2025-03-03@09:45:16 GMT
إجمالي نتائج البحث: 321

«Wata»:

    Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya yi watsi da batun aike wa da dakarun zaman lafiya zuwa kasar Ukiraniya kamar yadda kasashen turai suke tattaunawa akai. Ministan harkokin wajen kasar ta Rasha ya bayyana cewa, gwamnatin Amurka tana son a kawo karshen yaki, da shimfida zaman lafiya,amma kuma kasashen turai suna son a...
    Fitaccen dan siyasar kasar Lebanon Walid Junbilat ya bayyana cewa, ‘yan sahayoniya suna son yin amfani da kungiyoyin da ake da su a Syria domin tarwatsa hadin kan kasar. Walid Junbilat  wanda shi ne tsohon shugaban jam’iyyar “ al-takaddumil-Ishtiraki” ya ce zai ziyarci kasar Syria domin ganawa da mahukuntanta akan hatsarin dake tattare da tsoma...
    Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana cewa; al’ummar Iran tana fuskantar makiya kafirai da munafikai, amma kasar ba ta da matsala da sauran al’ummun duniya. Har ila yau jagoran ya ce, alkur’ani mai girma yana kunshe da hanyoyin da ya kamata a yi mu’amala da dukkanin wadannan makiyan,...
    Jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng ya bayyana a cikin wani jawabi ta bidiyo da ya gabatar ga taron kolin jagorancin Sin na Duke-UNC a ranar 28 ga watan Fabrairu cewa, kasancewar zaman lafiya mai dorewa tsakanin Sin da Amurka a duniya, abu ne da ya zama wajibi kuma nauyi ne dake kan wuyansu....
    Kwanan nan, aka wallafa littafin “Zababbun rubutu game da tattalin arziki na Xi Jinping” kashi na 1 a kasar Sin, wanda kwalejin nazarin tarihi da adabi na kwamitin kolin JKS ya tace. Littafin “Zababbun rubutu game da tattalin arziki na Xi Jinping” kashi na 1, ya kunshi muhimman ayyuka kuma na asali na rubutun Xi...
    Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres na mika sakon gaisuwa a yayin da al’ummar Musulmi a fadin duniya suka fara gudanar da azumin watan Ramadan. Ramadan yana kunshe da dabi’u na tausayi, tausayawa da karamci. Sannan dama ce ta sake haduwa da dangi da sauran al’umma. Kazalika dama ce ta tuna wadanda ba...
    Rahotanni da suke fitowa daga Nijar sun bayyana cewa; Wata kungiyar mai alaka da al-ka’ida ta  dauki alhakin kashe sojojin kasar 11 a kan iyaka da Aljeriya. A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai lamarin ya faru,kuma a jiya Asabar ne aka yi jana’izarsu a garin Agadez, kamar yadda wata majiyar watsa labara ta...
    Shugaban Ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce bai ga laifin da ya yi wa Shugaban Amurka Donald Trump, ballantana ya nemi afuwa. Zelensky ya bayyana haka ne bayan zazzafar cacar-baki da ya kaure a tsakaninsa da Trump a ofishin shugaban ƙasar Amurka. A cewarsa, “ina godiya ga Amurka da gudunmuwar da take ba mu,” in...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi watsi da shawarar da Isra’ila ta gabatar na tsawaita matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, inda ta yi kira ga kasashen duniya da su matsa wa gwamnatin mamayar lamba don ci gaba da mataki na biyu na yarjejeniyar kamar yadda aka tsara tun farko. Yau...
    Sunana Aisha T. Bello daga Jihar Kaduna: Rashi ramadan basket nasa a kore saurayi saboda ‘yan mata sun maida ramadan basket dole. Shawara ta ga al’ummar musulmi duniya shi ne; mu yi amfani da wannan dama gun rokon Allah, saboda in Allah ya nuna mana wanan mu gani ba lallai bane mu ga wani watan...
    Tawagar yan wasan Damben Gargariya ta kasar Iran sun zama zakara a wasan damben da ya gudana a birnin Tirana babban birnin kasar Albaniya a makon da ya gabata, inda suka tashi da lambobin yabo 6 wadanda suka hada da zinari 4 azurfa da tagulla. Wannan nasara da ta maida kasar a matsayin zakara a...
    ‘Fake Inbestment Schemes’: Masu cuta na amfani da shafukan zuba jari na bogi domin damfarar mutane. Ransomware: Wasu barayin yanar gizo na saka kwayoyin cutar kwamfuta domin su hana mutum amfani da na’urarsa sai ya biya kudi. Hanyoyin Kare Kanka Yi amfani da kwayoyin kalmomin sirri masu karfi – A guji amfani da kalmomin sirri...
    Ya bayyana cewa rundunar ta damu matuka da faruwar lamarin, kuma ta himmatu wajen tabbatar da an yi adalci, yana mai cewa “Muna hada kai da hukumomin makarantar da sauran masu ruwa da tsaki domin zakulo wadanda ake zargin tare da kama su. Za a sanar da ci gaban lamarin a kan lokaci,” in ji...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga cikin Kasashen  da su ka fara azumi a yau Asabar, da akwai Saudiyya, Katar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Omman, Bahrain da Kuwait. Saikuma Masar, Syria, Falasdinu, Yemen, Sudan,Somaliya, Libya, Tunisa da kuma Aljeriya. Kasar Moroko kuwa ta sanar da cewa, yau Asabar ne cikon watan Sha’aban, gobe Lahadi zai zama farkon Ramadan. A kasar Iraki,...
    Azumin watan Ramadan na daga cikin shika-shikan Musulunci, kuma Allah ne Ya wajabta shi a kan bayinsa. Wannan wata yana da falala da lada mai yawa, domin Allah Ya keɓe shi da girma da ɗaukaka. Ga wasu daga cikin falalar azumin watan Ramadan: 1. Ana buɗe kofofin Aljanna, ana rufe ƙofofin wuta, kuma ana ɗaure...
    Azumin watan Ramadan na daga cikin shika-shikan Musulunci, kuma Allah ne Ya wajabta shi a kan bayinsa. Wannan wata yana da falala da lada mai yawa, domin Allah Ya keɓe shi da girma da ɗaukaka. Ga wasu daga cikin falalar azumin watan Ramadan: 1. Ana buɗe kofofin Aljanna, ana rufe ƙofofin wuta, kuma ana ɗaure...
    Hukumar abinci ta duniya ( FAO) ta sanar da cewa bisa la’akari da yadda adadin mutanen Afirka yake karuwa da kaso 2.3% a kowace shekara, hakan yana nufin cewa amfani da alkama zai karu. Bugu da kari hukumar abincin ta duniya ta ce da akwai wasu dalilan da za su sa Rashan ta kara yawan...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Alkaluman da hukumar kididdga ta kasar Sin ta bayar a yau Jumma’a sun shaida cewa, yawan mutanen kasashen waje da suka shigo babban yankin kasar Sin ba tare da biza ba a bara, ya kai miliyan 20.12, adadin da ya karu da kaso 112.3%. Bisa ga alkaluman, yawan baki masu yawon shakatawa da suka shigo...
    Wata kungiyar kare hakkin bil’adama mai zaman kanta wacce take da cibiya a birnin Geneva na kasar Swizlanta ta bada sanarwan cewa ta sami cikekken shaidu wadanda suke tabbatar da cewa gwamnatin HKI tana azabtar da falasdinawa wadanda take tsare da su. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar tana bada wannan...
    Fadar mai alfarma sarkin Musulmi, ta sanar da ganin jinjirin watan Ramadan da maraicen Juma’ar nan a Sakkwato.   Cikin wata sanarwa da Mai Alfarma Sarkin Musulmin, Sa’ad Abubakar lll ya karanta a fadarsa, ya ce an ga watan a sassan ƙasar daban-daban.   Don haka ne ya ayyana ranar Asabar 1 ga watan Maris...
    “A karkashin Shugabancin Dantsoho, ya taimaka wajen ganin ana sauke sundukan kayan da aka yo jigilarsu a cikin sauki, musamman a Tashar Lekki wanda hakan ya taimaka, wajen rage cunkso a Tashar.” A cewar Mahukuntan Mullar. Mahukuntan Mullar sun kara da cewa, sun zabo Dantso ne, ganin cewa, shi ne, na farko da aka zaba...
    “PDP jam’iyyar siyasa ce, kuma muddin kuka ci gaba da kai mata hari, ba za ku samu ci gaba ba. Ba za ku iya daukar nauyin ‘yan baranda na siyasa da farfaganda don lalata mana kima ba don kawai burge Shugaba Bola Tinubu saboda ajandar ku ta 2027. “Ba wani dan Arewa mai hakali da...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce inganta hadin kai da alaka tsakanin kasashen musulmi da suka hada da Iran da Malaysia na daga cikin abubuwan da ake bukata a halin da ake ciki a duniya. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ta yi da ministan harkokin wajen Malaysia Dato’ Seri Utama...
    Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar Cibiyar Hulda da Jama’a ta Najeriya (NIPR) sun shirya taron karawa juna sani na tsawon kwanaki uku ga jami’an yada labarai.   Taron na da nufin baiwa Jami’an Watsa Labarai dabarun sadarwa na zamani, tare da mai da hankali kan sabbin hanyoyin inganta sadarwar jama’a a zamani.  ...
    Har ila yau yana daga hukuncin shari’a, ba a fara azumi da kokwanto, misali ka kwanta bacci sai ka kudirce a ranka cewa in an bayyana ganin wata ina bacci, zan tashi da azumi. Mun gode Allah, yanzu sabida na’u’rar zamani da wuri ake sanar da ganin wata. Lamarin ganin watan Ramadana abu ne mai...
      Shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ne ya tsaya a matsayin wakilin na angwaye yayin da Mai martaba Sarkin Gwandu, Manjo Janar Muhammad Iliyasu Bashar murabus ne ya tsaya a matsayin wakilin na amaren.   Gwamna Nasir Idris, yayin da yake godewa uwargidansa Hajiya Nafisa Nasir...
    Wadanda Suka Yi Nasara Aliyu Usman Adam – Matsayi na daya Aliyu Usman Adam, dan asalin Zariya ta Jihar Kaduna, an haife shi a shekarar 1984. Ya kammala karatunsa na firamare da sakandare a Zariya, sannan ya samu digiri a harshen Hausa daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya a 2008. Bayan hidimar kasa a Jihar Edo,...
    Kasar Aljeriya ta yi watsi da barazanar da kuma wa’adin da kasar faransa ta gindaya ma ta na cewa za ta soke yarjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma ta shekarar 1968 wacce ta ba Aljeriya matsayi na musamman. A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Aljeriya ta fitar ta ce “A cikin ci gaba...
    Ya kuma kara da cewa, gwamnatin jihar Kano ta bai wa ilimi fifiko, wanda Kano ce a gaba wajen ware kasafin kudi mai yawa a shekarar 2024 da 2025 a fannin Ilimi. Bugu da kari, gwamnatin ta ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi domin tabbatar da matasa sun samu ingantaccen ilimi wanda zai ba su...
    “Mun yi jimamin asarar rai da aka yi, kuma mun yi tattaki zuwa ga iyalan mamacin don jajantawa tare da tabbatar musu da gudanar da cikakken bincike don tabbatar da adalci,” in ji shi.   Don haka, ya bukaci jama’a da su kwantar da hankulansu domin Rundunar tana aiki tukuru don zakulo gaskiyar lamarin tare...
    Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayar da umarni ga jama’a da su fara duban jaririn watan Ramadan daga ranar Jumu’a 29 ga watan Sha’aban, 1446 Bayan Hijira, wanda ya yi daidai da 28 ga watan Fabrairu, 2025. Shugaban Kwamitin Bayar da Shawara kan Harkokin Addini a Fadar Sarkin Musulmi, Wazirin Sakkwato, Farfesa...
    Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Saad Abubakar ya yi kira ga al’ummar Musulmin kasar nan da su fara neman ganin jinjirin watan RAMADAN a gobe Juma’a 28 ga watan Fabrairu 2025, daidai da kalandar Musulunci 29 ga watan Sha’aban1446AH.   A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin...
    Sai dai Bukar ya musanta wannan iƙirari, yana mai cewa ya sanar da shugabansa kuma ya bi duk matakan da suka dace, amma har yanzu ba a bi masa haƙƙinsa ba. Ya ce sau da dama an buƙaci ya kawo bayanan asusun ajiyarsa na banki don duba matsalarsa, amma babu wani canji. Duk da cewa...
