Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, SP Abdullahi Usman, ya rasu bayan fama da doguwar jinya.
Kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ne, ya tabbatar da rasuwarsa cikin wata sanarwa a ranar Laraba.
- ’Yan fashi 4 sun mutu yayin tsere wa ’yan sanda a Nasarawa
- Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago
Ya bayyana Usman a matsayin jajirtaccen ɗan sanda kuma gada tsakanin jami’an tsaro da al’umma.
“SP Usman ya shafe shekaru uku yana ƙarfafa hulɗa tsakanin ’yan sanda da jama’ar Taraba.
“Ƙwarewarsa, mutuntaka da jajircewarsa wajen neman adalci sun an samu tasiri,” in ji Adejobi.
Ya ƙara da cewa rasuwar Usman babban rashi ne ga rundunar ’yan sanda, abokan aikinsa da duk wanda ya san shi.
Sashen hulɗa da jama’a na ’yan sanda ya miƙa ta’aziyya ga iyalansa da kuma ‘yan uwansa, tare da yin addu’ar Allah Ya masa rahama.
Za a ci gaba da tunawa da Usman saboda sadaukarwar a aikinsa da ƙoƙarinsa na kyautata hulɗa tsakanin ’yan sanda da al’umma a Jihar Taraba.