Larabar Nan Ce Duban Fari Na Watan Sha’aban – Mai Alfarma Sarkin Musulmi
Published: 28th, January 2025 GMT
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Saad Abubakar ya yi kira ga al’ummar Musulmin kasar nan da su fara neman ganin jinjirin watan Sha’aban a gobe Laraba 29 ga watan Janairu 2025, daidai da kalandar Musulunci 29 ga watan Rajab 1446AH.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addinin musulunci na jihar Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, Wazirin Sokoto ya ce idan an gan shi, sai a mika bayanan ga sarki mafi kusa domin sanarda mai alfarma Sarkin Musulmi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, duban yana fayyace kalandar Musulunci a cikin shekara guda, wanda hakan ya zai sa ganin watan Ramadan ya fi karbuwa ga al’ummar Musulmin kasar baki daya.
NASIR MALALI/Wababe
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Wata
এছাড়াও পড়ুন:
Mu Yi Riƙo Da Kyawawan Ɗabi’u Har Bayan Ramadan – Sudais
Ku kasance masu tausasawa da rahama, ku sadar da zumunta, ku sanya farin ciki azukatan al’umma kuma ku yada farin ciki, sannan ku nemi kusanci zuwa ga Ubangijinku ta hanyar ji da ɗa’a ga umarnin shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp