2025-04-14@20:44:46 GMT
إجمالي نتائج البحث: 184
«fararen hula»:
Rahotanni daga Nijar na cewa dakarun tsaron ƙasar sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda biyu tare da kama ‘yan bindiga 12 a yankunan Dosso da Diffa na ƙasar. Kafar watsa labarai ta ActuNiger ta ruwaito cewa a Boumba da ke yankin Dosso ne dakarun tsaron ƙasar suka yi nasarar kashe ‘yan ta’adda biyu bayan dakarun...
Wata mata mai suna Jennifer Castro ta shigar da ƙarar kamfanin jiragen sama na GOL da wata fasinja a kotu bisa wani faifan bidiyo aka wallafa da yake nuna matar ta ki barin kujerarta da ke kusa da taga saboda wani yaro da yake kuka. Matar ’yar ƙasar Brazil da ta ƙi barin kujerar...
Newcastle ta lallasa Leicester da ci 3-0 a ranar Litinin a gasar Firimiya Lig ta Kasar Ingila, wasan wanda ya kasance na 8 a jere da Leicester City ta buga ba tareda jefa kwallo a raga ba, Newcastle da Eddie Howe ke jagoranta na fatan ganin sun samu gurbi a gasar Zakarun Turai na...
Gwamnatin tarayyar Najeriya tace tana fatan samun dalar Amurka billiyon $200 a ko wace shekara, a ko wace shekara daga ayyukan sararin samani. Jaridar Premiun times ta Najeriya ta nakalto ministan kirkire-kirkira da fasahar sararin samaniya yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa kamfanonin sadarwan da suke cikin kasar kamar Starlink da DSTV. Banda...
Mata a Jihar Jigawa sun yi kira da gwamnati da kungiyoyin agaji masu zaman kansu da su samar da magungunan samun tazarar haihuwa kyauta domin inganta tsarin iyali. Matan da suka tattauna da wakilinmu a cibiyoyin kula da lafiya na Kudai da Kachi dake Dutse, a yayin bikin ranar Lafiyar Uwa ta duniya, wato “Safe...
A wannan rana a filin jirgin saman Legas, Babafemi ya ce jami’an ‘yansanda sun kama wata ‘yar asalin kasar Ghana mai shekaru 20, mai suna Parker Darren Hazekia Osei, mai shekaru 20 da haihuwa, dauke da fakiti 36 na Loud—wani nau’in tabar wiwi mai karfin gaske, a cikin wata katuwar jakar tafiya mai nauyin kilogiram...
A cewarsa, wadannan kudaden sun hada da biyan kudaden samar da kariya da na inshore da kuma sauran kudaden da ake biyan kamfanonin na waje. Ya sanar da cewa, wadanan kudaden da ake biya, na shafar ci gaban tattalun arzikin kasar, inda ya yi nuni da cewa, duk Jirgin ruwa daya da ya yi dakon...
Tun daga farkon bana zuwa yanzu, sau da dama kasar Sin ta mai da martani kan matakai na rashin adalci da kasar Amurka ta dauka, domin tana da karfin fuskantar da kalubaloli tare da kiyaye bunkasuwar tattalin arzikin kasar yadda ya kamata, sakamakon bunkasuwar manyan kasuwannin cikin kasa, da manufofin da gwamnatin kasar ta fidda...
Masu shigar da kara sun bukaci kotun da ta hana wadannan jami’an gudanarwa gudanar da taro, ko kuma jagorantar babban taron jam’iyyar na kasa, bisa hujjar cewa an kore su daga jam’iyyar NNPP. Ko da yake, alkali mai shari’a Justice MA Hassan ya yanke hukuncin cewa kotun ba ta da hurumin sauraren karar, inda ya...
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku ya kasance mai fafutukar tabbatar da hadin kan ‘yan adawa, yana mai jaddada muhimmancin hadin gwiwa wajen kayar da Tinubu a zaben 2027. A ranar 8 ga watan Maris ne ya bayyana kokarinsa na hada kan ‘yan adawa da kafa kawancen korar jam’iyyar APC. Bayan sauya shekar El-Rufa’i daga jam’iyyar...
Wannan ya hada da darajar kayayyakin da ake shigowa da su daga waje da kuma fitar da su, wanda ke nuni da irin dimbin alakar kasuwanci da ke tsakanin kasashen biyu. Kayayyakin da Nijeriya ke fitarwa a cikin gida da na waje da jirgin ruwa ya kai dala miliyan 473.6 a watan Fabrairun 2025, kadan...
A ƙalla shaguna 12 sun ƙone ƙurmus sakamakon gobarar da ta tashi da daddare a Agodi Gate, birnin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo. Lamarin ya faru ne a daren Alhamis a ginin Block A na kasuwar Siminti ta Mayegun, Araromi, kamar yadda hukumar kashe gobara ta Jihar Oyo ta tabbatar. Shugaban hukumar, Akinyemi Akinyinka,...
An gurfanar da wani mutum a gaban Kotun Majistare ta 17 a Kano bisa zargin shi da karɓar kuɗi a hannun wasu fursunoni da alƙawarin cewa zai fitar da su daga gidan yari. Ana zargin wanda ake tuhumar, Kabiru Ahmed, da karɓar jimillar kuɗi naira dubu dari shida da goma daga Abdul Mukhtar, Bilkisu Shehu...
Hukumar Kula Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta ci kamfanonin rarraba lantarki tarar naira miliyan 628 kan laifin karɓar kuɗin wuta fiye da kima daga hannun kwastomomi marasa mita. Hukumar ta kuma ba wa kamfanonin rarraba lantarkin da hakan ta shafa wa’adin ranar 15 ga watan Mayu, 2025, sun tabbatar sun biya kwastomomin da suka...
Kasar Sudan ta kai kukan HDL a gaban kotun MDD cewa ta keta dokar hana kisan kiyashi ta hanyar taimakawa dakarun kai daukin gaggawa. A jiya Alhamis kasar ta Sudan din ta bukaci kotun ta kasa da kasa dake karkashin MDD da ta ta fitar da hukunci na gaggawa na bayar da umarni ga HDL...
Jakadan Sudan a Tehran, Abdul Aziz Hassan Saleh, ya tabbatar da cewa, za a gudanar da zaman farko na kotun kasa da kasa da ke birnin Hague a yau Alhamis, domin duba korafin da Sudan ta shigar kan kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, kan rawar da take takawa a yakin da ake ci gaba da yi...
Gwamnatin Najeriya ta nuna damuwarta kan yadda masu safarar mutane ke ƙara amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen yaudarar mutane da kuma yi musu cin zarafi, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana wadda ba ta da iyaka kuma mai saurin yaɗuwa wadda ke buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa. Da yake jawabi a taron...
Adadin wadanda suka yi shahada a zirin Gaza ya karu zuwa 58 a cikin ‘yan sa’o’i da suka gabata, yayin da wasu 213 suka jikkata sakamakon kazamin harin bam da Isra’ila ta kai a yankin. Jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun kai hari kan fararen hula da gidajensu, a ci gaba da luguden wutar da...
Kasashen Mali, Nijar, da Burkina Faso sun janye jakadunsu daga kasa Algeria bayan takaddamar da ta barke tsakaninta da Mali. Kasashen uku da ke karkashin mulkin soja sun sanar da daukar wannan matakin hadin gwiwa ne bayan Mali ta zargi sojojin Algeria da harbo wani jirginta mara matuki a sararin samaniyarta a karshen watan Maris....
Wata gobara da ta ɓarke ta cinye garejin gyaran motocin kamfanin sufurin Borno Express na Gwamnatin Jihar Borno, inda ta lalata motocin bas sama da 10 masu daukar mutane 18 kowacce. Shaidu sun ce gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 12 na rana a ranar Litinin, bayan wani fashewa mai ƙarfi a harabar garejin....
A wani mataki na mayar da martani da nuna fishi, kasar Aljeriya ta yi wa jakadunta a kasashen Mali, da Nijar kiranye, tare da jinkirta aikewa da jakadanta a Burkina faso, bayan da kasashen guda uku na kawacen sahel suka dau irin wannan matakin domin goyan bayan Mali, bisa takadamar dake tsakaninta da Aljeriya biyo...
Ya kuma kara da cewa, binciken farko ya nuna cewa, da sa hannun ma’aikatan hukumar ake tafka wannan aika-aika. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jirgin da ke ɗauke da mutane sama da 200 daga Bali a ƙasar Indonesia zuwa Ostireliya, ya yi juyawar dole bayan wani fasinja ya yi yunƙurin buɗe ƙofarsa yayin da jirgin kamfanin Jetstar ke shawagi a tekun Indiya. “Mun samu wani jirgin sama ya koma Denpasar (filin jirgin sama na Bali) a daren Talata bayan...
Direba da kwandastan motar bas sun tsere domin tsira da rayukansu, inda suka bar fasinjoji a ciki yayin da wata motar bas ta BRT ta kama wuta a Maryland da ke Jihar Legas da safiyar ranar Asabar. Majiyar Channels TV da ke wajen da lamarin ya faru, ta ce motar ta taso ne daga yankin...
An ceto yara takwas da aka yi safarar su daga Jihar Taraba ta hanyar haɗin gwiwar ma’aikatar mata da ci gaban ƙananan yara ta Jihar Taraba da Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP). Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban yara ta jihar Taraba, Misis Mary Sinjen ta ce yaran da aka ceto sun fito...
Gwamna Umar Namadi ya amince da naɗin Dr. Jummai Ali Kazaure a matsayin sabuwar shugabar Kwalejin Ilimi, Shari’a da Nazarin Addinin Musulunci (JSCILS) da ke Ringim. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar. A cewarsa, kafin wannan naɗi, Dr. Jummai ta kasance malama a...
Gwamnatin Nijar ta saki kusan mutane 50 da suka hada da ministocin da aka tsare tun bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023. Baya ga tsaffin ministocin da akwai wasu sojoji da ake zarginsu da yunkurin juyin mulki a shekarar 2010 da suma aka sake su. “An sako wadannan...
Jamhuriyar Nijar ta ba da sanarwar ficewa daga Rundunar haɗin Kan Sojojin Kasashe Tafkin Chadi (MNJTF) da ke yaƙi da ta’addanci a yankin tafkin Chad. Sanarwar da aka fitar ta gidan talabijin na gwamnati kuma Reuters ta ruwaito, ta zo ne a lokacin da Nijar ke mai da hankali kan tsaron man fetur a cikin...
Nijar ta fice daga rundunar tsaro ta haɗin gwiwa da ke yaƙi da masu iƙirarin jihadi a Tafkin Chadi da ke yammacin Afirka yayin da take ƙoƙarin inganta tsaro kan albarkatun mai a cikin gida. A shekarar 2015 ce Nijeriya da Chadi da Kamaru da Nijar suka sake farfaɗo da rundunar haɗin gwiwa ta Multinational...
A shekarar 1468 wanda yake mulkin Sonni Ali Shugaban Songhai ya ci wurin da yaki.Shi ba wanda yake ya saki jikinsa bane musamman ma musulmai wadanda suke da ilimin musulunci,amma wanda ya gaje shi Askia Muhammad na daya (1) wanda ya yi mulkin kasar daga shekarar( zuwa 1493–1528)ya yi amfani ne da wadanda suka yi...
Akwai yiwuwar Barcelona za ta yi asarar maki saboda saɓa wata dokar Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) a wasan gasar La Liga wanda ta doke Osasuna. Rahotanni na cewa ƙungiyar Osasuna za ta shigar da ƙorafi kan wasan da Barcelona ta doke ta da ci 3-0, saboda zargin saɓa dokar FIFA kan amfani da...
A ranar Juma’a kasuwar ta rufe a cikin makon makon inda masu zuba hannun jarin, suka yi asarar Naira biliyan 166.43. Duk a cikin makon, saye da sayawar da aka yi ta shiyar ta kai ta jimlar Naira biliyan 3.281 da kuma wata shiyar ta Naira biliyan 63.517, duk a cikin hada-hada guda 60,782 da...
Aƙalla mutum 24 ne suka rasu a wata gobarar daji mai muni da ta auku a tarihin Koriya ta Kudu baya ga mummunar ɓarna da ta haddasa. Mukaddashin shugaban ƙasar ya sanar a ranar Laraba cewa wutar dajin ta rabu kashi daban-daban har fiye da goma tun ƙarshen mako, inda ta laƙume wasu yankunan kudu...
Wani rahoto da aka fitar yau Talata, yayin zaman taron shekara-shekara na shekarar 2025, na dandalin tattaunawa na Asiya na Boao, ya nuna yadda kasar Sin ke ci gaba da kasancewa cibiyar rarraba hajojin da masana’antu ke sarrafawa. Rahoton mai taken “Nazarin tattalin arzikin Asiya, da hadadden rahoton ci gaba na shekarar”, ya nuna yadda...
Ba wannan tarihi na kanfar iko da ayarin farko na “yan majalisun wannan kasa ke da shi ne abin kallo ko la’akari ba, cikakkiyar dama da suke da ita a yau, tare da turbude hancin bukatun masu zabe, shi ne babban abin nadama da kaico!!!. Idan a wancan lokaci za a ce Turawa sun rike...
“SDP jam’iyya ce mai zaman kanta, kuma za mu ci gaba da bin tsarukanmu da dokokinmu wajen zaɓen ‘yan takara,” in ji shi. “Za Mu Fi Mayar da Hankali Kan Ci Gaban Jama’a” Shugaban jam’iyyar ya bayyana damuwa kan halin da ‘yan Nijeriya ke ciki, musamman matsalar tsadar rayuwa da rashin tsaro. Ya ce SDP...
Jami’iyyar adawa ta “Turkish National Party” ta bayyana cewa dan takararta a zaben shugaban kasa na 2028 shi ne magajin garin Istanbul Akram Imam Ugulu wanda a halin yanzu yake a gidan kurkuku. Imam Uglu dan shekara 53 shi ne muhimmin dan takarar shugaban kasa a tsakanin ‘yan hamayya da ake hasashen cewa zai iya...
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya naɗa Sarkin Kauru, Mai Martaba Alhaji Ya’u Shehu Usman, a matsayin Amirul Hajj kuma jagoran tawagar jami’an jihar don aikin Hajjin 2025. A cikin wata sanarwa, Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna, Ibraheem Musa, ya bayyana cewa naɗin wannan basarake mai daraja ya biyo bayan sadaukarwarsa, da gaskiya, ...
Kungiyar da ke sa ido da kare hakkin dan adam ta Syria (SOHR) ta fitar da fayafan bidiyo guda hudu da ke dauke da hotunan azabtarwa da kisa da jami’an tsaron sabuwar gwamnatin kasar karkashin kungiyar Tahrir Sham suke aiwatarwa a kan fararen hula tsiraru marasa rinjaye a kasar. Kungiyar da ke sa ido kan...
Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Afganistan ta bada sanarwan cewa kasar Iran ce a gaba da dukkan kasashen makobta da kasar Afganisatan wacce tafi shigo da kayakinta cikin kasar a shekara ta 1403 ta kalandar Iraniyawa da ta kare. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar kasuwanci ta kasar Afganistan Abdussalam Jawad...
A kwanakin baya, bankin Deutsche, banki mafi girma na kasar Jamus ya yi bayani game da yanayin kashe kudi ta kasar Sin cewa, karin Sinawa suna kara son kashe kudi. Bisa sabon rahoton da bankin ya gabatar, an ce, idan aka kwatanta da na shekarar bara, yawan masu kashe kudi na kasar Sin yana karuwa,...
Gwamnatin Nijar ta ayyana zaman makoki na kwana uku bayan an kashe fararen hula 44 a kudu maso yammacin ƙasar a wani hari da “yan ta’adda” da ke da alaƙa da ƙungiyar ta’addanci ta Daesh suka kai. Ma’aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a gidan...
Wata gobara da ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Munna Albadawi da ke ƙaramar hukumar Jere a Jihar Borno, ta lalata wasu gidaje 10 tare da salwantar da rayuwar yaro mai shekara 7 mai suna Abubakar Gargar. A cewar shugaban sansanin, Babangida Mahmud gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 3:00 asubahin safiyar...
Sai dai, a yayin da yake yanke hukuncin; mai shari’a Omotosho, ya yanke hukuncin cewa, ya yi watsi da karar tasu da suka shigar saboda rashin cancanta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...

Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna Ta Bukaci Taimakon NAMA Don Gudanar Da Aikin Hajjin Bana Cikin Nasara
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta roƙi Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya (NAMA) ta ci gaba da ba da goyon baya domin tabbatar da nasarar gudanar da aikin Hajjin bana. A ziyarar ayarin hukumar ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gudanarwa, Malam Baba Mohammed Rufa’i, wanda ya wakilci Shugaban Hukumar, Malam Salihu...
Wata gobara mai muni ta laƙume gidaje uku a unguwar New GRA, a birinn jihar Gombe, a ranar Laraba inda ta bar iyalai cikin rashin matsuguni tare da asarar dukiya ta miliyoyin Naira. Waɗanda abin ya shafa sun koka kan rashin damar ceto komai daga kayan su, kuma yanzu haka suna neman tallafin gaggawa domin...
Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta yi Allah wadai da sake dawo da hare-haren wuce gona da irin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza tare da yin kira da a dauki matakin gaggawa na kasashen duniya domin dakile wadannan laifuka. Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta...
Wata gobara da ta tashi da sanyin safiya ta kone wani shago a wani gini mai daki 13 da ke rukunin gidajen Ile-Lodo a cikin garin Etan a karamar hukumar Ekiti a jihar Kwara. A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle ya fitar, ya ce bayan an...
An dakile fashewar wata babbar tankar mai a Sokoto bayan da jami’an tsaro da jami’an kwana-kwana da masu bayar da agajin gaggawa suka yi gaggawar kai dauki bayan da tankar ta kife a hanyar Gagi-Nakasari a karamar hukumar Sokoto ta Kudu. Wani shaidan gani da ido, Magaji Shanono ya shaidawa gidan rediyon Najeriya cewa...