Tinubu Zai Yi Amfani Da Dokar Ta-ɓaci Wajen Tsoratar Da Gwamnoni Gabanin Zaben 2027 – Amaechi
Published: 4th, April 2025 GMT
Ya kara nuna shakku kan dalilin da ya sa aka kafa dokar ta-baci a Jihar Ribas, yana mai cewa rashin tsaro ya addabi wasu sassan kasar nan, amma ba a kakaba dokar ta-baci ba ko kuma wani abu makamancin haka.
“Idan shugaban kasa ya ce saboda rashin tsaro ne, saboda sun fasa bututun mai, yaya batun sassan kasar da ake fama da rashin tsaro? Shugaban kasar yana cewa su ma su kafa masa dokar ta-baci a kansa.
Amaechi ya jaddada cewa alhakin tsaro ya rataya ne a wuyan gwamnatin tarayya, ba gwamnonin jihohi ba, wanda hakan ya sa dakatarwar Fubara ba ta dace ba.
“Gwamnan Ribas ba shi da alhakin tsaro, ya rataya a wuyan shugaban kasa, to me zai sa a hukunta mutumin da bai aikata wani laifi ba?” Ya tambaya.
Tsohon gwamnan na Ribas ya zargi Tinubu da saba ka’idojin tsarin mulki na yadda za a cire gwamna daga mukaminsa.
“Shugaban ya yanke hukunci ne ta wajen kundin tsarin mulki. Sashe na 188 ya bayyana yadda gwamna zai bar mulki, ko dai ya mutu, ko murabus, ko kuma a tsige shi. Amma bai ce wata rana ka farka ba, wani mutum da ake kira shugaban Nijeriya zai fid da ka daga mulki, wanda hakan ya saba wa dimokuradiyyar Nijeriya.”
Amaechi ya yi kira ga mazauna Ribas da su bijire wa dokar ta-baci, sannan ya bukace su da su yi zanga-zangar lumana wanda dimokuradiyya ta amince da shi.
Da yake magana kan rikicin siyasar da ke faruwa tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike da Gwamna Fubara, Amaechi ya yi zargin cewa rikicin kudi ne kawai.
“Abun da ke faruwa a tsakanin Gwamnan Jihar Ribas na yanzu da Ministan Babban Birnin Tarayya, shi ne batun raba kudi, idan ba haka ba, mene ne na rigima? ‘Yan Nijeriya ba sa son cin hanci da rashawa a wannan lokaci, ban ga wani a kan titi yana tambayar ko mene ne matsalar ba, ko su biyun za su iya magana da jama’a su fada mana matsalar?”
Amaechi ya koka da yadda a yanzu Jihar Ribas na karkashin mulkin soja ne, inda ta hana ‘yan kasar cin ribar dimokuradiyya.
“Yanzu an hana mu cin gajiyar dimokuradiyya. Jihar Ribas ce kadai jihar da ba ta jin dadin dimokuradiyya a halin yanzu, sun kakaba mana mulkin soja da karfin tsiya,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: dokar ta baci rashin tsaro Jihar Ribas
এছাড়াও পড়ুন:
Rashin Tsaro: Tinubu Ya Gana Da Shugaban Tsaro Da Ribadu Kan Kashe-kashen Rayuka
Matsalar tsaro ta kara tabarbare a jihohin Filato da Benuwai, inda rahotanni ke cewa, wasu da ake zargin makiyaya ne daga kasashen waje ne ke kai hare-haren kashe rayuka da kuma raba al’umma da matsugunansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp