Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana damuwa kan yadda ‘yan Boko Haram ke sake taruwa a wasu wurare a jihar, musamman a ƙauyen Tumbus na yankin Tafkin Chadi da kuma tsaunin Mandara da ke dajin Sambisa.
Zulum ya ce ‘yan ta’addan suna komawa cikin sauƙi ba tare da wani tarnaƙi daga sojojin Nijeriya ba, saboda matsalolin da sojoji ke fuskanta wajen gudanar da ayyukansu a yankunan.
- An Gudanar Da Dandalin Kirkire-kirkire Na Kafofin Watsa Labarai Na Duniya Karo Na 4 A Birnin Qufu Na Kasar Sin
- Kotu Ta Ɗaure Wani Mutum Kan Sare Bishiya Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano
Gwamnan ya bayyana haka ne a Maiduguri a ranar Jumma’a, lokacin da Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, da Babban Hafsan Sojoji, Janar Christopher Musa, da wasu manyan hafsoshi suka kai masa ziyara.
Duk da yaba wa ƙoƙarin sojoji, Gwamna Zulum ya ce akwai buƙatar ƙarin ƙoƙari, domin akwai yankunan da ‘yan ta’adda ke ci gaba da shiga kamar Tumbus da tsaunin Mandara.
“An kasa gudanar da ayyukan soji a Tsibirin Tumbus, inda ‘yan ta’adda ke rayuwa cikin sauƙi,” in ji shi.
Zulum ya bayyana wasu matsaloli da ke kawo tsaiko, ciki har da ƙarancin sojoji a yankunan Timbuktu Triangle, Tumbus, tsaunin Mandara, da kan iyakar Nijeriya da ƙasashen Sahel.
Ya roƙi Ministan Tsaro da ya turo ƙarin manyan makamai da motocin yaƙi na zamani zuwa Borno domin taimaka wa sojoji.
A nasa jawabin, Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta tura ƙarin kayan aiki da jami’an soja don magance matsalar tsaro a Borno da Arewa Maso Gabas.
Ya ce shugaban ƙasa ya umarce su da su tabbatar da samar da duk abin da ake buƙata domin murƙushe ‘yan ta’adda a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp