Sama da magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham 1,000 ne suka yi zanga-ganga kan shugaban kungiyar, Daniel Leby kafin wasa da Manchester United a Premier ranar Lahadin da ta gabata. An yi ta kuwa da cewar ”Leby ya bar kungiyar da kuma ”Enic ya bar Tottenham” yayin da magoya baya suka rinka daga tuta a kusa da filin wasa, wadanda ke kiraye-kirayen a kawo canji.
An kuma tsara yin zaman dirshan da zarar an tashi wasan Premier a karawa da United, inda magoya baya suka bukaci da kowa ya tsaya a filin wasan Tottenham. An kafa kyalle a wajen zaman masu gida da wajen zaman baki da aka rubuta sakon cewar ”lokacin canji ya yi” domin ”shekara 24 an sauya masu horarwa 16 da lashe kofi daya.”
- Firaministan Sin Zai Halarci Bikin Rufe Gasawar Wasannin Hunturu Ta Asiya Karo Na 9
- Babbar Gasar Wasannin Kankara Ta Zama Damar Tabbatarwa Duniya Niyyar Karfafa Zaman Lafiya
Kafin Tottenham ta buga wasa da Manchester United ranar Lahadi tana ta 15 a teburi, wadda ta ci wasa daya daga takwas baya da ta fafata. Tottenham ta lashe League Cup a 2008 – tun bayan da Leby da Enic suka mallaki kungiyar daga Sir Alan Sugar, kusan shekara 25 da ta wuce. To sai dai Tottenham ita ce kan gaba a samun riba a Premier League a tsawon shekarun, inda Leby ya samar da £1.2bn da aka gina katafaren filin wasa da kasaitaccen wajen atisaye.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp