2025-04-10@10:38:45 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3106
«wutar lantarki»:
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ba shi da wata adawa da Amurkawa masu zuba jari a kasar. “Muna maraba da masu zuba jari.” amma ba tare da tauye mutunci ko tsaron kasa ba. Har ila yau kalaman nasa sun sake tabbatar da kin amincewar da Iran ta dade tana yi na yin watsi da shirye-shiryen mallakar makamin nukiliya, wanda kasashen yammacin duniya ke zarginta da neman bama-baman nukiliya. “Muna shirye don yin shawarwari, ba kai tsaye ba. Ba mu amince da su ba. Dole ne a yi tattaunawa bisa mutunta juna inji shugaban kasar ta Iran. “Ba mu taba kera bama-bamai na nukiliyaba, ko a baya,...
Gwamnatin Washington ta sanar da kakabawa Iran sabbin takunkumai kan shirinta na nukiliya an zaman lafiya, a matakin da Amurka ke ganin shi ne kawai hanyar matsin lamba kan Iran domin ta mika wuya game da shirint ana nukiliya. Takunkumin, wanda ma’aikatar baitul malin Amurka ta sanar a jiya Laraba, ya shafi hukumomi biyar da kuma wani mutum guda da ke Iran, saboda abin da sashen ya bayyana a matsayin goyon bayan shirin nukiliyar Iran. Baitul malin na Amurka ya ce bangarorin da aka laftawa takunkumin na baya baya nan sun hada da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI) da ta karkashinta, Kamfanin Fasaha na Centrifuge na Iran. Sakataren baitul malin kasar Scott Bessent ya bayyana a cikin wata sanarwa...
Kungiyar ci gaban kasashen yammacin Afirka, ECOWAS ta nuna damuwa kan takun-tsakar da ya kunno kai tsakanin kasar Mali da makwafciyarta Aljeriya, lamarin da ya kai ga kasashen biyu janye jakadu a tsakaninsu. A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ecowas ta ce “Tana bibiyar abin da ke faruwa wanda ya shafi dangantakar da ke tsakanin kasar Mali da kuma Aljeriya. Ecowas din ta ce ta damu matuka kan lamarin, tana kuma mai kira ga kasashen na Mali da Aljeriya da su kai zuciya nesa, su yi amfani da hanyoyin diflomasiyya wajen warware sabanin ra’ayin da ke a tsakaninsu.” Dangantaka tsakanin Mali da Aljeriya, ta yi tsami ne bayan da a makon da ya gabata Aljeriya ta kakkabo wani jirgi...
A ranar Talata ne mai martaba Sarkin Kano Malam Mohammad Sunusi II ya amince da nadin Alhaji Mannir Sunusi a matsayin sabon Galadiman Kano. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ‘yan jarida da yada labarai na masarautar Kano, Saddam Nasir Na’ando ya fitar, kuma ya mika wa gidan rediyon Najeriya da ke Kano. Haka kuma Sarki Sunusi II ya amince da nadin Alhaji Kabiru Tijjani Hashim zuwa Wamban Kano. Sauran nada nade sun haɗa da “Alhaji Mahmoud Ado Bayero ya tashi daga Tafidan Kano zuwa Turakin Kano da Adam Sanusi yanzu ya zaman Tafidan Kano sai kuma Ahmed Abbas Sanusi ya zamaYariman Kano. Sanarwar ta kara da cewa wadannan nade-naden sun fara...
Wannan rikicin haraji ya faro ne tun shekarar 2018, lokacin da Trump ya fara ƙaƙaaba wa China da wasu ƙasashe haraji mai tsanani kan kayayyakin da ake shiga da su Amurka, a wani yunƙuri na kare masana’antu da ayyukan yi a cikin gida. Sai dai masana tattalin arziƙi sun ce wannan mataki zai iya kawo tasiri ga farashin kayayyaki a Amurka da kuma haifar da sabuwar ɓaraka a dangantakar cinikayya tsakanin manyan ƙasashen duniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mazauna karamar hukumar Gezawa ta Kano sun shiga cikin tashin hankali da makoki sakamakon nutsewar wasu mata biyu a cikin wani tafki. Rahotanni sun nuna cewa matan (an sakaya sunansu) sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke wanka a kogi bayan sun dawo daga aiki a wata masana’antar sarrafa hibiscus. A cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Yusif Abdullahi Gezawa hukumar kashe gobara ta samu kiran gaggawa daga ‘yan banga da ke yankin tare da bayyana cewa “Yan uwan matan biyu ne suka kai rahoton lamarin ga dan banga” Ya yi nuni da cewa, nan take aka tura tawagar masu aikin ceto zuwa wurin, inda suka yi nasarar...
Buhari ya gode wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bisa gyaran da aka yi masa a gidansa na Kaduna. Ya gode wa gwamnonin APC da suka kai masa ziyara domin taya shi murnar Sallah, inda ya ce wasu daga cikinsu ya yi aiki tare da su, yayin da wasu kuwa sabbi ne. Shugaban gwamnonin kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ya ce sun kai ziyarar ne domin nuna godiya da girmamawa da gudunmawar Buhari wajen gina demokradiyya da ƙarfafa jam’iyyar APC. Uzodinma ya yaba wa Buhari saboda salon shugabancinsa, da yadda ya miƙa mulki cikin natsuwa ga wani shugaban APC, tare da aiwatar da shirye-shirye a fannonin tsaro, noma, ilimi da ababen more rayuwa. Ya ce a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu,...
Ya tabbatar da cewa majalisar za ta ci gaba da mara wa shirye-shiryen da za su bunƙasa ilimi da jin daɗin al’umma baya. Shugaban majalisar ya ƙara da cewa salon shugabancin gwamnan wanda ke ku8nshe da gaskiya da riƙon amana ya taimaka wajen amincewar jama’a ga gwamnati. Ya ce Gwamna Yusuf jagora ne mai sauraron ƙorafin jama’a tare da himma wajen biyan buƙatunsu. Ya buƙaci gwamnan da kada ya yi ƙasa a gwiwa wajen ci gaba da aikinsa duk da sukar da wasu ke masa. Haka kuma ya shawarci sauran jami’an gwamnati da su kwaikwayi irin sadaukarwar gwamnan wajen yi wa al’umma aiki. An gudanar da bikin bayar da lambar yabon ne a Abuja, inda aka yaba wa Gwamna Yusuf...
Runduna ta 8 ta sojojin Najeriya ta fara gasar wasanni ta kasa da ake gudanarwa duk shekara a jihar Sokoto da nufin karfafa sojojin Najeriya don shiryawa tsaron kasa. Babban Jami’in Kwamandan runduna ta takwas Manjo Janar Ibikunle Ajose ya ce gasar tana nuni ne kai tsaye ga hafsan hafsoshin sojin kasar na ganin an gyara da sauya dabarun jagoranci da fagen fama a matakin farko. GOC wanda ya samu wakilcin kwamandan runduna ta 78 da ke samar da kayayyaki da sufuri, Birgediya Janar Moses Udom Ikobah, ya bayyana cewa fafatawar ta yi daidai da kokarin da rundunar sojojin Najeriya ke yi na inganta yaki da ta’addanci ta fuskar tsaro. Ya bukaci dukkan mahalarta taron da su...
Lauyan kare hakkin bil’adama Femi Falana SAN ya yabawa jihar Kano bisa yadda take tafiyar da harkokin shari’a. Falana ya bayyana hakan ne a yayin wani taron karawa juna sani ga masu gabatar da kara kan ingancin gudanar da shari’ar laifuka da Kurawa Hussein And Associates tare da hadin giwar Ma’aikatar Shari’a ta Kano suka shirya, wanda aka gudanar a otal din Bristol Kano. Falana ya yabawa jihar Kano bisa amincewa da dokar hukumar kula da laifuka ta FIDRA a shekarar 2019 tare da zama jiha ta farko da ta soke tuhumar da jami’an ‘yan sanda ke yi na aikata laifuka. Ya kuma jaddada bukatar masu gabatar da kara su samar da na’urori na zamani da...
Akalla malaman makarantun firamare 1,800, a fadin kananan hukumomi goma sha shida na jihar Kwara, aaka horar da su kan kara kuzari kan ilimin zamani, hanyoyin amfani da kayan zamani wajen koyarwa. Da yake bayyana taron bitar na kwanaki goma da aka bude a makarantar sakandire ta Queen Elizabeth da ke Ilorin wanda KwaraLEARN tare da hadin gwiwar hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kwara (KWSUBEB) ta shirya, kwamishinan ilimi da ci gaban bil’adama na jihar, Dokta Lawal Olohungbebe ya ce shirin na daya daga cikin manyan dabarun da jihar ta bullo da shi na bunkasa harkar ilimi domin ya dace da ka’idojin karni na 21. Ya kuma bukaci malaman da su ci gaba da jajircewa...
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya nuna kaɗuwar sa bisa rashin da aka yi na ɗan Majalisar Dokokin jihar, Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji, ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Ƙauran Namoda ta Kudu. Iyalai sun bayyana cewa Hon. Aminu Kasuwar Daji ya rasu ne a cikin barcin sa da asubahin ranar Larabar nan a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa gwamnan ya miƙa ta’aziyyar sa ga Majalisar Dokokin jihar da Iyalan mamacin. Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta aika da tawaga ta musamman, ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Mallam Mani Mummuni a yayin jana’izar ta marigayi Aminu K/Daji in...
Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, ta tabbatar da sace wani dalibi dan aji 4 na Jami’ar Tarayya ta Birnin Kebbi, mai suna Augustine Madubiya, mai shekaru 23 da haihuwa, wanda ke Sashen Tattalin Arziki zuwa inda ba a san inda aka nufa ba. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, ya shaida wa manema labarai cewa, wasu gungun ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai farmaki gidan Istijaba Villa da ke karamar hukumar Kalgo a jihar inda suka yi garkuwa da wani dalibi a dakin kwanan dalibai a harabar jami’ar, kuma abin bakin ciki, wani Malam Siddi Hussaini, wanda ke kusa yana kiwon shanun sa, a lokacin da yake kokarin shiga tsakani, shi...
“Ina rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, ya sa ya huta har abada.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) za ta hada gwiwa da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) a yaki da hako ma’adinai da kuma ayyukan ta’addanci a kasar nan. Mukaddashin Daraktan shiyyar Kaduna mai kula da shiyyar Kaduna, Mista Bawa Usman Kaltungo ne ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci tawagar ofishin shiyya ta Kaduna na EFCC zuwa NUJ a jihar Neja a Minna. Mista Bawa Usman wanda ya shaida wa manema labarai cewa an kama masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba amma ya ci gaba da cewa “yaki da wadannan laifuffuka ba na EFCC kadai ba ne domin yana da girma da yawa a gare mu don haka yana bukatar hadin...
Yankin Kogi ta Yamma na fama da matsalar tsaro, inda aka ruwaito wasu mazauna garin Oduape a Ƙaramar Hukumar Kabba Bunu sun gudanar da zanga-zanga a bara domin nuna fargabarsu game da yawaitar sace-sace da kashe-kashe. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Ina rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, ya sa ya huta har abada.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Buhari ya gode wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bisa gyaran da aka yi masa a gidansa na Kaduna. Ya gode wa gwamnonin APC da suka kai masa ziyara domin taya shi murnar Sallah, inda ya ce wasu daga cikinsu ya yi aiki tare da su, yayin da wasu kuwa sabbi ne. Shugaban gwamnonin kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ya ce sun kai ziyarar ne domin nuna godiya da girmamawa da gudunmawar Buhari wajen gina demokradiyya da ƙarfafa jam’iyyar APC. Uzodinma ya yaba wa Buhari saboda salon shugabancinsa, da yadda ya miƙa mulki cikin natsuwa ga wani shugaban APC, tare da aiwatar da shirye-shirye a fannonin tsaro, noma, ilimi da ababen more rayuwa. Ya ce a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu,...
Ya jinjina wa haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da al’umma, yana mai cewa hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar aikin. Gwamnati ta yaba da ƙwazon jami’an da suka halarci aikin kuma ta sha alwashin ci gaba da yaƙi da ‘yan ta’adda a faɗin jihar. “Za mu ci gaba da fatattakar waɗanda ke barazana ga zaman lafiya a Katsina. Za mu yi amfani da duk wata hanya da albarkatu domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a,” in ji Kwamishinan. Ya kuma buƙaci jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai, yana mai jaddada cewa haɗin kan al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen kawo ƙarshen ‘yan bindiga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...

Sin Ta Kara Wasu Kamfanonin Amurka 12 Cikin Jerin Wadanda Ta Dakatar Da Fitar Musu Da Wasu Kayayyaki Daga Kasar Sin
Bisa umarnin haramcin, za a dakatar da duk wasu huldodin fitar da hajoji daga kasar Sin zuwa wadannan kamfanoni nan take. Kazalika, a cewar ma’aikatar cinikayyar ta Sin, idan akwai wata bukata ta wajibi, dole ne sassan da za su gudanar da wata hulda mai alaka da hakan su tabbatar sun nemi izni. Ban da haka kuma, ma’aikatar ta ce kasar ta kara sunayen wasu kamfanonin Amurka 6, cikin jerin sassan da ba za a iya dogaro da su ba. Ma’aikatar wadda ta bayyana hakan a Larabar nan, ta ce kamfanonin su ne Shield AI, da Sierra Nevada Corporation, da Cyberlux Corporation. Sai kuma Edge Autonomy Operations LLC, da Group W and Hudson Technologies. Tun daga karfe...
An yi nasarar kashe wani ɗan bindiga yayin da jami’an tsaro suka kuɓutar da mutane 10 da aka sace a wani samame na haɗin gwiwa a karamar hukumar Musawa ta jihar Katsina. Waɗanda aka ceton da suka haɗa da mata shida da maza huɗu, an yi garkuwa da su ne daga kauyukan Kiroro, Kabbi, da Dogon Marke da ke karamar hukumar ta Musawa. Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 4, Sun Sace 45 A Katsina Sin Ta Fitar Da Takardar Matsayarta Kan Alakar Tattalin Arziki Da Amurka A cewar sanarwar da kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na Katsina, Nasir Mua’zu ya fitar, an kai samamen ne da misalin karfe 10 na daren ranar 8 ga watan Afrilu a...
Al’ummar Karamar Hukumar Maigatari sun yi kira ga gwamnatin jihar Jigawa da ta taimaka wajen gina hanyoyin da za su hada garuruwansu. Wani mazaunin yankin, Malam Ali A. Bulama Turbus, wanda ya wakilci al’ummomin yayin da yake magana da Rediyon Najeriya a Maigatari, ya jaddada muhimmancin aikin gina hanyar. Ya bayyana cewa samar da hanya a yankin zai rage matsalolin sufuri da mazauna yankin ke fuskanta, musamman wajen samun damar zuwa asibiti da sauran wuraren kula da lafiya. Ya ce, samar da hanyar kuma zai kara bunkasa harkokin kasuwanci, da karfafa dangantaka tsakanin al’umma da kuma saukaka wasu bukatu na yau da kullum da ke da matukar muhimmanci ga cigaban yankin. Malam Ali Turbus ya kuma roki shugabannin karamar hukumar...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta samu nasarar samo ingantaccen masauki ga alhazan jihar a birnin Makkah, gabanin gudanar da aikin Hajjin 2025. Daya daga cikin mambobin kwamitin musamman da ke kula da aikin hukumar, Malam Buhari Marabar-Jos ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata a Kaduna. Buhari Marabar-Jos ya bayyana cewa masaukan sun cika dukkan sharuddan da Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) da Ma’aikatar Hajji ta Saudiyya suka gindaya. Ya kuma bayyana cewa wata tawaga ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar, Malam Salihu Abubakar, tana can ƙasar Saudiyya don kammala sauran shirye-shirye kafin dawowarsu Najeriya. Ya jaddada cewa Gwamna Uba Sani ya ƙuduri aniyar kula da jin daɗin alhazan jihar, tare...
Idan Barcelona ta kai matakin gaba za ta hadu da PSG ko Aston Villa wadanda su ka buga dayan wasan da aka buga a daren ranar Laraba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Dokar bunkasa ci gaban Afirka da samar da dama ga yankin (AGOA), wacce ta bai wa kasashen yankin damar fitar da kayayyaki zuwa Amurka ba tare da haraji ba, ta shiga gararamba bisa yadda karin harajin zai kassara masana’antu kamar su masaku, da na karafa, da kuma noma. Nijeriya da Afirka ta Kudu da suka fi karfin tattalin arziki a yankin, Amurka ta kakaba musu haraji na kaso 14% da 30% bi-da-bi, saboda rashin imani kuma karamar kasa kamar Lesotho wacce du-du-du karfin tattalin arzikinta na GDP bai wuce dala biliyan 2 ba, aka dankara mata karin harajin da kashi 50%. Galibin tattalin arzikin kasashen Afirka ya fi dogaro ne da fitar da kayayyaki zuwa ketare don dorewar...
Assalamu alaikum masu sauraro barakammu da war haka, sharhin bayan labarummu zai yi magana dangane da ‘Siyasar Amurka ta fara yakin kudaden fito tsakaninta da China da kasashen Turai da sauransu. Wanda ni tahir amin zan karanta. ///.. A ranar laraba 2 ga watan Afrilun da muke ciki ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fidda jadawalin kudaden fito ga dukkan kayakin da suke shigowa Amurka daga wadannan kasashen, daga ciki har da kasashen Turai da kuma kasar Chaina, ya zuwa yanzu dai kasar china ta maida martani da kashi 34% na kayakin Amurka da suke shigowa kasar China, sannan Amurka ta kara maida martani ga kasha 104 kan kayakin kasar china masu shigowa Amurka, sannan kasashen turai da dama...
Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da wani mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai a garin Banga, da ke cikin karamar hukumar Kauran Namoda, inda aka kashe mutane biyu tare da sace wasu da dama. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar, DSP Yazid Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilinmu da ke Gusau, babban birnin jihar. DSP Abubakar ya ce bincike na ci gaba da gudana domin gano adadin mutanen da aka sace a harin. Ya tabbatar da cewa ana kokari don ganin an ceto mutanen da aka sace cikin koshin lafiya. Yazid ya kara da cewa an kara kaimi wajen daukar matakan tsaro domin hana faruwar irin...
Don haka bangaren Sin ya kalubalanci kasar Amurka da ta gyara kuskurenta cikin hanzari, ta soke dukkan matakan kara buga harajin kwastam kan kasar Sin daga bangare daya, kana ta hau teburin shawarwari tare da kasar Sin, don daidaita matsalolinsu bisa tushen girmama juna. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa JMI ba zata taba jada baya a kan shirinta na makamashin Nukliya ba, kuma yayi allawadai da duka wani shiri na kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar Hare-hare. Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana fadar haka a taron raya ranar Nukliya ta karo karo na 19 a wanda aka gudanar a nan Tehran. Shugaban ya kara da cewa, Iran bata neman yaki da kowa, amma zata maida martani kan duk wata takala daga HKI ko Amurka. Ya ce Iran ba zata amince wani ya hana mutanen kasar amfani da fasahar da All..ya hore masu ba. Ya kuma kara jaddada cewa JMI bata neman mallakar makaman Nukliya. A rana irin ta yau ce...

Tarayyar Turai Ta Yi Maraba Da Tattaunawa Tsakanin IRAN da Amurka Kan Shirinta Na Makamashin Nukliya
Kungiyar tarayyar Turai ta yi maraba da tattaunawa tsakanin Amurka da JMI dangane da shirinta na makamashin Nukliya, tare da kara jaddada cewa hanyar diblomasiyya kadai ta rage don warware wannan matsalar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a halin yanzu dai kungiyar tarayyar ta Turai ta na ci gaba da takurawa JMI da takunkuman tattalin arziki, masu tsanani, a lokaci guda tana fadar cewa hanyar Diblomasiyya ce kadai ta rage wajen warware matsalar shirin makamashin nukliya na kasar Iran, wanda ya tabbatar da fuska biyu na kasashen na Turai. Labarin ya kara da cewa, wani mai magana da yawun kungiyar ta EU wanda kuma baya son a bayyana sunansa, ya fadawa kamfanin dillancin labaran IRNA...
Sojojin kasar Yamen sun bada sanarwan maida martani ga hare-haren jiragen yakin kasar Amurka a kan kasar na baya-bayan nan, kuma zasu ci gaba da kai hare-haren kan wadannan wurare har zuwa lokacinda za’a kawo karshen yaki a Gaza. Tashar talabijin ta presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar Yemen Burgediya Janar Yahyah Saree yana fadar haka a yau Laraba . Ya kuma kara da cewa, a wannan karon sun yi amfani da jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa, kan wasu wurare masu muhimmanci a birnin Yaffa (tel’aviv). Haka ma sun cilla wasu makaman kan jirgin yaki mai daukar jiragen sama na Amurka wato USS Harry Truman dake arewacin tekun red Sea. Kafin haka dai jiragen Amurka...
Gwamnatin kasar China ta bada sanarwan kara kodaden fito kan kayakin Amurka wadanda suke shigowa kasa har na kasha 80% sannan a shirye take ta ci gaba da yakin kasuwanci da gwamnatin shugaba Trump har zuwa karshe. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jami’an gwamnatin kasar China na fadar haka a yau Laraba sun kuma kara da cewa, idan gwamnatin Trump bata dakatar da wannan yakin kasuwanci ba to kasar China tana da hanyoyi da dama wadanda zata ci gaba da wannan yakin har zuwa karshe. Kafin haka dai gwamnatin shugaba Trump ta karawa kayakan kasar China masu shigowa Amurka kudaden fito daga kashe 34% zuwa kasha 104 % kuma a yau Laraba ne dokar karin zai...
A ci gaba da kokarinsa na kawo sabon tsari domin inganta harkokin noma a jihar Jigawa, Gwamna Malam Umar Namadi ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar zuwa wani babban taro da manyan masu zuba jari na duniya da masu ruwa da tsaki a harkar noma. Taron wanda ya gudana jiya Talata a otal din Hilton da ke Abuja, ya kunshi wakilai daga kamfanonin SINOMACH, China CAMC Engineering Company Ltd, YTO Group Corporation, da Agra Consortium Ltd, da kuma asusun bunkasa noma na gwamnatin tarayya (NADFUND). Kyautar LEADERSHIP Ta Kara Zaburar Da Mu Kan Sauke Nauyin Al’ummar Jigawa Akanmu – Gwamna Namadi Kasar Sin Na Yaki Da Cin Zalin Da Amurka Ke Yi Ta Hanyar Dora Haraji Ne Bisa Sanin Ya Kamata...
Manajan daraktan cibiyar CGIAR Ismahane Elouafi, ta jaddada cewa idan ana son rage tsadar shigar da abinci nahiyar, wanda a yanzu ya kai kimanin dala biliyan 100 a kowacce shekara, zuba jari wajen inganta kyawun kasa da samar da ruwa da rainon ingantattun irrai masu samar da kyakkyawar yabanya, na da matukar amfani. Ta ce nahiyar Afrika za ta iya cin gajiyar fasahohin aikin gona na kasar Sin, da wanda ya dace da hadin gwiwar kasashe masu tasowa, domin bunkasa noma a cikin gida da ma fitar da amfanin gonar. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
Wadda aka tsara a cikin babi shida, takardar matsayar ta gwamnati ta sake tabbatar da yanayin moriyar juna ta cinikayya tsakanin Sin da Amurka. Ta kara da bayyana cewa, kasar Sin ba ta neman cin bulus a harkar kasuwanci, kuma bangarorin biyu sun samu riba mai yawa daga hadin gwiwar tattalin arziki da suke yi. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Sha’anin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya roƙi ’yan Najeriya da su daina biyan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane kuɗin fansa. Ribadu, ya ce biyan kuɗin fansa ba ya sa ana sakin waɗanda aka sace, kuma hakan na ƙara dagula al’amuran tsaro. Harajin China da Amurka: Mece ce makomar tattalin arziƙin duniya? Za a ci gaba da sayar da ɗanyen mai a farashin Naira — Gwamnati Ribadu ya bayyana haka ne a ranar Talata a Abuja, yayin da yake karɓar mutane 64 da dakarun tsaro suka ceto daga hannun masu garkuwa da su a Zangon Kataf da ke Kudancin Kaduna. “Don Allah ku daina bai wa waɗannan mutane (masu garkuwa) kuɗi, wannan shi...
Kungiyoyin biyu sun hadu sau 6 a tarihi, Barcelona ce ta samu nasara akan Dortmund sau 4 a tarihi yayin da aka buga canjaras a wasanni 2, Dortmund ba ta taba samun nasara akan abokan karawar ta su ta yau ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tattalin Arzikin Sin Na Bunkasa Yadda Ya Kamata Duk Da Kakkaba Mata Karin Harajin Kwastam Daga Amurka
A ran 7 ga watan nan da muke ciki bisa agogon gabashin kasar Amurka, kasar ta Amurka ta kara barazanar kakkaba wa Sin karin haraji na kashi 50%, kasar Sin a nata bangaren ta bayyana aniyarta ta daukar matakan da suka dace don kare muradunta. Tattalin arzikin Sin na samun bunkasa yadda ya kamata duk da matakin kakkaba mata karin harajin kwastam da Amurka ke dauka, kamar yadda shugaban kasar Mr. Xi Jinping bayyana cewa: “Tattalin arzikin Sin ya yi kama da teku a maimakon karamin tabki.” Teku ba ya tsoron mahaukaciyar guguwa, kuma yana iya tinkarar duk wasu kalubale daga waje. (MINA) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya tare da kasashe makwabta, da kuma kokarin bude sabon babi na ayyukan da suka shafi kasashe makwabtan kasar Sin. Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin kolin soja na kasar, ya bayyana hakan ne a taron koli kan ayyukan da suka shafi kasashe makwabta, wanda aka gudanar a birnin Beijing daga ranar Talata zuwa Laraba. (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
Sabon rikici ya sake kunno kai tsakanin ƙasashen China da Amurka, yayin da shugaba Donald Trump, ya ƙara wa kayayyakin da ake shiga da su ƙasar daga China haraji zuwa kashi 104. Wannan matakin ya shafi kayayyaki kamar wayoyin hannu, batir, kayan wasan yara da na’urorin wasanni. Za a ci gaba da sayar da ɗanyen mai a farashin Naira — Gwamnati Likitocin Nijeriya dubu 16 sun yi ƙaura zuwa ƙetare — Ministan Lafiya China ta ce ba za ta zuba ido ba China ta bayyana cewa ba za ta zuba ido ta yi tagumi yayin da ake gallaza mata. China ta mayar da martani da nata harajin kashi wanda ta ƙada zuwa kashi 34 kan kayayyakin Amurka, inda ta kuma...
Sabon rikici ya sake kunno kai tsakanin ƙasashen China da Amurka, yayin da shugaba Donald Trump, ya ƙara wa kayayyakin da ake shiga da su ƙasar daga China haraji zuwa kashi 104. Wannan matakin ya shafi kayayyaki kamar wayoyin hannu, batir, kayan wasan yara da na’urorin wasanni. Za a ci gaba da sayar da ɗanyen mai a farashin Naira — Gwamnati Likitocin Nijeriya dubu 16 sun yi ƙaura zuwa ƙetare — Ministan Lafiya China ta ce ba za ta zuba ido ba China ta bayyana cewa ba za ta zuba ido ta yi tagumi yayin da ake gallaza mata. China ta mayar da martani da nata harajin kashi wanda ta ƙada zuwa kashi 34 kan kayayyakin Amurka, inda ta kuma...
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da sayar da ɗanyen mai da man da aka tace farashin Naira, maimakon amfani da dalar Amurka. Wannan mataki na daga cikin manufofin gwamnati na bunƙasa tattalin arziƙin cikin gida, rage matsin lamba kan kasuwar musayar kuɗi, da kuma bunƙasa makamashi. ’Yan bindiga sun mamaye garuruwa 64 a Filato — Gwamna Mutfwang ’Yan bindiga sun kashe masunta 3 a Sakkwato Ma’aikatar Kuɗi ta bayyana hakan ne a shafinta na X, inda ta ce wannan ba mataki ne na wucin-gadi ba, sai dai tsari ne da ake son ya ɗore wanda Majalisar Zartaswa ta Ƙasa, ta aminta da shi. “Wannan manufa za ta taimaka wajen bunƙasa tace mai a gida, rage...
An yi kira ga Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja da ya sanya baki kan rikicin fili mai fadin sama da hektar saba’in da biyar da ake zargin Hakimin Tegina da ke karamar hukumar Rafi ya kwace daga hannun mamallakinsa a Pangu Gari. Babban Limamin Pangu Gari, Alhaji Umar Musa Danladi ne ya yi wannan kiran yayin da yake zantawa da manema labarai a Minna, inda ya bayyana cewa hakan yana da muhimmanci matuka, domin dakile rikicin da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin. Alhaji Umar Musa Danladi ya bayyana cewa ya gaji filin gonar ne daga mahaifinsa wanda ya rasu kusan shekaru goma da suka gabata, kuma yana da burin barin filin ga ‘ya’yansa su...
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da kudirin samar da kungiyar masu amfani da ruwan sha da makamantan su na 2025 ya zama doka. Kudirin wanda zai bunkasa samar da ruwan sha da amfani a fadin jihar, ya samu karbuwa da amincewa cikin gaggawa saboda muhimmancin ruwa ga rayuwar al’umma. Shugaban majalisar dokoki ta jihar, Yusuf Dahiru Liman ya sanar da amincewa da kudiring a lokacin zaman majalisar a Kaduna. Kudirin da bangaren zartarwa na jihar ya aike da shi majalisar, an mika shi ga kwamitin ayyukan al’umma da samar da ababen more rdayuwa domin yin nazari akai, inda daga bisani ‘yan kwamitin suka tuntubi masu ruwa da tsaki a bangaren domin jin ba’asin su, sannan ya gabatar da...
Gwamna Caleb Mutfwang ya bayyana damuwa kan yadda matsalar tsaro ta ƙara ƙamari, yana mai cewa a halin yanzu ’yan bindiga sun mamaye aƙalla garuruwa 64 na Jihar Filato. A wata hirarsa da gidan talabijin na Channels a yau Laraba, Gwamna Mutfwang ya ɗora alhakin matsalar tsaron da ake fuskanta a jiharsa kacokam a kan ta’addancin ’yan bindiga da ke ƙara ta’azzara. Ibas ya naɗa kantomomin ƙananan hukumomin Ribas ’Yan bindiga sun kashe masunta 3 a Sakkwato Gwamnan ya yi zargin cewa akwai masu ɗaukar nauyin hare-haren da ke aukuwa a jiharsa. “A haƙiƙanin gaskiya babu wani bayani da zan yi face cewa akwai masu ɗaukar nauyin ta’addancin nan,” a cewar gwamnan. “Abin tambayar shi ne, su wa ke ɗaukar...
Rundunar Sojin Nijeriya ta ce ba a biya kuɗin fansa ba kafin a ceto tsohon shugaban NYSC, Janar Mahrazu Tsiga (mai ritaya), daga hannun ‘yan bindiga. A wata sanarwa da Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, ya bayyana cewa an yi amfani da bayanan sirri da kuma dabarun soji wajen ceto Janar Tsiga. Dole Dukkanin Masu Umrah Su Fice Daga Saudiyya Kafin 29 Ga Afrilu – Hukumomi An Buɗe Sabbin Cibiyoyin Kula Da Masu Cutar Sankarau A Jihohi 6 An yi garkuwa da shi ne a mahaifarsa Tsiga da ke ƙaramar hukumar Bakori a Jihar Katsina, ranar 5 ga watan Fabrairu, tare da wasu mutane 13. Sojoji sun gudanar da samame a yankunan Ɗanmusa, Faskari da Kankara, inda ake tunanin...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya ce Amurka na da masaniya kan irin karfin kare kai da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke da shi, yayin da ya ce kasar ta shirya tsaf domin kare kanta. Ya kuma jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta yarda da Washington ba, amma duk da haka za ta gwada ta yayin tattaunawar da za a yi nan gaba a ranar Asabar mai zuwa,” in ji Abbas Araghchi yayin wani taron manema labara a Aljeriya. Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta neman yaki, amma idan ya zama dole ta san yadda za ta kare kanta. » “Muna shakkar aniyar Amurka kuma ba mu da tabbacin cewa suna da...
Amurka ta kai sabbin munanan hare-hare ta sama har sau 22 a wasu larduna da dama na kasar Yemen, jim kadan bayan kai wa kasar hare-hare da dama makamancin haka. A cewar majiyoyin na Yemen, wadannan sabbin hare-hare na Amurka sun auna yankuna daban-daban a ranar Laraba, ciki har da babban birnin kasar Sanaa da lardin Ibb da ke tsakiyar kasar. A Sana’a, an kai hare-hare ta sama guda takwas. Har yanzu ba a tabbatar da asarar rayuka ba, amma hare-haren sun shafi muhimman ababen more rayuwa, lamarin da ke kara tabarbare yanayin rayuwa ga fararen hula. An sami adadin wadanda suka mutu mafi muni a lardin al-Hudaydah da ke yammacin kasar, inda aka tabbatar da mutuwar fararen hula 6...
Majalissar Dokokin Rasha ta amince da yerjejeniyar huldar ta shakaru 20 tsakanin kasar da Iran. Wannan na nuna muhimmin mataki na zurfafa dangantakar siyasa, soja da tattalin arziki tsakanin Moscow da Tehran. Yarjejeniyar ta tsawon shekaru 20, wakilan majalisar sun amince da ita ne a kuri’ar da aka kada a ranar Talata ta yadda kasashen biyu za su iya yin hadin gwiwa cikin tsari da inganci. Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na kasar Iran Massoud Pezeshkian ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a cikin watan Janairu, da nufin karfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban da suka hada da tsaro, makamashi, kudi, sufuri, masana’antu, noma, al’adu, da kimiyya da fasaha. Yarjejeniyar ta kuma bada damar zuba jari a...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kantoman Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas, ya amince da naɗin sabbin kantomomi na ƙananan hukumomi 23 da ke faɗin jihar. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Ribas, Farfesa Ibibia Lucky Worika ya fitar a safiyar wannan Larabar a birnin Fatakwal. ’Yan bindiga sun kashe masunta 3 a Sakkwato Likitocin Nijeriya dubu 16 sun yi ƙaura zuwa ƙetare — Ministan Lafiya Sanarwar ta ce Ibas ya kuma amince da sauya duk majalisun gudanarwa na ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin jihar da a baya aka dakatar da ayyukansu. Sanarwar ta ce naɗin sabbin masu kula da gudanarwar ƙananan hukumomin zai fara aiki ne nan take daga ranar Litinin, 7 ga watan Afrilu. Sunayen kantomomin ƙananan hukumomin Ribas
Wasu ’yan bindiga da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne sun kashe masunta uku a wani hari da suka kai ƙauyen Sanyinna da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato. Wata majiyar a ƙauyen ta ce ’yan bindigar sun kashe mutanen ne a lokacin da suka kawo hari da safiyar Talata yayin da mutanen suka fita sana’arsu ta su. Kazalika, majiyar ta ce ko a ranar Litinin da ta gabata ’yan bindigar sun kai hari garin Sutti da Takkau duk a karamar hukumar inda sun jikkata mutum biyu. Mataimaki na musamman ga shugaban Ƙaramar Hukumar Tangaza kan tsaro, Alhaji Gazali Raka ya tabbatar da faruwar lamarin. Alhaji Raka ya bayyana cewa ’yan bindigar sun sace dabbobi da suka haɗa da Shanu...
Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Pate ya bayyana cewa, sama da likitoci dubu 16 sun fice daga Nijeriya a cikin shekaru biyar zuwa bakwai da suka gabata zuwa wasu ƙasashen duniya don ci gaba da aiki cikin ingantaccen yanayi. Farfesa Pate ya bayyana haka ne a wurin taron horas da Ƙungiyar Likitocin Afrika da ya gudana a birnin Abuja a ranar Talata. Nijar ta ayyana Hausa a matsayin yaren ƙasa DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’ Ministan ya bayyana cewa, ana ci gaba da samun wani adadi mai yawa na ƙwararrun likitocin da ke da burin fita zuwa wasu ƙasashen duniya aiki, suna fakewa da matsalolin tattalin arziƙi da rashin kyawun yanayin aiki...
An kori jakadan Isra’ila a Habasha Avraham Neguise daga taron kungiyar Tarayyar Afirka da aka gudanar a wannan Talata a Addis Ababa domin tunawa da kisan kiyashin da aka yi a Rwanda. An fitar da Neguise daga dakin taro na Mandela da ke hedikwatar Tarayyar Afirka bayan da kasashe da dama suka nuna rashin amincewarsu da halartarsa a taron shekara-shekara kan kisan kiyashin da aka yi a kasar Rwanda. Jakadan na Isra’ila ya shiga wurin taron ne ba zato ba tsammani, ba tare da an gayyace shi ba, a cewar majiyoyin diflomasiyyar da suka halarci taron. Majiyar ta kara da cewa tawagogin kasashen Afirka da dama sun nuna rashin amincewa da zuwansa, lamarin da ya sa aka dakatar da taron...
Wasu ‘yan kasar Amurka uku da aka daure bisa laifin yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, yanzu haka suna hannun Amurka bayan yanke hukuncin da aka yi a kansu a makon jiya, kamar yadda wasu jami’an Amurka da na fadar shugaban kasar Kongo suka bayyana ga kamfanin dillancin labarai na Reuters a wannan Talata. A ranar 19 ga Mayu, 2024, wasu ‘yan bindiga sanye da kakin sojoji sun mamaye ofishin shugaban kasar DRC Felix Tshisekedi bayan da suka mamaye gidan ministan tattalin arzikin kasar mai barin gado kuma dan takarar shugaban majalisar dokokin kasar Vital Kamerhe. An bayar da rahoton mutuwar mutane shida da suka hada da jami’an ‘yan sanda biyu a lokacin yunkurin...
A wani mataki na kara nesanta kanta da Faransa da ta yi mata mulkin mallaka, Nijar ta ayyana harshen Hausa a matsayin yaren ƙasa a madadin Faransanci. Kamfanin dillancin labarin kasar AFP ne ya ruwaito hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 31 ga Maris. Boko Haram na sake ƙwace ikon wasu yankuna a Borno — Zulum Ma’aikatar Jin-ƙai ce kan gaba wajen wawure kuɗin gwamnati — Tsohon Minista Tun bayan hambarar da gwamnatin farar hula ta Muhammad Bazoum, Nijar ɗin ke ɗaukar matakan nesanta kanta da Faransa, inda ta fara da korar sojojinta da kuma sauyawa wurare da dama da ke da alaƙa da kasar suna. Bayan haka kuma, Nijar ɗin da sauran ƙasashen da Faransan ta yi...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun kaka da kakanni an san Hausawa da kawaici da kunya da kuma girmama na gaba da su. Mai yiwuwa wadannan dabi’u ne suka sa matar Bahaushe ba ta iya hada ido da mijinta, balle ta kira shi da sunansa na yanka. To amma a zamanin yau ba abin mamaki ba ne a samu matar aure ta kalli kwayar idon mijinta, ta kuma kira shi da sunansa na yanka. NAJERIYA A YAU: Dabarun Samun Kuɗaɗe Ta Hanyar Amfani Da Wayar Hannu DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Arewa Ke Tafiya Kudu Farauta A kan wannan al’ada – asalinta da alfanunta da dalilan sauyawarta – shirin Daga Laraba na wannan makon za iyi nazari. Domin...
Duk da matsin lambar da Amurka ke yi, kasar Sin tana da dabararta, za ta ci gaba da mai da hankali kan ayyukanta, za ta kuma rika bude kofarta ga ketare. Har kullum kasar Sin na ganin cewa, ainihin huldar da ke tsakaninta da Amurka ita ce samun moriyar juna da nasara ga ko wane bangare. Ya kamata a daidaita sabanin ciniki ta hanyar tattaunawa cikin adalci. Amma idan Amurka ta fara dora harajin da ta yi shelar dauka, to, kasar Sin za ta dauki wajibabbun matakai, domin kiyaye halastattun hakkokinta. (Tasallah Yuan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
Sai dai ya koka da yadda hare-haren da aka kai kwanan nan, inda aka tarwatsa sansanonin sojoji a Wajirko, Sabon Gari a karamar hukumar Damboa, Wulgo a Gamboru Ngala, Izge a karamar hukumar Gwoza da sauransu wanda hakan ya yi sanadin kashe mutane ‘yan gari da jami’an tsaro, lallai abun damuwa ne matuka. Gwamna Zulum ya bayyana haka ne a wani taro na musamman na tsaro wanda ya samu halartar babban kwamandan runduna ta 7 ta rundunar sojojin Nijeriya, Manjo Janar Abubakar Haruna da kwamandojin sassan rundunar da kwamishinan ‘yansanda na jihar da shugabannin sauran hukumomin tsaro. Taron ya kuma samu halartar Shehun Borno Alh. Dr. Abubakar Garbai Al-Amin El-Kanemi; Shehun Bama, Sarakunan Biu, Uba, Askira, Gwoza, yayin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Declan Rice ne ya jefa ƙwallaye biyu a wasan kafin Mikel Merino ya jefa ta uku kuma ta ƙarshe a wasan, hakan ya sa Rice ya zamo dan wasa na farko a tarihin gasar Zakarun Turai da ya ci ƙwallaye biyu daga bugun tazara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Li Qiang ya yi nuni da cewa, a kwanakin baya, kasar Amurka ta sanar da kara buga harajin kwastam ga dukkan kasashe abokanta na cinikayya ciki har da Sin da Turai, wanda mataki ne da bangare daya ya dauka, da ba da kariya ga cinikayya, da cin zarafin tattalin arziki. Ya ce, kasar Sin ta dauki matakai don tabbatar da ikon mulkinta da moriyar samun ci gaba cikin aminci, kana da tabbatar da ka’idojin cinikayya da adalci a duniya. Ya kara da cewa, ya kamata Sin da Turai su kara mu’amala da juna, da bude kofa ga juna don tabbatar da yin ciniki da zuba jari cikin ‘yanci, da kiyaye tsarin samar da kayayyaki a duniya yadda ya kamata, ta...
CSP Wakil ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin bayan kammala bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Duk da wannan zullumi da ake ciki, a kwanakin baya, kasar Sin ta tattauna da wasu kamfanonin Amurka sama da 20 cikinsu har da Tesla, inda ta kara ba su tabbacin cewa, za ta ci gaba da bude kofarta ga kamfanonin kasashen waje da aiwatar da gyare-gyare a gida. Wannan shi ake nufi da babbar kasa mai sanin ya kamata, mai kuma la’akari da moriyar sauran kasashe maimakon moriyarta ita kadai. Idan Amurka na ganin matakanta za su danne ci gaban wasu kasashe, su kuma bata fifiko a duniya, to ta yi kuskure, domin yanzu ta budewa duniya ido, kuma kasashe da ma kamfanoninsu, za su koma ne ga inda suka tabbatar da cewa za su samu moriya, kuma...
Ya ce karin wa’adin na baya-bayan nan ya biyo bayan cikar wa’adin farko na ranar 1 ga Afrilu, 2025, wanda aka sanya tun da farko a ranar 24 ga watan Janairu. Umar ya kara da cewa, duk da wannan karin wa’adin, amma an ci gaba da samun karancin fitowar masu filaye domin sabunta takardunsu. Domin tabbatar da bin ka’ida, kwamishinan ya yi gargadin cewa, nan ba da jimawa ba, za a buga sunayen wadanda ba su bi ka’ida ba a jaridun kasar nan da kuma nuna su a allunan sanarwa a muhimman wuraren gwamnati da suka hada da dakin karatu na jihar Kano, Sakatariyar Audu Bako, Gidan Murtala, da kuma babbar kotun jihar. Daga kanmu, magana ta...
Tsohon Ministan Gidaje da Raya Birane, Nduese Essien, ya ce Ma’aikatun Harkokin Jin-ƙai na tarayya da jihohi sun zamo matattarar cin hanci da rashawa a Nijeriya. Essien, ya kuma zargi ministocin ma’aikatun da karkatar da biliyoyin naira da aka ware domin ‘yan ƙasar da ke cikin mawuyacin hali. Kotu ta daure ango wata 6 saboda likin kudi a bikinsa Gaza: Isra’ila ta kashe Falasdinawa 58 a awa 58 “Wani zai yi tunanin ƙirƙirar ma’aikatun nan zai inganta rayuwa da walwalar al’umma, amma abun takaici sun zamo mazurarar sace kuɗin al’umma ba tare da wata shakka ba. “Dukkanin ministocin ma’aikatun jin-ƙan Najeriya, babu wanda ba a zarga ba da karkatar da kuɗin al’umma.” In ji shi. Kazalika ya soki shirin ‘yan...
Tsohon Ministan Gidaje da Raya Birane, Nduese Essien, ya ce Ma’aikatun Harkokin Jin-ƙai na tarayya da jihohi sun zamo matattarar cin hanci da rashawa a Nijeriya. Essien, ya kuma zargi ministocin ma’aikatun da karkatar da biliyoyin naira da aka ware domin ‘yan ƙasar da ke cikin mawuyacin hali. Kotu ta daure ango wata 6 saboda likin kudi a bikinsa Gaza: Isra’ila ta kashe Falasdinawa 58 a awa 58 “Wani zai yi tunanin ƙirƙirar ma’aikatun nan zai inganta rayuwa da walwalar al’umma, amma abun takaici sun zamo mazurarar sace kuɗin al’umma ba tare da wata shakka ba. “Dukkanin ministocin ma’aikatun jin-ƙan Najeriya, babu wanda ba a zarga ba da karkatar da kuɗin al’umma.” In ji shi. Kazalika ya soki shirin ‘yan...

Kasar Sin Ta Lashi Takobin Sai Ta Ga Abin Da Ya Ture Wa Buzu Nadi Dangane Da Barazanar Haraji Ta Amurka
Ya kara da cewa, wannan ra’ayi ne na yin gaban kai wajen daukar mataki ba tare da la’akari da sauran bangarori ba, haka kuma kariyar cinikayya ne da cin zali a bangaren tattalin arziki, wanda kasa da kasa suka yi tir da shi. Game da ko Sin da Amurka sun tattauna ko sun tuntubi juna game da batun, Lin Jian ya ce, idan da gaske Amurka na son tattaunawa, ya kamata ta nuna girmamawa da adalci da kuma saka alheri da alheri. (Fa’iza Msutapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
Ya jaddada cewa, taken taron ya dace kuma yazo a kan lokaci “wanda na yi imanin cewa, dandalin zai taimaka wajen gabatar da jawabai a bangarori daban-daban na gyare-gyaren kasafin kudi da shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa a karkashin shirin renewed hope.” Ya ce, jawabin da ake gabatarwa a dandalin zai ba da gudummawa ga kudirin dokar gyaran haraji da ke gaban majalisar dokokin kasar don karfafa tsarin tarayyar Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Kula da Jin DDaɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta ayyana ranar Juma’a 11 ga Afirilun 2025 a matsayin ranar ƙarshe da za a kammala biyan kuɗin aikin hajjin bana ga dukkan maniyyatan jihar. Shugaban hukumar, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam ne ya bayyana hakan a yayin wata hira da manema labarai a Ilori. Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa jimillar kuɗin aikin hajjin bana ya kai naira miliyan 8,459,000. Ya yi kira ga dukkan maniyyatan da suka fara biyan kuɗi da su tabbatar sun kammala ragowar kuɗin kafin ranar ƙarshe, wato 11 ga Afrilu, domin ba za a ƙara lokaci ba. Alhaji Abdulsalam ya kuma buƙaci maniyyatan da su gaggauta miƙa fasfo ɗin su na tafiya ƙasashen waje ga jami’ansu domin fara...
Wasu ’yan bindiga a ranar Lahadin da ta gabata sun kai harin ɗaukar fansar kashe ƙasurgumin ɗan ta’addan nan, Kachalla Isuhu Yellow da aka fi sani da Ɗan Isuhu. ’Yan ta’addan sun kai harin ne ƙauyen Keta da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, domin ɗaukar fansar kashe jagoransu da jami’an tsaro suka yi makonni biyu da suka gabata. Kotu ta daure ango wata 6 saboda likin kudi a bikinsa Gaza: Isra’ila ta kashe Falasdinawa 58 a awa 58 Mazauna sun ce maharan sun kashe mutum ɗaya yayin da suka ƙone motoci 11 sannan kuma suka wawushe kayayyaki a kantinan ’yan kasuwa a yayin harin. Bayanai sun ce ana zargin ’yan ta’addan da suka kai wannan hari mayaƙan Adamu...
Sojojin HKI sun kara yawan hare-haren da suke kaiwa kan Falasdinawa a Gaza, a dai-dai lokacinda ake kiranta zuwa tsagaita wuta a gazar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar kungiyar kare fararen hula ta falasdinawa a Gaza, tana fadar haka a safiyar yau Talata. Ta kuma kara da cewa, Ta kuma kara da cewa a daren jiya kadai jiragen yakin yahudawan sun kashe akalla falasdinawa 19 mafi yawansu yara kanana. Labarin ya nakalto kakakin kungiyar kare fararen hula na Gaza Mhmood Bassal yana fadar haka, ya kuma kara da crawa , a garin Deir Balah jiragen yakin yahudawan sun kai hari a kan wani gida inda suka kashe yara 5 da manyan mutane 4. Sannan sun...

Trump Yayi Barazanar Karawa China Kashi 50% Na Kudaden Fito A Dai-Dai Lokacinda Suka Shiga Tsakiyar Yakin Tattalin Arziki
Shugaban kasar Amurka Donal Trump yayi barazanar karwa kasar China kasha 50% na kudaden fiton da zata karba daga kayakin kasar China da zasu shiga kasar, idan har bata janye maida martanin da tayi na kasha 34% dai dai karin kudin fito da Amurka ta kara mat aba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a shafinsa na yanar gizo wato ‘Trump Social”. Kafin haka dai shugaban kasar Amurka ya karawa kasashen duniya da dama wadanda suke huldar kasuwanci da ita kudaden fito na kayakin da suke shigo da su Amurka daga cikin har da kasar China inda Trump ya kara mata kasha 34% na dukkan kayakin China da suke shiga Amurka. Amma kwana...

Yan Sanda A Saudiya Sun Tsare Wata Bafalasdinya Saboda Bayyana Tutar Kasarta A Kan Jakarta A Masallacin Ka’aba
Jami’an yan sanda a birnin Makka sun tsare wata Bafalasdiniya wacce ta baje Jakarta dauke da tutar kasarta Falasdinu tare da zarginta na bayyana wani abu na siyasa a lokacin aikin umran da take yi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Mint-Press yana cewa matar ta shiga masallacin haramin Ka’aba dauke da jakanta mai tutar falasdinu. Kuma bayan sun kamata sun tsare, Bafalasdiniyar wacce har yanzun ba’a bayyana sunanta ba, ta ce masu tana ganin wasu masu aikin umra wadanda suke shigowa masallacin Ka’aba tare da tutocin kasashen su, daga cikinsu akwai yan kasashen Morocco, Turkiyya, da sauransu, don haka itama tana dauke da tutar kasarta ce Falasdinu don nuna daga inda ta fito....
Gwamnatin kasar Aljeriya ta dakatar da duk zirga-zirgin jiragen sama daga kasar Mali da kuma zuwa kasar saboda abinda ta kira keta hurumin sararin samaniyar kasar. Shafin yanar giza na watsa labarai “Africa News” ya nakalto tashar talabijin ta kasar Aljeriya na fadar haka a daren Lahadi. Kafin haka dai matsalolin sun tashi tsakanin kasashe yanken Sahel 3 Niger, Mali da Burkiya faso kan kakkabo jirgin saman yaki wanda bai da matuki wanda ya keta sararin samar kasar ta Aljeriya a makon da ya gabata, wanda ya sa kasashen uku suka janye jakadunsu daga kasar. Gwamnatin kasar Mali dai bata yi magana a kan wannan matakin da gwamnatin kasar ta Aljeriya ta dauka ba. Sai dai dakatar da zirga-zirgan jiragen...
Jami’in ya ce, barazanar da Amurka ke yi game da kara tsananta matakin da za ta dauka, kuskure ne dake nuna muguwar aniyarta ta dakile moriyar sauran kasashe, kuma tabbas Sin ba za ta amince ba ko kadan. Kasar Sin ta sake nanata ra’ayinta cewa, ba wanda zai ci gajiyar tayar da zaune tsaye a goggayar ciniki, da aiwatar da manufar kariyar ciniki, don haka tana kalubalantar Amurka da ta gyara kuskurenta, tare da soke harajin da ta kakkaba mata, da daina matsa mata lamba kan tattalin arziki da ciniki, da warware matsalolin da ke tsakaninsu ta hanyar shawarwari bisa turbar mutunta juna. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke wa wani shahararren mai sana’ar gyaran fuska, Abdullahi Musa Huseini, wanda aka fi sani da Amuscap, hukuncin daurin watanni shida a gidan yari saboda yin likin da takardun Naira a lokacin bikin aurensa. Mai Shari’a S.M. Shu’aibu ya yanke wa Huseini Amuscap hukuncin ne bayan ya amsa laifinsa da ake tuhumar sa, wanda ya saba wa sashe na 21(1) na Dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) ta shekarar 2007. Takardar tuhumar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 6 ga Disamba, 2024, a Cibiyar Bikin Ali Jita da ke Kano, inda aka ga angon a wani bidiyo yana yin kari da Naira dubu dari a takardun Naira dubu daya-daya...
LEADERSHIP tana karrama mutane da ƙungiyoyin da suka taka rawar gani a fannoni daban-daban kamar gwamnati, kasuwanci da al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani magidanci ya shiga hannun hukuma bayan da ya lakada wa ’yarsa mai shekaru 27 duka har lahira a yankin Ojo da ke Jihar Legas. Kakakin ’yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa rundunar ta cika hannu da magidncin ne bayan ya yi aika-aikan a ranar 3 ga watan nan na Afrilu. Hundeyin ya ce makwabta ne suka kwarmata wa Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke yankin Okokomaiki, bayan mutumin ya kashe ’yar tasa ya kuma binne ta a cikin harabar gidansu. Jami’in ya ce ““Bayan samun rahoto jami’anmu suka ce suka gano kabarin, suka tono gawar aka gudanar da bincike,” shi kuma yana hannun hukuma yana amsa tambayoyi. Mali, Nijar, da Burkina Faso sun janye jakadunsu daga Algeria...
Kasashen Mali, Nijar, da Burkina Faso sun janye jakadunsu daga kasa Algeria bayan takaddamar da ta barke tsakaninta da Mali. Kasashen uku da ke karkashin mulkin soja sun sanar da daukar wannan matakin hadin gwiwa ne bayan Mali ta zargi sojojin Algeria da harbo wani jirginta mara matuki a sararin samaniyarta a karshen watan Maris. A ranar 1 ga Afrilu, Algeria ta sanar cewa ta harbo wani jirgin sama mara matuki mai dauke da makamai a sararin samaniyarta, amma ba ta yi karin bayanin ba. A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Wajen Mali ta ce hukumomi sun tabbatar da “cikakken yakini” cewa an harbo jirgin ne a cikin “A matsayin harin makiya da aka shirya daga gwamnatin Algeria.” Gobara ta...
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa ta yi imani da tattaunawa, amma ba a karkashin wulakanci da kaskanci ba.” Ya jaddada cewa Iran ba ta neman yaki, ko tada zaune tsaye, ko kuma mallakar makamin nukiliya, yana mai kira ga kasashen duniya da su amince da hakan. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a yammacin Lahadin da ta gabata, yayin wata ganawa da wakilan jam’iyyun siyasa da manyan kungiyoyi a kasar, inda ya tattauna batutuwan da suka shafi sauye-sauyen harkokin mulki, da manufofin harkokin waje, da kalubalen tattalin arziki da zamantakewar kasar. Da yake magana game da kalubalen gudanar da harkokin mulki, shugaban na Iran ya bayyana cewa, ba za a iya cimma gyara halayen kungiyoyi da bangarorin gwamnati ta...
A safiyar jiya litinin an kashe wani dan jarida Bafalasdine da wani matashi tare da raunata wasu da dama a lokacin da jirgin Isra’ila ya kai hari kan wani tanti na ‘yan jarida a kusa da rukunin likitocin Nasser da ke Khan Younis a kudancin Gaza. Wakilin Al Mayadeen ya ruwaito cewa dan jarida Hilmi al-Faqawi da wani matashi mai suna Yousef al-Khazindar sun yi shahada, yayin da wasu ‘yan jarida da suka hada da Ahmed Mansour, Hassan Islayh, Ahmed al-Agha, Mohammed Fayek, Abdullah al-Attar, Ihab al-Bardini, Mahmoud Awad, da Majed Qudaih, suka samu raunuka a tashin bam din. Kungiyar Kafafen Yada Labarai ta Falasdinu ta yi Allah wadai da wannan harin da Isra’ila ta kai a kan tantin ‘yan...
Hajiya Zainab ta kuma tuna da marigayi mijinta, Sam Nda-Isaiah, wanda ya kafa LEADERSHIP a shekarar 2004. “Tun shekaru ashirin da suka gabata, wanda ya kafa wannan jarida ya shigo harkar wallafa da wani babban buri — Don Allah da kuma ƙasar nan. “Wannan buri har yanzu yana jagorantarmu, kuma da yardar Allah za mu isar da shi zuwa ga ƙarni na gaba,” in ji ta. Ta ƙare da jan hankalin kowa da ya yi tunani a kan irin gudummawar da zai bayar wajen gina Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ci gaba da gudanar da tarurrukan bita ga maniyyata aikin Hajjin bana, bayan kammala azumin watan Ramadan. Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, hukumar za ta tabbatar da cewa maniyyata sun sami horo da ilimi kan yadda ake aiwatar da aikin Hajji domin dacewa wannan ibada da suka kashe makudan kudade don gannin sun aiwatar da ita. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce, za a wayar da kan alhazai da kuma koya musu yadda za su kula da kansu da kuma yadda za su aiwatar da aikin Hajji bisa ga koyarwar addini. Ya ce, ana gudanar da...
Gwamnatin Saudiyya ta ayyana 1 ga watan Dhul Qada, wadda za ta yi daidai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar karshe da duk wani bako da ke kasar da zummar aikin Umarah da ya fice daga ƙasar. Sanarwar da ma’aikatar aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta fitar ta ce ta dauki matakin ne domin fara gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji mai zuwa. Cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce ranar 15 ga watan Shawwal, da ya yi daidai da 13 ga watan Afrilu, ita ce ranar karshe da masu shiga kasar domin aikin Umrah za su daina shiga, sai dai a fita. Ma’aikatar ta jaddada cewa duk wanda aka samu ya ci gaba da zama a kasar har...
An gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wada ta barke a wasu manyan biranen Nijeriya da suka haɗa da Abuja da Legas da kuma Fatakwal. Zanga-zangar wadda wata kungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta shirya na gudana ne duk da gargadin da ’yan sanda suka yi na neman a jingine ta. A Abuja, babban birnin Nijeriya, fitaccen dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore da lauyan nan mai kare hakkin bil Adama, Deji Adeyanju ne ke jagorantar zanga-zangar duk da yunkurin ’yan sanda na hana su rawar gaban hantsi An kuma hangi masu zanga-zangar ɗauke da alluna da kwalaye masu dauke da rubutun bayyana buƙatunsu a wasu hanyoyi da ke Ikeja, babban birnin Jihar Legas. A Jihar Ribas kuma,...
Shugaban sojin ya ce za a kamo waɗanda suka aikata wannan mummunan ta’asa, kuma za a hukunta su. Haka kuma ya yi alƙawarin tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankunan da abin ya shafa domin kare rayuka da dukiyoyi. A nasa jawabin, Manjo Janar Folusho Oyinlola, kwamandan Operation Safe Haven, ya ce za su ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya musamman a lokacin girbin gonaki. Ya bayyana cewa ganawar da shugabannin yankin na zuwa a lokaci mai muhimmanci duba da yadda matsalar tsaro ke ƙaruwa. Dagacin Manguna, Alhaji Alo Raymond, ya ce hare-haren da ake kai musu na da nasaba da yunƙurin karɓe musu filayen gado. Ya roƙi gwamnati ta kare su da gidajensu, tare...
Lamarin ya ƙara tayar da hankali a Jihar Kebbi, duba da yadda hare-haren ’yan ta’adda ke ƙaruwa a yankunan Arewacin Nijeriya. A baya, wata kotu a Nijeriya ta ayyana Lakurawa a matsayin ƙungiyar ’yan ta’adda domin bai wa hukumomin tsaro damar amfani da ƙarfi wajen yaƙar su. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sai an ga yadda za ta kaya a Emirates yau. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata gobara da ta ɓarke ta cinye garejin gyaran motocin kamfanin sufurin Borno Express na Gwamnatin Jihar Borno, inda ta lalata motocin bas sama da 10 masu daukar mutane 18 kowacce. Shaidu sun ce gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 12 na rana a ranar Litinin, bayan wani fashewa mai ƙarfi a harabar garejin. Ko da yake babu wanda ya rasa ransa a wannan lamarin, wani ma’aikacin hukumar kashe gobara ya samu raunuka yayin da yake kokarin kashe gobarar. Wani ganau ya ce, “Gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar tukunyar gas — inda wani kara mai ban tsoro ya sa ma’aikata da matafiya a yankin suka yi ta gujegujen domin tsira.” Gobara ta laƙume ƙauyuka a Borno Mahara sun...
NCDC ta buƙaci jama’a su kula da lafiyarsu tare da kai rahoton duk wani mutum da ya nuna alamun cutar domin samun kulawa da wuri. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kotu ta dage shari’ar kisan Manjo Janar Idris Alkali mai ritaya zuwa ranakun 28 da 29 ga watan Mayu, 2025, domin waɗanda ake tuhuma su fara gabatar da shaidunsu. Babbar kotu da ke zamanta a Jos, Jihar Filato, ta ɗage shari’ar ne biyo bayan bayan ɓangaren masu ƙara su. gabatar da ga Manjo Janar U. I. Mohammed mai ritaya game da kisan. Janar Alkali, wanda ya kasance tsohon shugaban gudanarwa a Hedikwatar Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya, ya ɓace ne makwanni kaɗan bayan ya yi ritaya daga aikin soja, a lokacin da yake hanyar tafiya Bauchi daga Abuja. Mamacin ne yake tuƙa kansa a lokacin da yake tafiyar inda ya biya ta Jihar Filato. A lokacin da ya ba ce...
Gwamnatin Sakkwato ta yi barazanar sanya ƙafar wando da waɗanda ta yi zargi suna ƙoƙarin kawo mata cikas a yaƙin da take yi da ’yan bindiga da sauran matsalolin tsaro a Jihar. Ta gargaɗi mazauna da su shiga taitayinsu game da yin kalamai da za su iya kawo cikas ga ƙoƙarinta na magance matsalar rashin tsaro a jihar. Wannan gargaɗin ya biyo bayan wata sanarwa da ake dangantawa wani mai suna Basharu Altine Guyawa wanda ya yi ƙoƙarin nuna cewa gwamnati ba ta yi abin da ya kamata ba a fannin tsaro. Mai ba Gwamna Ahmed Aliyu shawara na musamman kan harkokin tsaro, Kanar Ahmed Usman mai ritaya, ya yi wannan gargaɗin a cikin wata sanarwa da ya fitar a...
Mazauna yankin ƙaramar hukumar Funtua ta Jihar Katsina sun ce ’yan bindiga sun shiga wasu ƙauyukan yankin, inda suka kwashi mutane sama da 50 da suka hada da mata da ƙananan yara. Maharan sun kuma kashe akalla mutum shida, inda suka sake kai wani hari a yankin Ƙaramar Hukumar Ɗandume ta jihar. Rahotanni sun ce tun daga ranar Asabar maharan suka shiga yankin kuma ba su fita ba har zuwa ranar Lahadi da rana. Malam Ya’u Ciɓauna mazaunin garin Layin Gara ne na Ƙaramar Hukumar Funtua, kuma ya ce “Misalin 10:30 na dare suka zo kuma sun kwashi maza da mata da ’yan mata da matan aure da kuma ƙananan yara har 53. “Sun kashe mutum a Layin Gara na...
Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta bayyana cewa za ta fata tattaunawa wacce ba ta kai tsaye ba da Amurka a ranar Asabar mai zuwa a kasar Oman. Ministan harkokin wajen Iran din ne Abbas Araghchi ya bayyana hakan a shafinsa na ‘’X’’ a safiyar Talata. “Iran da Amurka za su gana a Oman ranar Asabar don tattaunawa mai zurfi, inji ” Araghchi. “Wannan wata dama ce, kuma kwallo yana hannun Amurka,” ta nuna da gaske ta ke in ji shi. Kalaman Araghchi na zuwa ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa Amurka da Iran suna tattaunawa kai tsaye, bayan ganawa da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a Washington. Shugaban na Amurka ya ce tattaunawar da za a yi...
A wani mataki na mayar da martani da nuna fishi, kasar Aljeriya ta yi wa jakadunta a kasashen Mali, da Nijar kiranye, tare da jinkirta aikewa da jakadanta a Burkina faso, bayan da kasashen guda uku na kawacen sahel suka dau irin wannan matakin domin goyan bayan Mali, bisa takadamar dake tsakaninta da Aljeriya biyo bayan kakkabo jirginta marar matuki. Haka zalika ma’aikatar tsaron kasar Aljeriya ta sanar da rufe sararin samaniyarta ga dukkan jiragen da ke zuwa kasar Mali”, ba tare da bayar da wani karin bayani ba, wanda ke nuni da cewa jiragen farar hula na kasuwanci da kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa su ma abin ya shafe su. Takaddama dai ta yi zafi tsakanin Aljeriya...
Shugabannin kasashen Faransa da Masar da kuma Jordan sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suka bukaci a tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Gaza, tare da sukar Isra’ila kan gazawarta wajen tabbatar da ayyukan jin kai a zirin. Kiran tsagaita wuta ya nuna bukatar samar da agajin jin kai cikin gaggawa a Gaza kuma ya nuna damuwar da kasashen duniya ke ci gaba da yi kan tashe-tashen hankula da rikicin jin kai a Gaza. Haka kuma sanarwar wadannan kasashe uku ta nuna muhimmancin hanyar diflomasiyya na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. A baya dai shugaba Macron ya nuna adawarsa da mamaye yankunan Falasdinawa da Isra’ila ta yi. Macron ya kuma kira sabbin hare-haren da Isra’ila ta...
A Isra’ila dubban masu zanga-zanga ne suka fito kan titunan birnin Tel Aviv a wata sabuwar zanga-zangar kin jinin gwamnati a daidai lokacin da firaminista Benjamin Netanyahu ya gana da shugaban Amurka Donald Trump a birnin Washington. Masu zanga-zangar a ranar Litinin sun yi Allah wadai da manufofin Netanyahu, ciki har da yunkurinsa na korar manyan jami’an tsaro da na shari’a na gwamnatin. Sun kuma yi Allah wadai da sake dawo da yakin kisan kare dangi da ake yi wa al’ummar Gaza. Iyalan ‘yan Isra’ilar da aka yi garkuwa da su a Gaza su ma sun shiga zanga-zangar, inda suka bukaci a kawo karshen yakin da kuma kulla yarjejeniyar tabbatar da sakin mutanen da aka kama. Kungiyar dai ta ce...