“مَنِ اسْتَعَاذَ بِاللَّهِ صَادِقًا أَعَاذَهُ”
Fassara:
“ Duk wanda ya nemi tsari a wurin Allah da zuciya ɗaya, to Allah zai ba shi kariya”
Duba Kitãbu at-Tashīlu fi Ulūmi at-Tanzil [1/30]
Fashin Baƙi:
Wannan magana tana nuni da cewa idan mutum ya nemi kariya a wurin Allah da zuciya ɗaya, to Allah zai amsa roƙonsa kuma zai kare shi daga duk wani abu mai cutarwa. Wannan yana da asali a cikin koyarwar Musulunci, inda ake koyar da Musulumi su nemi tsari wurin Allah kaɗai daga sharrin Shaiɗanun aljanu da mutane da duka wani maicutarwa a cikin halittu baki ɗaya, da kuma neman tsari da kariya daga miyagun halaye, da duk wani abu da zai cutar da su a duniya da lahira. Allah Ya yi umurni da a nemi tsari da kariya a wurinsa inda Ya ce: “ Idan kuma wani tunzuri daga Shaiɗan ya tunzura ka, to sai ka nemi tsari daga Allah; lalle Shi mai ji ne, Masani” Suratu Fussilat aya ta 36.
A taƙaice, wannan magana ta Ibnu Juzai a-Kalbi tana da muhimmanci sosai a rayuwar Musulumi, domin tana ƙarfafa imani da cewa duk wanda ya dogara ga Allah kuma ya nemi kariya da gaske, Allah zai kare shi daga duk wani sharri. Wannan yana ƙarfafa Musulumi su kasance masu gaskiya a addu’arsu da neman tsari da Allah cikin kowane hali.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp