Karin Sinawa Suna Son Kashe Kudi
Published: 23rd, March 2025 GMT
A kwanakin baya, bankin Deutsche, banki mafi girma na kasar Jamus ya yi bayani game da yanayin kashe kudi ta kasar Sin cewa, karin Sinawa suna kara son kashe kudi. Bisa sabon rahoton da bankin ya gabatar, an ce, idan aka kwatanta da na shekarar bara, yawan masu kashe kudi na kasar Sin yana karuwa, kashi 52 cikin dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu a binciken sun ce suna son kara kashe kudi, adadin da ya kai matsayin koli a shekara daya da ta gabata.
Me ya sa karin Sinawa suke son kashe kudi? Farfesa Wang Xiaosong na kwalejin ilmin tattalin arziki na jami’ar Renmin ta kasar Sin ya yi nuni da cewa, tun daga shekarar bara, tattalin arzikin Sin ya samu karuwa, kudin shiga na jama’ar kasar shi ma ya karu, lamarin da ya zama silan karuwar kudi da ake kashewa. Kana gwamnatin kasar Sin ta gabatar da jerin matakan tallafi don sa kaimi ga fadada kashe kudi a kasar.
Kasar Sin tana da mutane fiye da biliyan 1 da miliyan 400, tana daya daga cikin manyan kasuwanni na duniya. Kamfanin McKinsey ya yi hasashen cewa, ya zuwa shekarar 2030, mazaunan biranen kasar Sin za su sa kaimi ga karuwar kashe kudi ta duniya da kashi 91 cikin dari, biranen kasar Sin 700 za su samar da gudummawa ga karuwar kashe kudi na biranen duniya da dala triliyan 7, wanda ya kai kashi 30 cikin dari. Kashe kudi ya sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki, ana kara kashe kudi a kasar Sin, babu shakka za a samu sabon karfin raya tattalin arzikin duniya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: a kasar Sin
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe Uba da ’ya’yansa biyu a ƙauyen Filato
Rahotanni sun ce an kashe wani uba da ‘ya’yansa biyu a ƙauyen Zogu da ke Gundumar Miango a Ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato.
Kakakin Ƙungiyar ci gaban Irigwe (IDA), Sam Jugo, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Jos, ya bayyana sunayen waɗanda harin ya rutsa da su kamar haka, Weyi Gebeh a mai shekara 56, da Zhu Weyi mai shekara 25 da Henry Weyi mai shekara 16.
‘Tell Your Papa’: NBC ta haramta amfani da waƙar da ke sukar Tinubu An kama mutum 8 kan faɗan daba a KanoA cewar Jugo, an kashe mutanen ne cikin dare a lokacin da suke barci, inda ya bayyana lamarin a matsayin dabbanci.
Ya ce, “An sanar da shugabannin Ƙungiyar ci gaban Irigwe (IDA) game da wani harin da aka kai ƙauyen Zogu, Miango wanda ya yi sanadin mutuwar wani uba da ‘ya’yansa biyu waɗanda suka haɗa da: Weyi Gebeh da Zhu Weyi da Henry Weyi.
“Wannan harin na baya-bayan nan ya kai ga mutuwar mutane tara a cikin makon nan kaɗai, Ƙungiyar IDA ta nuna rashin jin daɗinta game da taɓarɓarewar al’amura a yankin Irigwe tare da yin kira ga jami’an tsaro da su yi duk abin da ya kamata don daƙile wannan ɓarna a yankinmu tare da kama waɗanda suka aikata laifin don fuskantar shari’a.
Kakakin rundunar ‘Operation Safe Haven’ Manjo Samson Zhakom da rundunar ’yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, har yanzu ba su mayar da martani ga saƙon da wakilinmu ya aika masu ba.