Rahoton Kungiyar Kasashe Masu Samar da Man Fetur (OPEC) ya nuna cewa Nijeriya ta ci gaba da riƙe matsayinta na ƙasa mafi yawan samar da ɗanyen man a nahiyar Afirka a watan Maris.
OPEC ta ce hakan ya faru ne duk da raguwar yawan man da ƙasar ta samar a watan da ya gabata.
Sabon rahotonta na wata-wata da ta fitar a ranar Litinin ya ce yawan man da Nijeriya ta samar ya ragu zuwa ganga miliyan 1.40 a kowace rana a watan Maris, idan aka kwatanta da ganga miliyan 1.46 a kowace rana a watan Fabrairu.
A cewar rahoton, duk da raguwar, yawan man da Nijeriya ta samar shi ne mafi yawa a Afirka, inda ya zarce Algeria da Congo.
- An yi garkuwa da masu ibada a Kogi
- Noman rake: Najeriya da China sun kulla yarjejeniyar kasuwancin $1bn
- Isra’ila ta kashe Palasdinawa 17 ta jikkata 69 a awa 24 a Gaza
OPEC ta kara da cewa ta hanyar ci gaba da ƙarfin da ta samu a watan Fabrairu, Nijeriya ta zarce Algeria, wacce ta samar da ganga 909,000 a kowace rana, da kuma Congo, wacce ta samar da ganga 263,000 a kowace rana.
Ta ci gaba da da cewa Nijeriya ta samar da ganga miliyan 1.51 a kowace rana a watan Maris, idan aka kwatanta da ganga miliyan 1.54 a kowace rana a watan Fabrairu.
Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Sama ta Nijeriya (NUPRC) ta ce yawan man da ƙasar ta samar ya ragu zuwa ganga 1,400,783 a kowace rana a watan Maris.
Duk da raguwar yawan man da aka samar a watan Maris, NUPRC ta ce matsakaicin yawan ɗanyen man da aka samar ya kai kashi 93 cikin ɗari na adadin ganga miliyan 1.5 da OPEC ta ware wa Nijeriya.