HausaTv:
2025-04-13@04:56:20 GMT

Araghchi : Iran za ta mayar da amsa ga wasikar Trump cikin kwanaki masu zuwa

Published: 21st, March 2025 GMT

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martani ga wasikar shugaban Amurka Donald Trump a cikin kwanaki masu zuwa ta hanyoyin da suka dace.

Araghchi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi kai tsaye a gidan talabijin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRIB) jiya Alhamis.

Araghchi ya kuma lura cewa a wannan karon, ci gaban ya zo tare da wani yunkuri na diflomasiyya daga Amurkawa, ciki har da wasika da bukatar yin shawarwari.

Ya kuma bayyana cewa manufar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a bayyane take. “Ba za mu shiga tattaunawa kai tsaye karkashin matsin lamba, barazana, ko karin takunkumi.”

A cewar Araghchi, tilas ne a gudanar da shawarwari bisa daidaito da kuma kyakkyawan yanayi.

Ministan harkokin wajen kasar ya kuma bayyana cewa wasikar “mafi yawan barazana ce,” amma kuma akwai damamaki a ciki.

“Mun yi nazari sosai kan dukkan bangarorin wasikar, tare da yin la’akari da kowane daki-daki sosai,” in ji shi.

A farkon watan Maris ne Trump ya bayyana cewa ya rubuta wasika zuwa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.

A karshen watan Fabrairu, Ayatullah Khamenei, a wata ganawa da jami’an sojin sama a Tehran, ya bayyana cewa bai ga amfanin tattaunawa da Amurka saboda ba zata warware matsaloli ba.

Kalaman nasa sun zo ne sa’o’i bayan da gwamnatin ta Trump ta kakaba wa Iran takunkumai da Trump ya bayayana  da “mafi girman matsin lamba” kan Iran.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: bayyana cewa

এছাড়াও পড়ুন:

Iran da Amurka zasu ci gaba da tattaunawa a mako mai zuwa

An kammala zagayen farko na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a babban birnin Muscat a shiga tsakanin kasar Oman.

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da Steve Witkoff, manzon musamman na shugaban Amurka kan harkokin yankin gabas ta tsakiya ne suka jagoranci shawarwarin yau Asabar.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar ta ce bangarorin sun yi musayar ra’ayi game da shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya, da kuma dage takunkumi.

Ya kara da cewa an gudanar da shawarwarin ne cikin yanayi mai ma’ana kuma bisa mutunta juna.

A karshen sama da sa’o’i biyu da rabi na tattaunawar, shugabannin tawagogin Iran da na Amurka sun yi jawabi na ‘yan mintoci kadan a yayin da suke barin wurin taron a gaban ministan harkokin wajen Omani,” in ji ma’aikatar.

Bangarorin kuma zasu sake tattaunawa nan da mako mai zuwa, saidai ba’a bayyana takaimaimai wajen da tattauanwar za ta wakana ba.

A gefen tattaunawar, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmaeil Baghaei ya shaidawa kafar yada labarai ta IRIB a birnin Muscat cewa, Iran na da manufa guda daya tabbatar da muradun kasa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran da Amurka zasu ci gaba da tattaunawa a mako mai zuwa
  •  A Yau Asabar Ne Ake Bude Tattaunawa A Kasar Oman Akan Shirin Makamashin Nukiliyar Iran
  •  Limamin Tehran: Iran Ba Ta Tsoron Tattaunawa
  • Iran: Akwai damammaki na diflomasiyya da za mu jarraba aniyar Amurka a kansu
  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Zayyana Wa Masu Zuba Jari Na Faransa Irin Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Nijeriya
  • Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (2): Kyawawan Dabi’u Ke Fayyace Tsoron Allah A Musulunci
  • Netanytahu Ya Fusta Da Furucin Kasar Canada Akan Kisan Kiyashi A Gaza
  • Za a mayar da tubabbun ’Yan Boko Haram cikin al’umma – Gwamna Buni
  • Ministan harkokin wajen Iran ya tattauna da takwaransa na Masar kan halin da ake ciki a yankin
  • Trump ya janye harajin da ya kara wa duniya, amma ya laftawa China 125%