’Yan Najeriya miliyan 150 sun samu ingantacciyar wutar lantarki – Minista
Published: 18th, April 2025 GMT
Ministan Wutar Lantarki, Adedayo Adelabu ya bayyana cewa kimanin ’yan Najeriya miliyan 150 ne yanzu ke samun isasshiyar wutar lantarki, yayin da miliyan 80 ke da ƙarancin wutar lantarki.
Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a yayin taron sabunta sassan ministoci na 2025 da aka gudanar a Abuja, inda ya yi magana tare da ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Malagi, da sauran masu ruwa da tsaki.
Adelabu ya bayyana cewa ci gaban ya samo asali ne daga shigar Najeriya cikin shirin “Mission 300” – wani gagarumin ƙoƙarin haɗin gwiwa na Bankin Duniya da Bankin Raya Afirka (AfDB) da nufin samar da wutar lantarki ga ‘yan Afirka miliyan 300 nan da shekarar 2030.
“Ƙa’idar ta tsara kyawawan manufofi don haɓaka hanyoyin samar da wutar lantarki, ƙara haɓaka makamashi da inganta hanyoyin magance matsalolin dafa abinci mai tsabta ga miliyoyin ‘yan Najeriya – wato Mission 300, kuma muna samun ci gaba mai kyau a kan wannan,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, “Ina mai farin cikin gaya muku cewa cikin ‘yan Afirka miliyan 300 da Bankin Duniya da AfDB ke son cimmawa, Najeriya na kan hanyar da za ta biya ƙasa da kashi 25 cikin 100, wanda ke nufin kusan ‘yan Najeriya miliyan 75. Da muka gabatar da yarjejeniyarmu, sun amince da mu.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan Najeriya Adedayo Adelabu Wutar Lantarki wutar lantarki yan Najeriya
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Ainihin Abin Da Ke Hana Matan Arewa Koyon Ilimin Kimiyya
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Dakta Zainab Muhammad ’yar Arewacin Najeriya ce da ta jajirce tare da ƙudirin cika burinta na karantar fannin kimiyya duk da ƙalubalen da matan yankin suke fuskanta wurin karantar fannin.
Dakta Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci ɗaya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala, wanda a mafi yawan lokuta, ba mata kaɗai ba, har da mazan ma na ƙaurace wa karatar sa.
NAJERIYA A YAU: Dalilan Rikice-Rikice A Jihar Filato DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan RiƙoZainab ƙwararriyar likita ce wacce ta shahara wajen kula da marasa lafiya a asibitoci.
Domin sauke shirin, latsa nan