    Masar ta yi watsi da shawarar da jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya gabatar na cewa Alkahira, maimakon kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta karbi ragamar zirin Gaza na wucin gadi, tana mai danganta irin wadannan tsare-tsare da cewa “ba za a amince da su ba.” Kamfanin dillancin labarai na MENA ya nakalto kakakin...
    Majalisar Dattijan Aljeriya ta “dakatar da duk wata hulda da Majalisar Dattijan Faransa. Majalisar al’ummar kasar, kwatankwacin majalisar dattijai a kasar Aljeriya, ta sanar da cewa ta “dakatar da dangantakarta” da majalisar dattawan Faransa, domin nuna adawa da ziyarar da shugabanta Gérard Larcher ya kai a ranakun Litinin da Talata a yankin yammacin Sahara. Ziyarar...
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce Gwamna Umar Namadi ya amince da nadin sabbin jami’an cibiyoyi 27 da za su gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025. Babban Daraktan Hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar. Ya ce, an zabo sabbin jami’an cibiyar...
    A yau Laraba, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta daina bai wa Taiwan makamai, ta kuma guji yin kafar ungulu ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin Taiwan. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa kullum, lokacin...
    Hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran ta kaddamar da kayakin aikin da ake bukata don samar da garin sinadarin (Tellurium Dioxide) wanda ake hada maganin cutar daji wanda ake kira (Iodine-131) da shi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar hukumar makamashin nukliyar ta Iran, na cewa ana samar da wannan sinadarin...
    A ranar 25 ga wata ne zaunannen wakilin kasar Sin a majalisar dinkin duniya Fu Cong, ya bayyana a taron kwamitin sulhu na MDD game da batun Isra’ila da Falasdinu cewa, tilas ne a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza baki dayanta, don tabbatar da tsagaita wuta mai dorewa. Ya kuma yi...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari biyar domin biyan diyya ga wadanda aikin gina tituna a cikin  gari ya shafa. Kwamishinan yada labarai da matasa da wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jiha...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sama da Naira Biliyan Biyar domin biyan diyya ga wadanda aikin gina tituna a cikin  gari ya shafa. Kwamishinan yada labarai da matasa da wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a...
    Wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne sun yi fashi da makamin wasu kwale-kwalen kamun kifi guda takwas a hannun masunta a Doron Baga da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno. Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a ƙauyen Kaimo da ke da tazarar kilomita huɗu daga garin...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A duk lokacin da aka ɗaura aure, wata addu’a da ’yan uwa da abokan arziki kan yi ita ce “Allah Ya kawo ƙazantar ɗaki”. A bisa tafarkin addini da kuma al’ada, ɗaya daga cikin manyan dalilan yin aure shi ne samun haihuwa. Sai dai a wasu lokuta, wasu...
    Biyo bayan umarnin da hukumar kula da aikin hajji ta kasa ta bayar, hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta kara wa’adin biyan kudin kujerar aikin hajjin 2025. Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ne ya bayyana hakan a yau yayin taron bita ga  ma’aikata da...
    Ministar harkokin wajen Madagascar Rasata Rafaravavitafika ta bayyana a Tananarive, hedkwatar kasar jiya Litinin cewa, ana godiya ga Sin da ta dade take tura tawagogin likitanci zuwa kasar cikin shekaru 50 da suka gabata, don ba da tallafin jinya na zamani a yankuna masu nisa na Madagascar, da ceton rayuka na miliyoyin mutane dake wuraren....
    Bisa labarin da aka bayar, an ce, gwamnatin Trump ta kasar Amurka tana tsara wasu tsauraran matakan kayyade samar wa kasar Sin sassan na’urorin hada laturoni na semiconductor, da kara matsin lamba ga kasashen kawacenta, tare da bukatarsu da su tsaurara dabaibayi a kan sha’anin samar da fasahar matattarar bayanai ta microchip ga kasar Sin....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An gurfanar da wadanda ake zargin ne bisa laifuka daban-daban, da ke da alaka da laifukan zamba ta yanar gizo, mallakar wasu takardu da ke dauke da shaidar karya, da kuma satar bayanan sirri.   Dukkansu sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su a lokacin da aka karanta musu tuhumar, sai dai...