2025-02-21@14:25:50 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1113

«a kasar Sin»:

    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta daƙile wani yunƙuri da ’yan bindiga suka yi na sace wani mutum a Sabon Garin Lassa da ke Ƙaramar Hukumar Askira Uba. Rundunar ta kuma cafke wasu mutum uku tare da ƙwato wata bindiga ƙirar gida a hannunsu. Babban mai kai wa Bello Turji makamai ya shiga hannu NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ba Za Mu Sauke Farashin Burodi Ba —’Yan kasuwa Majiyoyin tsaro sun shaida wa Zagazola Makama cewa, lamarin ya faru ne a ranar 20 ga watan Fabrairu da misalin karfe 1 na dare. Wasu ’yan bindiga huɗu suka kai hari gidan Mohammed Abubakar, mazaunin Sabon Gari Lassa, da nufin sace shi. “Wanda suka yi niyyar sacewa ya yi ƙoƙarin kare kansa...
    daya daga cikin masu sana’ar a yankin Yashin Tuwo a karamar Hukumar Karim-Lamido a jihar, Mallam Dauda Adamu, ya tabbatar da wannan kalubalen da masu sana’ar ke fuskanta a jihar, inda ya sanar da cewa, lamarin ya tilasta wasu masu sana’ar rungumar aikin noma da kama wasu sana’oin daban, domin samun kudaden shiga. “A baya masu sana’ar a kullum suna samun kudaden shiga masu yawan gaske, sai dai; saboda raguwar Kifin a Koguna, kudaden shigar da suke samu sun ragu”, in ji Dauda. Wani jami’i a Ma’aikatar Aikin Gona ta Jihar, wanda bai bukaci a ambaci sunansa ba, ya tabbatar da wannan raguwa ta Kifin a Kogunan jihar. Kazalika, Mallam Dauda ya alakanta wannan kalubalen kan irin yanayin kamun Kifin...
    Jami’an Tsaro a Jihar Sakkwato, sun kama babban mai yi wa Bello Turji safarar makamai, mai suna Hamza Suruddubu. Rahotanni sun bayyana cewar ana zarginsa da yi wa wasu maharan safarar makamai a jihar. An tara Naira 16 a taron ƙaddamar da littafin IBB Ba ni da hannu a kisan Dele Giwa — Janar Babangida Wata majiya, ta shaida wa Zagazola Makama cewa Suruddubu ɗan yankin Gabashin Sakkwato ne, kuma ya daɗe yana safarar makamai daga jihar Zamfara zuwa sansanonin ‘yan ta’adda a Gabashin Sakkwato. “Shi ne babban mai yi wa ƙasurguman ’yan bindiga irin su Bello Turji, Boka, da Halilu Buzu safarar makamai,” in ji majiyar. Bincike, ya nuna cewa ba makamai kawai Suruddubu ke safara ba, har da...
    Sun ci gaba da cewa, tattalin arzikin ya karu zuwa kaso 3.5, a zango na uku a 2024, daga kaso 3.2 a zango na biyu a 2024. A cewarsu, Nijeriya ta samu wannan nasarar ce, saboda tsaurara tsare-tsaren hada-hadar kudade, inda kuma fannin da bai shafi Man Futur na kasar ba, ya bayar da gagarumar gudunmawa, tare da samar da tsare-tsaren sakuka yin hada-hadar kasuwanci a kasar. Sun kara da cewa, fannin Mai ya ci gaba da bayar da gudunmawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar, musamman duba da yadda Matatar Man Fetur ta dangote ke samar da yawan Man a kasar, inda hakan ya kuma daidaita samar da Man da kuma rabar da shi, a cikin farashi mai rahusa. Sai...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhafa barakammu da  sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masi muhimmanci a wannan makon wadanda suka hada da wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakewa tsaro na sauransu, da fatana masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yua. //….. Madallah masu sauraro shirimmu na yau zia yi magana dangane da makamin bom masu suna MK-84 wanda kuma yake da Laba 2000 yake da katfin lalatawa da halaka mutane. Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyanan bayan ya dare kan kujerar shugabancin kasar Amurka ya aikawa HKI manya-manyan boma-bomai masu nauyin ton guda ko wannan ake kira MK-84. Kara kashe Falasdinawa, `wannan...
      Tarkon Dark Web: Wasu yara na iya fada cikin rukunin yanar gizo da ke da hadari.   Dabara Da Yaudara A Wasanni (Gaming Scams): Wasu yara na fuskantar barazana a cikin wasannin da suke bugawa online. Yadda Za A Kare Yara Daga Wadannan Barazanar Iyaye su lura da abin da yaran su ke yi online – Kula da shafukan da suke ziyarta da kuma mutanen da suke magana da su. Amfani da ‘Parental Control’ – A saita wayoyin yara domin hana shiga shafuka masu illa. Ilimantar da yara kan sirri – A koya musu kada su bada bayanan sirrinsu kamar lambar waya, adireshi, ko hotuna. Kafa iyaka kan amfani da intanet – Iyaye su saka ka’ida kan lokacin da...
    Kwamatin lura da kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya kaddamar da rangadi na yini biyu a karamar hukumar Jahun, domin tantance kwazon karamar hukumar ta fuskar gudanar da ayyukan raya kasa da sha’anin mulki da kashe kudade. Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Gwiwa, Alhaji Aminu Zakari, ya ce ziyarar na daga cikin ayyukan majalisa da suka hada da duba kasafin kudi da yin doka da kuma tantance abubuwan da gwamnati ta ke gudanarwa kamar yadda tsarin mulki ya tanadar. Ya ce a lokacin wannan ziyara, kwamatin zai tantance kundin bayanan ayyukan raya kasa da rahoton zangon shekara da bayanan tarukan kwamatin tsaro da na gudanarwa. Ya ce kwanitin zai kuma tantance bayanan ayyukan majalisar kansiloli da kuma alkaluman...
    Gwamnatin kasar Iran ta gargadi hukumar IAEA mai kula da al-amuran makamashin nukliya a duniya, bayan da babban sakataren kungiyar Rafaei Grossy ya fita daga matsayin dan ba ruwammu, a cikin harkokin siyasa a aikinsa, inda ya furta wasu jawabai dangane da shirin makamashin nukliya na kasar Iran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Gorossi ya fita daga matsayinsa na gwararre da kuma masanin harkokin makamashin nukliya ya kuma dauki bangare a wani taro da yan jirudu da ya gabatar a birnin Tokyo na kasar Japan. A cikin jawabin da yayi wa yan jaridu Grossi ya Iran tana ‘gasa makamashin Uranium har zuwa kasha 60% wanda ya kusan kaiwa ga makamashin Nukliya, sannan bata bawa hukumar IAEA hadin...
    Hamshakan attajirai da ’yan siyasa sun bayar da gudunmawar sama da Naira biliyan 16 a bikin kaddamar da littafin tarihin tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida. Taron ƙaddamar da littafin, mai suna ‘A Journey in Service’, wanda aka gudanar a Abuja ya tara manyan baƙi daga ciki da wajen Najeriya. Mahalarta taron da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis sun bayar da gudunmawar ne domin ginin dakin karatun da tsohon shugaban ƙasan ke shirin ginawa. Attajiri mafi yawan arziki a Afirka kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin Ɗangote, Alhaji Alikon Ɗangote ya ba da gudunmawar Naira biliyan takwas, Naira biliyan biyu a duk shekara, na tsawon shekara huɗu. Ya kuma yi alƙawarin karin biliyan biyu a duk shekara...
    MDD ta bada sanarwan cewa tattalin arzikin kasar Siriya na bukatar shekaru 50 nan gaba kafin ta koma kamar yadda take kafin yakin basasa a kasar. Tashar talabijan ta Presstv ta nakalato shugaban hukumar UNDP Achim Steiner yana fadar haka a jiya Alhamis, ta kuma kara da cewa hukumar ta ta gudanar da bincike kuma ta gano cewa, rikici da yakin basasa da kuma mamayar kasar da sojojin kasashen yamma suka yiwa kasar, ya sa al-amura sun lalace a kasar, ta yadda idan tana bukatar komawa matsayinta kafin shekara ta 2011 tana bukatar rabin karni kafin hakan ya samu. Wato kasar Siriya ba zata koma kamar yadda take a shekara ta 2011 ba sai nan da shekara 2080. Tace Siriya tana...
    Tashar jiragen sama ta birnin Beirut tana cike da masu shiga kasar daga kasashen daban-daban don halattar jana’izar Shahidai kuma shuwagabannin kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasarallah da kuma Magajinsa Shahid Sayyid Hashimi Safiyyuddeen wanda za’a gudanar a ranar 23 ga watan Fabarairu da muke ciki. Kamfanin tafiye-tafiye na “Ajuz Travillin Agency’ ya fadawa tashar talabijin ta Almanar kan cewa tun yawan jiragen sama masu zuwa daga kasashen waje suka nin nink tafiye-tafiyensu zuwa Beiru, daga cikinsu, akwai Iraq Air wanda yake zuwa Beiru  har sau biyu. Amma daga yau ya kara shi zuwa har sau ukku. Kamama Egypt Air ya ninka zuwasa Beirut har sai yu. Da kuma Tarksih Air shi ya ninninka ta fiyasa zuwa kasar. Labarin ya kara...
    A dai-dai lokacinda shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana a fili kan cewa baya son nganin tokwaransa na kasar Ukraine Volodimir Zelesky kan kujerar shugabancin kasarsa. Al-amura suna kara tabarbarewa a Kiev. Jaridar Economist ta kasar Burtaniya ta bayyana cewa al-amarin ya bayyana kiri-kiri ne a lokacinda shugaban kasar Amurka ya zanta ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladimi Putin. Sannan aka gudanar da taro na farko tsakanin Amurka da Rasha a birnin riyad na kasar Saudiya ba tare da an gayyaci Zelesky ba haka ma, babu wani Jami’in tarayyar Turai da aka gayyata. Jaridar ta nakalto wani babban jami’in gwamnati a Kiev yana cewa tun lokacinda suka fahinci cewa Trump baya son a ci gaba da yaki...
    Jami’an diblomasiyya da dama daga kasashen kungiyar G20 ne suka isa birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu, don halattar taro na kwanaki biyu. Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya isa birnin Johannesburg a jiya Alhamis kwanaki biyu kacal da ya gana da tokwaransa na kasar Amurka a birnin Riyad na kasar Saudiya. Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News’ yace ana saran kasashen turai zasu kara jaddada goyon bayansu ga kasar Ukraine a yakin da take fafatawa da kasar Rasha. Duk tare da cewa gwamnatin kasar Amurka tana son kawo karshen yakin ba tare da su ba. Kasashen Burtaniya , Faransa, Jamus da kuma tarayyar Turai EU gaba daya suna goyon bayan Ukraine a yakinta da Rasha....
    Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta nesanta hannunsa da kisan gogaggen ɗan jarida kuma Babban Editan Jaridar Newawatch, Dele Giwa. An kashe Dele Giwa wanda fitaccen mai sukar gwamnatin Babangida ne, ta hanyar wasikar bom a gidansa da ke Legas a ranar 19 ga watan Oktoban 1986. Kwana biyu kafin kisan nasa wani babban jami’in Rundunar Leƙen Asiri ta Soji ya zargi Dele Giwa da yin fasa-kwaurin makamai da ƙasashen da nufin tayar da zaune tsaye a Najeriya Sakamakon haka, dan jaridar ya yi hanzarin sanar da lauyansa, Gani Fawehinmi, game da halin da ake ciki. Na yi nadamar soke zaɓen 1993 — Babangida NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ba Za Mu Sauke Farashin Burodi...
    Domin magance wannan kalubale, Muhammed ya ba da shawarar ka da a bar mutane su dauki kudi fiye da naira 50,000 a rumfunan zabe. “Sayen kuri’u na daya daga cikin manyan barazana ga sahihin zabe a Nijeriya. Muna bukatar dokar da ba wai kawai ta haramta wannan dabi’ar ba har ma da sanya matakan kariya,” in ji Muhammed. Bayan sayen kuri’u, jami’an INEC sun sake jaddada bukatar da suka dade suna yi na a kafa hukumar da ke yaki da laifukan zabe, suna masu cewa hukumar zabe ba ta da karfin gurfanar da masu laifi a gaban kotu. A cewar Muhammed, “INEC na iya bakin kokarinta wajen ganin an gurfanar da masu laifukan zabe a gaban kotu, amma muna bukatar...
    Ta ƙara da cewa wannan shiri yana nuna jajircewar gwamnati wajen tabbatar da gaskiya, riƙon amana, da hulɗa kai-tsaye da jama’a.   Za a fara jerin tarukan ne da gabatarwar Ministan Raya Kiwo, Mukhtar Maiha; da Ministan Cigaban Yankuna, Injiniya Abubakar Momoh.   Ma’aikatar ta gayyaci ‘yan jarida, masu ruwa da tsaki, da jama’a gaba ɗaya don halartar wannan muhimmiyar tattaunawa da nufin bayyana wa jama’a irin cigaban da gwamnati ke samu.
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Iran ce zata yanke shawara a nan gaba kan matsayin kasarta, ba Trump ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a yammacin jiya Alhamis ya jaddada cewa: Iran ce take da hakkin yanke shawara kan makomarta ba Trump ba, yana mai jaddada wajabcin sauya ra’ayi domin dakile duk wani takunkumin da Trump ya kakabawa kasarsa. A jawabin da shugaba Pezeshkian ya gabatar a wajen taron shugabannin lardin Tehran ta yamma da majalisar gudanarwa ta garuruwan Mallard, Shahriar da Quds, shugaba Pezeshkian ya bayyana cewa, ma’anar gudanarwa ita ce sanin damammaki da barazana a ciki da wajen kasar da kuma sanin irin karfi da ake da shi. Shugaban kasar ya jaddada cewa: Trump na fadin wani...
    Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Amurka da gwamnatin ‘yan Sahayoniyya ba su yi nasara a yakin da suka kaddamar kan ‘yan gwagwarmaya a Gaza ba Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Hossein Salami ya jaddada cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba za ta samu wanzuwa idan babu Amurka, yana mai cewa, ita kanta Amurka ta kama hanyar rugujewa. Ya kara da cewa: Wadannan al’amura suna faruwa ne a kasa kuma wani bangare ne na makomar al’umma, don haka wajibi ne al’umma su dogara ga Allah kuma su yi duk abin da za su iya. A yayin ganawarsa da Ziyad al-Nakhala babban sakataren kungiyar Jihadul-Islami, Manjo Janar Salami ya yi...
    Jimi’in ofishin siyasa na kungiyar jihadul-Islami ya bayyana cewa: Marigayi Sayyid Hasan Nasrallah ya baiwa Falastinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya siffanta shi ba Mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul-Islami ta Falasdinu Ihsan Ataya ya yaba da irin tsayin dakan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi a fagen goyon bayan hakkokin Falasdinawa da gwagwarmayarsu, yana mai jaddada cewa: Shahidin al’ummar Sayyed Hassan Nasrallah ya gabatar wa Falasdinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya ambata ba. A cikin wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin ta Al-Alam, Adaya ya yi cikakken bayani kan yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da yahudawan sahyoniya, yana mai jaddada cewa: Gwagwarmaya...
    Motocin bas-bas guda uku sun tarwatse a birnin Tel Aviv, lamarin da ya haifar da rudani a tsakanin yahudawan sahayoniyya Motocin bas-bas guda uku sun fashe da yammacin jiya Alhamis a wurare daban-daban a yankin Bat Yam da ke kudancin birnin Tel Aviv a tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila. Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun bayyana cewa: Ma’aikatan tsaron cikin gidan haramtacciyar kasar Isra’ila ta “Shin Bet ta fara binciken wadanda ake zargin dasa ababen fashewa da suka yi sanadiyyar tarwatsewar motocin bas-bas din, kuma sun ba da rahoton zargin cewa; An samu wasu bama-bamai guda biyu wadanda ba su fashe ba. Har ila yau, kafofin watsa labaran ‘yan mamayar sun ruwaito cewa: An dakatar da zirga-zirgan jiragen kasa gaba...
    ‘Yan tawayen Sudan na Dakarun Kai Daukin Gaggawa sun aikata muggan laifuffuka a yankin Al-Qatana da ke Jihar White Nile ta Sudan Rahotonni sun bayyana cewa: Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan fararen hula a birnin Al-Qatana da ke arewacin jihar White Nile a Sudan, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan fararen hula tare da tarwatsa al’ummar yankin, inda suka fantsama zuwa gudun hijira. Ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta tabbatar da cewa: Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun gudanar da wani kisan kiyashi da ya yi sanadin mutuwar mutane 433 a kauyukan birnin Al-Qatana na jihar White Nile. Ma’aikatar harkokin wajen Sudan a cikin wata sanarwa da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A daidai lokacin da al’umma ke murnar saukar farashin kayayyakin abinci kamar shinkafa da masara da sauran kayan hatsi. Shi ma farashin fulawa da ake amfani da shi wajen sarrafa burodi, gurasa da sauran maƙulashe ya sauka a kasuwa. Sai dai duk da saukar farashinta, al’ummar na ci gaba da kokawa kan yadda har yanzu ba su gani a ƙasa ba. Tun makonni biyu da suka gabata aka sanar da saukar farashin fulawar kamar sauran kayayyakin masarufi. To amma ba kamar sauran kayan abinci ba, har yanzu ba a ga sauyi a farashin burodi ba. NAJERIYA A YAU: Tanadin Dokar Kasa Kan Kirkirar Gwamnatin Bibiya A Kano DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya...
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce zai ci gaba da tallafa wa jihar Jigawa wajen gina tsarin kiwon lafiya na al’umma. Shugaban hukumar UNICEF a Najeriya, Dr. Shyam Sharan-Pathak ya bayyana haka a wajen bikin mika aikin ga gwamnatin jihar Jigawa na tsawon shekaru 3 na GAVI, a hukumance a Dutse babban birnin jihar. A cewarsa, UNICEF za ta ci gaba da tallafa wa jihar don bunkasa muhimman ayyuka daga cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko na PHC, gami da ayyukan rigakafi na yau da kullun. Dokta Shyam ya ci gaba da bayyana cewa, gagarumin ci gaban da aka samu ta hanyar shirin, shaida ce ta hadin gwiwa da jajircewa ga kowane yaro,...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta yi alkawarin ci gaba da gudanar da ayyukan kiwon lafiya da aka gudanar karkashin hadin gwiwarta da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), da shirin samar da rigakafin cututtuka a kasashe masu tasowa(GAVI) a cikin shekaru uku da suka gabata. Haɗin gwiwar wanda aka fara shi da yarjejeniyar fahimtar juna da aka rattaba hannu a shekarar 2022, an yi shi ne don haɓaka tsarin bada lafiya na jihar, da inganta tsarin rigakafi ta hanyar samar da kayan aiki da wadatattun ma’aikatan lafiya. A wajen mika kayan aikin da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, Gwamna Umar Namadi ya ce shirin ya bayar da gudunmawa musamman wajen samar da inshorar lafiya...
    Gwamnatin jihar Kano ta dauki wani gagarumin mataki na bunkasa ilimin addinin musulunci a jihar ta hanyar hada hannu da kungiyar Agaji ta Musulunci da ke Birtaniya,  wato Muslim Charity For United Kingdom a turance. Wannan haɗin gwiwar na nufin tallafa wa makarantun Islamiyya da kayayyakin koyon  ilimi na zamani, da sauransu. A cewar daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru, wannan shiri ya yi daidai da kokarin da gwamnati ke yi na karfafa fannin ilimi. Haɗin gwiwar zai magance matsalolin da ke addabar ilimin addinin Islama, da tabbatar da cewa makarantun Islamiyya sun sami tallafin da ya dace don samu  ingantaccen yanayin karatu da koyarwa. Ya yi nuni da cewa, Kwamishinan Ilimi...
    An Bude Cibiyar Horar Da Malaman Harshen Sinanci A Ghana
    Yawan Kamfanonin Da Aka Kafa Da Jarin Waje A Sin Ya Zarace Miliyan 1.23
    Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya kaddamar da shirin Da’awah na mata a hukumance, domin karfafawa mata ilimin addinin musulunci, da karfafa alakar iyali, da kyautata rayuwa a tsakanin. Da yake jawabi a wajen bikin a Dutse, Gwamna Namadi ya jaddada muhimmiyar rawar da mata ke takawa wajen tsara tarbiyar al’umma da kyawawan dabi’u. “Kamar yadda aka sani, kusan rabin al’ummar jihar Jigawa mata ne, wadanda suka hada da iyayenmu, da ‘ya’yanmu, wanda hakan ya sa ya zama wajibi a kara zage dantse domin kula da addini da kuma tarbiyyarsu”. Malam Umar Namadi ya jaddada wajibcin addini da ya rataya a wuyan maza na tallafa wa mata da bi da su hanyar shiriya, inda ya bukaci maza da...
    Ya ce, motocin da aka kwato sun hada da wata farar mota kirar Howo, wacce aka sace daga Riruwai, karamar hukumar Doguwa, Kano, a ranar 17 ga watan Janairu, 2025, aka kuma gano ta a Lokoja, jihar Kogi.   Akwai wata bakar mota kirar Honda Accord 2013, wacce aka sace daga Abuja ranar 18 ga watan Janairu, 2025, aka gano ta a filin jirgin sama na Kano.   Bugu da kari, akwai wata farar mota kirar Mercedes Benz GLK wacce aka sace a hanyar Magwan Kano a ranar 27 ga watan Janairu, 2025, aka gano ta a Hotoro Quarters Kano da wata jar Toyota Corolla LE da aka sace a Abuja a ranar 30 ga Janairu, 2025, aka gano ta...
    Kamfanin mai na kasar Sin (CNPC) ya sanar a yau Alhamis cewa, ya kammala aikin hakar rijiyar man fetur mafi zurfi a yankin Asiya, yayin da rijiyar ta kai zurfin mita 10,910 a hamadar arewa maso yammacin kasar Sin. Rijiyar wacce aka fi sani da “Shenditake 1” da ke tsakiyar hamadar Taklimakan a cikin kwarin Tarim, a jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur, ta kasance wani gagarumin aiki na binciken kimiyya. Bayan neman albarkatun man fetur da gas, an kuma tsara aikin rijiyar don zurfafa nazarin juyin halittar duniya da kuma zurfafa ilimin binciken kasa. A cewar kamfanin CNPC, an fara aikin hakar rijiyar ne a ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2023, inda aka shafe fiye da...
    Wani ginin ajujuwa a Kwalejin ’Yan Mata ta Kimiyya da Fasaha (GGTC) Potiskum ya rufta, inda daliba ɗaya ta rasu kuma wasu da dama suka jikkata. Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da ɗalibai ke tsaka da karatu. An rufe Jami’ar Kogi saboda zanga-zangar ɗalibai EFCC ta gargaɗi ciyamomi kan amfani da kuɗaɗen jama’a a Gombe Gini ya faɗa kansu ne ba zato ba tsammani, lamarin ya haddasa mummunan tashin hankali tare da jefa ɗalibai da dama cikin baraguzan gini. Bayan aukuwar lamarin, an yi gaggawar ceto ɗaliban, inda aka garzaya da su zuwa Asibitin Ƙwararru na Potiskum domin ba su kulawa. Duk da an samu nasarar ceto da dama daga cikinsu, wata ɗaliba ta rasa ranta...
    Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Laraba, Ogbugo Ukoha, Babban Darakta a sashen rarraba mai tare da adanawa na NMDPRA, ya ce matakin ya biyo bayan karuwar firgicin hadurran da ke tattare da manyan motocin dakon man.   “Kwamitin fasaha na masu ruwa da tsaki ya gana a yau don cimma wasu muhimman kudurori guda 10 da nufin rage karuwar yawan hadurran tankokin mai da ke janyo asarar rayuka,” in ji Ukoha.   An cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki da suka hada da DSS, hukumar kashe gobara ta tarayya, hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), kungiyar masu sufurin mota ta kasa (NARTO), kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas...
    Hukumomin Jami’ar Tarayya da ke Lokoja a Jihar Kogi, sun rufe jami’ar har zuwa wani lokaci domin daƙile ci gaba da asarar rayuka da dukiya. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun magatakarda kuma sakatariyar majalisar Jami’ar, Dokta Rebecca Aimiohu Okojie, a ranar Alhamis kuma ta bayyanawa manema labarai a Lokoja. Jihar Gombe na ƙarfafa haƙƙoƙin yara masu nakasa — Ƙungiyar JONAPWD NNPP ta rasa Ɗan Majalisa na farko da ya koma APC Hukumar Jami’ar ta yi zargin cewa, ɗaliban sun tare babbar ƙofar shiga jami’ar ne tun bayan haɗarin da ya yi sanadin mutuwar ɗaliban jami’ar biyar a ranar Litinin, wanda ya sa shiga harabar jami’ar ke da wuya. “Rufewar jami’ar ya biyo...
    Taron muhawara na kasar a Jamhuriyar Nijar, ya nemi sojoji su yi mulkin rikon kwarya na shekaru biyar. Haka zalika taron ya nemi a yi afuwa ga sojojin da sukayi juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023. Wasu shawarwarin kuma da mahalarta taron suka bukata ita ce, baiwa mambobin kwamitin ceton kasa na CNSP, damar tsayawa takara a zabubuka masu zuwa, sannan a amince da islama a matsayin addini mai rinjaye a kasar. Taron ya kuma bukaci rushe dukkan jam’iyun siyaya 172 a kasar. A yayin rufe taron janar Tiani ya yi alkawarin biyan bukatun mahalarta taron. A shekarar 2023 ne sojoji suka kwace mulkin Nijar, bayan hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum, bisa hujjar tabarɓarewar matsalar tsaro da rashin...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya danganta takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky da “mai mulkin kama karya,” yana mai bukatarsa da ya gaggauta daukar matakin tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya da Rasha ko kuma ya yi kasadar rasa kasarsa. Trump ya yi wadannan kalamai ne, kwana guda bayan da ya zargi Ukraine da haddasa yakin Rasha, yana mai cewa hakan ya janyo Washington cikin rikicin na shekaru uku. An shirya wa’adin shekaru biyar na Zelensky zai kare a watan Mayun 2024, amma saboda dokar soja da aka kafa a watan Fabrairun 2022, ba za a iya gudanar da zabe ba. Kalaman na Trump sun jawo martani cikin gaggawa daga jami’an Ukraine, inda ministan harkokin wajen kasar Andrii Sybiha ya jaddada cewa...
    Saudiyya ta kira shugabannin kasashen Larabawa na yankin Gulf da kuma Masar da Jordan a wani taron domin tattauna batun Gaza. Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ne ya gayyaci shugabannin a taron na gobe Juma’a, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiyyar SPA ya ruwaito. Kasashen Larabawa sun yi alkawarin yin aiki a kan wani shiri na bayan yakin Gaza da kuma  sake gina Zirin a wani mataki na tunkarar shawarar shugaban Amurka Donald Trump na sake gina yankin da mayar da shi wurin shakatawa na gabar tekun kasa da kasa bayan korar mutanen Gaza zuwa wasu wurare. Saudiyya ta ce taron na ranar Juma’a zai kasance ba na hukuma ba kuma za a yi shi...
    Ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Uganda Jeje Odongo a cibiyar MDD da ke birnin New York. Yayin ganawar a ranar 18 ga wata, Wang Yi ya bayyana cewa, ana bukatar ra’ayin Afirka yayin da ake yada ra’ayin bangarori daban daban da kuma daidaita harkokin duniya baki daya. Ya ce kasar Sin tana son hada hannu da kasashen Afirka wajen kafa tsarin daidaita harkokin duniya mai adalci da kuma samar da gudummawa wajen shimfida zaman lafiya da samun ci gaba a duniya. Wang Yi ya ce Sin tana yabawa kasar Uganda bisa muhimmiyar rawar da ta taka yayin da take shugabantar kungiyar kasashe ‘yan ba ruwanmu wato NAM, da taya ta murnar zama kasar...
    Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Kara Haraji
    Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), ta gargaɗi shugabannin ƙananan hukumomi da su guji almundahana tare da yin amfani da kuɗaɗen jama’a bisa gaskiya da adalci. Shugaban EFCC, Mista Ola Olukoyede ne, ya bayyana haka yayin wani taro da aka shirya a Jihar Gombe kan ’yancin cin gashin kai na ƙananan hukumomi. Jihar Gombe na ƙarfafa haƙƙoƙin yara masu nakasa — Ƙungiyar JONAPWD Na yi nadamar soke zaɓen 1993 — Babangida A cewarsa, samun ‘yancin cin gashin kai ba yana nufin cewa shugabannin ƙananan hukumomi ba za a iya hukunta su ba idan sun aikata ba daidai ba. “Shugabannin ƙananan hukumomi ba su da kariya a tsarin mulkin ƙasa. Idan aka samu rashin gaskiya wajen sarrafa kuɗaɗen jama’a,...
    Jakadan Sin dake kasar Najeriya Yu Dunhai ya gana da karamar ministar harkokin waje ta kasar Bianca Odumegu-Ojukwu. Jakada Yu ya bayyana cewa, a shekarar bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu, sun sanar da inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, wanda ya zama babban ci gaba ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. A farkon shekarar bana kuma, memban hukumar kula da harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya kai ziyara Najeriya cikin nasara, hakan ya kara kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa sabon matsayi. A cewar jakadan, Sin tana son...
    Ƙungiyar Masu Nakasa ta ƙasa reshen Jihar Gombe (JONAPWD), ƙarƙashin jagorancin Shugabanta kuma Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Masu Nakasa ta Jihar, Dokta Isiyaku Adamu. Ƙungiyar ta shirya taro na musamman tare da iyayen yara da suke fama da matsala irin ta nakasar jiki da kuma ta taɓin hankali. NNPP ta rasa Ɗan Majalisa na farko da ya koma APC Harin ’Yan bindiga: Mun yi asarar shanu sama da miliyan 4 – Miyetti Allah Wannan taron na musamman, wanda aka gudanar a ofishin JONAPWD da ke Gombe, ya zama wata muhimmiyar dama don tattauna matsaloli, musayar ƙwarewa da kuma ƙarfafa fafutuka don kare haƙƙoƙin yara masu fama da matsala irin ta nakasar jiki da kuma ta taɓin hankali. A...
    Abiola Ne Ya Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Na 12 Ga Watan Yuni 1993 – Janar IBB
    Jam’iyyar adawa ta NNPP ta rasa ɗaya daga cikin mambobinta a Majalisar Wakilai zuwa jam’iyyar APC mai mulki. Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Gwaram ta Jihar Jigawa, Yusuf Shitu Galambi. Shi ne ɗan jam’iyyar NNPP na farko da ya sauya sheƙa ya koma APC. Na yi nadamar soke zaɓen 1993 — Babangida Hisbah ta rufe gidajen rawa a Katsina Idan dai za a iya tunawa, ’yan jam’iyyar adawa na PDP da LP da dama sun sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC. Ɗan Majalisa Galambi ya bayyana cewa, ya bar jam’iyyar NNPP ne saboda rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar wanda ya haifar da wasu ƙararraki da suka shafi ayyukan jam’iyyar. Ya kuma ƙara da cewa, Jam’iyyar NNPP...
    Tsohon Shugaban Mulkin Soja na Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce ya yi nadamar soke zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993. Ya ce da zai samu wata dama da zai yanke wani hukunci daban. Harin ’Yan bindiga: Mun yi asarar shanu sama da miliyan 4 – Miyetti Allah Majalisa ta fara bincike kan zargin USAID na tallafa wa Boko Haram Babangida ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Alhamis, yayin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwarsa mai suna ‘A Journey in Service’. Yayin da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, ke nazarin littafin, Babangida ya amsa alhakin soke zaɓen da aka gudanar tsakanin Moshood Abiola na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) da Bashir Tofa na jam’iyyar...
    Ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) ta yi iƙirarin cewa wasu ’yan bindiga sun sace sama da shanu miliyan huɗu na mambobinta musamman a yankin Arewa maso Yamma. Shugaban Ƙungiyar MACBAN na ƙasa, Baba Usman ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da sababbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙungiyar na jiha a Jihar Kebbi. ’Yan bindiga sun kashe mutum 12, sun sace wasu a Zariya Hisbah ta rufe gidajen rawa a Katsina Ya ce, ɓarayin shanu na yawan kai wa Fulani makiyaya hari, lamarin da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi. Usman ya jaddada cewa, ana yawan sauya fahimtar Fulani makiyaya da kuma yin kuskuren sanya su a matsayin masu tayar da fitina, inda ya buƙaci jama’a su riƙa ganin su...
    “Wannan mataki yana cikin shirin Hisbah na tabbatar da cewa al’ummar Katsina na tafiyar da rayuwarsu bisa koyarwar addini da kyawawan ɗabi’u,” in ji shi.  
    “Wannan mataki yana cikin shirin Hisbah na tabbatar da cewa al’ummar Katsina na tafiyar da rayuwarsu bisa koyarwar addini da kyawawan ɗabi’u,” in ji shi.  
    Majalisar Wakilai ta kafa kwamiti na musamman da zai binciki zargin da ake yi wa Hukumar Bayar da Agaji ta Ƙasa da Ƙasa ta Amurka (USAID), da tallafa wa Boko Haram. An yanke wannan hukunci ne bayan ɗan majalisa, Inuwa Garba, ya gabatar da buƙatar gaggawa a zaman majalisar na ranar Alhamis. ’Yan bindiga sun kashe mutum 12, sun sace wasu a Zariya Hisbah ta rufe gidajen rawa a Katsina Garba, ya nuna damuwa game da kalaman da ɗan majalisar dokokin Amurka, Scott Perry, ya yi kwanan nan, inda ya zargi USAID da bai wa ƙungiyoyin ’yan ta’adda, ciki har da Boko Haram tallafi. Ya jaddada cewa Boko Haram ta haddasa babbar matsalar tsaro a Najeriya sama da shekara 10....
    ’Yan bindiga sun kashe wasu ’yan kasuwar Gwari 12, tare da sace wasu yayin da suke kan hanyarsu ta komawa Zariya bayan cin kasuwa. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Tafoki da ke Jihar Katsina, bayan ’yan bindigar sun buɗe wa motarsu wuta. An haramta wa manyan tireloli aiki a Najeriya Jami’an tsaron al’umma 6 sun mutu a artabu da ’yan bindiga a Sakkwato Masu sana’ar Gwari da abin ya shafa ’yan kasuwar Ɗan Magaji ne daga Ƙaramar Hukumar Zariya, a Jihar Kaduna. Aminiya ta tattauna da wasu daga cikin waɗanda suka tsira, waɗanda suka ji raunuka, da kuma waɗanda aka sako bayan biyan kuɗin fansa Naira miliyan biyu. Muhammad Zaharraddeen Sharaihu shi ne mutumin da ya kai wa ’yan...
    Gwmanatin Tarayya ta haramta wa tireloli masu ɗaukar man fetur da nauyinsa ya kai lita 60,000 aiki a Najeriya daga ranar 1 ga watan Maris mai kamawa. Hukumar Albarkatun Man Fetur ta Kasa (NMDPRA) ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne da nufin taƙaita yawan haɗuran tirelolin man fetur da ke sanadiyyar asarar ɗaruruwan rayuka da dukiyoyi na miliyoyin kuɗaɗe. Hukumar ta ƙara da cewa zuwa ƙarshen wannan shekara ta 2025 za a haramta wa motoci masu ɗaukar man fetur lita 45,000 hawa titunan Najeriya. Ta bayyana cewa bayan wani taron da aka gudanar kan yawan haɗuran tirelolin man fetur da irin asarar da hakan ke haifarwa, masu ruwa da tsaki a harkokin mai da sufuri hukumomin tsaro da sauransu...
    Arziƙin hamshakin attajirin nan ɗan jahar Kano Alhaji Aliko Dangote ya ninka na bara inda ya ƙaru zuwa dala biliyan 23.9, wanda hakan yasa ya cigaba da kasancewa mutumin da yafi kowa dukiya a nahiyar Afrika kuma ya koma matsayi na 86 a jadawalin masu kudin Duniya kamar yadda mujallar Forbes mai ƙididdiga akan masu kuɗin Duniya ta fitar, Forbes ta zaɓi Aliko Dangote a matsayin mutum na 144 mafi arziƙi a duniya a shekarar 2024 da dala biliyan 13.4. Forbes ta yi kiyasin cewa dukiyar Dangote ta kai dala biliyan 23.9, musamman saboda hannun jarin sa na kashi 92.3 na matatar man dangote, Aliko Dangote mai shekaru 67, ya sake zama ɗaya daga cikin manyan attajirai 100 a duniya,...
    Hukumar Hisbah ta rufe gidajen rawa da ke gudanar da harkokinsu a Jihar Katsina. Hukumar ta umarci ɗaukacin masu gidajen rawa da ke gudanar da harkokinsu a cikin dare a faɗin jihar da su rufe. Shugaban Hukumar, Dakta Aminu Usman ne ya bada umarnin tare da gargaɗin masu wuraren da matakin ya shafa. Ya bayyana cewa ɗaukar matakin ya zama dole domin kare tarbiyya da dokokin addinin Islama da kuma barazanar tsaro a jihar. Jami’an tsaron al’umma 6 sun mutu a artabu da ’yan bindiga a Sakkwato NAJERIYA A YAU: Tanadin Dokar Kasa Kan Kirkirar Gwamnatin Bibiya A Kano Sanarwar da ya fitar ranar Laraba ta bayyana cewa tabbatar da tarbiyya da kare dokokin Musulunci sun zama wajibi. Ya ci...
    Mutum shida daga cikin Jami’an Tsaron Al’umma na Jihar Sakkwato sun kwanta dama bayan wata musayar wuta da ’yan bindiga a Kamarar Hukumar Sabon Birni. Wasu majiyoyi sun bayyana cewa jami’an tsaron sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suka kai ɗauki ga al’umma da ’yan bindiga suka kai wa hari. A hanyarsu ne ’yan bindiga suka yi musu kwanton ɓauna. Wata majiya ta bayyana cewa abokin aikinsu ne ya kira ya sanar da cewa, ’yan bindiga suna hanyarsu ta kawo hari ƙauyensi da ke kusa da Unguwan Lalle. “Jami’an tsaron sun nemi abin hawa daga hukumar karamar hukumar amma an hana su, saboda an hana su gudanar da ayyukan tsaro na yau da kullum su kaɗai ba tare...
    Mutum shida daga cikin Jami’an Tsaron Al’umma na Jihar Sakkwato sun kwanta dama bayan wata musayar wuta da ’yan bindiga a Kamarar Hukumar Sabon Birni. Wasu majiyoyi sun bayyana cewa jami’an tsaron sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suka kai ɗauki ga al’umma da ’yan bindiga suka kai wa hari. A hanyarsu ne ’yan bindiga suka yi musu kwanton ɓauna. Wata majiya ta bayyana cewa abokin aikinsu ne ya kira ya sanar da cewa, ’yan bindiga suna hanyarsu ta kawo hari ƙauyensi da ke kusa da Unguwan Lalle. “Jami’an tsaron sun nemi abin hawa daga hukumar karamar hukumar amma an hana su, saboda an hana su gudanar da ayyukan tsaro na yau da kullum su kaɗai ba tare...
    Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof ya bayyana cewa falasdinawa masu kasa ne zasu fayyace makomar kasarsu, don haka shirin da wasu manya-manyan kasashen duniya suke dashi a kan makomar Falasdinu da Falasdinawa ba dai-dai bane kuma zamu yi yaki da shi. Tashar talabijan ta Presstv a nan Teran ta nakalto shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammada Bakir Qolibft yana fadar haka a taron shuwagabannin majalisun dokoki na kasashen Asia a birnin Baku na kasar Azaibaijan. Qolibof ya kuma kara da cewa shirin shugaban kasar Amurka yake yi na kwace gaza da kuma inda za’a maida Falasdinawa ba zai kai ga nasara ba. Qalibof ya yi allawadai wadai da shugaba Trump kan shishigin da yake yi a cikin...
    Dubban Falasdinawa ne suka kauracewa gidajensu a yankin yamma da kogin Jordan. Tun ranar 21 ga watan Jeneru na wannan shekara ta 2025, wato kwanaki biyu kacal da tsaida wuta a Gaza, sojojin HKI suka fadawa sansanin yan gudun hijira na Jenen inda suka fara fafatawa da dakarun Falasdinawa a yankin. Da nufin korarsu.   Dagan nan ne dubban Falasdinawa suka fara kauracewa gidajensu a yankin. Wasu suka dauki dukkan iyalansu su a mota su tafi inda ba’a tashin hankali. Wasu kuma sukan taka da kafafuwansu zuwa nesa daga inda ake fada da tashin hankali. Wani dan agaji a yankin ya bayyana wa Jaridar ‘Arabsnews’ cewa bai taba ganin irin wannan kaurar da Falasdinawa suke yi ba, sai wanda aka...
    Gwamnati Ta Haramtawa Tankokin Dakon Mai Ɗaukar Fiye Da Lita 60,000
    Gwamnati Ta Haramtawa Tankokin Dakon Mai Ɗaukar Fiye Lita 60,000
    Gwamnati Za Ta Haramta Amfani Da Tankoki Masu Ɗaukar Lita 60,000 Aiki Daga Maris 1
    Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran ( IRGC) ta yaye kallabin sabbin makamai a atisayen soja mai yaken “Rasulul-A’azam” da suke ci gaba da yi a halin yanzu. Daga cikin makaman da aka kaddamar da akwai makamai masu linzami dake cin dogon zango, sai kuma jiragen sama marasa matuki da kuma makaman Atilare. A jiya Laraba ne dai aka kaddamar da sabbin makamai masu linzamin  wanda ya sami halartar manjo janar Muhammad Bakeri da shi ne babban hafasan hafsoshin sojan kasar Iran. Shi kuwa janar Ali Kuhistani da shi ne mataimakin kwamandan rundunar ta IRGC a fagen kayan yaki, ya ce; Sabbin makamai sun kunshe da kayan aiki na zamani masu muhimmanci da aka hade su wuri daya....
    An yi zaman farko na tattaunawar sulhu a tsakanin kasashen Habasha da Somaliya a birnin Ankara wanda kasar Turkiya take a matsayin mai shiga tsakani. Ministan harkokin wajen kasar Turkiya Hakan fidan ya yi ganawa da  daban-daban da ministocin harkokin wajen kasashen na Habasha da Somaliya. Bayan wannan ganawar minstan harkokin wajen na Turkiya ya bayyana cewa; Yin aiki tare a tsakanin kasashen yankin yana da matukar muhimmanci a wannan zamanin da duniya take cike da sarkakiya.” Haka na kuma ya kara da cewa:  Kai wa ga nasara a wannan tattaunawar yana da matukar muhimmanci fiye da kowane lokaci a baya. Kamfanin dillancin labarun “Anatol” na Turkiya ya nakalto ministan harkokin wajen kasar yana yin ishara da babbar dama da...
    Kungiyoyin Falasdina mabanbanta sun yi kira da a gudanar da taron musamman na al’ummar Falasdinu domin a tattauna hanyoyin da za a dakile batun tilastawa mutanen Gaza yin hijira. Kungiyoyin na falasdinawa sun bayyana hakan ne dai a wani taro da su ka yi a Gaza domin karfafa gwiwar mutanen wannan zirin su ci gaba da jajurcewa da tsayin dakar da suke yi, tare da kara da cewa; Babu yadda za a yi al’ummar Falasdinu su fita daga kasarsu. Mahalarta taron na Gaza sun bayyana furucin da shugaban kasar Amurka ya yi akan  fitar da Falasdinawa daga Gaza da cewa yana nuni akan yadda Amurka da ‘yan sahayoniya su ka yi tarayya a laifukan da aka tafka akan Falasdinawa, haka...
    Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali Khamnei wanda ya gana da sarkin Katar  a jiya Laraba ya bayyana cewa; Siyasar Iran ta ginu ne akan kyautata alaka da kasashen makwabta, kuma tuni an cimma sabbin matakai a wannan fagen. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma fada wa sarkin na Katar Tamim Bin Hamad ali-Sani cewa, ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci yana fadi tashi a wannan fagen na kyautata alaka da kasashen makwabta, tare da yin kira da cewa yarjeniyoyin da aka kulla su zama masu kare maslahar kasashen biyu. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana kasar Katar a matsayin kasa abokiya, kuma ‘yar’uwa ta Iran, duk da cewa har  yanzu da akwai wasu batutuwa da ba a...
    Shugaban kasar na Amurka Donald Trump ya wallafa wani sako a shafinsa na “Truth Social” da a ciki ya bayyana Volodymyr Zelenskyy dad an kama-karya, kuma abinda ya fi yi masa alheri shi ne ya yi wani abu da sauri, domin idan ba haka ba,zai yi asarar kasarsa baki daya. Shugaban na kasar Amurka ya kara da cewa; Volodymyr Zelenskyy ya sa Amurka ta kashe dala biliyan 350 da ya shiga cikin yakin da ba zai iya samun nasara ba.  Har ila yau, shugaban na Amurka ya ce, shi kanshi Volodymyr Zelenskyy ya yi furuci da cewa, rabin kudaden da mu ka aika masa sun bace, kuma ya ki gudanar da yin zabe, don haka masu goyon bayansa ‘yan kadan...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan sanarwar shirin kafa gwamnatin bibiya ko kuma ‘shadow government’ a turance da wata kungiya ƙarƙashin Jam’iyyar APC a Jihar Kano tace za ta yi ne  ne dai al’umma da dama ke ta jefa ayar tambaya kan halascinta. Kungiyar dai ta bayyana cewa za ta kafa wannan gwamnati ne don bibiyan ayyukan gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf don tabbatar da ana abin da ya kamata. Sai dai wannan sanarwa na ci gaba da yamutsa hazo inda wasu ke kallon halascin wannan gwamnati. NAJERIYA A YAU: Ci-gaban Da Hukumomin Raya Shiyyoyi Za Su Samar DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci...
    A karshe dai, ya nanata muhimancin raya karfin kasa da kasa ta hanyar aiwatar da ayyuka masu alaka da hakan. Wang Yi ya jaddada cewa, kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa da sassa daban daban, domin bude sabon babin raya huldar cude-ni-in-cude-ka, tare da kafa tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa mai inganci. Bayan taron, ya kuma amsa tambayoyin ‘yan jaridu, game da yadda kwamitin sulhu na MDD zai karfafa kwarewarsa ta gudanar da ayyuka, da matsayin kasar Sin kan batun Gaza da dai sauransu. (Mai Fassara: Maryam Yang)    
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta sake doke Manchester City da ci 3 da 1 a filin wasa na Bernabeu. Madrid ta karɓi baƙuncin Man City a wasan zagaye na biyu na gasar Zakarun Turai, bayan doke ta a gida da ci 3 da 2. Gobara ta ƙone gidaje, dabobbi da kayan abinci a Kano Hana Biza: Najeriya ta cancanci a girmama ta – Babban Hafsan Tsaro Kylian Mbappe ne ya zama tauraro a wannan wasan, inda ya jefa wa Manchester City ƙwallaye uku rigis a raga. Ɗan wasan gaban na Real Madrid, ya fara jefa ƙwallo ta farko a minti na 4 da fara wasa, sannan ya jefa ƙwallo ta biyu a minti na 33. Bayan dawowa daga...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta dauki matasa fiye da 6,000 aiki a fannoni daban-daban a fadin jihar, a kokarinta na ganin ta inganta rayuwarsu. A saboda haka ne ma matasan da aka dauka aikin suka karrama Gwamnan Jihar, Malam Umar Namadi, bisa kokarinsa na samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arzikin al’ummar jihar. Wakilinmu Usman Mohammed Zaria ya ruwaito cewa, taron karramawar, wanda aka gudanar a gidan Gwamnati dake Dutse Babban Birnin Jihar, ya hada da wadanda suka ci gajiyar shirye-shiryen gwamnati da suka hada da  J-Teach, da  J-Agro, da  J-Health, da  J-Millionaires, da sabbin likitocin da aka dauka aiki a bangaren lafiya. A yayin taron, kowanne rukuni ya mika lambar yabo ga Gwamna Umar Namadi don nuna...
    Kafofin yada labarai da manazarta na kasa da kasa, sun jinjinawa babban taron ‘yan kasuwan kamfanonin kasar Sin masu zaman kansu da aka gudanar ranar Litinin, inda suka ce gwamnatin Sin na marawa wadannan kamfanonin baya wajen taka rawar gani a bangaren kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire, kuma Sin ta gabatar da sako mai yakini na karawa wadannan kamfanoni kwarin gwiwar bunkasuwa. A wannan taro dai, ba nanata niyyar nacewa ga manufofi masu tushe da ake bi wajen raya kamfanoni masu zaman kansu a nan kasar Sin kadai aka yi ba, an kuma gabatar da alkiblar samun ingantattun ci gaba yadda ya kamata a wannan bangare. Hakan ya sa, “kwarin gwiwa” ta sake zama muhimmiyar kalma ga kasashen waje don...
    Sin Ta Tabbatar Da Goyon Bayanta Ga Kafa Kasashe Biyu Ga Isra’ila Da Palasdinu
    Wata gobara da ta tashi cikin dare a garin Satigal da ke Ƙaramar Hukumar Bunkure a Jihar Kano, ta ƙone gidaje da dama, dabbobi, da rumbunan ajiyar hatsi guda shida. Sai dai kawo yanzu babu labarin rasa rai a gobarar. Ukraine ce mai laifi a yaƙin da ta ke yi da Rasha — Trump Hana Biza: Najeriya ta cancanci a girmama ta – Babban Hafsan Tsaro A cewar wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na shiyyar Rano, Rabi’u Kura, ya fitar, mazauna yankin sun haɗa kai wajen kashe gobarar da kuma ceton rayuka da dukiyoyi. Bayan haka, an kai rahoton lamarin ga Sarkin Rano, Dokta Muhammad Isa Umaru, a fadarsa. Hakimin Satigal, ya jagoranci wasu mazauna yankin zuwa wajen sarkin,...
    Taron dai na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da majalisar dattawan kasar a ranar Laraba ta gayyaci shugabannin hukumar leken asiri don gudanar da bincike kan zargin da dan majalisar dokokin Amurka, Perry Scott ya yi na cewa, hukumar bayar da tallafi ta kasa da kasa ta Amurka, USAID na tallafa wa kungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram.   Da yake jawabi a zaman taron na ranar Laraba, Akpabio ya ce Nijeriya ba za ta bar Hukumar USAID ta ci gaba da aiki a Nijeriya ba idan aka same ta da laifin daukar nauyin ta’addanci.   Ya ci gaba da cewa, yana da muhimmanci Nijeriya ta tabbatar da gaskiyar wannan zargi.
    Gidauniyar Tunawa Da Sir Ahmadu Bello Za Ta Gudanar Da Taronta Karo Na 11 A Bauchi.Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta sanar da cewa za ta gudanar da bikin tunawa da Sir Ahmadu Bello na shekara karo na 11 a ranar Litinin, 24 ga Fabrairu, 2025, a Bauchi, Jihar Bauchi. Taron, wanda aka shirya tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Bauchi, zai girmama marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato kuma Firaministan tsohuwar Yankin Arewa. A bana, taken laccar shi ne “Arzikin Halitta: Juya Albarkatun Yankin Arewa Zuwa Ci Gaban Tattalin Arziki Mai Dorewa.” Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan yadda za a yi amfani da albarkatun noma da ma’adanai da ruwa don bunkasa ci gaban tattalin arzikin...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Dokta Danjuma Adamu Ismaila a matsayin shugaban kwalejin koyon tukin jiragen sama ta Najeriya (NCAT) da ke Zariya. Sanarwar da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce Dakta Ismaila, kwararre kan harkokin sufurin jiragen sama, da manufofin tattalin arziki, ya kammala karatunsa na digiri a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya samu digiri a fannin kimiyyar lissafi a shekarar 1989. Ya kuma yi babbar Difloma ta a fannin Sufuri sannan ya halarci kwasa-kwasan da dama, da tarukan karawa juna sani. Hakazalika memba ne na kungiyar masana harkar sufurin jiragen sama ta Birtaniya, wato Aeronautical Society, UK, da Ƙungiyar Binciken Sufurin Jiragen Sama, da...
    Shugaban kasar Iran da Sarkin kasar Qatar sun jaddada muhimmancin hadin gwiwa da taimakekkeniya tsakanin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamid Al Thani sun gudanar da taron manema labarai na hadin gwiwa a birnin Tehran, inda suka jaddada karfin dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma muhimmancin kara inganta taimakekkeniya a tsakanin kasashensu. Shugaban na Iran ya fada a yammacin yau Laraba cewa: Ci gaba da tarukan tsakanin jami’an kasashen biyu ke yi na tabbatar da kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu, yana mai jaddada karfafa alaka da kasashe makwabta, musamman kasar Qatar, a matsayin wani muhimmin ka’ida na manufofin ketare na Iran. Shugaban kasar ya ci gaba da...
    Ofishin Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF da ke Kano, ya ce zai ci gaba da hada gwiwa da gwamnatin jihar Jigawa a bangarori da dama da suka hada da kiwon lafiya, da ilimi, da samar da abinci mai gina jiki, da kare yara, da al’umma. Shugaban ofishin , Mista Rahama Rihood Farah ya bayyana hakan a Dutse, babban birnin jiharJigawa. Ya kara da cewa, hadin gwiwar da UNICEF ya yi da gwamnatin jihar Jigawa ya samu nasarori da dama, kamar karfafa tsarin tantance yaran da suke cikin kangin talauci, ta hanyar binciken da aka gudanar a kwanan baya (GHS), da samar da muhimman tsare-tsare da tsare-tsare, da kuma sanya masu ruwa da tsaki a tsarin....
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta fuskanci cewa dole ta mika wuya tare da amincewa da sulhu da ‘yan gwagwarmaya da ta nemi murkushe su Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya ba su cimma ko daya daga cikin munanan manufofinta ba, kuma daga karshe ya zama tilasta su mika wuya tare da amincewa da sulhu da bangarorin da suke son kawar da su. Babban sakataren kungiyar jihadul-Islami ta Falasdinu Ziyad Nakhalah, da ya ziyarci birnin Tehran a karkashin jagorancin wata tawaga don tuntubar hukumomin kasar Iran ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sayyid Abbas Araqchi a yammacin jiya Talata. Haka nan yayin da yake ishara da halaltacciyar  gwagwarmayar...
    Kwamandan dakarun juyin juya halin Musulunci na rundunar sararin samaniya ya jaddada cewa; Babu shakka Iran zata kaddamar da harin daukan fansa kan haramtacciyar kasar Isra’ila na alkawarin gaskiya na 3 Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na rundunar Sojin sararin samaniyar Iran, Birgediya Janar Amir Ali Hajizadeh, ya jaddada cewa za a gudanar da farmakin daukan fansa na Alkawarin Gaskiya na 3 idan Allah Ya yarda, amma Iran ba zata barnatar da kwarewarta a banza  kamar yadda ya faru a harin alkawarin Gaskiya ta 1 da ta 2 ba, don haka babu shakka za a gudanar da harin daukan fansa kan haramtacciyar kasar Isra’ila. Ya kara da cewa: Yankin yammacin Asiya ya samu ci gaba da dama, kuma...
    Kungiyar Hamas ta ki amincewa da sabbin sharuddan fira ministyan gwamnatin mamayar Isra’ila na yarjejeniyar Gaza kashi na biyu Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu a hukumance ya yanke shawarar fara tattaunawa kan mataki na biyu na yarjejeniyar Gaza, tare da sanya sabbin sharudda. A nata bangaren kungiyar Hamas ta ki amincewa da sharadin ficewarta daga yankin Zirin Gaza da kuma yin fatali da bukatar ajiye makamai a matsayin wani bangare na kowace yarjejeniya. A yayin da ake fara shirye-shiryen fara gudanar da mataki na biyu na shawarwari tsakanin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da kungiyar Hamas bisa tsarin tsagaita bude wuta da yarjejeniyar musayar fursunoni, gwamnatin yahudawan sahayoniyya yana ci gaba da yin jinkiri ta hanyar kokarin kafa sabbin...
    Jarin da kasar Sin ke zubawa wajen inganta lafiyar muhalli mai dorewa a duniya ya nuna muhimmiyar rawar da take takawa ta wannan fuskar. A shekarar 2024, kasar ta jagoranci duniya wajen zuba jarin sauya makamashi, inda ta zuba dalar Amurka biliyan 818 a wannan bangare. Wannan jarin ya sanya kasar Sin ta zama cibiyar samar da makamashi mai tsafta a duniya domin ita ke da kusan kashi 50 cikin dari na tasoshin samar da man “hydrogen” mara gurbata muhalli a duk duniya. Kasar Sin ta nuna wa duniya kyakkyawan misali abin koyi kamar yadda Shugaba Xi na kasar ke ci gaba da yayata muhimmancin kiyaye halittun doron kasa da kuma maye makamashi mai gurbata muhalli da mai tsafta. Shi...
    Kungiyar manyan sakatarorin ma’aikatun jihar Zamfara(ZASPEF) ta sha alwashin ci gaba da bayar da shawarwari don inganta iyyuka da sha’anin mulki. Zababben shugaba Malam Yakubu Sani Haidara ne ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da su a matsayin sabbin shugabannin kungiyar a Gusau. Yakubu Sani Haidara ya bayyana cewa, yayin da ma’aikatan gwamnati ke ci gaba da bunkasa, za su ci gaba da bayar da shawarwarin ci gaba da gudanar da shirye-shirye na inganta karfin harkokin mulki. Shugaban ya bayyana cewa, wannan yunkurin zai sa a fi amfani da shawarwarin manyan  Sakatarorin wajen tsara manufofi da aiwatar da su. Sani Haidara ya kuma ce a matsayinsu na manyan masu gudanar da mulki, ya ba da tabbacin goyon bayansu...
    Ban da haka, idan mun mai da hankali kan cudanyar kasashe daban daban, da zamansu tare a cikin duniya, za mu san huldar da ake da ita tare da Amurka, wani bangare ne kawai na huldar kasa da kasa. Saboda haka, yayin da wata kasa ta gamu da matsala, idan wata kasa ta nade hannu, ba ta son ba da taimako, tabbas ba za a rasa bangarorin da ke son samar da taimakon ba. Matukar an yi kokarin kulla abokantaka bisa ra’ayi na daidaiwa daida, da amfanawa kowa, to, tabbas ba za a rasa abokin hulda ba. Sai dai idan mun nazarci sabbin matakan gwamnatin kasar Amurka, za mu ga kusan dukkansu na da nufin tsimin kudi da tabbatar da...
    ’Yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da yin awon gaba da aƙalla wasu 10 a hare-haren da suka kai Ƙananan Hukumomin Wushishi da Rafi a Jihar Neja. Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa waɗanda aka kashe sun haɗa da ɗan sa-kai da wani mutum mai saran itace. Hana Biza: Najeriya ta cancanci a girmama ta – Babban Hafsan Tsaro Rayuka 10 da dukiyar N11bn sun salwanta yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a Kano Har ila yau, ya ce wani ɗan sa-kai na daga cikin waɗanda aka sace. “A halin yanzu, ’yan bindiga suna cikin dajin Akare. Sun sace ɗaya daga cikin ‘yan sa-kai, kuma yana da bindigogi biyu a tare da shi...
    Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya gargaɗi ƙasashe cewa Najeriya ba za ta yarda da rashin girmamawa daga kowace ƙasa ba. Ya bayyana hakan ne bayan da Ƙasar Kanada ta hana wasu jami’an sojin Najeriya takardae izinin shiga ƙasar, duk da cewa an gayyace su don halartar wasannin Invictus a Vancouver. ’Yan bindiga sun Kashe mutum 2 kan jinkirin biyan kuɗin fansa Gwamnatin Gombe ta horar da makiyaya kan sabbin hanyoyin kiwo Da yake jawabi a Hedikwatar Tsaro da ke Abuja, bayan tarbar sojojin da suka halarci gasar, Musa ya nuna takaicinsa kan yadda ake nuna wa ‘yan Najeriya rashin adalci a wasu ƙasashe. “Mun bi dukkanin matakan da suka dace. An aiko mana da gayyata, jami’an gwamnati...
    Shugaba Tinubu, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar, ya yaba da irin hazakar da Ishiekwene ke da ita a fannin sharhi da nazari kan harkokin siyasa, tattalin arziki da halin da Nijeriya ke ciki.   Shugaban ya yaba da gudummawar da ya ke bayarwa wajen bunkasa yanayin kafafen yada labarai na Nijeriya, don haka, shugaba Tinubu na yi masa fatan alkairi a rayuwa ta gaba mai zuwa da karin kaifin basira.   Ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da Ya ba dan jaridan lafiya da samun biyan bukata a dukkan ayyukansa.
    ’Yan bindiga sun kashe wasu mazauna ƙauyen Gwargwada da ke Ƙaramar Hukumar Kuje a saboda jinkirin biya musu kuɗin fansa. Mutanen da aka kashe, sun haɗa da Mohammed Danladi da Nasiru Yusuf, wanɗanda aka sace su ne a ranar Laraba tare da wani makiyayi da wata mata a mahaɗar Gwombe, a kan hanyar Gwargwada zuwa Rubochi. Gwamnatin Gombe ta horar da makiyaya kan sabbin hanyoyin kiwo Rayuka 10 da dukiyar N11bn sun salwanta yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a Kano Wani ɗan uwan mamatan, Shuaibu Abdullahi, ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun nemi iyalan waɗanda lamarin ya shafa su biya wa kowa Naira 500,000 amma Naira 500,000 suka iya tattaraws baki ɗayansu. “Shugaban maharan ya kira mu ranar Juma’a, muka...
    Gwamnatin Jihar Gombe ta horar da makiyaya 684, ciki har da nakasassu, mata, matasa, da tsofaffin ma’aikata, kan sabbin dabarun kiwon awaki da kasuwancinsu. Wannan horo ya gudana ne ƙarƙashin shirin Livestock Productivity and Resilience Support (L-PRES). Rigima ta sake kaurewa tsakanin PDP da APC a Zamfara Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno Kwamishinan Aikin Gona, Kiwo, da Hada-hadar Ƙungiyoyi na Jihar Gombe, Dokta Barnabas Malle ne, ya jagoranci ƙaddamar da horon a Gombe. Yayin da yake jawabi, ya jaddada ƙudirin gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, na inganta kiwon dabbobi da tallafa wa al’umma. Ya ce: “Shirin ya dace da manufofin gwamnati na bai wa kowa damar cin gajiyar shirye-shiryen da ake gudanarwa.” Shugaban shirin L-PRES...
    A cewarsa, amincewar wani gagarumin yunkuri ne na tallafawa dorewar tsafar muhalli a jihar.   Ya yaba da yadda jihar ke ci gaba da kokarin inganta rayuwar ‘yan jiharta da kuma tsaftar muhalli.
    Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan zanga-zangar yunwa, ya gano cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum bakwai suka samu munanan raunuka. Rahoton ya kuma bayyana cewa an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11, sakamakon ƙone-ƙone, sace-sace, da lalata kadarorin gwamnati da na ’yan kasuwa a faɗin jihar. Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram Da yake jawabi a taron majalisar zartaswar ta jihar karo na 25 a ranar Talata, Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi rahoton daga shugaban hannun kwamitin, Mai shari’a Lawan Wada (ritaya). Ya tabbatar da cewa za a fitar...
    Wani sabon rikici ya sake kunno kai a tsakanin manyan jam’iyyun siyasa biyu a Jihar Zamfara. Rigimar wadda ta kunno tsakanin APC da PDP ta samo asali ne tun bayan da wasu matasa suka yi yunƙurin hana wani taro na ɗan Majalisar Wakilai da za a gudanar a garin Maru. Mutum 10 sun rasu, an lalata dukiyar N11bn yayin zanga-zangar yunwa a Kano — Rahoto Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno Hakan ya sa Gwamnatin Zamfara ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal ta ɗauki wani matakin da take ganin zai kawo lafawar lamarin. Sai dai kuma matakin da gwamnatin ta ɗauka bai yi wa jam’iyyar APC daɗi ba, inda ta nuna rashin gamsuwa tare da zargin ba a...
    Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan zanga-zangar yunwa, ya gano cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum bakwai suka samu munanan raunuka. Rahoton ya kuma bayyana cewa an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11, sakamakon ƙone-ƙone, sace-sace, da lalata kadarorin gwamnati da na ’yan kasuwa a faɗin jihar. Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram Da yake jawabi a taron majalisar zartaswar ta jihar karo na 25 a ranar Talata, Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi rahoton daga shugaban hannun kwamitin, Mai shari’a Lawan Wada (ritaya). Ya tabbatar da cewa za a fitar...
    “Kungiyar malaman jami’o’i, reshen KASU na son sanar da jama’a cewa, majalisar zartaswarta ta kasa ta amince da bukatar reshen kungiyar na tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar, 18 ga Fabrairu, 2025.   “Majalissar ta yi watsi da alkawuran da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka na rashin tabbaci, da cikakkun bayanai, da kuma lokacin da za a iya aiwatar da alkawuran kan biyan hakkokin mambobin kungiyar,” in ji sanarwar.
    Aƙalla mutum 11 sun shaƙi iskar ’yanci bayan kuɓuta daga hannun ƙungiyar mayaƙan Boko Haram masu iƙirarin jihadi a Jihar Borno. Waɗanda suka shaƙi iskar ’yancin na daga cikin mutanen da ƙungiyar Boko Haram ta sace a wani wurin kamun kifi a Doron Baga. Majalisar Edo ta tanadi hukuncin kisa kan masu garkuwa da mutane USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram Wata majiya ta bayyana cewa, wani kwamandan ’yan ta’addan mai suna Tar ne ya jagoranci garkuwa da mutanen ne a ranar 13 ga watan Fabrairu 2025. Tar da tawagarsa da ke addabar masunta da manoma a gaɓar Tafkin Chadi sun ɗauke mutanen ne yayin da suka afka wa al’ummar Shawaram da ke ƙarƙashin Ƙaramar...
    Kamfanin dillancin labarun Qatar ( Qana) ya sanar da cewa, sarkin kasar Sheikh Tamim Bin Hamad ali-Sani ya baro Doha akan hanyarsa ta zuwa Tehran. Majiyar ta kara da cewa, sarkin na Qatar zai zo da tawagar tattalin arziki da kuma siyasa. Baya ga batun tattalin arziki, bangarorin biyu za su tattauna  batutuwan da su ka shafi  Gaza da kuma Amurka, kamar yadda kamfanin dilllancin labaun Mehr ya nakalto. Jakadan Jamhuriyar musulunci ta Iran a Qatar, ya saanr da cewa ziyarar da sarkin na Qatar zai kawo Tehran tana a karkashin kokarin bunkasa alakar kasarsa da Iran.
    Shugaban kungiyar Hamas Khalilul-Hayyah, ya fadi cewa; A ranakun Alhamis da Asabar masu zuwa ne za a mikawa ‘yan mamaya fursunoni rayayyu da kuma wasu gawawwaki a cikin bude wani shafin na musaya.  A jiya Talata ne dai Khalilul-Hayyah ya sanar da cewa, a bisa yadda aka cimma matsaya a musayar farko da aka yi, a cikin mako na shida daga kulla yarjejeniya, za a shiga wani sabon shafin na  gaba na musayar fursunoni.  Khalil Hayya ya kuma ce a ranar Asabar din mai zuwa ne za a mika sauran fursunoni rayayyu da su ka saura, kamar yadda aka cimma matsaya da adadinsu shi ne 6, biyu daga cikinsu ana rike da su ne tun 2014, yayin da ‘yan mamaya...
    Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran sun sanar da gano da kuma rusa wata kungugun masu yi wa Amurka da Isra’ila leken asiri a yankin Arewacin Iran. Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci a yankin Mazandaran dake arewacin Iran ne ya sanar da bankado da kuma rusa gungun masu yi wa abokan gabar leken asiri, ta hanyar amfani da ‘yan kasashen waje da masu zuwa yawon bude ido. Kwamandan dakarun kare juyin juya halin na Mazandaran ya kara da cewa; Da dama daga cikin wadanda suke leken asirin suna fakewa ne a karkashin kamfanoni na kasuwanci, cibiyoyin al’adu da kuma kungiyoyin agaji.  Bugu da kari kwamandan na dakarun kare juyin juya halin musulunci a gundumar ta Mazandaran...
    Rundunar sojan kasar Sudan ta sanar da kwace iko da  hanyoyin da suke isa al-Fasha, kamar kuma yadda su ka killace fadar shugaban kasa dake birnin Khartum. Sanarwar sojojin na Sudan ta kuma tabbatar da cewa, killace wannan hanyar da su ka yi, ya  yanke duk wata dama da dakarun “Rundunar Kai Daukin Gaggawa” suke da ita, ta samu dauki. Birnin al-Fasha dai shi ne babbar birnin jahar Arewacin Darfur, kuma sojojin na Sudan sun ce, suna ci gaba da kutsawa a cikin jahar. A gefe daya, wani jami’in sojan Sudan Yasir Adha, ya sanar da cewa; Babu yadda yaki zai tsaya har sai an ‘yanto da kowane taku daya na kasar Sudan daga hannun ‘yan tawaye. Adha ya bayyana...
    Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da cewa, ta kakkabo jiragen saman marasa matuki 9 da kasar Ukiraniya ta harba mata. Sanawar ta ma’aikatar harkokin tsaron Rasha ta ci gaba da cewa; A daren jiya ne  aka kakkabo jiragen sama  marasa matuki 3 na kasar Ukiraniya da aka harba a kan yankin Biryansk, sai kuma wani jirgin saman guda daya akan sararin samaniyar Tatrastan. Bugu da kari makaman saman na Rasha  sun kakkabo wasu jiragen sama marasa matuki guda 4 a sararin samaniyar “Bahrul-Aswad”, sai kuma jirgi guda daya a saman yankin Tula. A gefe daya  a jiya ne aka bude wani kwarya-kwaryar taro a tsakanin kasashen Amurka da Rasha a kasar Saudiyya domin tattauna hanyoyin kawo karshen yakin Ukinraniya. Sakataren...
    Ta ce: “Fafutukar sa, hikimar sa mai zurfi, da jajircewar sa wajen cigaban ƙasa sun sa shi ya zama murya mai matuƙar tasiri a siyasar Nijeriya. Za a yi kewar shawarwarin sa masu amfani da kuma gudunmawar sa ba tare da son rai ba wajen gina ƙasa.”   Idris ya miƙa ta’aziyya ga iyalan Cif Clark, da gwamnatin Jihar Delta, da ɗaukacin ’yan Nijeriya da suka amfana da irin rayuwar sa ta hidimar jama’a.   “Muna addu’ar Allah ya jiƙan sa, ya uma ba iyalan sa da duk masu jimami haƙuri da juriya,” inji shi.