2025-04-25@15:06:00 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3754

«jihar Ribas»:

    A nasa bangare kuma, firaministan kasar Senegal Ousmane Souko ya bayyana cewa, kasar Senegal tana son hadin gwiwa da cibiyar nazarin ilmin kimiyyar zamantakewar al’umma ta kasar Sin don kara cudanyar juna da gudanar da ayyukan nazarin ilmi tare, baya ga samar wa kasashen dake yammacin nahiyar Afirka dabarun neman samun ci gaba.   Bugu da kari, shugaban kwalejin nazarin hukumomin kasar Senegal ya ce, aikin kulla yarjejeniyar kafa cibiyar nazarin Sin da Afirka cikin hadin gwiwa, ya shaida yadda hadin gwiwar kwararru a tsakanin Sin da Afirka ya kai wani sabon matsayi. (Mai Fassara: Maryam Yang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
    Haka zalika, mazauna jihohin da abin ya shafa, sun koka kan wasu abubuwan more rayuwa, kamar ruwan sha da sauran makamantansu. Masu Sayar Da Ruwa Sun Kara Farashi A Kano A Jihar Kano, wani mazaunin unguwar Hotoro ta Arewa, a Karamar Hukumar Nassarawa, Malam Gambo Muhammad, ya ce; ana sayar da kowacce jarka daya kan Naira 70, kafin samun wannan karancin wutar lantarki, wanda a halin yanzu kuma ake sayar da ita kan Naira 120. “Muna wahalar samun ruwan sha da arha a wannan yanki namu, manyan hanyoyin samun ruwa a Kano su ne, ta hanyar rijiyoyin burtsatsai (Boreholes), sannan ana iya samun ruwan ne ta hanyar amfani da wutar lantarki. Don haka, da zarar an ce babu wutar lantarki,...
    Hon. Ibrahim ya yi nuni da cewa a karkashin jagorancin Gwamna Abba an samu ci gaba sosai wajen tabbatar da samar da ingantaccen ilimi ga kowa da kowa da kyautata harkar lafiya da sufuri da biyan ma’aikata da ‘yan fansho hakkokinsu ba tare da jinkiri ba.   Kwamishinan ya jaddada goyon bayansa ga irin ayyukan raya kasa da Gwamna Abba ke yi, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya, bunkasa matasa da bunkasa harkar kasuwanci da sufuri a fadin Jiha Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    Kungiyar Shugabannin Arewa (NEF) ta zargi Shugaba Bola Tinubu da nadin mukaman gwamnati ba tare da daidaito tsakanin yankunan Nijeriya ba, wanda ta ce yana fifita yankin Kudu maso Yamma a kan sauran yankuna shida na kasar. Mai magana da yawun kungiyar, Farfesa Abubakar Jiddere, a cikin wata sanarwa a yau Juma’a a Abuja, ya bayyana cewa nadin da aka yi sun karkata ne wajen goyon bayan Kudu maso Yamma, yayin da sauran yankunan suka samu kadan ko kuma aka danne su. Gazawar Gwamnatin Tinubu Ce Ke Haddasa Zubar Da Jini A Filato – Ƙungiyar Dattawan Arewa Rurum Ya Shawarci Mafarautan Arewa Da Su Daina Zuwa Kudu Farauta  NEF ta bayyana cewa wannan lamari ya sabawa tsarin hadin kan kasa,...
    Farfesa Ibrahim Amos, wani Malamin cocin Katolika, ya samu ‘yanci daga hannun masu garkuwa da mutane a Jihar Kaduna, bayan an sace shi a ranar Alhamis, 24 ga Afrilu, 2025, daga gidansa a St. Gerald Quasi Parish, Kurmin Risga, ƙaramar hukumar Kauru. Wani shugaba a ɗariƙar dake Kafanchan, Rev. Fr. Jacob Shanet, ya tabbatar da sakin farfesan a cikin wata sanarwa da aka mikawa manema labarai. Ya bayyana cewa Farfesa Amos ya dawo lafiya jiya Alhamis ɗin da aka sace shi, amma bai bayyana yadda aka sake shi ba ko sun biya kuɗin fansa ba. Tinubu Ya Kaddamar Da Ci Gaba Da Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna  2027: Dalilan Da Suka Sa ‘Yan Siyasa Ke Tururuwar Zuwa Gidan Buhari A Kaduna...
    Wasu mutane 13 sun faɗa a komar ’yan sanda ka zargi da zubar da ciki da kuma mutuwar wata budurwa ’yar shekara 18 a Jihar Bauchi. Kakakin ’yan sandan jihar, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya ce ana tuhumar huɗu daga cikin mutanen da aikata laifin fyade, zubar da ciki da kuma mutuwar budurwa a garin Misau da ke Ƙaramar Hukumar Misau. Wakil ya ce, a ranar 4 ga Afrilu, 2025 sun samu bayanai ewa, kimanin watanni hudu da suka gabata, wasu matasa biyu a yankin Lariski da ke Misau, sun kama wata yarinya mai shekaru 18 da suka yi ta yi lalata da ita sau da yawa. Ya ce a lokacin da suka lura tana ɗauke da juna biyu, sai...
    Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta bullo da tsarin da kowanne maniyyaci zai san masaukinsa a kasa mai tsarki tun daga nan gida najeriya. Shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a shalkwatar hukumar dake Dutse. Yana mai cewar, wannan shi ne karon farko da hukumar ta bullo da tsarin domin maniyyaci ya san masaukinsa a nan gida kafin zuwa kasa mai tsarki. Game da batun kudade kuwa, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kuma kaddamar da kwamitin canjin kudaden guzuri na maniyyata domin samun saukin canji yayin aikin Hajjin. Ya ce an kafa kwamitin ne domin  bibiyar maniyyata kan canjin kudin guzuri, kasancewar wasu batagari na...
    Ofishin jakadancin kasar Iran a kasar Netherlands ta yi watsi da zargin da gwamnatin kasar takewa JMI na kokarin aiwatar da kashe-kashe har guda biyu a shekarar da ta gabata. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran tace Ofishin jakadancin Iran da ke Netherlands  ta fidda wannan sanarwan ne a jiya Alhamis. Ta kuma kara da cewa, kasar Iran wacce ta fi ko wace kasa a duniya fama da yan ta’adda, ba za ta yi kokarin kasashe wani a wani wuri ba. Sanarwan ta bayyana cewa wannan al-amarin siyasace ta tsakanin jami’an siyasa na kasar ta Netherlands  don neman amincewar masu kuri’a. Kafin haka dai wata cibiyar ayyukan tsaro ta kasar Netherlands  mai suna AIVD ta bada rahotomta na shekara...
    Gwamnatin kasar Amurka ta gargadi kasar Ukraine a dai dai lokacinda ta gabatar da shirin zaman lafiya da kasar Rasha na karshe. Shirin da shugaban kasar Donal Trump ya bayyana shi ne karshe dai, ya bukaci gwamnatin shugaba Volodimir Zelesky ta amince da yankin Cremea da kuma sauran yankunan hudu wadanda Rasha ta mamaye da karfi shekaru uku da suka gabata su zama mallakin kasar Rasha har’ abada. Sannan ta amince a daukewa kasar Rasha takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata tun bayan fara yakin. Sannan daga karshe ta amince ba zata shiga kungiyar tsaro ta NATO ba. Shawara bata yi maganar wani abu banada wadannan hudu ba, duk da cewa Ukraine tana da wasu bukatu a yarjeniyar tsagaita...
    Sojojin kasar ayemen sun kakkabo jiragen yaki na kasar Amurka wadanda ake sarrafashi daga nesa a kan kasar Yemen, da dama wadanda kimarsu ya kai dalar Amurka miliyon $200 a cikin makonni 6 kacal. Tashar talabijin ta Pressstv a nan Tehran ya bayyana cewa wadan nan jiragi suna aikin leken asiri ne a kan kasar ta Yemen, kuma duk da cewa suka tashi fiye da kafa 40,000 a sama, amma sojojin yemen suna iya kakkabosu. Wannan yana zuwa ne a dai lokacinda shugaban kasar Amurka Donar Trump ya kara umurnin a kara yawan hare-haren da ake kaiwa kasar ta Yamen. Mafi yawan hare-haren da suke kaiwa yana kasa mata da yara da kumalalata kamfanoni da kuma cibiyoyin samar da ruwa...
