Wata kungiya mai rashin tabbatar da mulkin demukradiyya na kwarai a Nijeriya mai suna ‘Eyes on Democracy Nigeria’ reshen jihar Bauchi, ta yi tir da kamun da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta yi ma Akanta-janar na jihar Bauchi, Sirajo Mohammed Jaja.
kungiyar ta yi ikirarin cewa kamun bai rasa nasa da siyasa wanda aka shirya aka tsara da nufin sanyaya guiwowin gwamna Bala Muhammad wanda ya zama na gaba-gaba wajen fitowa bainar jama’a domin sukar manufofin gwamnatin APC da suke janyo matsin rayuwa da jefa jama’an kasa cikin rashin walwala.
- EFCC Ta Cafke Mutum 21 Bisa Zarginsu Da Zambar Intanet A Bauchi
- ‘Yansanda Sun Cafke Mutum 2 Kan Zargin Kashe Ɗan Achaɓa Da Sace Babur Ɗinsa A Bauchi
Da ya ke ganawa da manema labarai a ranar Litinin, shugaban kungiyar, Kwamared Munir Aska, ya soki matakin na EFCC tare da misalta hakan a matsayin abun kaito da ke neman jefa damuwa a cikin gwamnatin jihar Bala ƙarƙashin Bala Muhammad.
“Mun yi Allah wadai da wannan kamun, muna ganin hakan a matsayin adawar siyasa da aka tsara domin musguna wa Gwamna Bala Muhammad da gwamnatinsa.
“Wannan matakin kai tsaye yunkuri ne na kokarin rufe bakin jagoran da ke da kwarin guiwar fitowa ya fada wa shugabanni gaskiya,” ya shaida.
kungiyar ta koka kan cewa bai dace a yi amfani da EFCC wajen kamun Jami’an gwamnatin jihar Bauchi da nufin nuna yatsa wa Gwamna Bala Muhammad wanda ya kasance mai fitowa da hakikanin gaskiyar halin da talakawa ke ciki da nema musu hakkinsu daga wajen shugaban kasa.
kungiyar ta lura da cewa in ana amfani da irin wannan salon lallai za a samu nakasu wajen kyautata demukradiyya a kasar nan domin mutane da dama za su yi shiru kan abubuwan da suke tafiya ba daidai ba domin gudun musgunawa.
Eyes on Democracy ta kuma nuna shakku kan yadda aka kama Akanta Janar din a lokacin da yake halartar taron FAAC a Abuja, inda ta bayyana cewa hukumar EFCC ba ta gayyace shi ba balle ya ki zuwa da har za a dauki matakin kamashi.
“Babu ko shakka cewa Gwamna Bala Mohammed yana tafiyar da harkokin kudi da dukiyar jihar cikin tsanake da gaskiya, a karkashin shugabancinsa jihar Bauchi na samun ci gaba da ba a tava ganin irinsa ba kuma cikin sauri a sassa daban-daban,” kungiyar ta shaida.
Ƙungiyar ta bukaci ‘yan Nijeriya, kungiyoyin farar hula, da sauran kasashen duniya da su lura da wadannan ayyukan da ba su dace da tsarin dimokradiyya ba, su bijirewa duk wani yunkuri na mayar da hukumar EFCC dandalin cin zalin siyasa.
Bugu da kari, kungiyar ta yi kira ga hukumar EFCC da ta yi aiki bisa doka, sannan ta bukaci da a gaggauta sakin Akanta Janar din, idan har akwai zarge-zarge na gaskiya da ake yi masa, kungiyar ta dage cewa a bi su kamar yadda doka ta tanada.
“Muna tsayawa tsayin daka da Gwamna Bala Mohammed da dukkan masu fada a ji na gaskiya da adalci a Nijeriya. Babu wata barazana da za ta hana a gudanar da gangamkn na tabbatar da dimokuradiyya, gaskiya da rikon amana,” in ji ƙungiyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp