Aminiya:
2025-03-23@14:16:16 GMT

An ayyana zaman makoki na kwana uku bayan kashe mutum 44 a Nijar

Published: 22nd, March 2025 GMT

Gwamnatin Nijar ta ayyana zaman makoki na kwana uku bayan an kashe fararen hula 44 a kudu maso yammacin ƙasar a wani hari da “yan ta’adda” da ke da alaƙa da ƙungiyar ta’addanci ta Daesh suka kai.

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a gidan talabijin na ƙasar a ranar Juma’a.

An yi wa wata karya tiyatar ceton rai Za a hukunta ma’auratan da suka ci zarafin yarinya a kan mangwaro — Zulum

Sanarwar ta ce ‘yan ta’addan sun kashe fararen hular ne a lokacin da suka afka cikin wani masallaci a ƙauyen Fombita da ke Kokorou inda suka far wa masallata.

Ma’aikatar ta yi Allah-wadai da harin inda ta kira shi da hari na “rashin imani” tare da shan alwashin ƙara matsa ƙaimi domin yaƙi da ta’addanci a yankin.

Zaman makokin da gwamnatin ta Nijar ta sanar na awa 72 zai fara aiki ne daga ranar Asabar domin girmama waɗanda suka rasu.

Za a ɗaga tutocin Nijar rabi a faɗin ƙasar, haka kuma za a dakatar da taruka a daidai lokacin da ƙasar ke cikin makoki.

Yankin kudu maso yammacin Jamhuriyar Nijar, musamman yankunan da ke kusa da kan iyaka da Mali da Burkina Faso, na fuskantar tashe-tashen hankula a ‘yan shekarun nan, inda ƙungiyoyi irin su Daesh ke amfani da rashin zaman lafiya wajen kai munanan hare-hare kan ƙauyuka da jami’an tsaro.

Harin dai ya nuna ƙalubalen tsaro da ƙasar da ke yankin Sahel ke fuskanta, duk kuwa da ƙoƙarin da gwamnati da ƙawayenta na ƙasa da ƙasa suke yi na daƙile ayyukan tada ƙayar baya.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta ɗauki alhakin kai harin, ko da yake ma’aikatar harkokin cikin gidan ƙasar ta danganta shi da Daesh saboda kasancewar ƙungiyar a yankin.

Hukumomin ƙasar dai sun yi alƙawarin gudanar da cikakken bincike tare da ɗaukar ƙwararan matakai domin gurfanar da waɗanda suka aikata laifin a gaban kuliya.

Kashe-kashen na baya-bayan nan na ƙara yawan asarar rayukan fararen hula a Nijar, inda al’ummomi ke ci gaba da fuskantar barazanar tashe-tashen hankula.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: fararen hula Nijar

এছাড়াও পড়ুন:

Karin Sinawa Suna Son Kashe Kudi

A kwanakin baya, bankin Deutsche, banki mafi girma na kasar Jamus ya yi bayani game da yanayin kashe kudi ta kasar Sin cewa, karin Sinawa suna kara son kashe kudi. Bisa sabon rahoton da bankin ya gabatar, an ce, idan aka kwatanta da na shekarar bara, yawan masu kashe kudi na kasar Sin yana karuwa, kashi 52 cikin dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu a binciken sun ce suna son kara kashe kudi, adadin da ya kai matsayin koli a shekara daya da ta gabata. Kididdigar da gwamnatin kasar Sin ta gabatar ita ma ta shaida wannan yanayi, a farkon watanni biyu na shekarar bana, yawan kudin kayayyakin da aka sayar a kasar Sin ya kai Yuan triliyan 8 da biliyan 373 da miliyan 100, karuwar da ta zarce zaton da aka yi.

Me ya sa karin Sinawa suke son kashe kudi? Farfesa Wang Xiaosong na kwalejin ilmin tattalin arziki na jami’ar Renmin ta kasar Sin ya yi nuni da cewa, tun daga shekarar bara, tattalin arzikin Sin ya samu karuwa, kudin shiga na jama’ar kasar shi ma ya karu, lamarin da ya zama silan karuwar kudi da ake kashewa. Kana gwamnatin kasar Sin ta gabatar da jerin matakan tallafi don sa kaimi ga fadada kashe kudi a kasar.

Kasar Sin tana da mutane fiye da biliyan 1 da miliyan 400, tana daya daga cikin manyan kasuwanni na duniya. Kamfanin McKinsey ya yi hasashen cewa, ya zuwa shekarar 2030, mazaunan biranen kasar Sin za su sa kaimi ga karuwar kashe kudi ta duniya da kashi 91 cikin dari, biranen kasar Sin 700 za su samar da gudummawa ga karuwar kashe kudi na biranen duniya da dala triliyan 7, wanda ya kai kashi 30 cikin dari. Kashe kudi ya sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki, ana kara kashe kudi a kasar Sin, babu shakka za a samu sabon karfin raya tattalin arzikin duniya. (Zainab Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran ta yi Allah-wadai da harin ta’addanci da aka kai a wani masallaci a kudu maso yammacin Nijar
  • Karin Sinawa Suna Son Kashe Kudi
  • Kwana Daya Bayan Kwace Fadar Shugaban Kasa, Sojojin Sudan Sun Kwace Babban Bankin Kasar
  • An yi wa wata karya tiyatar ceton rai
  • Bam ya kashe mutum 4 da jikkata wasu a Borno
  • Jagora: Amurka Ta Kwana Da Sanin Cewa Ba  Wata Riba Da Za Ta Ci Ta Hanyar Yi Wa  Iran Barazana
  • Sojoji sun ceto mutum 84 da ’yan bindiga suka sace a Katsina
  • Hauhawar Farashi A Nijeriya Ta Ragu Zuwa 23.18 Cikin 100 A Fabrairu — NBS
  • An kori shugaban hukumar leken asiri ta cikin gidan Isra’ila