassan da Alhussain (a) ya na kuma roka masu All.. kan sharrin mahada.
-Har’ila yau, yana daga cikin hadisan da suka shahara a cikin musulmi kan cewa manzon All..(s) ya fada, dangane da Alhassan da Alhussian (a) kan cewa : Alhassan da Alhusain shuwagabanni ne, Idan sun tashi sun yunkura, ko sun zauna.
Wadannan shima, kamar yadda ya zo cikin wannan hadisin, zamu fahinci cewa, babu wanda All..zai sanya shi shugaba, sai ya tsarkakashi daga aikata laifi. Ko kuma sai ya bashi isma.
Mai littafin al-isaba fi Ma’arifatus Sahaba,ya karbo daga Abu na’im, daya daga cikin manya-manyan sahabban manzon All..(s), shi kuma ya rawaito daga Amirulmuminina (s) ya na fadar wannan hadisin.
-A wani hadisin manzon All..(s) yakan yi addu’a ya na neman tsari daga All..wa yayansa Imam Alhassan da Alhussain (s) daga hasadan masu hasada,. Kamar yaddda annabi Ibrahim (a) yake nemen tsar iwa “ya”yansa, Isma’ila da Ishaka.(a)
Sannan mun san yadda Annabi Ibrahim (s) ya zama annabi manzo, sannan All..ya bashi limamanci bayan manzaci, sai ya roki All..T ya bashi limamai, a cikin zuriyyarsa, sai All..ya karbi addu’arsa. Amma ya ce azzalumai daga cikinsu ba zasu same shi ba.
All..T ya na cewa
{Kuma a lokacinda Ubangiji ya jarrabi Ibrahima da kalmomi, sannan ya cikata, Sai ya ce: Zan sanyaka limami, sai yace daga zurriyata, sai Yace: wani azzalumai ba zai sameshi ba}.
A wannan hadisan da muka karanta, manzon All..(s) ya na magana, kan cewa ‘ya’yansa biyu, Alhassan da Alhussain (s) Limamai ne, irin limancin annabi Ibrahim (s), ko sun yunkura sun tashi kan azzaluman shuwagabanni ko kuma wata masalaha ta sa su zama.
Anan ya na tabbatarwa Al-ummarsa kan cewa wadannan yayan na sa, sun cancanci limancin irin na Ibrahim (a), wannan ya tabbatar da cewa su ma’asumai ne, tunda All..Yace: Ba wanda zai sami limamanci sai wanda ya kasanve masumi, wato ba azzalumi ba.
Sai kuma kashi na ukku, inda hadisan sun tabbatar da matsayin dukkan iyalan gidan manzon All..(s). Wato Aliyu da Fatima da kuma Alhassan da Alhussain (s).
Hadisan masu inganci ne,kuma wadanda yawansu ya kai haddin Tawaturi, daga manzon All..(s) dangane da wajibcin son iyalan gidansa, wadanda muka ambato, da farko akwai sonsu, irin son da suke masa. Ya ce soyeyyersu gareshi(s) ba zai cika ba sai tare da son wadannan iyalan gidan na sa.(a)
A cikin wasu hadisan yana cewa, yakar su yakarsa ne, kuma mai zaman lafiya ne ga wanda ya zauna lafiya da su. A wasu hadisan ya gwamasu da Alkur’ani mai girma. ya sanya su a matsayin jirgin tsira, su aminci ne ga al-ummarsa, da sauransu, kamar yadda zamu gani a cikin hadisan da zamu kawo.
Zaidu dan Arkam ya ruwaito daga manzon All..(s) yana fadawa Aliyu(a) da Fatimah da Alhassan da Alhusain (s), ya na cewa: Ni mai yakar wanda ya yakesu ne, kuma mai zaman lafiya ne ga wanda ya zauna lafiya da su. Daga Abubakar Yace na ga manzon All..(s) ya kafa Khaima, sannan ya dogara da bakan irin ta larabawa, sannan Aliyu, da Fatimah da kuma Alhassan da Alhussaini (a) su na cikin haimar, sai ya ce: Ya ku musulmi, ni mai aminci ne ga wanda ya amintar da ma’uta wannan Khaimar, kuma mai yaki ne ga wanda ya yake su kuma mai jibantan al-amarin wanda ya jibanci al-amarinsu ne, ba mai son su sai wanda yake da kaka mai rabu, (ba dan zina ba), ba kuma mai kinsu sai sai shakiyyin kaka, kuma mai mummunan haihuwa. Ahmad dan Hambal ya ruwaito Hadisi, kan cewa manzon All..(s) Ya rike hannun Alhassan da Alhusain (a) sai ya ce: Wanda ya ke sona, to ya so wadannan biyu, da babansu, da mahaifiyarsu. Wanda ya yi haka zai kasance tare da ni a darajata a Aljanna. Sannan jabir dan Abdullahin Alnsaran, ya ce wata rana a Arafah, Aliyu dan Abitalib (s) ya na tare da shi. Sai yace masa: Matso kusa ya Aliyu ! sai ya ce masa: An halicceni da kai daga itaciya guda, nine asalinta, kai ne babban reshenta, sannan Alhassan da Alhussaini su ne, rassanta, duk wanda ya yi riko da wani abu daga gareta (wato itaciyar) All..zai shigar da shi aljanna. Ibn Abbas ya ce: manzon All…(s) yace: Taurari aminci ne ga ma’abuta kasa, daga nutsewa, sannan iyalan gidana na kuma amince ne ga al-ummata daga sabani, idan wata kabila daga cikin kabilun larabawa ta saba masu, zata sami sabani a cikinta sai su zama rundunar shaitan. Zaidu dan Arkam ya ce manzon All..(s) ya ce: Lalle ni zan barmaku wani abu, idan kun yi riko da su, ba za ku taba bata ba, a bayana, dayansu yafi dayar nauyi, littafin All…Igiyar All..mikekkiya, daga sama zuwa kasa, da dangina, iyalan gidana, ba za su taba rabuwa da juna ba, har sai sun iskeni a tabaki, ku duba ku ga, yadda zaku kula mani da su a bayana.Wannan shi ne hadisi wanda ya shahara da ‘nauyaya biyu’, ya na daga cikin hadisan manzon All..(s) da suka fi inganci, da kuma yaduwa a cikin musulmi.
Malamai sun himmatu da wannan hadisin sosai, saboda abinda yake kunshe da shi, na bangaren akidun musulunci na gaskiya.
Banda haka, wannan hadisin ya na daga cikin manya-manyan hujjoji wadanda mabiya mazhabar iyalan gidan manzon All.. (s), wadanda aka fi saninsu da shi. Suke kuma dogara da shi don tabbatar da akidarsu ta taikaita shugabancin al-ummar musulmi bayan wafatin manzon All..a cikin iyalan gidansa su kadai.
Har’ila yau da wannan hadisin ne, wato hadisin nauyaya biyu suke tabbatar da Ismansu, ko tsarkinsu daga aikata laifi ko zunubi, wato ba sa kuskure.
Saboda manzon All..(s) ya gwamasu da alkur’ani mai girma, wanda bata ba zai zo masa ta gabansa ba, ko kuma ta bayansa.
Dayan abubuwan biyu, ba zai taba rabuwa da dayar ba har abada. Don da za su taba sabawa alkur’ani ba.
Amma tunda ba zasu taba sabawa alkur’ani ba, to kuwa su ma’asumaine ba za su taba sabawa All..T ba.
A cikin hadisin manzon All..(s) ya ce: Ba za su taba rabuwa ba, har abada, har sai sun riskeshi, a tabki. Wannan ya isa hujjar kasancewarsu ma’asumai, kamar yadda alkur’ani ya kasance ma’sumi daga sauyawa don kariyar da All..ya yi alkawalin bashi.
Kuma ya tabbata cewa manzon All..(s) ya maimaita wannan hadisin, a wurare da dama.
Don ya na son kare wannan al-ummar daga bata, ya na son kareta daga karkata daga addinin da ya barsu a kansa, idan har sun yi riko da su.
Don ya na son su ci gaba da riko da iyalan gidansa a bayansa, kada su bar su ko su yi gaba da su, ko baya da, su halaka.
Dangane da sanandi da kuma ingancin wannan hadisin, ta bangaren malaman hadisi, wadanda suka yi rubutu a kan wannan fannin, sun wadatar da mu, daga bincikensa a mam. Don haka duk wanda yake bukatar sannin wadannan al-amura, ya nemi litafan da suka dace.
Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Tawayen M23 Sun Kara Shimfida Ikonsu A Garin Goma
Kungiyar M 23 da take samun goyon bayan Rwanda tana kara karfafa ikonta a garin Goma dake gabashin jamhuriyar Demokradiyyar Congo, da su ka hada da filin saukar jiragen sama, kamar yadda MDD ta sanar.
A yau Laraba shugaban kasar Rwanda da gwmanatinsa take goyon bayan ‘yan tawayen kungiyar M23, ya yi kira da a tsagaita wutar yaki.
Da safiyar yau Laraba an sami dawowar kwanciyar hankali a cikin birnin na Goma bayan da a jiya mazaunansa fiye da miliyan biyu su ka kasance a cikin zullumi da fargaba.
Mazauna birnin na Goma sun fadawa kamfanin dillancin Labarun (AP) cewa ‘yan tawayen kungiyar ta M 23 ne suke rike da mafi yawancin birnin.
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai kungiyar ta M 23 ta sanar da cewa ta kame wannan birnin na Goma bayan mayakanta suka dauki kusan mako daya suna matsawa kusa da shi.
Kungiyar M 23 daya ce daga cikin kungiyoyin tawaye 100 da ake da su a cikin kasar ta jamhuriyar Demokradiyyar Congo da kowace daya daga cikinsu take son shimfida iko a cikin yankunan da ake da ma’adanai.
Ita dai kasar DRC tana da dimbin arzikin ma’adanai da suke kwance a karkashin kasarta, da ya sa kasashen makwabta da kuma na nesa suke taimakawa wasu daga cikin kungiyoyin ‘yan tawaye saboda su yi kaso mu raba da arzikin wannan kasar.
Tun da kasar ta Sami ‘yanci daga kasar Belgium, ba ta sami zaman lafiya ba har zuwa yanzu.