Harbin dai ya samu Comfort ne a kai, inda nan take ta mutu, yayin da wasu harsasai suka samu mijinta a mukamuki da kafadarsa dama.

Yayin da ‘ya’yansu ke kururuwar firgici, rahotanni sun ce jami’an sun gudu daga wurin.

An kori Musiliu daga aikin ‘yansanda ne a ranar 17 ga watan Satumba, 2015, daga bisani kuma aka bayar da belinsa a shekarar 2017 ba tare da sanin dangin da ya kashewa ‘yan uwa ba.

Bayanan kotun sun nuna cewa mai shari’a O.A. Taiwo na Kotun 26, Babban Kotun Ikeja, ya bayar da belin Musiliu a kan Naira miliyan 1 tare da mutane biyu.

A hukuncin kotun, Mai shari’a Taiwo ya bayyana cewa, “Sashe na 115(1) na dokar shari’a ta shekarar 2011 ya bai wa kotu damar bayar da belin wanda ake tuhuma da laifin kisa.

“Don haka kotu na da hurumin bayar da belin wanda ake tuhuma da laifin kisa ko kuma a’a, hakkin mai nema ne ya nuna ta hanyar bayar da wasu bukatu na musamman wadanda za su bai wa kotu damar yin amfani da damar da ta ga ya dace ga mai bukata.”

Tun lokacin da aka bayar da belin Musiliu, jaridar PUNCH Metro ta gano cewa har yanzu ba a san inda Musiliu yake ba duk da zaman kotun da aka yi da kuma yunkurin kama wadanda za su tsaya masa.

Da yake zantawa da jaridar PUNCH, Godwin Udoh ya bayyana takaicinsa da irin wannan rashin imani.

“Na yi mamaki da ban gan shi (dan sandan) a kotu ba kafin daga baya na gano cewa an bayar da belinsa, babu wanda ya yi tsammanin za a bayar da belinsa.

“Duk lokacin da suka nemi gidan yarin da su gabatar da shi a gaban kotu, sai su ba da uzuri kamar rashin man da za su yi jigilarsa. A haka na fara binciken abin da ke faruwa,” in ji Udoh.

Udoh ya bayyana cewa binciken da ya yi ne ya sa ya gane cewa lallai an saki Musiliu.

“Kotun da ke tafiyar da shari’ar a yanzu tana babbar kotun TBS, amma ba su taba kawo shi wurin domin gurfanar da shi ba, lokacin da aka taba gurfanar da shi a gaban kotun majistare da ke Ebute Metta a shekarar 2015 da lamarin ya faru,” in ji shi.

“Alkalin mai shari’a, Hon. Justice Akintoye, har ma ya rubuta wa dukkan gidajen yarin Jihar Legas wasiku, amma sun ki gabatar da wannan mutum a kotu, har ma sun bayar da sammacin kama mutum biyun da za su tsaya masa.

Udoh ya koka da cewa, “Kotun gaba daya ba ta yarda an bayar da belinsa ba, sai da ni kaina na je na gano shi, a lokacin ne na tabbatar da cewa kotun Honarabul Taiwo da ke Ikeja ta bayar da belinsa, yanzu mutumin ya bace, ba mu sake jin komai a kansa ba.”

Har yanzu dai ana ci gaba da shari’ar, inda aka shirya zaman kotu na gaba a ranar 9 ga watan Afrilu, sai dai Udoh bai da tabbas ko za a yi adalci.

“Babu wanda ya tsaya masa a kotu a matsayin lauyansa, sai dai mai gabatar da kara daga ma’aikatar shari’a ta Jihar Legas ya ce in yi kokarin ganin su a Alausa domin su samu hanyar gurfanar da shi a gaban kotu,” in ji shi.

Udoh, yayin da yake tunani a kan rayuwarsa bayan wani mummunan lamari da ya faru a shekarar 2015, ya bayyana cewa an bar shi da ‘ya’yansa suna kokawa su kadai, duk da alkawuran da shugabannin ‘yansanda suka dauka na tallafa musu.

“Ciwon da nake ji daga wannan rauni har yanzu ba na iya jurewa,” in ji shi.

“Har yanzu akwai wani karfe a cikin mukamukina da ya kamata a cire, likitan ya ce suna bukatar fitar da shi a maye gurbinsa da kashi don in iya tauna da kyau. Amma yayin da nake magana da ku, karfen yana ci gaba da cutar da ni.

Udoh ya kuma tunatar da yadda ‘yansanda suka kasa taimakawa wajen binne matarsa marigayiya a shekarar 2016.

“Na gana da kwamishinan ‘yansandan Jihar Legas, amma ya ce min ‘yansanda ba sa binne kowa kuma in yi da kaina,” in ji shi.

Ya koka da cewa duk da tabbacin da ‘yansandan suka yi sun yi watsi da shi da iyalansa.

“Sun yi alkawari za su kula da ni, da biyan duk kudin da nake kashewa na jinya, da kuma tabbatar da cewa an yi mini tiyatar da ta dace, amma sun bar ni ina shan wahala.

“Kudin aikin cire wannan karfe daga mukamukina ya kai miliyoyin Naira, kuma ba ni da wannan kudin,” in ji shi.

Udoh ya ci gaba da bayyana cewa, rundunar ‘yansandan ta kuma yi alkawarin tallafa wa ‘ya’yansa na kudi, kula da lafiya, da bayar da tallafin karatu.

“Sun ce za su saka ni a cikin lissafin albashi don in sami akalla tallafin kudi a kowace shekara. Babu wani abu da ya faru,” in ji shi.

Hatta takardar shedar karatu da aka bai wa ‘ya’yansa daga baya an dawo da su.

“Sun ce kuskure ne kuma za su gyara su mayar da shi ga sufeto-janar domin ya amince min, har yau ban samu ba.”

Ta’asar da ‘yansanda ke yi wa fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba ya zama ruwan dare duk da kokarin da ake na shawo kan jami’an da ke da ra’ayin aikata laifuka.

Rundunar ‘yansandan ta kori Sufeto Usman Dikko daga mukaminsa bisa rasuwar Baale na Lotu, Marigayi Cif Fatai Jubril, a shekarar 2023.

An kori wani jami’in da ya yi wa wata yarinya fyade da bindiga a cikin ofishin ‘yansanda a Legas.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Naira bayar da belinsa bayar da belin bayyana cewa

এছাড়াও পড়ুন:

Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16m

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya ziyarci iyalan mafarauta 16 da aka kashe a yankin Uromi da ke Jihar Edo, tare da ba su tallafin Naira miliyan 16.

Matan matatan sun fito ne daga ƙananan hukumomin Bunkure, Kibiya, Rano, da Garko a Jihar Kano.

Mutum 2 sun rasu, 13 sun ɓace a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano

Barau ya gana da iyalan mamatan a Masallacin At-Taqwa da ke Bunkure a ranar Laraba tare da Ministan Harkokin Gidaje, Yusuf Abdullahi Ata da sauran manyan jami’ai.

Barau, ya yi ta’aziyya da kuma tabbatar da cewa waɗanda suka aikata laifin za su fuskanci hukunci.

“Na zo nan ne domin na taya ku jaje kan wannan mummunan al’amari da ya jawo rasuwar ’yan uwanku 16 a ranar Alhamis da ta gabata.

“Allah Ya Aljanna Firdausi ta zama makomarsu, Ya bai wa waɗanda suka ji rauni lafiya,” in ji Barau.

“Ba za mu ɗauki hakan da sauƙi ba. Za mu tabbatar cewa waɗanda suka aikata laifin za su fuskanci hukunci.”

Barau, ya kuma sanar da bai wa kowane daga cikin iyalan mamatan kyautar Naira miliyan ɗaya, wanda ya kai jimillar Naira miliyan 16.

Da yake magana a madadin iyalan mamatan, Sheikh Zainul Abidina Auwal, limamin yankin, ya gode wa Barau bisa ƙoƙarinsa da yadda ya damu da lamarin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An haramta wa Akpabio da Natasha tattaunawa da manema labarai
  • Gwamnati Za Ta Dawo Da Sayar Wa Dangote Ɗanyen Mai Da Farashin Naira
  • Wata Babbar Kotu A Seoul Ta Tube Shugaban Kasa Daga Mukaminsa Saboda Doka Ta Bacin Da Ya Kafa
  • Kisan ma’aikatan ceto : MDD ta gargadi Isra’ila game da aikata laifin yaki
  • Rasha ta gargadi Amurka kan duk wani gigin ka wa kasar Iran hari
  • Burundi ta zargin Rwanda da yunkurin kai mata hari
  • IMF ta nemi Tinubu ya kyautata rayuwar talakawan Najeriya 
  • Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16m
  • Kisan Mafarauta: Babu wanda aka kai wa harin ramuwar gayya a Kano — Ƙungiyoyin Matasa