‘Yan bindiga sun kai hari a ƙauyukan Bajat da Dole da ke ƙaramar hukumar Safana a Jihar Katsina a ranar Talata, inda suka kashe kwamandan ‘yan sa-kai, tare da jikkata wasu da dama.
Wani shaida, ya bayyana cewa harin ya faru da misalin karfe 6 na yamma, lokacin da ‘yan bindigar suka afka wa ƙauyukan suna harbi babu ƙaƙƙautawa, wanda ya jefa jama’a cikin fargaba.
- Sabbin Motocin Bas 100 Masu Aiki Da Lantarki Sun Fara Jigilar Fasinjoji A Birnin Addis Ababa
- Shugaba Putin Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Sin
A lokacin harin, ‘yan bindigar sun harbe Nura Baushe, kwamandan ‘yan sa-kai, har lahira yayin da yake ƙoƙarin kare al’ummarsa.
Sauran waɗanda suka jikkata sun haɗa da Amadu Dole, Surajo Shehu, da Shafiu Sulaiman, waɗanda aka garzaya da su zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina domin samun kulawar likitoci.
Daga bisani jami’an tsaro sun isa yankin tare da kwantar da tarzomar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp