Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kwara ta sanar da cewa rukunin farko na maniyyatanta za su tashi daga filin jirgin sama na Ilorin zuwa kasar Saudiyya a ranar 12 ga watan Mayu.
Sakataren zartarwa na hukumar Abdulsalam Abdulkadir ne ya bayyana haka a lokacin wani shiri na wayar da kan alhazai na shekarar 2025 a ranar Lahadi a Ilorin.
- Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci Ta Yaba Wa Gwamna Lawal Kan Matakan Yaƙi Da ‘Yan Bindiga A Zamfara
- Ƴan Ta’adda Sun Kashe Maharba 10 A Adamawa
Ya bayyana cewa rukunin na biyu zai tashi ne a ranar 14 ga Mayu, na uku kuma zai tashi a ranar 16 ga Mayu, sai kuma a ranar 17 ga Mayu.
A cewarsa, tuni aka shirya wuraren kwana da abinci ga maniyyatan a kasar Saudiyya.
Abdulkadir ya tabbatar da cewa, ana shirye-shirye, inda za a yi alluran rigakafi a ranar 28 ga Afrilu, za a raba tufafi a 30 ga Afrilu, sannan kuma za a raba jakunkuna a ranar 1 ga Mayu.
Ya kara da cewa maniyyatan da suka biya sama da Naira miliyan 8.4 na kudin aikin Hajji, za a biya su bayan sun dawo daga Saudiyya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp