2025-02-20@09:11:15 GMT
إجمالي نتائج البحث: 83

«bayyana cewa»:

    Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof ya bayyana cewa falasdinawa masu kasa ne zasu fayyace makomar kasarsu, don haka shirin da wasu manya-manyan kasashen duniya suke dashi a kan makomar Falasdinu da Falasdinawa ba dai-dai bane kuma zamu yi yaki da shi. Tashar talabijan ta Presstv a nan Teran ta nakalto shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammada Bakir Qolibft yana fadar haka a taron shuwagabannin majalisun dokoki na kasashen Asia a birnin Baku na kasar Azaibaijan. Qolibof ya kuma kara da cewa shirin shugaban kasar Amurka yake yi na kwace gaza da kuma inda za’a maida Falasdinawa ba zai kai ga nasara ba. Qalibof ya yi allawadai wadai da shugaba Trump kan shishigin da yake yi a cikin...
    Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali Khamnei wanda ya gana da sarkin Katar  a jiya Laraba ya bayyana cewa; Siyasar Iran ta ginu ne akan kyautata alaka da kasashen makwabta, kuma tuni an cimma sabbin matakai a wannan fagen. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma fada wa sarkin na Katar Tamim Bin Hamad ali-Sani cewa, ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci yana fadi tashi a wannan fagen na kyautata alaka da kasashen makwabta, tare da yin kira da cewa yarjeniyoyin da aka kulla su zama masu kare maslahar kasashen biyu. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana kasar Katar a matsayin kasa abokiya, kuma ‘yar’uwa ta Iran, duk da cewa har  yanzu da akwai wasu batutuwa da ba a...
    Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan zanga-zangar yunwa, ya gano cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum bakwai suka samu munanan raunuka. Rahoton ya kuma bayyana cewa an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11, sakamakon ƙone-ƙone, sace-sace, da lalata kadarorin gwamnati da na ’yan kasuwa a faɗin jihar. Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram Da yake jawabi a taron majalisar zartaswar ta jihar karo na 25 a ranar Talata, Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi rahoton daga shugaban hannun kwamitin, Mai shari’a Lawan Wada (ritaya). Ya tabbatar da cewa za a fitar...
    Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan zanga-zangar yunwa, ya gano cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum bakwai suka samu munanan raunuka. Rahoton ya kuma bayyana cewa an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11, sakamakon ƙone-ƙone, sace-sace, da lalata kadarorin gwamnati da na ’yan kasuwa a faɗin jihar. Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram Da yake jawabi a taron majalisar zartaswar ta jihar karo na 25 a ranar Talata, Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi rahoton daga shugaban hannun kwamitin, Mai shari’a Lawan Wada (ritaya). Ya tabbatar da cewa za a fitar...
    Aƙalla mutum 11 sun shaƙi iskar ’yanci bayan kuɓuta daga hannun ƙungiyar mayaƙan Boko Haram masu iƙirarin jihadi a Jihar Borno. Waɗanda suka shaƙi iskar ’yancin na daga cikin mutanen da ƙungiyar Boko Haram ta sace a wani wurin kamun kifi a Doron Baga. Majalisar Edo ta tanadi hukuncin kisa kan masu garkuwa da mutane USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram Wata majiya ta bayyana cewa, wani kwamandan ’yan ta’addan mai suna Tar ne ya jagoranci garkuwa da mutanen ne a ranar 13 ga watan Fabrairu 2025. Tar da tawagarsa da ke addabar masunta da manoma a gaɓar Tafkin Chadi sun ɗauke mutanen ne yayin da suka afka wa al’ummar Shawaram da ke ƙarƙashin Ƙaramar...
    Kakakin ma’aikatan shari’a a kasar Iran ya bayyana cewa jami’an tsaro na kasar Iran sun kama mutane biyu yan kasar Burtaniya tare da tuhumar aikin liken asiri a lardin Kerman na kasa. Kamfanin dillancin labaran (IP) na kasar Iran ya bayyana cewa mutanen biyu suna tafiye-tafiye zuwa lardunan kasar Iran suna tattara bayanai a cikin watan Jeneru na wannan shekarar a lokacinda suka fada hannun Jami’an tsaron kasar. Labaran sun kara da cewa mutanen biyu sun sauya kamamnci, zuwa kamar masu yawon bude ido suna tsammanin cewa ba za’a ganesu ba. Kakakin ma’aikatar Shari’ar ya bayyana cewa ma’aikatan liken asirin kasashen turai da dama sun fi aiki ne a bangaren karatu a makarantun kasar Iran. Asghar Jahangir ya bayyana cewa...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci A nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya gana da shuwagabannin kungiyar Jihadul Islami na kasar Falasdinu da aka mamaye a jiya Talata. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Ziyad Nakhalah shugaban kungiyar ne ya jagoranci tawagar kungiyar zuwa ganawa da jagoran. Labarin ya nakalto Jagoran juyin juya halin musulunci ya fadar cewa a halin yanzu babu wani abunda HKI zata yi a gaza sai idan kungiyoyi masu gwagwarmaya suna sun abin ya faru, saboda kekkyawar riko da suka yiwa yankin. Imam Seyyed Ali Khamenei, ya yabawa kungiyoyin falasdinawa kan hadin kai da suka nuna a yankin da ya gabata. Ziyad al-Nakhalah, babban sakataren kungiyar Jihad Islami,   ya bayyana cewa sun...
    Gwamnatin tarayya ta ce ta bai wa gwamnatin jihar Jigawa tallafin kayayyakin noma na sama da naira biliyan 5 domin bunkasa noman abinci a fadin jihar.     Ministan noma da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a garin Dabi da ke karamar hukumar Ringim a bikin ranar manoman alkama ta bana.   Ya bayyana cewa, matakin na daga cikin kudirin gwamnatin tarayya na tallafawa jihar wajen bunkasa noma domin kasuwanci.   Sanata Kyari ya yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya ta gamsu sosai da yadda gwamnatin jihar Jigawa da manoma suka yi, na rungumar ayyukan noman rani. Ministan ya yaba da kokarin gwamnatin jihar Jigawa da manoma,...
    Kasar Sin na maraba da duk kokarin da ake yi cikin lumana don warware rikicin kasar Ukraine, ciki har da tattaunawa tsakanin Amurka da Rasha, kuma Sin na fatan dukkan bangarori da masu ruwa da tsaki za su shiga cikin shawarwarin samar da zaman lafiya in lokaci yayi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na yau Talata, yana mai cewa, ko da yaushe kasar Sin tana da yakinin cewa, tattaunawa da yin shawarwari, ita ce hanya daya tilo da za a iya warware rikicin, kuma ta himmatu wajen inganta shawarwari don samar da zaman lafiya. Ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga wata tambaya game da ganawar da jami’an...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Barazanar makiya a kan kasar Iran da al’ummarta ba ta yi nasara ba Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa: Gagarumar zanga-zamga da al’ummar Iran suka gudanar a ranar 22 ga watan Bahman ta tabbatar da cewa barazanar makiya a kan Iran da al’ummarta ba ta cimma nasara ko yin tasiri ba. Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayin da yake karbar bakwancin dubban mutane daga lardin gabashin Azarbaijan a Husainiyar Imam Khumaini da ke Tehran fadar mulkin kasar a ranar Litinin din da ta gabata, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan zagayowar bore mai tarihi na al’ummar Tabriz a ranar 29 ga watan...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Iran tana taka rawa ta musamman wajen wanzar da kwanciyar hankali da tsaron yankin Tekun Pasha Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta hanyar mallakar mafi yawan layukan kan iyaka da tekun Pasha da kuma iko da mashigar Hormuz, ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da kwanciyar hankali da tsaron wannan ruwa da yankunan makwabtanta. Abbas Araqchi ya bayyana hakan ne a yayin taron tarihin huldar kasashen waje na Iran karo na 8, mai taken “Manufar harkokin wajen Iran da gabar tekun Pasha a cikin mahallin tarihi,” wanda aka gudanar a safiyar yau Talata a cibiyar nazarin siyasa da kasa da kasa na ma’aikatar harkokin...
    Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan ta’addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan Zirin Gaza, wanda ya shafe tsawon watanni 15 kafin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni a watan Janairun da ya gabata. A cewar jaridar, sojoji 15,000 da ke cikin sojojin mamayar Isra’ila suka jikkata tun farkon yakin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, yayin da wasu 846 suka sheka lahira. Daga cikin wadanda...
    Ana fargabar cewa gobara ta yi ajalin wata uwa da ’ya’yanta biyu a yankin Onipakala da ke Ƙaramar Hukumar Ondo West a Jihar Ondo. Bayanai sun ce musibar ta auku ne da tsakar daren Lahadi yayin da jama’a ke sharar barci, lamarin da ya jefa makwabta cikin zullumi. Saudiyya ta bai wa Kano da Abuja tallafin dabino albarkacin watan Ramadana Mutum biyu sun shiga hannu kan yi wa ’yar shekara 12 fyaɗe a Yobe Aminiya ta ruwaito cewa, zuwa wayewar gari Litinin, matar da ’ya’yanta —Bukola da Ifeoluwa— sun ƙone ƙurmus a sakamakon gobarar. Wani maƙwabcinsu da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce tun tsakar dare gobarar ta tashi amma ana ji ana gani ta rutsa da mutanen uku...
    Gwamnatin Katsina ta kashe kimanin Naira biliyan 5.4 domin bai wa mata 3,610 tallafin kiwon awakai. Gwamna Dikko Umar Radda ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da shirin raba tallafin awakan a gundumar Dan-Nakolo da ke Ƙaramar Hukumar Daura ta jihar. Gwamnati ta kashe N5bn domin bai wa mata tallafin kiwon awakai a Katsina NAJERIYA A YAU: Dalilan Saukar Farashin Kayan Masarufi A Kaswanni Ya bayyana cewa, a ƙarƙashin shirin, an raba wa mata 3,610 awakai huɗu-huɗu a gundumomi 361 da ke faɗin jihar. Gwamnan ya bayyana cewa wannan shiri wani ginishiki ne na bunƙasa harkokin noma da kiwo wanda yake da burin ganin Katsina ta zama ja gaba a fannin dogaro da kai a Arewacin Nijeriya da ma...
    Kungiyoyin Hamas, Jihad Isalami da kuma sauransu a kasar Falasdinu da aka mamaye sun bayyana yi allawadi da HKI saboda yadda suke zazabtar da fursinonin Falasdinawa a gidan yarin Ofer, kamar yadda labari ya ke isa daga ca. Tashar talabijin ta Presstv  na takalto cewa gidan yarin ofer ya na yammacin birnin Ramallah, a yankin yamma da kogin Jordan. Kungiyoyin sun bayyana cewa, wannan shi ne halin ta’addanci da kuma kekacewar zuciya yahudawan sahyoniyya. Daga karshe kungiyoyun sun yi kara da wadanda abin ya shafa su rika sanya ido sannan su aikata abinda ya dace don kawo karshen wahalar falasdinawa a gidajen yarin Ofer.
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa kasashen Turai basa cikin tattaunawar tsagaita wuta a Ukraine. Jaridar Daily Mail ya bayyana cewa hankalin shuwagabannin kasashen turai ya tashi a lokacin da JD Vance mataimakin shugaba Trump ya fada masu cewa ba wani shugaba daga cikin shuwagabannin kasashen Turai da zasu halarci taron tsagaita wuta na Ukraine. Wannan labarin ya Eu ta kira taron gaggawa don tattauna wannan batun. Sannan Sir Keir Starmer ya kuma hanya zuwa Amurka da gaggawa. Mataimakin shugaban kuma yakadansa na musamman a kan shirin tsagaita wuta a Ukraine ya bayyanawa Ukrain kan cewa batun shigar Ukraine kungiyar tsaro da NATO bai da wani muhimmanci a wajen shugaba Trump a yanzu. Mr Vances ya bayyana hakane...
    Gwamnatin Katsina ta kashe kimanin Naira biliyan 5.4 domin bai wa mata 3,610 tallafin kiwon awakai. Gwamna Dikko Umar Radda ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da shirin raba tallafin awakan a gundumar Dan-Nakolo da ke Ƙaramar Hukumar Daura ta jihar. Ya bayyana cewa, a ƙarƙashin shirin, an raba wa mata 3,610 awakai huɗu-huɗu a gundumomi 361 da ke faɗin jihar. Gwamnan ya bayyana cewa wannan shiri wani ginishiki ne na bunƙasa harkokin noma da kiwo wanda yake da burin ganin Katsina ta zama ja gaba a fannin dogaro da kai a Arewacin Nijeriya da ma ƙasar baki ɗaya. A cewar Gwamnan, kiwon awakai yana da muhimmanci kuma ɗaya ne daga cikin muradin gwamnantinsa na bunƙasa harkokin noma da...
    Wani matashi da aka kama kan yin gunduwa-gunduwa da budurwarsa da suka haɗu a Facebook bayan ta je ɗakinsa ya bayyana dalilinsa na aikata hakan. Matashin mai shekaru 29 da ke iƙirarin malumtar addini ya amsa a wurin ’yan sanda masu bincike cewa shi ne ya yi wa gawar budurwar tasa gunduwa-gunduwa. Ya shaida musu cewa a Facebook ya haɗu da ita, inda daga bisani ta ziyarci ɗakinsa a unguwar Olunlade a garin Ilori, bayan ta je wani biki. Sai dai ya musanta zargin da ake masa na kashe ɗalibar mai suna Hafsah Yetunde Bello domin yin tsafi. Jirgin soji ya kashe fararen hula a Katsina Malaman addini sun yi wa ’yan siyasa juyin mulki —Sule Lamiɗo Ku tona asirin...
    Bishop na Cocin Katolika da ke  Kontagora, Babban Rabaran Bulus Yohanna ya gudanar da bikin aure ga ma’aurata ashirin da daya a jihar Neja. A lokacin da yake jawabi yayin bikin daurin aurea cocin St. Mark Catholic da ke Nsanji Nkoso a karamar hukumar Magama ta jihar Neja,  Bishop din ya bayyana cewa, bai kamata masoya na zama tare ba har sai coci ya tabbatar da su a matsayin ma’aurata bayan an biya sadaki da kuma bin ka’idoji. A cewar Most Reverend Bulus Yohanna “mafi yawansu sun fi dogaro da auren gargajiya wanda a baya ya basu damar zama tare. “Kuma muna bukatar mu tabbata cewa babu wani daga cikinsu da aka tilastawa”. “Dole ne mu ƙarfafa su  su...
    Gwamnatin jihar Kano, KNSG, ta ce ta tanadi hanyoyin dakile mace-macen mata masu juna biyu maimakon rage yawan mace-macen.   Kwamishinan lafiya na jihar Dr Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wajen taron hadin gwiwa na Partners Coordination Forum (PCF) da aka gudanar a Kano.   A wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta jihar Kano Ibrahim Abdullahi, ta bayyana cewa, Dakta Abubakar Labaran ya bayyana cewa gwamnati ta himmatu sosai wajen kawo sauyi a fannin kiwon lafiya a karkashin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, da niyyar ganin ba macen da ta mutu a lokacin haihuwa.   Ya yi karin haske kan gyare-gyaren da aka...
    Kungiyoyin farar hula masu yaki da zazzabin cizon sauro, rigakafi da abinci mai gina jiki (ACOMIN), reshen jihar Taraba, ta koka kan matsalar karancin kayan gwajin cutar kanjamau a jihar.   Shugaban kungiyar na jiha, Alhaji Muhammad ​​Danburam ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar wayar da kan hukumar yaki da cutar kanjamau ta Taraba (TACA), ofishin kula da magunguna masu muhimmanci, da gidauniyar REDAID Nigeria Foundation., a Jalingo.   Danburam ya bayyana cewa, wani bincike da aka yi kwanan nan a wasu cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 18 a kananan hukumomin Ardo-kola, Bali, da Takum, ya nuna cewa kayan gwajin cutar kanjamau sun kare a cibiyoyin.   “Rashin kayan gwajin zai kawo cikas ga kokarin...
    An shiga ruɗani bayan da wasu sojoji sun lakaɗa wa wasu ’yan sanda da ke bakin aiki duka a Ƙaramar Hukumar Okpe da ke Jihar Delta. Rikicin jami’an tsaron ya samo asali ne bayan ’yan sanda sun yi kamen wasu matasa da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi. ’Yan sanda sun tsare motar matasan ne a yayin wani samame, inda suka kama ɗaya daga cikinsu da loud da wiwi, bayan sauran sun tsere. Suna tsaka da tafiya da shi zuwa ofis ne suka bi ta wani shigen bincike na Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, suka umarce su da su sake shi. Bayan ’yan sandan sun ƙi amincewa suka nemi a bi ƙa’ida ba ne, rikici ya ɓarke a tsakaninsu. A...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Al’ummar Iran ba zata taba amincewa da gudanar da duk wani zaman tattaunawa karkashin matsin lamba ba Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta mayar da martani ga yarjejeniyar tsaron kasa ta shugaban kasar Amurka, tana mai jaddada cewa: Iran ta yi watsi da duk wata tattaunawa karkashin matsin lamba, tana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran bisa tsarinta na asali a ko da yaushe tana goyon bayan samar da hanyoyin diplomasiyya kan batutuwa daban-daban da suka hada da batun Shirin makamashin nukiliya, kuma tana goyon bayan warware al’amura ta hanyar diflomasiyya ciki har da batun Shirin makamashin nukiliyarta, sannan ta tabbatar da hakan a tsawon shekaru fiye da ashirin na yin riko da...
    Hukumar kula da ‘yan sama jannati na kasar Sin (CMSA), a yau Laraba, ta bayyana sunayen tufafin ‘yan sama jannati da motar zirga-zirga a duniyar wata na aikin binciken wata na kasar. CMSA ta ce, an sa ma tufafin na ‘yan sama jannati suna Wangyu, wanda ke nufin kallon duniyar sama, kuma ya yi daidai da sunan tufafin da ‘yan sama jannati su kan sa lokacin da suka fita daga tashar sararin samaniya, wato Feitian, wanda ke nufin tashi zuwa sararin samaniya. Wata Ɗalibar Kwalejin Fasaha Ta Tarayya Da Ke Bauchi Ta Rasa Ranta A Haɗarin Mota Yawan Motocin Da Sin Ta Fitar Zuwa Ketare A 2024 Ya Karu Da Kaso 23% Kazalika, sunan motar zirga-zirga a duniyar wata shi...
    “Wannan shi ne dalilin da ya sa Gwamna Dauda Lawal ya bayyana a cikin takardar yaƙin neman zabensa gabanin zaben 2023 cewa batun tsaro ne zai sa a gaba, inda ya yi alƙawarin aiwatar da matakan shawo kan lamarin. “A halin yanzu an shaida cewa Gwamna Lawal ya cika alƙawarin. “Gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta ba da fifiko kan harkokin tsaro a jihar Zamfara, kuma ta ɗauki matakin da ya dace tun farko cewa sulhu da ‘yan bindiga ba komai ba ne illa ‘je ka na yi ka’. “A cikin hirarraki da manema labarai daban-daban, gwamnan ya sake bayyana cewa gwamnatin jihar Zamfara ba za ta yo sulhu da ‘yan bindigar da ke addabar jihar ba. “Ya kamata a bayyana...
    A ci gaba da kokarinta na samun tagomashi a fannin tattalin arziki da ci gaban jihar ta hanyar kawo sauyi a harkar noma, gwamnatin jihar Jigawa na shirin hada gwiwa da wani kamfani da ke samar da dabino  da bayar da shawarwari a harkar noma, wanda ke da ofishi a Najeriya a kasar Saudiyya domin bunkasa noman dabino a jihar. Gwamna Malam Umar Namadi ne ya bayyana hakan a yayin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga daya daga cikin manyan kamfanonin noma na kasar Saudiyya, wadanda suka kware a harkar noman dabino da sarrafa gonaki, karkashin jagorancin Abdul’aziz Abdurrahman Al-Awf, wadanda suka kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati dake Dutse. Babban makasudin ziyarar ita ce tattaunawa...
    Dan Majalisar Tarayya mai Wakiltar Zangon Kataf/Jaba daga Jihar Kaduna, Honorabul Amos Gwamna Magaji ya sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulki. A safiyar Talata Shugaban Majalisar, Abbas Tajuddeen ya sanar da sauya shekar, yana mai bayyana rikicin cikin gidan PDP a mastayin dalilin ficewar dan majalisar daga jam’iyyar. Dan majalisar ya  bayyana cewa kafin ya sauya shekar sai da ya tuntubi al’ummar mazabarsa inda suka ba shi hadin kai da kuma amincewa.
    Dalibai 179 za su samu shaidar Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a yayin bikin yaye ɗalibai na Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Abba, ya bayyana cewa dalibai 4,402 ne za a yi bikin yaye su a ranar farkon, inda a za a ba su shaidar kammala Digirin farko da Difloma da sauran makamantansu. Bikin yaye ɗaliban shi ne karo na 39 da za a gudanar a jami’ar ta BUK. Bikin na kwana huɗu ya kunshi jawabai da laccoci da taruka da kuma bayar da kyaututtuka da takardun shaida a matakai daban-daban. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya? Farfesa Sagir Abbas ya bayyana cewa a rana ta biyu za a...
    Dalibai 179 za su samu shaidar Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a yayin bikin yaye ɗalibai na Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Abba, ya bayyana cewa dalibai 4,402 ne za a yi bikin yaye su a ranar farkon, inda a za a ba su shaidar kammala Digirin farko da Difloma da sauran makamantansu. Bikin yaye ɗaliban shi ne karo na 39 da za a gudanar a jami’ar ta BUK. Bikin na kwana huɗu ya kunshi jawabai da laccoci da taruka da kuma bayar da kyaututtuka da takardun shaida a matakai daban-daban. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya? Farfesa Sagir Abbas ya bayyana cewa a rana ta biyu za a...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Sirrin nasarar da Iran ta samu shine haɗin kai da kasancewar mutane a cikin kowane fagen neman ci gaba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa juyin juya halin Iran ya samu nasarar korar azzalumai daga kasar Iran ce, kuma sirrin ire-iren nasarorin da aka samu bayan nasarar juyin juya halin Musulunci shi ne kasantuwar kasa ta taka rawar al’umma da kyakkyawar hadin kai. Shugaba Pezeshkian ya kara da cewa a jawabin da ya gabatar a karshen jerin gwanon na tunawa da nasarar juyin juya halin Musulunci a birnin Tehran: Ba za su taba mika wuya ga kasashen waje ba. Ko da yake Iran bata neman yaki, amma tun ranar farko makiya suke...
    Sai dai yadda gwamnatin Trump ta sanar da rufe USAID ya ba da damar tona asirinta, kuma tabbas tarihi zai tabbatar da cewa, gaskiya na hannun wadanda ke kokarin samar da ci gaba da kiyaye hadin gwiwar cin moriyar juna da ma wadanda ke kokarin tabbatar da makomar dan Adam ta bai daya.    
    Babban hafsan hafsishin sojojin Iran Manjo Janar Muhammad Bakri ya bayyana cewa sojojin Iran a shirye suke fiye da ko wani lokaci don kare JMI daga makiyanta. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Bakiri ya bayyana haka ne a lokacinda yake tattaki na bukukuwan cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran a nan birnin Tehran a safiyar yau Litinin. Ya ce: Halin da sojojin JMI suke ciki yafi na ko wani lokacin kyau, don haka a shirye suke su gudanar da ayyukansu a duk lokacinda bukatar haka ta taso. Dangane da tattaunawa tsakanin Iran da Amurka kuma, Janar Bakiri ya bayyana cewa, jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul...
    Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya bayyana cewa sharaɗinsa na sulhu da ’yan bindiga shi ne kawai su daina kashe-kashe su zubar da makamai sannan su miƙa wuya. A baya dai Gwamna Dare ya sha nanata cewa ba zai yi sulhu da ’yan fashin daji ba. Gwamna Sule ya naɗa Kwamishinoni 16 a Nasarawa Atiku da Obasanjo suna ganawar sirri Ko a watan Yulin 2024, sai da wani mai magana da yawunsa, Alhaji Faruk Ahmad, ya bayyana cewa babu wani matsin lamba da zai sa gwamnatinsu ta yi sulhu da ’yan ta’addan. Ya kuma jaddada cewa mataki ɗaya da gwamnatin ta ɗauka wanda kuma yana haifar da ɗa mai ido shi ne yaƙar ’yan bindigar amma babu batun sulhu. Sai...
    Wasu ’yan daba sun gine-ginen makaranta a yankin Okpoga da ke Karamar Hukumar Okpogwu da ke Jihar. Ɓata-garin sun ƙona gine-ginen ne a Makarantar Sakandaren Central UBE da ke Ogwu-Okpoga da kuma Makarantar Ƙaramar Sakandare s ake Obossa. Wani shaida ya bayyana wa wakilinmu cewa a makon da ya gabata ne ’yan daban suka yi wannan aika-aika. Shaidan wanda bai amince a bayyana sunansa ba, ya yi zargin wata manufar siyasa ce ta sa ’yan daban suka cinna wa gine-ginen wuta. Ya bayyana damuwa kan yawaitar irin wannan aika-aika a ’yan kwanakin nan. Kokarinmu ma ji daga kakakin ’yan sanda ta Jihar Binuwai, Catherine Aneneh, bai yi nasara ba, saboda mun kira ta a waya ba ta shiga ba. ’Yan...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Kano. Nadin na kunshe cikin wata sanarwar da Kakakin Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafukansa na sada zumunta a yammacin ranar Asabar 08, ga Febarairun 2025. Dalilan Da Suka Sa Gwamnan Kano Sallamar SSG Da Wasu Kwamishinoni 5 Gwamnan Kano Ya Karyata Jita-jitar Rikicinsa Da Sakataren Gwamnatin Jihar Nadin Na Ibrahim zai fara aiki ne daga ranar Litinin mai zuwa 10, ga Febarairun 2025. Sanarwar nadin ta bayyana cewa an zabi, Ibrahim a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Jihar saboda shafe sama da shekaru talatin ya na aikin gwamnati da tarin kwarewar aiki da yake da ita a hukumomi da ma’aikatu daban-daban...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Kano. Nadin na kunshe cikin wata sanarwar da Kakakin Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafukansa na sada zumunta a yammacin ranar Asabar 08, ga Febarairun 2025. Dalilan Da Suka Sa Gwamnan Kano Sallamar SSG Da Wasu Kwamishinoni 5 Gwamnan Kano Ya Karyata Jita-jitar Rikicinsa Da Sakataren Gwamnatin Jihar Nadin Na Ibrahim zai fara aiki ne daga ranar Litinin mai zuwa 10, ga Febarairun 2025. Sanarwar nadin ta bayyana cewa an zabi, Ibrahim a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Jihar saboda shafe sama da shekaru talatin ya na aikin gwamnati da tarin kwarewar aiki da yake da ita a hukumomi da ma’aikatu daban-daban...
    A gasar Serie A 14:03 – Joao Felix (Chelsea – AC Milan) aro   Premier League 01:00 – Adel Disasi (Chelsea – Aston Billa) aro- 00:25 – Marshall Munetsi (Reims – Wolbes) ba a fayyace kudin ba. 00:15 – Carlos Alcaraz (Flamengo – Eberton) aro- 00:00 – Nasser Djiga (Red Star Belgrade – Wolbes) ba a fayyace kudin ba. 23:15 – Ben Chilwell (Chelsea – Crystal Palace) aro- 23:10 – Mathys Tel (Bayern Munich – Tottenham) aro – 23:00 – Nico Gonzalez (Porto – Manchester City) £50m 22:50 – Eli Junior Kroupi (FC Lorient – Bournemouth) ba a fayyace kudin ba. 21:32 – Somto Boniface (Chelsea – Ipswich) ba a fayyace kudin ba. 21:32 – Aled Palmer (West Brom –...
     Wanda ya jagoranci sallar juma’a a yau anan birnin Tehran, Hajjatul-Islam Kazim Saddiki, ya bayyana cewa: Trump yana yin baraza da tsoratarwa da cewa zai rage karfin da Iran take da shi a fagen fasahar Nukiliya da kuma matsayin da take da shi a cikin wannan yankin na yammacin Asiya, sai dai kuma ya kamata ya fahimci cewa kamar yadda shugaban da ya gabace shi ya yi kuskuren lissafi, to shi ma haka yake yi.” Limamin na Tehran ya kuma ce,Kamar yadda shugaban Amurka da ya gabaci Trump bai sami nasara akan Iran ba, shi ma haka ba zai cimma manufarsa ba. Hajjtul-Islam Siddiki ya kuma kara da cewa; Bai kamata ace muna  kallon cewa ta hanyar abubuwa na zahiri...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya ya bayyana cewa juyin juya halin musulunci  a nan Iran ya zo ne da sakon zaman lafiya ga dukkan kasashen duniuya, don haka ne ta haramtawa kanta mallakan makaman nukliya wanda yake kissan kare dangi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Alhamis a taron da jakadun kasashen waje da manya-manya baki suka halatta a gidan shugaban kasa a nan Tehran. Sai dai shugaban ya kara da cewa kissan kananan yara baa bin amincewa ne a garemu, Sannan ya ce JMI bata amince da samuwar yan ta’adda a ko ina ba, kuma kasar Iran tana daga cikin kasashe wadanda suka fi cutuwa da ayyukan ta’addanci a duniya....
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Jigawa ta ce ta mikawa hukumar alhazai ta kasa NAHCON kudaden aikin hajjin maniyyatan jihar  na shekarar 2025 kimanin naira biliyan 4.5. Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar. Ya ce hukumar ta aika wa NAHCON Naira Biliyan Huda da Miliyan Dari Biyar da Ashirin (4.520), a yayin da take sa ran za ta kara biyan wasu kudaden kafin cikar wa’adin da NAHCON din ta bayar. Ya bayyana cewa hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta baiwa jihar kujeru 1,809. A cewarsa, tuni hukumar ta raba kashi 40 cikin 100 ga kananan hukumomin jihar domin gudanar da aikin hajjin bana. Don...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa : Gabadayen Falastinu tun daga kogi har zuwa teku ta al’ummar Falasdinawa ce. Jagoran ya jaddada goyon bayan Iran ne ga gwagwarmayar Falasdinawa kan kasarsu mai dimbin tarihi, tun daga kogin Jordan zuwa tekun Bahar Rum, kamar shafin offishin jagoran ya sanar. Kallaman Jagoran na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da wata shawara mai cike da cece-kuce na kaurar da Falasdinawa daga zirin Gaza da kuma sanya Amurka ta karbe yankin da yaki ya lalata. Ta hanyar yada wannan sako a cikin harsuna da dama, Iran ta nanata kudurinta na tabbatar da Falasdinu. Shugaba Trump na Amurka ya tsaya...
    An kama wani ɗalibin firamare mai shekara 13 ɗauke da bindiga a makaranta, inda yake barazanar harbe abokan karatunsa da ita. Bayan nan ne jami’an tsaro suka yi nasarar kama shi a Makarantar Firamare ta St. Paul da ke ƙauyen Ikot Ibiok a Ƙaramar Hukumar Eket a Jihar Akwa Ibom. A safiyar Alhamis ne kakakin runduanr ’yan sandan jihar, DSP Timfon John, ta sanar da kama yaron. DSP Timfon John ta bayyana cewa, a yayin bincike sun gano cewa yaron ya shafe kimanin wata uku yana zuwa da bindigar makaranta. An kashe wa ma’aurata ’ya’yansu uku an ɓoye gawarsu a firinji Zargin Tinubu: Gaskiya Naja’atu ta fada kan Nuhu Ribadu —El-Rufai NAJERIYA A YAU: Tasirin Yankan Angurya A Rayuwar Mata...
    Kasashen larabawa masu kawance da Amurka sun kasance a sahun gaba wajen mayarwa da shugaban kasar Amurkan martani, bayan da ya bayyana cewa kasarsa za ta shimfida ikonta a Gaza, bayan fitar da Falasdinawa da Gaza. Gabanin wannan sanarwar ta  Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa ya tuntubi kasashen Jordan da Masar masu makwabtaka da Falasdinu da su karbi bakuncin mutanen Gaza na wani lokaci har zuwa sa’adda za a gyara wajen. Masar da Jordan sun yi watsi da wannan shirin da suke dauka a matsayin wata dabara ce ta fitar da Falasdinawa daga cikin kasarsu, da maye gurbinsu da yahudawa ‘yan share wuri zauna. A wani bayani da kungiyar hadin kan Larabawa ta fitar ta bayyana cewa; Abinda  Trump...
    Gwamnatin jihar Neja ta karbi yara ashirin da daya da aka kama a kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar yayin da ake safarar su zuwa Sudan.   Mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Yakubu Garba wanda ya bayyana haka a lokacin da yake karbar yaran a madadin gwamnatin jihar Neja a Minna, ya ce an kama yaran ne a cikin kasashen Kamaru da Mali da Jamhuriyar Nijar da kuma Sudan.   Kwamared Yakubu Garba ya bayyana cewa yaran da aka ceto ‘yan karamar hukumar Magama ne a jihar Neja, amma ya yaba da kokarin gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da kuma hukumar fataucin bil’adama bisa nasarar ceto yaran.   Ya ci gaba da cewa ta’addancin ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya...
    Mataimakin shugaban kasar Iran kan al-amuran na Musamman Muhammad Javad Zareef  ya bayyana cewa tattaunawa kadai da Amurka, ba zai warware matsalolin Iran ba. Kamfanin dillancin labarum IP na kasar Iran ya nakalto Zareef ya na fadar haka a taron majalisar ministocin da aka gudanar a jiya Laraba  a nan Tehran. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iram ya kuma nakalto mataimakin shugaban kasar yana cewa, maslahar daga Amurka Itace ta dagewa takunkuman tattalin arziki. Wasu masana dadama, sun bayyana cewa idan trump ya na son tattaunawa da Iran to da dole ne ta farko Amurka ta dorawa iran sannan a yi maganar tattaunawa. A jiya ne shugaban Trump ya bayyana anniyarsa ta shiga tattaunawa da kasar Iran yana kuma...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Tsananta matsin lamba da ake son dauka kan Iran ba zai yi wani tasiri ba Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Manufar matsin lamba da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka kan Iran za ta sake yin kasa a gwiwa tare da rashin nasara. Araqchi ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar bayan kammala zaman majalisar ministocin a yau Laraba, inda ya ce mafi girman matsin lamba shi ne gwajin da aka yi kan kasar Iran da bai yi nasara ba, ya kara da cewa; Idan babban batu shi ne cewa Iran ba ta kama hanyar mallakar makamin nukiliya ba, to hakan na iya yiwuwa kuma babu...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran za ta mayar da martani ga duk wata barazana ko matsin lamba gwargwadon tsayin dakarta Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Iran ta sha tabbatar da cewa a shirye take ta gudanar da huldar siyasa da diflomasiyya don tabbatar da moriyar kasa, kuma tana shirye ta gudanar da kumajin siyasa da diflomasiyya wajen kare muradunta da tsaron kasa, sannan tana da azamar daukan duk wani matakin kare kanta da masalaharta tare da mayar da martani ga duk wata barazana ko matsin lamba gwargwadon tsayin daka da gwagwarmayarta. Isma’il Baqa’i ya bayyana haka ne a yayin da yake mayar da martani ga tambayar cewa; Maganganun da shugaban...
    Sojojin Sudan sun kwace iko da birnin Al-Kamlin da ke jihar Aljazira a tsakiyar kasar Rundunar sojin Sudan ta sanar a yau jiya Talata cewa: Sojojinta da mayakan da suke goya musu baya sun kwace iko da birnin Al-Kamlin da ke jihar Aljazira a tsakiyar kasar, kuma babban hafsan hafsoshin rundunar sojin kasar Janar Abdul-Fattah Al-Burhan ya yi alkawarin samun nasara a nan kusa kadan kan wadanda ya kira ‘yan tawaye. Sojojin Sudan sun watsa labarin ta hanyar kafofin Facebook da Instagram tare da wallafa faifan bidiyon yadda al’ummar birnin suka fito kan tituna suna bayyana murnarsu da ‘yantar da birninsu daga hannun ‘yan tawaye tare da bayyana wannan nasara a matsayin babban ci gaba ga sojojin Sudan. A nasa...
    Wata gobara da ta tashi a wata makarantar tsangaya da ke Ƙaramar Hukumar Kaura-Namoda a Jihar Zamfara, ta yi ajalin almajirai 17. Dukkanin almajiran sun ƙone ƙurmus, ta yadda ba a gane kowa a cikinsu ba. Saura ƙiris Bello Turji ya zo hannu – Ministan Tsaro Tinubu ya ƙara kasafin kuɗin 2025 zuwa N54.2trn Shaidu sun bayyana cewa gobarar ta farq ne cikin daren ranar Talata, kuma ta ɗauki kimanin sa’o’i uku tana ci. Rahotanni sun bayyana cewar wasu almajirai 16 sun samu munanan raunuka a gobarar. Wani mazaunin yankin, Abdulrasaq Bello Kaura, ya bayyana cewa gobarar ta fara ne sakamakon kamawar wasu itatuwa da aka ajiye. Wani ganau ya shaida cewar, “Abin ya faru ne a makarantar Malam Ghali,...
    Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya bayyana cewa sun kusa da kama ƙasurgumin ɗan ta’addan nan da ya addabi yankin Arewa Maso Yamma, Bello Turji. Ministan ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya tana da tabbacin cewa matsalar tsaro za ta zama tarihi kafin ƙarshen shekarar 2025. Sarkin Jiwa a Abuja ya yi rashin mahaifiya  Tinubu ya ƙara kasafin kuɗin 2025 zuwa N54.2trn “Shugaban ƙasa na cewa yaushe matsalar tsaro za ta ƙare, saboda lokacin da ya kamata ta ƙare ya yi. “A wani zama da muka yi da shi da shugabannin hafsoshin tsaron, an tattauna sosai, kuma shugaban ya ce su faɗa masa yaushe matsalar za ta ƙare, suka ce da yardar Allah zuwa ƙarshen shekarar nan,” in ji shi....
    Shugaban Majalisar Wakilai Dr Abbas Tajuddeen, ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar fitaccen dan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, Alhaji Bala Abdulwahab da ke Zariya, wanda aka fi sani da Albabello. A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Malam Musa Abdullahi Krishi ya fitar, Dakta Abbas Tajuddeen, ya ce masarautar Zazzau da jihar Kaduna sun yi rashin babban dan kasuwa wanda ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen yi wa al’umma hidima. Shugaban majalisar ya jaddada cewa, Albabello, ta hanyar sahihancinsa na kasuwanci, ya samar da ayyukan yi ga dubban jama’a a Zariya da ma fadin kasar nan, ta hanyar amfani da rassan kamfaninsa daban-daban. Ya ci gaba da cewa Albabello, ya kuma...
    Kungiyar Hamas wacce take iko da yanin zirin gaza ta bada sanarwan cewa a shirye take, masu shiga tsakanin, wato kasar Masar ta fara tattaunawa marhala ta biyu na tattaunawar tsagaita wuta a Gaza. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin laran AFP na kasar Faransa yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, wani jami’in kungiyar wanda baya son a bayyana sunansa ya ce kungiyar a shirye take a fara tattaunawar.. A wannan tattaunawa dai ana saran za’a fayyace filla-filla kan yadda al-amura zasu kasance a nan gaba a zirin gaza. Labarin ya kara da cewa jami’an Hamas sun bayyana haka ne a ranar da aka yi musayar fursinoni da HKI a garin Khan Yunus....
    Babban kwamnandan dakarun kare juyin juya halin Musuluncin na Iran ya jaddada cewa: Makamai masu linzamin Iran za su iya kai hari kan kowane makiyi Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Husaini Salami ya tabbatar da cewa: Makamai masu linzami na Iran suna da karfin kai hari kan duk wani wuri da ke da alaka da makiya a yankin da kuma fatattakar makamai masu linzami, yana mai jaddada cewa; sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci suna da karfin kalubalantar makiya a kowane lokaci. Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musuluncin ya gabatar da jawabi ne a wajen bikin “Malik Ashtar” karo na 14 a safiyar yau Litinin, inda ya ce...
