Kungiyar ECOWAS, ta sanar da cewa tawagarta da ta je Guinea Bissau, ta bar kasar bayan barazanar data fuskanta daga shugaban kasar.
A wata sanarwa da ta fitar, tawagar ta ce ta bar kasar “da sanyin safiyar Asabar sakamakon barazanar korar da shugaba Umaro Sissoco Embalo ya yi.”
Tawagar kungiyar ECOWAS ta ziyarci kasar Guinea-Bissau tsakanin ranakun 21 zuwa 28 ga watan Fabrairu domin taimakawa wajen warware rikicin siyasar kasar dangane da sanya ranar gudanar da zaben shugaban kasa.
ECOWAS ta ce ta bar kasar ne don gujewa wannan wulakanci.
Kafin hakan dai shugaban kasar ya gana da tawagar ta masu shiga tsakani na kungiyar ta ECOWAS a ranar Litinin da ta gabata.
Amma daga bisanio ya zarge su da wuce gona da iri ta hanyar tattaunawa da wasu shugabannin ‘yan adawa.
Ita dai tawagar ta ECOWAS, an dora mata alhakin samar da mafita ta samar da zaman lafiya a kasar Guinea-Bissau, ta hanyar mai da hankali kan cimma matsaya ta siyasa kafin zaben da aka shirya yi a ranar 30 ga watan Nuwamba.
Wannan dai ba shi ne karon farko da Umaro Sissoco Embalo ke shiga takun tsaka da tawagar ECOWAS a kasar sa ba. A lokacin da ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa tare da goyon bayan jami’an tsaro, ya kori mambobin ECOWAS da ke kasar tare da tare da cewa bai maraba da wakilin kungiyar.