Aƙalla mutum ɗaya ne ya mutu, sannan aka yi garkuwa da wasu mutum biyu a daren jiya Juma’a bayan da masu garkuwa da mutane suka farwa garin Kajuru, a jihar Kaduna.
Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Kajuru a majalisar dokokin jihar Kaduna, Usman Danlami Stingos ne ya tabbatarwa da jaridar LEADERSHIP a yau Asabar.
- ‘Yan Bindiga Sun Harbe Mutum 2, Sun Yi Garkuwa Da Wasu 5 A Kaduna.
- Masu Garkuwa Sun Nemi Fansar Miliyan 250 Kafin Su Saki Tsohon Shugaban NYSC, Janar Tsiga
Ya ce a ranar Juma’a 21 ga watan Fabrairu na shekarar 2025 da misalin ƙarfe 11:40 na dare aka yi garkuwa da wani mahaifi da ƴarsa a kauyen Kufana da ke karamar hukumar Kajuru.
Ya ƙara da cewa ‘yan bindigar sun kashe wani mai suna, Ishaya Soda, a unguwar Barde kuma tuni aka binne shi a ƙauyen Dutse Gaya.
Ɗan majalisar ya bayyana cewar an ɗan samu sauƙin hare-haren da ake kaiwa a yankin amma kuma har yanzu ana kashe mutane sannan da sace su domin karɓar kuɗin fansa.
“Duk da cewa an dan samu raguwar kai hare-hare amma har yanzu ana samun wasu su shiga su kashe mutane sannan su tafi da wasu domin kuɗin fansa” in ji ɗan majalisar.
Sannan ya kuma kalubalanci rashin hanya mai kyau a yankunan wanda a cewarsa hakan ma yana kawo tsaiko wajen fatattakar yan ta’adda.
Danlami Stingos ya kuma yabi gwamnatin jihar Kaduna bisa kokarin da take yi na yaƙi da yan ta’adda sannan ya kuma riko gwamnatin da ta dage wajen samar da hanyoyi a yankunan da suke fama da hare-haren ‘yan bindiga.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp