Moscow : Dole ne Rasha da China su shiga tattaunawar nukiliya da Iran
Published: 23rd, March 2025 GMT
Kasar Rasha ta bayyana cewa dole Moscow da Beijing su shiga shawarwarin tattaunawar nukiliya da Iran.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta bayyana cewa, Moscow a shirye take ta samar da ingantacciyar hadin gwiwa da dukkan bangarorin kan batun yarjejeniyar nukiliyar Iran.
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa ya aike da wasika zuwa Tehran domin fara tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran; yayin da shi da kansa ya fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran a wa’adinsa na farko.
A halin da ake ciki dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martani ga wasikar shugaban Amurka Donald Trump a cikin kwanaki masu zuwa ta hanyoyin da suka dace.
Araghchi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi kai tsaye a gidan talabijin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRIB) ranar Alhamis.
Araghchi ya kuma lura cewa a wannan karon, ci gaban ya zo tare da wani yunkuri na diflomasiyya daga Amurkawa, ciki har da wasika da bukatar yin shawarwari.
Ya kuma bayyana cewa manufar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a bayyane take. “Ba za mu shiga tattaunawa kai tsaye karkashin matsin lamba, barazana, ko karin takunkumi.”
Ministan harkokin wajen kasar ya kuma bayyana cewa wasikar “mafi yawan barazana ce,” amma kuma akwai damamaki a ciki.
A farkon watan Maris ne Trump ya bayyana cewa ya rubuta wasika zuwa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: bayyana cewa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Amurka Ta Yi Da’war Cewa; Ba Ta Neman Tashin Hankali Tsakaninta Da Iran
Gwamnatin Amurka ta sanar da cewa: Ba ta neman tada tashin hankali tsakaninta da Iran
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Samuel Werberg ya bayyana cewa: Kasarsa ba ta neman kara ruruta wutar rikici da Iran, yana mai jaddada cewa har yanzu kofar diflomasiyya a bude take, duk kuwa da kakkausar murya da Amurka ta yi na kin amincewa Iran ta mallaki makamin nukiliya.
Werberg ya kara da cewa; Za su ci gaba da riko da siyasar matsin lamba da nufin dakatar da ci gaba a shirin nukiliyar Iran.
Kakakin na Amurka ya bayyana cewa, “Dole ne Iran ta nuna kyakkyawar niyyarta kafin ta yi magana kan duk wata nasara da za a samu.