2025-02-20@08:57:13 GMT
إجمالي نتائج البحث: 62
«bayar da belin»:
Kungiya mai gwagwarmaya ta Falasdinawa Hamasa ta bayyana cewa tana iya sakin fursinoni yahudawa wadanda suke hannunta gaba daya a lokaci guda a marhala ta biyu ta musayar fursinoni tsakaninta da tare da sharadin ta cika al-kawulan da ta nauyi alhakin aiwatar da shi a wannan karon. Daga cikin har da maida tsagaita wutan na din din din Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Taher Al-Nounou ya cewa idan an yi haka za’a kammala musayar fursononin gaba daya, sannan HKI ta sake duk fursinonin falasdinawa gaba daya da suke hannunta. Yin hakan ya na nuna yanda al-amarin musayar Fursinoni yake da muhimmancin ga falasdinawa. Kafin wannan sanarwan dai ministan yaki na HKI Isarael Katz ya bayyana cewa...
Kasar Sin na maraba da duk kokarin da ake yi cikin lumana don warware rikicin kasar Ukraine, ciki har da tattaunawa tsakanin Amurka da Rasha, kuma Sin na fatan dukkan bangarori da masu ruwa da tsaki za su shiga cikin shawarwarin samar da zaman lafiya in lokaci yayi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na yau Talata, yana mai cewa, ko da yaushe kasar Sin tana da yakinin cewa, tattaunawa da yin shawarwari, ita ce hanya daya tilo da za a iya warware rikicin, kuma ta himmatu wajen inganta shawarwari don samar da zaman lafiya. Ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga wata tambaya game da ganawar da jami’an...
Majalisar Wakilai ta sanya Laraba, 26 ga watan Fabrairu, a matsayin ranar da za ta buɗe zauren sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin dokokin haraji. Kakakin Majalisar, Abbas Tajudeen wanda ya bayyana hakan a ranar Talata, ya ce za a gudanar da sauraron ra’ayin jama’ar a zauren majalisar na wucin-gadi. Abba ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaro ta Kano Za a binciki INEC kan jinkirin gudanar da zaɓen cike giɓi Ya bayyana cewa, kwamitin majalisar kan harkokin kuɗi ne zai jagoranci zaman sauraron ra’ayin jama’ar haɗi da wasu ƙusoshin majalisar na wasu kwamitocin. Aminiya ta ruwaito cewa, a makon jiya ne ƙudirin kafa dokokin harajin guda huɗu da Shugaba Bola Tinubu ya aike wa majalisar suka tsallake karatu na...
Babban kwamandan sojojin kasar Iran ya bayyana cewa: Sun sabunta hanyoyin da sojojin Iran zasu mayar da martani kan duk wani harin wuce gona da iri kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bada umarni Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdur-Rahim Mousawi ya bayyana cewa: Tun tsawon kwanaki da suka gabata jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewa: Idan Amurka ta farma tsaron al’ummar Iran, to lallai Iran za ta kai farmaki kan tsaronta ba tare da wata shakka ba, wannan ya kasance umarni ne bayyananne ga dakarun Iran, kuma kwamandojin sun sabunta shirinsu na aiwatar da wannan umarni, kuma a halin yanzu Iran a shirye take tsaf don gudanar da umarni a aikace. Manjo Janar...

Jaridar Maariv Ta Isra’ila Ta Bayyana Wasu Daga Cikin Hasarorin Da Yakin Gaza Ya Janyo Wa Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya
Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan ta’addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan Zirin Gaza, wanda ya shafe tsawon watanni 15 kafin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni a watan Janairun da ya gabata. A cewar jaridar, sojoji 15,000 da ke cikin sojojin mamayar Isra’ila suka jikkata tun farkon yakin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, yayin da wasu 846 suka sheka lahira. Daga cikin wadanda...
Sarkin Qatar Tamim bin Hamad Al-Thani zai fara ziyarar aiki na kwana guda a nan Tehran, don tattauna al-amura masu muhimmanci da Jami’an gwamnati JMI. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbass Aragchi ya bayyana cewa, a gobe muna tare da sarkin Qatar Tamim bin Hamad Athani, inda zamu tattauna al-amura masu muhimmanci a tsakanin kasashen biyu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar cewa kasar Qatar ta taka rawa a tsagaita wuta tsakanin HKI da kuma kungiyar Hamas, sannan tana da dangantaka mai karfi da kasar Iran. Ya ce yankin gabasa ta tsakiya tana fuskantar sauye-sauye masu yawa, da kuma barazana iri-iri, kuma wannan zuwan zai kasance sabonta dangantaka tsakanin kasashen biyu ne. Duk da...

Yawan Tikitin Kallon Fim Din “Ne Zha 2” Da Aka Sayar a Karshen Mako Ya Shiga Sahun Gaba Na Fina-Finai 5 A Arewacin Amurka
Kamfanin dake gudanar da nazari na Comscore na Amurka ya ba da kididdiga cewa, yawan tikitin da aka sayar a karshen mako na kallon fim din kasar Sin mai suna “Ne Zha 2” ya shiga sahun gaba na fina-finai 5 a arewacin Amurka. An yi kiyasin cewa, yawan kudin da aka samu a kwanaki 3 na karshen makon da ya gabata ya zarce dala miliyan 7, inda fim din ya zama mafi shahara a matakin koli da Sin ta gabatar a karshen makon a Amurka. An ce, an fara nuna wannan fim a gidajen sinima 770 dake arewacin Amurka daga ranar 14 ga watan nan da muke ciki, a matsayin fim din da Sin ta gabatar, kana yawan kudin da...
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da aikin gina titin Kanya Babba (Kwanar Duzau) zuwa Kankare zuwa Ballada zuwa Duzau zuwa Danhill zuwa Kyambo zuwa Mundu zuwa Goron Maje. Aikin wanda aka bayar da shi kan kudi naira biliyan 6 da miliyan 300, wani muhimmin mataki ne a yunkurin gwamnatin jihar na inganta ababen more rayuwa da hanyoyin sada yankuna. Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Namadi ya jaddada muhimmancin hanyoyin, wajen samar da ci gaban tattalin arziki, da inganta hanyoyin samar da ababen more rayuwa, da inganta rayuwar al’ummar yankin. Ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na samar da ingantattun ababen more rayuwa da za a dade ana amfana da su. Ya kuma bayyana cewa, ana sa ran ...
Bugu da kari, Tinubu ya amince da rashin shinge a sabuwar harabar jami’ar ne ya kawo wannan takaddamar, inda nan take ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta ware kudade domin gudanar da aikin kafa katafaren shinge a tsakanin kauyen da Jami’ar. Ya kuma jaddada kudirin gwamnatin na inganta ababen more rayuwa na jami’o’i a fadin kasar nan.
Sojojin mamayar HKI suna cigaba da kai hare a yankin Tul-Karam da sansanonin ‘yan gudun hijira da suke cikinta wanda ya dauki kwanaki 21 suna yi. Bugu da kari, sojojin mamayar suna cigaba da kama Falasdinawa a wannan yankin,inda a daren jiya su ka kutsa cikin unguwanni mabanbanta. Har ila yau, sojojin mamayar sun kwace gidajen Falasdinawa da dama da suke a kusa da sansanin Tul-kram, da mayar da su zama sansanonin soja. Ya zuwa yanzu adadin Falasdinawan da ‘yan sahayoniyar su ka tilastawa yin hijira daga sansanonin Tul-Karam da Nuru-Sahmsh, sun kai 10,000. Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinawa ta sanar da cewa, adadin mutanen da su ka yi shahada a cikin kwanaki 21 na hare-hare sun kai 11, yayin...
kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta mika wasu ‘yan Isra’ila uku da ta yi garkuwa da su ga kungiyar agaji ta Red Cross a wani musayar fursunonin da aka sako Falasdinawa 369 a wata musanya ta baya-bayan nan a karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta. An saki ‘yan Isra’ilan uku a birnin Khan Yunus da ke kudancin Gaza, inda Isra’ilawan suka yi jawabi ga jama’a kafin mika su ga kungiyar agaji ta Red Cross. Sakin dai shi ne na shida tun bayan da tsagaitawar ta fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu bayan fargabar da ake yi a makon da ya gabata cewa yarjejeniyar ta kusa rugujewa bayan da Isra’ila ta ki ba da isassun kayan agaji a Gaza. Yawancinsu...
Salma Muhammad Salisu matashiya ce da ba ta taba mafarkin yin sana’ar kayan makulashe ba, bayan da ta kammala digirinta na farko a fannin Kididdiga (Statistics). Shekara biyar da kammala jami’a, matashiyar ta tsinci kanta cikin matsalar rashin aikin ofis, duk kuwa da karancin kwararru mata a fannin da ta karanta. Hakan ya sa ta fara tunanin yadda za ta fara sana’a domin dogara da kanta kafin Allah Ya kawo mata aiki. Daga nan ne tunanin fara kasuwancin harkar girke-girke da hada lemo ya zo mata, har ta fara ‘M&S Mannah Wassalwa Kitchen’. Labarin Salma na kama da matasan Nijeriya da dama da suka kammala manyan makarantu, amma ba su samu aikin ofis ba. Hakan ne ya sanya a baya-bayan...
CBN ya ci gaba da cewa, dole ne dilolin su sayar da kudaden musayar ga masu hada-hadar sayar da kudaden, daidai da farashin kasuwar musayar kudade ta kasa, wato NFEM, musamman don a tabbatar da ci gaban tafiyar da farashin. Bankin ya kuma sanya kashi daya a cikin dari a tsakanin farashin da masu musayar kudaden, za su iya chazar masu sayen kudaden. “Dole ne dilolin da su gabatar da rahotannin su ga sashen kusuwanci da musayar kudade na CBN, na kudaden da suka sayar ga masu hada-hadar musayar kudaden, inda su kuma masu hada-hadar musayar kudaden, dole ne su rinka gabatar da ribar da suka samu a kullum ta saye da sayar kudaden, ta hanyar amfani da tsarin cibiyoyin...
Limamin da ya jagoranci sallar Jumu’a a birnin Tehran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran sun mayar da martani ga shugaban Amurka ta hanyar gudanar da bikin tunawa da samun nasarar juyin juya halin Musulunci Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya bayyana cewa: Al’ummar Iran sun mayar da martani da kakkausar murya ga kalamai da kuma matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka ta hanyar halartar gagarumar zanga-zangar tunawa da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran. Ayatullah Khatami ya kara da cewa: A yau daga mimbarin Juma’a da ke birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran yana tabbatar da cewa: Miliyoyin Iraniyawa ne suka halarci...
‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa suna ci gaba da mayar da martini kan hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suke kai wa kan gabar yammacin kogin Jordan Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai farmakin soji a cikin dare da safiyar kan garuruwan da suke gabar yammacin kogin Jordan, inda sojojin mamayar suka kaddamar da munanan hare-hare a kan sansanin Jenin sannan wani jirgin yakin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi luguden bama-bamai kan gidajen Falasdinawa. A gefe guda kuma, ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa sun gudanar da arangamar da sojojin mamayar, a sansanin Askar da ke gabashin Nablus. Yayin da a birnin Nablus aka yi artabu mai tsanani tsakanin ‘yan gwagwarmayar na Falasdinu da sojojin mamayar Isra’ila. A halin da...
Alhaji Ahmad Haruna Zago da aka fi sani da Ɗan zago, gogaggen ɗan siyasa ne da ya fara siyasa tun a Jamhuriya ta biyu. Bayan dawowar Najeriya mulkin farar hula a shekarar 1999, ya shiga Jam’iyyar APP, inda ya kasance na gaba-gaba a tafiyar siyasar jam’iyyar a Kano da ma kasa baki ɗaya. Yana daga cikin waɗanda suka jawo Muhammadu Buhari shiga cikin harkokin siyasa. 2003. Gabanin zaɓen 2003, Alhaji Ahmadu Haruna zago ya taka rawa a tunja-tunjar da ta biyo bayan zaɓen fitar da gwani na Jam’iyyar APP, da ta kai ga karɓe takarar gwamna daga hannun tsohon shugaban jam’iyyar, Ibrahim Al’amin Little, aka bai wa Malam Ibrahim Shekarau. 2007 Sai dai tun ba a je ko’ina ba,...
Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta sanar da cewa, za a ci gaba da musayar fursunoni kamar yadda aka tsara a karkashin yarjejeniyar da aka cimmawa. A yau Alhamis ne dai kungiyar ta Hamas ta sanar da cewa za ta saki fursunoni kamar yadda yake a jadawalin da aka tsara. Tashar talabijin din Aljazira ta ambato majiyar kungiyar ta Hamas tana cewa, tawagarta tana tattaunawa d a Masar da Katar a matsayinsu na masu shiga tsakani musamman akan yadda za a kai wa mutanen Gaza, hadaddun matsugunan da za su rayu a ciki da kuma magunguna da sauran bukatu na kiwon lafiya na gaggawa. Haka nan kuma an warware matsalar kai kayan agaji da za a bari su rika shiga...
Wata Babbar Kotu a Abuja, ta ɗage yanke hukunci kan buƙatar bayar da belin Tsohon Shugaban Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, wanda ke fuskantar zargin cin hanci da rashawa. A ranar Laraba ne, Mai shari’a Chinyere Nwecheonwu, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Yusuf a gidan gyaran hali na Kuje har zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu. Sojoji sun doki ’yan sanda kan kama ‘mai laifi’ Fitaccen ɗan siyasa Ahmadu Haruna Zago ya rasu A lokacin ne kotun za ta yanke hukunci kan buƙatar bayar da belinsa. Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), na zargin Yusuf da karkatar da kuɗaɗen gwamnati lokacin da yake jagorancin NHIS a shekarar 2016. Ana...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi watsi da barazanar da Isra’ila da Amurka ke yi kan batun musayar fursunoni. Kakakin kungiyar Hamas Hazem Qassem ya fada cewa Isra’ila tana kaucewa aiwatar da wasu tanade-tanade na yarjejeniyar tsagaita bude wuta,” yana mai gargadin cewa ba za a sako mutanen da ake garkuwa da su ba idan ba Isra’ila ta mutunta yarjejeniyar ba. Qassem ya ce, “Matsayinmu a fili yake, kuma ba za mu amince da barazanar Amurka da Isra’ila ba,” in ji Qassem, bayan firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu ya yi barazanar komwa yaki idan har ba a sako mutanen da aka kama ba zuwa ranar Asabar. A ranar Laraba, ministan harkokin soji na gwamnatin ya yi gargadin cewa Isra’ila za...
A yau Laraba, kafar yada labarai ta CGTN ta hada gwiwa da tashar watsa labarai ta lardin Heilongjiang na kasar Sin ta kamfanin CMG, wajen shirya wani bikin musayar al’adu na kasa da kasa, wanda ya shafi gasar wasannin kankara ta nahiyar Asiya dake gudana a Harbin, gami da bikin fitilu na gargajiyar kasar Sin. Mahalartar bikin sun hada da ‘yan wasa da ‘yan jaridu na kasashen nahiyar Asiya daban daban. (Bello Wang)

Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Murkushe Falasdinawa A Birnin Tulkaram Da Ke Gabar Yammacin Kogin Jordan
Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da rusa ababen more rayuwa a birnin Tul-karam da sansanoninsa na Falasdinu tare da kama Falasdinawa da tilasta wa jama’a yin gudun hijira Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai hare-hare kan birnin Tul-Karam da sansanoninsa guda biyu Tul-karam da Nourul- Shams a rana ta 16 a jere, a daidai lokacin da sojoji ke ci gaba da barnata kayayyakin more rayuwa da kadarorin jama’a da kuma kame jama’a gami da tilastawa dubban mazauna sansanonin biyu gudun hijira. Sojojin mamayar suna ci gaba da killace sansanonin Tulkaram da Nourul Shams, sannan kuma suna kara yawan sintirin motocinsu da na tankokin yakinsu da kuma sintiri da kafa a yankuna da unguwannin su, a daidai lokacin...
Sama Da Masu Amfani Da Kayayyakin Laturoni Miliyan 20 Ne Suka Nemi Tallafin Musayar Kayan Laturoni
NUC Ta Dakatar Da Bayar Da Lasisin Gina Sabbin Jami’o’i Masu Zaman Kansu
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta gabatar da kayan agaji ga gwamnatin jihar Zamfara domin tallafawa wadanda gobara ta shafa a wata makarantar Islamiyya da ke Kaura Namoda. A lokacin da take mika kayayyakin, Darakta Janar na Hukumar Hajia Zubaida Umar, ta ce matakin ya nuna damuwar gwamnatin tarayya kan halin da wadanda abin ya shafa ke ciki. Babbar Daraktar wanda shugaban NEMA shiyar Sokoto, Aliyu Shehu Kafindangi ya wakilta, ya ce tallafin ya hada da kayan abinci kamar buhunan shinkafa, da masara, da man girki, da kayayyakin amfani gida. A baya dai Hajiya Zubaida Umar ta ziyarci wadanda lamarin ya rutsa da su wadanda har yanzu suke ci gaba da karbar magani a asibitin...
Wata gobara da ta tashi a wajen sayar da gas a Sabon Wuse da ke Ƙaramar Hukumar Tafa a Jihar Neja, ta yi sanadin ƙonewar motoci da shaguna da kuma kayan abinci. Lamarin ya faru ne a daren ranar Asabar lokacin da wata tanka ke sauke gas a wajen sayar da gas. Gwamnatin Kano ta dakatar da wani fim mai suna Zarmalulu Me ya sa ake musayar yawu tsakanin APC da PDP? Wutar ta ɗauki sa’o’i tana ci kafin isowar jami’an kashe gobara. Wani mazaunin garin, Abdul Sabon-Wusa, ya ce bindigar ta girgiza yankin, inda mutane suka firgita suka fito daga gidajensu domin neman mafaka. Wutar ta kuma bazu zuwa wani gidan mai, inda ta ƙone shaguna da motoci da...
Falasdinawa sun fitar da martanin farko mai gauni kan kalaman fira ministan ‘yan mamayar Isra’ila dangane da furucinsa ga Saudiyya Kungiyar ‘yantar da Falasdinu ta yi Allah wadai da kalaman da fira ministan mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi game da kafa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya. Sakataren kwamitin zartarwa na kungiyar ‘yantar da Falasdinu Hussein Al-Sheikh ya bayyana cewa: Suna yin Allah wadai da matakin da mahukuntan yahudawan sahayoniyya suka dauka na kai cin mutunci da raina kimar masarautar Saudiyya da ‘yancinta, wanda suka yi kira da a kafa kasar Falasdinu a kasar Saudiyya, kuma wannan furuci na Rashin tunani ya yi cin karo da dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar kasa da kasa. Ya kara da cewa:...
Sojojin mamayar Isra’ila sun fara janyewa daga yankin Netzarim da ke tsakiyar Zirin Gaza Kafofin yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila za su fara ficewa daga yankin Netzarim da ke tsakiyar Zirin Gaza a daren jiya. Jaridar Yedioth Ahronoth ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta watsa rahoton cewa: Rundunar sojin mamayar Isra’ila ta ba da umarnin ficewa daga yankin Netzarim da ke tsakiyar Gaza a wani bangare na aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kungiyar Hamas da gwamnatin mamayar Isra’ila a yankin. Jaridar ta bayyana cewa: Runduna ta 162 ta sojojin mamayar ta sake matsawa zuwa kusa da kan iyaka da kuma janyewa daga yankin Netzarim na nufin cewa, babu sojojin mamayar Isra’ila a arewacin...
Duk da cewa akwai sauran lokaci kafin babban zaben 2027, ana ci gaba da musayar yawu kan shirye-shiryen manyan ‘yan siyasa da ke hamayya da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, inda suke tarurruka tare da tuntuɓar juna kan yadda za su kayar da Jam’iyyar APC mai mulki a Zaɓen 2027. Fadar Shugaban kasa ta mayar da martani kan kalaman da wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyun adawa da na cikin gidanta suke yi, inda suka zarge ta da sauka daga kan turbar da jam’iyyar take. Katsina ta zama cibiyar haɗin kan ƙabilun ƙasa a Arewa — Gwamna Radda Ta kashe saurayinta saboda ya gaisa da tsohuwar abokiyar karatunsa Fadar Shugaban kasa na mayar da martani ne bayan wani taro da jagororin hamayya...
Isra’ila za ta saki fursunonin Falasdinawa 183 yau Asabar, a madadin wasu mutanenta uku daga cikin wadanda kungiyar Hamas ke garkuwa da su a Gaza a wani bangare na aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza da suka cimma. Kamar dai a makon da ya gabata, za a yi musaya ta biyar a wurare biyu a zirin Gaza a jere inji rahotanni. A maimakon haka, Isra’ila za ta saki fursunonin Falasdinawa 183, ciki har da 18 da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai, ciki har da wasu fitattun mutane irin su Iyad Abu Shidam, wanda Isra’ila ta yankewa hukuncin daurin rai da rai a Beersheva a shekara ta 2004. Bayanai sun ce kimanin 111 daga cikin wadannan...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Idan Amurka ta yi barazana ga tsaron kasar Iran, to lallai Iran ta kalubalance ta Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Tattaunawa da Amurka ba wayo ba ce, kuma ba hikima ba ce, kuma gogewa ta tabbatar da hakan. Yayin ganawarsa da tawagar kwamandojin sojojin sama da na sararin samaniya na sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada cewa: Idan Amurkawa suka yi barazana wa Iran, to lallai za su fuskanci mayar da martani, idan kuma suka aiwatar da wannan barazanar, to za su fuskanci mayar da martani Iran mai gauni, kamar yadda idan suka kawo hari kan kasar Iran, za...
“Kowannen masu hada-hadar musayar kudade da aka san da zamansu da suka biya kudinsu na sake sabunta lasisinsu na 2025, an shawarce su da su rubuta zuwa ga Daraktan sashen kudi da tsare da sanya ido na Bankin, domin su karbi kudansu, da aka dakatar da biyan kudi, zuwa cikin asusunsu.” Inji Takardar Takardar ta bayar da tabbacin cewa, Bankin na CBN, har yanzu a tsaye yake akan kafarsawajen ganin ya samar da daidaito da bin ka’ida, musamman wajen gann ana gudanar da hada-hadar musayar kudade na waje a kasuwar musayar kudi.
“Wannan sauye-sauyen an yi su ne, bisa manufar bin ka’idar shigar cikin Tashar, musamman domin a dakile satar hanyar shiga cikin Tashar ga manyan motocin da ba su gabatar da takardun shedar ka’idar shiga cikin Tashar ba.” Acewar Sanarwar. Kazalika, Hukumar ta NPA, ta bayar da umranin da a gaggauta wanzr da sauyin, biyo bayan sauya wadannan sabbin matakan da Hukumar ta yi, wanda za su fara aiki a cikin watan Fabirairun 2025. “Bisa wannan sauyin, daga yanzu daukacin manyan motocin da suka tunkaro domin shiga cikin Tashar, dole su kasance suna sanye da lambar manyan motocin, domin bin ka’idojin da Hukumar ta gindaya.” Inji Sanawar. “Dole ne manyan motocin su manna kwafin takardun shedar bayar bayar da kariya wato...

“Yar Sakon Amurka A Kasar Lebanon Morgan Ortagus Tana Shan Mayar Da Martani Daga Bangarori Mabanbanta
Bangarori mabanbanta na kasar Lebanon suna mayarwa da ‘yar sakon Amurka martani saboda tsoma baki da ta yi a kan yadda za a kafa gwamnati a kasar. Morgan Ortagus wacce ta gana da jami’an kasar Lebanon ta bayyana cewa, bai kamata a kafa gwamnati a kasar ta wakilan kungiyar Hizbullah a ciki ba. Kungiyar malaman addinin musulunci ta fitar da bayani da a ciki ta ce; “Furucin mataimakin manzon Amurka a gabas ta tsakiya, Morgan Ortagus wacce ‘yar sahayoniya ce,tsoma baki ne a harkokin cikin gidan Lebanon wanda ya tsallake ka’idojin aikin diplomasiyya.” Ita ma gwamnatin kasar ta Lebanon ta fitar da bayani tana mai cewa abinda Ortugas din ta furta, ra’ayinta ne, bai shafi gwamnatin Lebanon ba. Shi kuwa...
Majiyoyin sojin Sudan sun sanar da cewa: Sun sake samun nasarar kwace iko da babban birnin kasar Khartoum Majiyoyin sojin Sundan sun sanar da cewa: Cikin dan gajeren lokaci sun samu nasarar sake kwace iko da birnin Khartoum fadar mulkin kasar daga mamayar dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces, bayan da suka yi birnin kawanya daga bangarori hudu. A nata bangaren, Ma’aikatar yada labaran Sudan ta zargi bangarorin waje da jagorantar gudanar da fadace-fadacen da ‘yan tawayen dakarun kai daukin gaggawa ke yi don samun damar cin gajiyar albarkatun kasar, idan ‘yan tawaye suka yi nasara. Rayuwa ta fara inganta a birnin Omdurman kuma kasuwanni sun fara farfadowa, inda jama’a suke komawa ci gaba da harkokinsu na yau...
Sojojin HKI sun sanar da cewa a Yau Alhamis biyu daga cikinsu sun halaka, yayin da wasu 8 su ka jikkata sanadiyyar abinda su ka kira faduwar injin daukar abubuwa masu nauyi akansu, a kusa da Gaza. Sanarwar sojojin na mamaya ta kuma ce, biyu daga cikinsu suna da mukamai da suke a karkashin bataliyar rundunar Gulani ta 51.
Kasashen larabawa masu kawance da Amurka sun kasance a sahun gaba wajen mayarwa da shugaban kasar Amurkan martani, bayan da ya bayyana cewa kasarsa za ta shimfida ikonta a Gaza, bayan fitar da Falasdinawa da Gaza. Gabanin wannan sanarwar ta Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa ya tuntubi kasashen Jordan da Masar masu makwabtaka da Falasdinu da su karbi bakuncin mutanen Gaza na wani lokaci har zuwa sa’adda za a gyara wajen. Masar da Jordan sun yi watsi da wannan shirin da suke dauka a matsayin wata dabara ce ta fitar da Falasdinawa daga cikin kasarsu, da maye gurbinsu da yahudawa ‘yan share wuri zauna. A wani bayani da kungiyar hadin kan Larabawa ta fitar ta bayyana cewa; Abinda Trump...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya nada Sheikh Na’im Qassim a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya nada babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah Sheikh Na’im Qassim a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon. Marigayi Sayyid Hassan Nasrullahi tsohon babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah da ya yi shahada, a yakin baya-bayan nan kan kasar Lebanon, shi ne tsohon wakilin mai martaba Imam Khamenei a kasar Lebanon kafin shahadarsa.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran za ta mayar da martani ga duk wata barazana ko matsin lamba gwargwadon tsayin dakarta Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Iran ta sha tabbatar da cewa a shirye take ta gudanar da huldar siyasa da diflomasiyya don tabbatar da moriyar kasa, kuma tana shirye ta gudanar da kumajin siyasa da diflomasiyya wajen kare muradunta da tsaron kasa, sannan tana da azamar daukan duk wani matakin kare kanta da masalaharta tare da mayar da martani ga duk wata barazana ko matsin lamba gwargwadon tsayin daka da gwagwarmayarta. Isma’il Baqa’i ya bayyana haka ne a yayin da yake mayar da martani ga tambayar cewa; Maganganun da shugaban...
Shugaban kasar Amurka Donald Trump zai rattaba hannu kan wasu takardun bayar da umarni na bangaren zartaswa, game da janyewar Amurka daga hukumar kare hakkin bil’adama ta majalisar dinkin duniya (UNHRC) da kuma dakatar da bayar da tallafi ga hukumar bayar da agaji ga Falasdinu ta majalisar dinkin duniya (UNRWA). Wata kafar yada labarai ta cikin gida a Amurka ta bayar da rahoton haka, daga wata majiya ta hukuma a fadar White House. Yau talata kuma Trump na ganawa da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda ya dade yana sukar hukumar ta bayar da agaji ga Falasdinu ta UNRWA. A lokacin wa’adin farko na mulkin Trump a watan Yunin 2018, Amurka ta fice daga hukumar kare hakkin bil’adama ta majalisar dinkin...
Sakamakon sanarwar da Amurka ta fitar kwanan baya a kan kara haraji na kashi 10 cikin dari a kan daukacin kayayyakin kasar Sin da ake kaiwa kasar tare da kafa hujja da wasu batutuwa irin su maganin Fentanyl, a yau Talata, ma’aikatar cinikayya da takwararta ta kudi ta kasar Sin sun fitar da wata sanarwa cewa, Sin ta dauki matakan mayar da martani a kan Amurka tare da fara aiwatarwa. Matakan da suka jibanci lamarin sun hada da cewa, da farko, kasar Sin za ta sanya harajin kashi 10% zuwa 15% kan wasu kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka, daga ranar 10 ga Fabrairu. Sannan na biyu, kasar Sin ta yanke shawarar shigar da rukunin kamfanonin US PVH...
Kungiyoyin kare bil’adama ta Falasdinawa guda biyu sun bada rahoton cewa gwamnatin HKI tana azabta falasdinawa da suke tsare da su. Sun kuma kara da cewa sojojin HKI tana wulakanta Fursinonin Falasdinwa suna kuma azbtar da su, musamman bayan sakin 183 daga cikinsu, a musaya ta huda. Inda Falasdinawa suka mika masu fursinoni 4 da ke hannunsu. Hukuma mai kula da fursinoni Falasdinawa ko (PPS) ta bayyana cewa a marhala ta 4 Falasdinawar 183 yahudawan suka sallama, ammam 111 daga cikinsu wadanda sojojin yahudawan suka tsare a lokacinda ake yaki na watanni 15 da su ne. Har’ila yau daga cikin wadanda aka sallama a jiya Asabar 18 daga cikinsu ta yanke masu hukuncin daurin rai da rai ne, har mutuwa....
‘Yan gwagwarmayar Siriya sun sanar da fara kaddamar da hare-haren daukan fansa kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila Sojojin mamayar Isra’ila sun yifuruci da cewa; Sun fuskanci bude wuta daga yankin kudancin Siriya, wanda kungiyar gwagwarmayar al’ummar Siriya ta yi ikirarin kai harin wanda shi ne irinsa na farko tun bayan da sojojin mamaya suka kutsa kai cikin yankunan Siriya bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad. Sojojin mamayar Isra’ila sun tabbatar da kai wani farmaki kan rundunar sojinsu a kudancin Siriya a jiya Juma’a. A jiya ne sojojin mamayar Isra’ila suka kai farmaki kauyen Taranja da ke yankin Quneitra a kudu maso yammacin kasar Siriya, inda suka kame mutane biyu. Wakilin gidan rediyon sojojin mamayar Isra’ila ya...
Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai farmaki kan birnin Tulkarm da sansaninsa da ke gabar yammacin kogin Jordan Sojojin mamayar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun shiga rana ta shida suna kai hare-haren wuce gona da iri kan birnin Tulkarm da sansaninsa, inda yanayin tsoro da tarwatsa gine-gine suka lullube mazaunan yankunan, adaidai lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suke ci gaba da kai hare-hare da kutsawa cikin gidajen Falasdinawa, lamarin da ya yi sanadin barnatar da dukiyoyin Falasdinawa da dama tare da tilastawa iyalai masu yawa tsarewa zuwa gudun hijira. Sojojin mamayar Isra’ila suna gudanarda sintiri da kafa ta hanyar gudanar gudanar da yawo a kan tituna a cikin birnin musamman a yankunan yamma, kudanci da kuma gabas, inda...
Har ila yau, sun bayar da wannan shawara ce, duba da irin rawar da wadannan kalubale biyar ke takawa a lokacin kakar noma ta 2023 da kuma ta 2024. 1- Kalubalen Rashin Tsaro: Wannan matsalar na jawo wa manoma da sauran masu son zuba hannun jari a fannin koma baya, musamman duba da yadda ‘yan bindigar daji ke halaka manoma da kuma yin garkuwa da su da dama a 2024. Hakan ya haifar da hauhawar farashin kayan abinci da ya kai kimanin kashi 39.84, musamman a watan Disambar 2024. Kwararrun sun bayar da shawarar cewa, idan har ana bukatar samar da wadataccen abinci a 2025, ya zama wajbi a dauki matakan da suka dace, don kare rayukan manoma da kuma...
Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar kasuwanci ta Sin ya amsa tambayoyin ‘yan jarida game da shirin Japan na aiwatar da matakan hana fitar da kayayyaki zuwa Sin, ciki har da semiconductor. Kakakin ya bayyana cewa, shirin bangaren Japan na aiwatar da matakan, zai kawo cikas ga tsaro da kwanciyar hankali na tsarin masana’antu, da gurgunta mu’amalar kasuwanci na yau da kullum dake tsakanin kamfanoni, da kuma lalata muradun kamfanonin kasashen biyu. Dangantakar Cinikayya Da Sin Ta Budewa Afrika Kofar Samun Ci Gaba Ana ɗar ɗar Kan Mutuwar Sojoji Bayan Da Mota Ta Kwace A Legas Sin na fatan kasar Japan za ta ji ra’ayoyin masana’antu, ta kuma gaggauta gyara ayyukan da ta yi bisa tushen kiyaye ka’idojin tattalin arziki da cinikayya...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da ke ziyara a Qatar ya gana da shugabannin Hamas a inda suka tattauna batun sake gina Gaza. Tattaunawar a birnin Doha ta hada fitattun jami’an kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas da suka hada da Mohammed Darwish shugaban majalisar tuntuba ta Shura da Khalil al-Hayya babban mai shiga tsakani na kungiyar. A yayin ganawar, Darwish ya bayyana Operation Al-Aqsa Storm a matsayin wani sabon salo a gwagwarmayar da al’ummar Palastinu ke yi da gwamnatin mamaya. Ya jaddada cewa yunkurin gwamnatin Isra’ila na raba al’ummar Falasdinu da kasarsu ta hanyar yakin kisan kare dangi da sauran hanyoyi ya ci tura. Ya nanata cewa al’ummar Falastinu sun ci gaba da dagewa wajen kare hakkinsu da kuma...
“Kamafanin na LNG na kasa, na bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunkasa tattalin azrikin Nijeriya da kuma kara bayar da goyon baya wajen ganin ana fitar da kaya zuwa ketare, kuma zamu tabbatar da cewa, an kara karfafa hadaka a tsakanin Hukumar da Kamfanin.” Inji Dantsoho. “Rarar da Nijeriya ta samu na hada-hada ta kai ta Naira tiriliyan 5.81 wacce ta yi daidai da dala biliyan 3.7, a zango na uku hudu a 2024.” Kamar yadda rukunonin taron bunkasa tattalin arziki na Nijeriya NESGya ruwaito. Rahoton ya sanar da cewa, an samu wannan nasarar ce, biyo bayan amfanin da Tashoshin Hukumar Jiragen Ruwa ta Kasa NPA.
Kungiyar Hamas ta sanar da sunayen mutum uku da za ta mika wa kasar Isra’ila a Gaza a ranar Asabar a ci gaba da musayar fursunonin yaki tsakaninsu. Bayan sako ’yan Isra’ila uku da ’yan kasar Thailand biyar a ranar Alhamis, Rundunar Qassam , sashen sojin Hamas ta sanar ranar Juma’a cewa wadanda kungiyar za ta sako su ne Ofer Kalderon da Keith Siegel da kuma Yarden Bibas. Hakan na zuwa ne bayan a cikin dare jiragen yakin Isra’ila sun kashe Palasdinawa 10 a sansanin ’yan gudun hijira na Jenin da ke garin Tammun da ke yankin Yammacin Kogin Jordan. Kazailka ’yan sandan Isra’ila sun kama Palasdinawa 12 a yankin Gabashin Birnin Kudus a yayin da suke murnar sako ’yan...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, sun kama wasu mutum biyu da ake zargi da satar dabbobi. Waɗanda aka kama sun haɗa da Abdulkadir Tukur mai shekara 35 da Ibrahim Saidu mai shekara 20. KAROTA za ta kashe N250m wajen gyaran motoci 5 a Kano Ana biyan wasu kuɗi don kare gwamnatin Tinubu — El-Rufai An same su da tumaki 28 da awaki 57, jimillar dabbobi 85 da ake zargin da sato su. An kama su ne a ranar 25 ga watan Janairu, 2025, bayan da Dagacin Tulmi a Ƙaramar Hukumar Akko, Abubakar Umar, ya kai wa ‘yan sanda rahoto. Wani mafarauci mai suna Yayaji Muhammad ne ya tare su a garin Tulmi, inda suka kasa bayar da cikakken bayani kan...
Firai ministan HKI Banyamin Natanyahu Ya bada umurnin a dakatar da musayar fursinoni da kungiyoyi masu gwagwarmaya a Gaza. Bayan da Falasdinawa sun Saki mutane 8 ya zuwa yanzu, yahudawa 3 da kuma wasu yan kasar Thailand 5. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labaran yahudawan suna fadar haka. Sun kara da cewa firai ministan ya ce a dakatar da sakin fursinoni Falasdinawa 110 wadanda yakamata HKI ta sallamesu a yau. Kafin haka dai Falasdinawan sun salami wadannan fursinonin yahudawan 8 ne a zagaye uku na musayar fursinoni da kuma janyewar sojojin yahudawan daga yankunan gaza. Majiyar ofishin firay ministan ya bayyana cewa an dakatar da musayar fursinonin ne har sai abinda hali yayi. Da...
Sowore, wanda ya taɓa tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa, na fuskantar tuhume-tuhume guda 17 daga rundunar ‘yansanda, ciki har da laifi a kafafen sada zumunta da kuma kiran Shugaban ‘Yansanda na ƙasa, IGP Kayode Egbetokun, da “IGP na ƙarya.”
Isra’ila ta dakatar da sakin fursunonin Palasɗinawa ba zato ba tsammani yayin da ake ci gaba da musayar fursunoni da waɗanda aka kama ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, a cewar rahoton Army Radio. Hukumomi ba su bayyana dalilin dakatarwar ba, kuma babu tabbas kan lokacin da za a ci gaba da tsarin. Wani Ɗan Pakistan Ya Kashe ‘Yarsa Kan Ɗora Bidiyon Kanta A TikTok Hisbah Ta Kama Matashi Da Matashiya Kan Yin Aure Saɓanin Dokokin Musulunci A Kano Yarjejeniyar tsagaita wutar an ƙulla ta ne don bayar da damar musayar fursunonin da Hamas ke riƙe da su da kuma waɗanda ke tsare a Isra’ila. Sai dai wannan matakin ba zato ba tsammani ya haifar da rashin tabbas kan ci...
Ministan harkokin wajen Iran ya ce Tehran ba ta samu wani sako daga sabuwar gwamnatin Amurka dangane da tattaunawar janye takunkumin ba. Abbas Araghchi ya fada a ranar Laraba cewa duk wani matakin shiga irin wannan tattaunawa ya ta’alaka kan kwarin gwiwar da gwamnatin Donald Trump take da shi. Ministan ya ce Iran ta riga ta shiga tattaunawa da bangarorin Turai da ke cikin yarjejeniyar nukiliyar ta 2015, kuma tana jiran Washington ta fayyace manufofinta. “Ba a aika ko karbo wani sako na musamman ba tsakanin kasashen biyu ba; saidai abubuwan da muke ji a kafafen yada labarai kawai.” An yi ta rade-radin cewa gwamnatin Trump ta yi musayar sakonnin sirri da Iran. “A baya mun cimma yarjejeniya; Iran ta...
Kungiyar fursunonin Falasdinu ta ce za a sako wasu karin Falasdinawa 110 daga gidajen yarin Isra’ila a yau Alhamis a mataki na uku na yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni tsakanin Isra’ila da Hamas. Ana sa ran galibin Falasdinawan da aka ‘yantar za su isa yankin Radana na Ramallah da ke yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye da misalin karfe 12:00 na safe agogon kasar, in ji kungiyar fursunonin Falasdinu. Wannan ba zai hada da fursunoni 20 da za a tura gudun hijira a wajen Falasdinu ba. Kungiyar ta kuma fitar da jerin sunaye da shekarun fursunonin da za a saki wadanda suka hada da akalla yara 30. Sakin da za’ayi wa Falasdinawan 110 a yau zai sanya...
Ministan Harkokin Wajen Iran ya shawarci shugaban Amurka da ya mayar da yahudawan sahayoniyya zuwa Greenland Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump da ya yi kan ba da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, maimakon haka Araqchi ya ba da shawarar kwashe ‘yan sahayoniyya Greenland. Ministan harkokin wajen Iran ya yi ishara da haka ne a wata hira da kafar yada labarai ta Sky News, yana mai bayyana cewa: A mahangar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, a bayan da Trump ya shiga fadar White House a farkon wa’adinsa ya gabatar da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, amma kokarinsa ba ta yi nasara ba. hakan yana nufin rashin yiwuwar korar Falasdinawa...
Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa wasu gidaje da rumbun ajiya a sansanin Tulkaram a Gabar yamma da Kogin Jordan Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa gidaje da rumbun adana kayayyaki a sansanin ‘yan gudun hijira na Tulkarm da ke Gabar yammacin Kogin Jordan a cikin daren jiya, inda haka ya yi sanadiyyar tashin gobara. Shafin watsa labaran Falasdinawa na yanar gizo ya bayyana cewa: Wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa wani rumbun ajiyar kaya da ke kasan benen wani ginin da ke unguwar Al-Wakala a tsakiyar sansanin, lamarin da ya yi sanadin tashin gobara mai tsanani ta ya shafi wani shagon sayar da silinda gas da ke yankin da wasu gidaje da yawa...
Sai dai, an kwashe fasinjoji 53 da ke cikin jirgin ba tare da jin wani rauni ba cikin aminci. Ita ma Hukumar kula da Tsaro ta Nijeriya (NSIB) ta fara gudanar da bincike kan lamarin. Amma hukumar da ke kula da harkokin tsaro, NCAA, a wata sanarwa da ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce za ta bayar da duk wani tallafin da ake bukata ga NSIB domin gudanar da cikakken bincike kan wannan lamarin. Daraktan Hulda da Jama’a, Michael Achimugu a cikin wata sanarwa ya ce, “NSIB ce kadai za ta iya bayyana musabbabin wannan hatsarin idan ta kammala bincikenta.”
Wani jirgin kamfanin Max Air ya tsallake rijiya da baya yayin sauka a filin jirgin Malam Aminu Kano (MAKIA) a ranar Talata da daddare. Jirgin wanda yake ɗauke da fasinjoji 53 da ma’aikata shida yana dawowa daga Jihar Legas ne lokacin da haɗarin ya faru. Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Mun kama mutum 46 da miyagun ƙwayoyi a Yobe — NDLEA Wani fasinja ya bayyana cewa jirgin ya rasa tayar gabansa yayin sauka a filin jirgin. Fasinjan ya yi karin bayani da cewa cewa tayar jigin ta fashe sannan ta kama da wuta a daidai lokacin da ya sauka cikin filin da misalin karfe 10:19 na dare. “Daidai lokacin da tayar ta...
Shugaban Max Air reshen Kano, Bello Ramalan, ya tabbatar da cewa duk fasinjoji sun tsira cikin koshin lafiya kuma ya nemi afuwar jama’a kan abin da ya faru. Hukumar binciken hatsarin jiragen sama ta Nijeriya (AIB) na gudanar da bincike kan musabbabin lamarin, wanda ake zaton ya faru ne sakamakon matsalar taya. Max Air ya tabbatar da cewa za ta tallafa wa fasinjoji wajen dawo musu da kayansu yayin da bincike ke gudana.

Dan Majalisar Dattijan Amurka Ya Mayar Da Martani Kan Kalaman Trump Na Tilastawa Falasdinawa Gudun Hijira
Dan Majalisar Dattawan Amurka ya bayyana kiran da shugaban Amurka ya yi tilastawa Falasdinawa gudun hijira Falasdinawa da cewa kokari ne na shafe wata al’umma daga kan doron kasa Dan Majalisar Dattawan kasar Amurka Sanata Bernie Sanders a jiya Litinin ya fara mayar da martani ga shugaban Amurka Donald Trump inda ya bayyana kiran da Trump ya yi na korar Falasdinawa daga Zirin Gaza zuwa kasashen da ke makwabtaka da su a matsayin kokarin “Shafe wata al’umma ce daga kan doron kasa kuma laifin yaki ne” inda ya bukaci dukkan Amurkawa da su yi Allah wadai da wannan furuci. A ranar Asabar da ta gabata ce shugaban Amurka Donald Trump ya ba da shawarar mayar da Falasdinawa daga zirin Gaza...
Tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya ce ya bayar da hayar ɗaya daga cikin gidaje uku kacal da ya mallaka domin sayen abinci. Buhari ya faɗi hakan a yayin wani taro na jam’iyyar APC da aka gudanar ranar Litinin a Fadar Gwamnatin Katsina. Tsohon Shugaban Ƙasar ya ce duk da ya shafe shekaru takwas a kan madafan iko, bai yi amfani da kujerar mulki wajen azurta kansa ba. “Nijeriya ƙasa ce mai wuyar sha’ani ta fuskar jagoranci amma galibin ’yan ƙasar ba su fahimci hakan ba. “Ba za a taɓa fahimtar irin sarƙaƙiyar da ke cikin riƙo da akalar jagoranci ba da ma ita kanta Ƙasa Nijeriya sai mutum ya tsinci kansa a kan madafan iko. “A yanzu na ƙara...