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana cewa: Iran tana goyon bayan duk wata gwamnati da ke da goyon bayan al’ummar Siriya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Isma’il Baqa’i ya tabbatar a yau Litinin, a taron manema labarai na mako-mako cewa: Iran tana goyon bayan duk wata gwamnati da ke samun goyon bayan al’ummar Siriya. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya gudanar ya amsa tambayoyin ‘yan jaridu dangane da batutuwan da suka shafi shiyya-shiyya da na kasa da kasa da kuma huldar diflomasiyyar Iran. Baqa’i ya tabo batun ziyarar da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya kai zuwa kasar Qatar, inda ya bayyana cewa ziyarar ta zo ne bisa tsarin alakar diflomasiyya ta al’ada tsakanin kasashen biyu....
    Jakadan kasar Iran a Pakisatan ya bayyana bukatar shuwagabannin kasashen biyu su kara yawan musayar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, zuwa dalar Amurka biliyon $10. Tashar talabijian ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Reza Amiri Moghadam yana fadar haka a wani taro da aka gudanar tsakanin Jami’an kasashen biyu a cibiyar kasuwanci ta Rawalpindi a kasar ta Pakistan. Ya kuma ce dole ne shuwagabannin kasashen biyu tsara yadda hakan zai kasance. Muqaddam ya kuma kara da cewa gwamnatocin kasashen biyu suna da dangantaka ta hanyoyi da dama, wadanda suka hada da kasuwanci, al-adu, addini da tsaro da sauransi. Cibiyar kasuwanci da kuma kamfanoni a kasar Pakistan yana daga cikin cibiyoyin kasuwanci mafi girma a kasar ta Pakistan. Daga karshe Jakadan...
    Jakadiyar MDD na musamman kan al-amuran Falasdinawa, ta bada sanarwan cewa HKI ta fadada aikin kissan kare dangi da take yi a Gaza zuwa dukkan kasar Falisdinu, ta kuma kara da cewa wannan halin ya nuna cewa HKI tana son ta kara fadada kissan kiyashin zuwa garin Jenin da kuma yankin yamma da kogin Jordan gaba daya. Francesca Albanese ta bayyana haka ne a shafin ta na X, a jiya Lahadi, ta kuma yi kira ga kasashen duniya su shigo cikin al-amarin don kawo karshen kisan kare dangi da kuma rusa gidajen Falasdiwa da ta fara a yankin Jeneen. Daga karshe Jami’ar ta MDD ta bayyana cewa a halin yanzu kissan kiyashi da rushe-rudhen gidajen falasdinawa bai tsaya kan Gaza...
    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna, ta bayyana cewa sama da mahajjata 3,000 da suka yi aikin Hajjin 2023 sun karɓi ragowar kuɗinsu da ya yi saura. Mai magana da yawun hukumar, Malam Yunusa Abdullahi ne, ya bayyana hakancikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Kaduna. ’Yan sanda sun ceto mutum 23 da aka sace a Kaduna Arsenal ta yi sukuwar salla a kan Man City da ci 5 Ya ce hukumar ta karɓo kuɗaɗen daga Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON). Ya ce kowanne mahajjaci ya samu Naira 61,080. Ya kuma ce an tura wa kuowa kuɗinsa kai-tsaye zuwa asusun bakinsu. “NAHCON ta mayar da waɗannan kuɗaɗen ne saboda matsalar katsewar wutar lantarki da ta faru...
    Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin ƙara farashin wutar lantarki a watanni masu zuwa, tana mai cewa hakan ya zama dole domin samar da tsarin farashin da ya dace da kuɗin aiki, wanda zai jawo zuba hannun jari daga fannoni masu zaman kansu a ɓangaren makamashi. Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin makamashi, Olu Verheijen, ne ya bayyana hakan a taron shugabannin ƙasashen Afrika kan makamashi da aka gudanar a Dar es Salaam, Tanzaniya, inda Nijeriya ta gabatar da shirin dala biliyan 32 na faɗaɗa samar da wuta zuwa shekarar 2030. An Sace Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki 18 A Cikin Kwanaki 6 – TCN Jami’in Kenya: Fasahar Sin Na Ingiza Samar Da Wutar Lantarkin Kenya Ta ce duk da...
    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yau Lahadi cewa, kasar Sin ta nuna adawa da rashin amincewa da matakin da Amurka ta dauka na sanya karin harajin kashi 10 cikin dari kan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasar Sin, kuma za ta dauki matakan da suka dace don kare halaltattun hakkokinta da moriyarta. Kakakin ya jaddada cewa, “Kasar Sin tana tsaye kan matsayinta ba ja da baya. Babu wanda zai yi nasara a yakin cinikayya da haraji.” Yana mai cewa, karin harajin bangare daya na Amurka ya sabawa ka’idojin WTO. Kuma wannan matakin ba zai iya magance matsalolin Amurka na gida ba kuma mafi mahimmanci, ba zai amfanar da kowane bangare ba,...
    Haduwar farko shine wanda AC Milan ta yi nasara da ci 3–2 tsakaninta da Internazionale Milan a gasar Italian Football Championship a ranar 10 January, 1909.   Wanda yafi yawan jefa kwallaye: Andriy Shevchenko kwallaye 14.   Nasara mafi girma: inter Milan 0–6 Ac Milan a gasar Serie A (11 May 2001).   Dan wasan dayafi buga wasan Derbi Madonnina Paolo Maldini wasanni 56.   Haduwar da akafi jefa kwallaye Inter Milan 6-5 Ac Milan (6 Nuwamba 1949).   Dan wasan da yafi yawan kwallaye a wasa guda José Altafini kwallaye 4 (27 Maris 1960).   Dan wasa mafi shekaru daya jefa kwallo a wasan Zlatan Ibrahimović Shekaru 39 (26 Janairu 2021).   Gaba daya a tarihi, kungiyoyin biyu...
      Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta biya fiye da Mahajjata dubu uku da suka kammala aikin Hajjin shekarar 2023 kudaden da Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON) ta mayar masu.   Mai Magana da Manema Labarai na hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi, shine ya bayyana hakan sannan ya kara da cewa an turawa kowane mahajjati ya karɓi sama da naira dubu sittin da ɗaya a asusunsa bakinsa.   Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON ta bayyana cewa an mayar da kudaden ne saboda katsewar wutar lantarki a lokacin da maniyyata ke Muna, wanda ya shafi tsarin sanyaya iska kuma hakan ya janyo musu matsala.   Hukumar Alhazai na Jihar Kaduna ta ta yaba da hakurin wadanda har yanzun basu same...
    Ministan harkokin wajen kasar Abbas Aragchi yana bayyana matakan da sabuwar gwamnatin Amurka zata dauka idan har tana son sake samun yardar samun yardar kasar Iran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a lokacinda yake hira ta musamman da tashar talabijin ta Al-jazeera ta kasar Qatar a birnin Doga. Ministan ya kara da cewa gwamnatocin Amurka da suka shude daga ciki har da gwamnatin Trumps suka yi a baya musamman ficewarta su daga yarjeniyar JCPOA.  Abbas Argchi ya bayyana cewa abu mafi muhimmanci wanda dole ne Amurka ta yi idan tana son jawo hankalin iran dangane da tattaunawa da ita shi ne sako kudaden ta masu yawa wadanda ta hana a yi amfani...
    Sojojin kasar Iran sun nuna karfinsu a yankin Asiya ta kudu tare da itisayen da ta yi ta gudanarwa a cikin yan makonnin da suka gabata. Tare da nuna iya diblomasiyyar kasar tare da sauran kasashen yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rear Admiral Habibollah Sayyari mataimakin shugaban rundunar sojiji na kasar yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, iya diblomasiyyar kasar Iran a tsakanin  kasashen yankin, ya tabbatar da karfin da kasar take da shi a fagen karfin soje. Kuma ta tabbatar da cewa zata iya kula da al-amuran tsarom da kuma tabbata shi a yankin. Sayyari yace an gudanar da atisayen na sojoji kimani rundunonin fiya da 100 inda suka yi musayar tunani...
    A wani bayani da kungiyar ta Hizbullah ta fitar ta bayyana alhininta na shahadar babban hafsan mayakan rundunar “Kassam” ta kungiyar Hamas Muhammad Dhaif  tare da wasu abokan aikinsa, tare da bayyana rawar da  suka taka a fagen gwagwarmaya. Kungiyar ta Hizbullaha ta mika sakon ta’aziyya da kuma barka akan shhadar Muhammad Dhaif ga kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas da sauran kungiyoyin Falasdinawa da kuma al’ummar Falasdinu. Haka nan kuma kungiyar ta Hizbullah ta mika sakon ta’aziyyar ga iyalan shahidan. Kungiyar gwgawarmayar musuluncin ta Lebanon ta kuma ambaci cewa, Muhammad Dhaif ya tafiyar da dukkanin rayuwarsa ne wajen fada da ‘yan sahayoniya da kwankwasar kansu, musamman ma dai a yayin farmakin Aksa, da ya kasance daya daga cikin fitattun wadanda...
    An bayyana dangantakar cinikayya tsakanin kasar Sin da Afrika a matsayin wadda ta taimaka wajen gaggauta ci gaba da samar da irin zamanantarwar da nahiyar ke bukata domin ta kasance cikin takara a duniya. Muya Guo, shugabar sashen Sin a bankin Stanbic na Kenya ne ta bayyana haka yayin wata hira a Nairobin Kenya, inda ta ce dangantakar cinikayya tsakanin Sin da Afrika tare da jarin da kasar ta nahiyar Asiya ke zubawa, sun dora nahiyar kan tafarkin samun ci gaba, yayin da ta zamanantar da muhimman bangarori kamar na kere-keren kayayyaki. ‘Yan Adawa Sun Caccaki Buhari Kan Kalamunsa Na Cewa, ‘Allah Ne Kadai Zai Iya Gyara Nijeriya’ Fatara Da Talauci Na Yi Wa ‘Yan Nijeriya Miliyan 13 Barazanar Fadawa...
    Masu haƙar zinare aƙalla mutum 10 sun mutu wasu da dama sun ɓace bayan zaftarewar ƙasa a kansu a wani filin haƙar ma’adinai yankin Koulikokro na ƙasar Mali. Hukumomin yankin sun bayyana cewa mata ne yawancin masu haƙar zinaren da abin ya rutsa da su mata ne, kuma an kasa ciro gawarwakinau, “saboda tsananin sarƙaƙiyar yanayin.” Gwamnatin yankin ya bayyana cewa ajali ya rutsa da su ne a ƙauyen Danga, a cikin wani rami mai ruwa da laka, wanda zaftarewar ƙasar ta binne su a ciki a ranar Laraba. Ta bayyana a shafinta na Facebook cewa “abin takaicin shi ne babu ko mutum ɗaya da ya tsira a cikin su.” Matashi ya yi lalata da ’yan firamare biyu a Zariya...
    A nata jawabin, babbar mai shari’a ta Jihar Gombe, Mai Shari’a Halima S. Mohammed, ta bayyana cewa an shigar da kararraki guda 616 wadanda suka shafi manya da kananan laifuka da kuma cin zarafi a babbar kotun jihar, daga cikinsu 555 an kammala shari’arsu, inda wadanda suka rage ba su kai 70 ba. Ta bayyana godiya ga Gwamna Yahaya bisa ba da kwangilar biliyoyin naira na gina babbar sakatariyar kotun da sauran taimako da dama. Babban Lauyan gwamnatin jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Barrister Zubairu Muhammad Umar, ya bayyana cewa gwamnatin Yahaya ta taka rawar gani wajen samun nasarorin da ma’aikatarsa ta samu a yunkurinta na ciyar da sashin shari’a gaba.
    Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya kori kwamishinoni guda biyar daga muƙamansu. Wannan ma cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Architect Samuel Jatau, ya fitar da yammacin ranar Alhamis. Ɓarayin dabobbi sun shiga hannu, an ƙwato awaki 85 a Gombe Ana biyan wasu kuɗi don kare gwamnatin Tinubu — El-Rufai Sanarwar ta bayyana cewa sauke kwamishinonin na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka, sai dai ba a bayyana dalilin korarsu ba. Sanarwar ta bayyana cewa korar kwamishinonin ba zai rasa nasaba da gudanar da aikinsu yadda ya kamata ba, musamman ganin yadda suka kwashe shekara guda wajen gudanar da ayyukansu. A cewar wata majiya, gaza yin aiki yadda ya kamata ne ya sa aka cire su daga...
    Kamfanin dillancin labaran BBC ya bayyana cewa mutane 64 ne suke cikin jirgin fasinja na kamfanin American Airline, sannan mutane 3 ne a cikin jirgin yaki mai saukar ungulu samfurin Black Hawk suka yi karo a birnin washinton a safiyar yau Alhamis. Labarin ya kara da cewa, a halin yanzu sun tashi daga kubutar da wadanda suke da rai zuwa neman gawaki kawai, tunda ana ganin da wuya a sami wani da rai a cikin fasinjojin jirgin. Ya zuwa yanzu dai an tsamo gawakin mutane 30, kuma suna ci gaba da aikin gano wasu karin gawakin. Jami’an gwamnatin kasar Amurka sun bayyana cewa jirgin fasinjar ya rabu zuwa kasha ukku sannan ya fada cikin wani ruwa mai zurfin mita 7....
    Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, ya bayyana cewa sojojin ƙasar na tunkarar ’yan tawayen M23 da suka kaɗɗammar da munanan hare-hare tare da ƙwace ikon muhimman wurare a Birnin Goma da ke gabashin ƙasar. Hare-haren mayaƙan M23 da ke samun goyon bayan ƙasar Rwanda sun kashe Gwamnan Birnin Goma, a makon jiya a yayin da dubban mutane ke gudun hijira domin tsira da rayukansu. A ranar Laraba mayaƙan M23 suka ƙwace wasu yankuna biyu a Lardin Kivu da ke gabashin ƙasar, daga hannun sojoji. A jawabinsa na ranar Laraba ta talabijin, Shugaba Tshisekedi ya zargi ƙasashen duniya kan rashin ɗaukar mataki kan lamarin, musamman hannun Rwanda a cikin lamarin, wanda ya ce katsalandan ne ga dimokuraɗiyya kuma yana...
    Jami’an Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), sun cafke Tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, bayan kai sumame a gidansa da ke Abuja. Aminiya ta tabbatar da cewa jami’an EFCC ɗauke da makamai sun isa gidansa da misalin ƙarfe 4:46 na yammacin ranar Laraba, inda suka kama shi a gaban matarsa da ’ya’yansa. Mutum 20 sun rasu a hatsarin jirgin sama a Sudan ta Kudu Jami’an tsaro sun mamaye sakatariyar PDP bayan ɓarkewar rikici Sai dai har yanzu ba su bayyana dalilin cafke shi ba. Wata majiya ta bayyana cewa an kama tare da tafiya da Farfesa Yusuf zuwa wani waje da ba a bayyana ba. Duk da cewa hukumomi ba...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce karamin yankin Gaza ya durkusar da gwamnatin Isra’ila duk da makaman da ta ke dasu da kuma cikakken goyon bayan Amurka. Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa : tsayin daka da aka fara a Iran din, ya jawo farkawar wasu al’ummar musulmi kuma durkusar da Isra’ila a Gaza da Labanon misali ne. Jagoran ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wata ganawa da jakadun kasashen musulmi a birnin Teheran, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan zagayowar ranar aiko da sakon annabta ga Manzon Allah Muhammad (SAW). Jagoran ya ce “A yau, bayanin da muke bayarwa na mulkin mallaka da girman kai yana bayyana gaba daya...
    Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja ya bayyana cewa gwamnatin jihar na hada rijistar manoma da masu rike da mukaman siyasa a cikin shirinta na inshorar lafiya domin tabbatar da ayyukan kiwon lafiya ga daukacin ‘yan kasa.   Gwamnan ya bayyana haka ne a Minna, a lokacin da ya karbi bakuncin abokan hulda na ci gaba daga kungiyar Global Alliance for Vaccine Immunisation GAVI, UNICEF da WHO da suka je jihar domin bikin rufe taron GAVI da ke tallafawa tsarin karfafa tsarin PHC a jihar Neja.   Umar Bago ya ce manoma da masu rike da mukaman siyasa da makiyaya za a yi musu rajista ta ma’aikatar makiyaya sannan ya nuna cewa duk ma’aikatan gwamnati da masu rike da...
    Kungiyar masu ruwa da tsakin masana’antu a fannin mai ta Najeriya NEITI da hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, na kokarin kwato kusan dala biliyan shida da kuma wani naira biliyan 66 da gwamnatin tarayya ke bin gwamnatin tarayya bashin.   Sakataren zartarwa na hukumar Mista Orji Ogbonnaya Orji, wanda ya bayyana haka a lokacin kare kasafin kudin 2025 a gaban kwamitin majalisar kan albarkatun man fetur.   Mista Orji Ogbonnaya, ya bayyana cewa tuni hukumar ta gabatar da dukkan rahotannin da ta ke a masana’antar hako mai ga majalisar a wani bangare na matakan tabbatar da samun nasarar kwato kudade daga hukumomin gwamnati.   Ya ce wasu daga cikin abubuwan da hukumar ta sa a...
    Sakatare Janar Na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guteres ya bayyana damuwarsa game da matakin da Shugaba Donald Trump ya dauka na dakatar da taimakon kasashen waje daga Amurka yayin da sabuwar gwamnatin Amurka ke aiwatar da sabbin manufofinta na ketare, kamar yadda mai magana da yawun Guterres ya bayyana. “Ya yi kira da a yi la’akari da halin da ake ciki don tabbatar da ci gaba da samar da muhimman ayyukan ci gaba da na jin kai ga al’ummomin da ke da rauni a duniya,” in ji Stephane Dujarric ga manema labarai. ” Ya ce akwai al’umomin da suka dogara da wannan tallafin,” inda ya kara da cewa Amurka na “daya daga cikin manyan masu ba da agaji” a duniya....
    Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Nijeriya na da wadataccen arzikin da za ta ci gaba da ɗawainiyar duk wasu tafiye-tafiyen Shugaba Bola Tinubu zuwa ƙetare. A bayan nan dai ’yan Nijeriya na ci gaba da bayyana damuwa kan yawan tafiye-tafiyen da shugaban ƙasar ke yi a kai-a kai zuwa ƙetare la’akari da tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar. Da kuɗin hayar gidana da ke Kaduna nake sayen abinci a yanzu — Buhari ’Yan sanda sun yi ƙarin haske kan barazanar harin ’yan ta’adda a Kano Ana kuma ci gaba da jefa ayar tambaya ko shin tafiye-tafiyen da shugaban ƙasar ke yi suna haifar da ɗa mai ido ta hanyar kalato wa ƙasar wata riba. Sai dai...
    Ana fargabar cewa wani mutum mai shekaru 30, Rabiu Sani, ya mutu a wani kududdufi da ke unguwar Kunture a Ƙaramar Hukumar Ungogo da ke Jihar Kano. Mai magana da yawun rundunar hukumar kwana-kwana, Saminu Yusuf Abdullahi ne ya sanar da hakan a ranar Litinin. ’Yan majalisa sun nemi cin hancin N480m kafin amincewa da kasafin jami’o’i —Bincike NAJERIYA A YAU: Dabarun Bunƙasa Kasuwanci Ta Intanet Ya bayyana cewa ofishin karɓar koken gaggawa ne ya samu kira daga wani Silas Munkhaila dangane da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa jami’ansu sun isa kududdufin inda suka tsamo gawar mutumin wanda ya je ɗebo wa mahaifinsa ruwa. Ya ƙara da cewa sun miƙa gawar mamacin a hannun mai unguwar Kunture, Uba Abdulkadir. Kazalika,...
    Ana zargin ’yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa sun ɓullo da sabon salon cin hanci inda suke tatsar jami’o’i da sauran manyan cibiyoyin ilimi na tarayya. Kafar yaɗa labarai ta Premium Times ta ruwaito cewa ’yan majalisar suna barazana ga kowane shugaban jami’a ya ba su cin hancin Naira miliyan takwas kafin sun amince da kasafin makarantarsa na shekarar 2025. Binciken ya gano cewa kwamitin manyan makarantu da na Asusun Tallafin Manyan Makarantu (TETFUND) a Majalisar Wakilai da ta Dattawa sun buƙaci kuɗaɗen ne daga shugabannin manyan makarantun kafin su amince da kasafinsu na 2025. ’Yan majalisar sun nemi kowanne daga cikin shugaban Jami’o’in Tarayya 60 da ke ƙasar nan ya ba su Naira miliyan huɗu ga kwamitin majalisar dattawa da...
    Wani magidanci mai suna Rabiu Sani mai shekaru 30 ya rasa ransa bayan ya zame cikin wani tafki a lokacin da yake diban ruwa a garin Kunture da ke karamar hukumar Ungogo.   Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif Abdullah, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Kano.   A cewarsa, hukumar ta samu kiran gaggawa daga jami’in ‘yan sanda, Silas Munkaila, inda nan take aka tura tawagar ceto zuwa wurin.   Saminu ya yi nuni da cewa, duk da kokarin da suka yi, an tabbatar da rasuwar Rabiu.   Haka zalika, wata budurwa mai suna Binta da ke fama da damuwa da tabin hankali ta rasa ranta bayan ta fada rijiya...
    Wasu jami’an MDD sunn bayyana cewa, a cikin halin da ake ciki a kudancin kasar Lebanon ba ya yuwa mutane yankin su koma gidajensu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ba bayyana cewa a yau ne wa’adin kwanaki 60 na ficewar sojojin HKI daga kudancin kasar Lebanon kamar yadda ya zo a cikin yarjeniyar da suka cimma da gwamnatin kasar Lebanon watanni biyu da suka gabata. A safiyar yau ne sojojin HKI suka kashe mutan akalla 15 sannan wasu kimani 83 suka ji rauni a lokacinda suka yi kokarinn komawa gidajensu da ke kudancin kasar Lebanon wadanda sojojin HKI suke mamaye su. Wakilin MDD na musamman a kan al-amuran kasar Lebanon Jeanine Hennis-Plasschaertand da kuma shugaban rundunar UNIFEL ta...
    Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Atisayen soji na “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Admiral Ali Reza Tangsiri ya sanar da cewa: Atisayen soji mai take “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara da burin da ake son kai wa bayan samun nasarar gwada sabbin na’urori da gudanar da ayyuka daban-daban, tare da samun nasarar gwajin kai hari kan wuraren abokan gaba. A wata hira da ya yi da manema labarai a yau Lahadi, Admiral Tangsiri ya bayyana cewa: A rana ta biyu ta atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19”...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta kasar Iran ya bayyana cewa: Atisayen sojin mai take “‘Manzon Allah Mai Girma na 19” ya bayyana ƙarfin sojojin Iran Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran, Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19” a cikin ruwan Tekun Fasha ya bayyana Alamar da ƙarfin sojojin Iran suke da shi. Mohammad Baqir Qalibaf ya bayyana haka ne a yayin zaman majalisar shawarar Musulunci a yau Lahadi: Atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19″ na sojojin ruwa da ke karkashin dakarun kare juyin juya halin Musulunci suka yi a cikin ruwan tekun Fasha, da kuma makaman tsaro da aka mika wa sojojin kasa na sojojin Iran, wanda a lokacin aka yaye shamakin...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya zayyana wani ra’ayi mai manufar tsarkake zirin Gaza. Trump na mai cewa yana son aikewa da Falasdinawa daga yankin zuwa kasashen Masar da Jordan “na dan lokaci” ko kuma “a cikin dogon lokaci”. don samun zaman lafiya. Ana dai ganin tamakar Trump na kwatanta yankin Falasdinu da “wurin rushewa nan gaba” bayan watanni 15 na yakin da Isra’ila ta kadamar kan Gaza.
۱