    A cikin sabban hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan kasar Yemen a jiya Alhamis sun kai hare-hare kan larduna guda 4 . Tashar talabijin ta Presstva anan Tehran ta nakalto majiyar labarai daga kasar ta Yemen jiragen yakin Amurka suna kai hare-haren a kan kasar kusan ko wani rana. Amurka dai tace tana kai wadan nan hare-hare kan kasar Yemen ne sai ta dakadar da kaiwa HKI hare-hare don goyon bayan Falasdinawa a Gaza, sannan ta dakatar da kaiwa Jiragen HKI da kuma na Amurka hare-hare a cikin tekun maliya. Kamfanin dillancin labaran SABA NEWS na kasar Yemen ya nakalto wani jami’an gwamnatin kasar wanda bai son a bayyana sunansa yana cewa jiragen yakin Amurka sun kai hare...
    Irin wannan zanga-zangar, ta sha ban-ban, da irin wadda ake gudanawar a kasashen da suka ci gaba kuma suke gudanar da mulki, irin na Dimokiradiyya, kamar da kasar Amurka, Birtaniya, Isara’ila da sauransu.   Sashe na 40, na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 da aka sabunta, ya bai wa ‘yan kasar ikon haduwa a waje guda su kuma yi hudda da sauran jama’a.   Kazalika, sashe na 11 na yarjejeniyar nahiyar Afirka, da ke magana kan ‘yancin ‘bil’Adama, wanda ita kanta Nijeriya ta rattaba hannu kan wannan yarjejeniyar na barin ‘yan kasar su gudanar da zanga a cikin lumana.   Amma sai dai, abin takaicin duk da ‘yancin na wannan sashen, mahukunta Nijeriya, suna yawan take wannan ‘yancin, kan...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rattaba hannu kan wasu sabbin dokoki guda huɗu da suka kafa muhimman hukumomi domin ƙarfafa tsarin gudanarwa na jihar da kuma haɓaka ci gaba mai ɗorewa. Waɗannan dokokin za su samar da Hukumar Kare Hakkokin Jama’a ta Jihar Kano (KASPA), Hukumar Kula da Tallace-tallace da Rubuce-rubuce ta Jihar Kano (KASIAA), Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Zamani ta Jihar Kano (KASITDA), da kuma Hukumar Bunƙasa Ƙananan Kasuwanci da Matsakaita ta Jihar Kano (KASMEDA). Gwamna Abba, ta bakin mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana muhimmancin waɗannan dokokin wajen ƙarfafa ƙirƙire-ƙirƙire, tallafa wa ƙananan kasuwanci, tsara tallace-tallace, da inganta kare hakkin jama’a da samar da ayyuka. Ya jaddada cewa waɗannan hukumomi za...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gbaata wadanda suka shafi siyasa, tsaro tattalin arziki zamantakewa da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ///… Madalla, masu sauraro shirimmu nay au zai yi Magana dangane da Yakin da Amurka take yi a tekun maliya kan kasar Yemen da kuma yadda kasashen yamma suke son su fitar da kwararru daga cikin zirin gasa don amfani kansu sannan su ga kashe dukkan Falasdinawa da suke yankin. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na...
    Wani kwararre a fannin lafiya da ke aiki da asibitin koyarwa na Aminu Kano ya ce bisa kididdigar baya-bayan nan sama da mutane miliyan 11 ne ke dauke da ciwon suga a Najeriya, wasu da dama kuma ba a gano su ba.       Farfesa Zuba Ilyasu, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron shekara-shekara na kungiyar likitocin endocrinologists of Nigeria (ACEN) karo na 14, wanda ya gudana a Tahir Guest Palace Kano.       Farfesa Ilyasu ya yi nuni da cewar akwai bukatar wayar da kan jama’a game da salon rayuwa da ake bukatar a yi amfani da su wajen magance matsalar ciwon suga da kuma kiba.     Shugaban taron,...
    –Ya Kamata Malamai Su Karfafa Zamantakewa Ta Wayewar Musulunci A Duk Inda Musulmi Suke   Assalamu alaikum wa rahmtullahi ta’ala wa barkatuh, ya Shehunmu da sauran daukacin Bayin Allah, muna mika sakon gaisuwa da kuma ziyara ta ‘yan’uwantaka ta Musulunci a dukkanin matakai da Annabi (SAW) ya zo mana da shi na Musulunci da Imani da kuma Ihsani. Bayan haka, muna godiya da irin bayanin da aka yi mana a karatunka na Tafsiri na rana ta 11 a game da muhimmancin karfafa zamantakewa ta wayewar Musulunci a tsakanin Musulmi a duk inda suke. Tabbas, lokaci ya yi da masu wa’azin Musulunci ya kamata su daina kafa hujjar yaki da ayoyin Surar Bara’a a wuraren da ba su dace ba, domin akwai...
    A kokarinta na ganin an gudanar da jarrabawar hadin gwiwa ta hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB, gwamnatin jihar Kano ta dakatar da aikin tsaftar muhalli na watan Afrilun 2025.   An dauki wannan matakin ne bayan nazari da tuntubar masu ruwa da tsaki, a kokarin baiwa daliban jihar Kano damar rubuta jarabawarsu ba tare da wata matsala ba.   A wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi, Ismail Garba Gwammaja ya fitar, ya ruwaito kwamishinan yana cewa.   “Dakatar na da nufin hana duk wani cikas da zai iya kawo cikas ga aikin jarrabawar da kuma tabbatar da cewa ‘yan dalibai za su iya zana jarabawarsu ba tare da wani shamaki...
    Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa duk waɗanda ke son barin jam’iyyar PDP su tafi yanzu, domin a bai wa masu kishin jam’iyyar damar sake gina ta. Saraki ya fitar da wannan bayanin ne a martani ga yawan sauye-sauyen jam’iyya da ake yi a PDP, ciki har da ficewar Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, wanda ya koma jam’iyyar APC. Saraki ya bayyana cewa ya samu kiran waya daga mambobin jam’iyyar da dama da kuma matasa masu goyon bayan dimokuraɗiyya, suna nuna damuwarsu game da barin jam’iyyar PDP, musamman ma a sashin jihar Delta. A cikin sanarwar, Saraki ya jaddada cewa yana da muhimmanci jam’iyyar ta kasance da mambobi masu cikakken kishin gaskiya fiye da yawan mambobin da...
    Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana a kan ‘wani makircin da kasar faransa ta kullawa falasdinawa a gaza’ don su amfana da kwararrunsu’ wanda ni tahir amin zan karanta. ///… Shugaba kungiyar kare hakkin bil’adama masi suna [the Euro-Mediterranean Human Rights Monitor] ta fallasa wani shiri tsakanin gwamnatin kasar faransa da HKI na fitar da kwararru da kuma masana falasdinawa da suka rage a Gaza, zuwa wajen yankin, kafin HKI ta fa wani gagarumin kissan kiyashi a yankin kashe falasdinawa da suka rage a yankin. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakalto Ramy Abdu shugaban kungiyar na fadar haka, ta kuma kara da cewa, offishin jakadancin kasar Faransa da ke birnin Qudus da aka...
    ”Wannan lokaci ne na bakin ciki, kuma a cikin irin wadannan lokutan ne kuka san wadanda ke kulawa da ku da gaske.”   Ribadu ya bayyana cewa Gwamnatin Bola Tinubu ta gaji tashin hankali da ke fama da shi a kasar nan, kuma tana aiki tukuru don gyara abubuwan da suka lalace.   Ya ce, “Na zo nan ne don in jajanta muku da sauran mutanen kirki na Benuwai kan asarar rayuka da aka yi da kuma tabbatar muku da cewa muna tare da ku.   “Benuwai jiha ce mai matukar muhimmanci a Nijeriya. Ta kasance daya daga cikin jihar da ake samar da abinci a kasa, ita ce ta farko wurin samar da abinci, kuma muna alfahari da hakan....
    Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ta yi watsi da bukatar Isra’ila na soke ko kuma ta dakatar da sammacin kama firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan harkokin sojin kasar Yoav Gallant. A cikin wata sanarwa da ta fitar, kotun ta ICC ta ce ta amince da daukaka karar da Isra’ila ta shigar na sake duba hurumin kotun kan laifukan da aka aikata a yankunan Falasdinu. A watan Nuwamba 2024, kotun ICC ta bayar da sammacin kame Netanyahu da tsohon ministansa na harkokin soji, Yoav Gallant, bisa laifukan cin zarafin bil’adama da laifukan yaki da suka shafi kisan kare dangi da Isra’ila ke ci gaba da yi kan Falasdinawa a zirin Gaza. Hukuncin ya tilastawa dukkan...
    ’Yan bindiga sun kashe wani sabon ango, sun kuma yi wani gaba da amaryasa bayan kwanaki 11 da ɗaura aurensu a wata unguwa a Jihar Nasarawa. Ganau sun shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun kai hari gidan sabbin ma’auratan ne da misalin ƙarfe karfe 11:00 na dare ranar Laraba, inda suka harbe angon har lahira, sannan suka tafi da matar zuwa wani wuri da ba a sani ba. Name(required) Email(required) Website Message Submit Lamarin ya faru ne a ƙauyen Akaleku, da ke Ƙaramar Hukumar Obi ta Jihar Nasarawa, a kan hanyar Lafia zuwa Makurɗi. Ma’auratan, Mista da Misisi Alu Anzaku, an ɗaura aurensu ne a ranar 12 ga Afrilu, 2025. An kama mata 2 na ƙoƙarin sayar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa ba tabbas ko za’a iya kawar da cutar zazzabin cizon sauro nan da shekarar 2030, musamman a nahiyar Afrika. Fiye da mutane miliyan 263 ne suka kamu da cutar a cikin 2023, kuma kusan 600,000 ne suka mutu sanadin cutar a cewar alkalumman na MDD. Musamman a wannan lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya rage kashe kudaden tallafi na kasa da kasa, inji rahoton. A cikin shekaru 25, zuba jari a yakin da ake yi da zazzabin cizon sauro ya hana kamuwa da cutar ga mutane biliyan 2 da kuma mutuwar mutane miliyan 13, musamman a Afirka. “Akwai babbar barazana, da kuma bukatar jajircewa wajen samar da magunguna in ji Philippe Duneton, darektan...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Zazzaɓin cizon sauro, wato maleriya, na cikin cututtuka mafiya shahara da kuma haɗari a Najeriya. Wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya nuna cewa Najeriya na da kaso mafi girma na mace-macen da cutar take haifarwa a duniya. Sau da yawa wanda ya kamu da cutar ta maleriya kan sake kamuwa da ita bayan ya warke. Ko me ya sa magungunan zazzaɓin cizon sauro suka daina aiki a jikin mutane? NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Amfani Da Kafofin Sada Zumunta Wajen Haɓaka Kasuwanci DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa Wannan batu shirin Najeriya A Yau zai duba yayin da ake bikin Ranar Malaria ta Duniya. Domin sauke shirin,...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Aisha ba wai mawaƙiyar amshi ba ce kawai a wajen Rarara ba. Sun yi matuƙar shaƙuwa da juna, kuma mu da muka san su ba abin mamaki ba ne don an ce za a yi wannan aure,” in ji majiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Najeriya ta amince kuma ta sanar cewa za a bai wa mahajjatan ƙasar kuɗin guzirinsu a hannu maimakon amfani da kati ko kuma asusun banki. Hakan ya biyo bayan tsoma bakin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi wanda ya roƙi shugaba Bola Tinubu a madadin maniyyatan ta hannun Hukumar Alhazai ta Ƙasa NAHCON. Ficewar Kawu a jam’iyyarmu zai kawo zaman lafiya – Shugaban NNPP na Kano An kori lakcara kan neman lalata da ɗaliba matar aure Hukumar NAHCON a ƙarƙashin jagorancin Farfesa Abdullahi Saleh, ta dage cewa ɓullo da hada-hadar kuɗi ta amfani da kati zai shafi shirin hukumar na gudanar da ayyukan hajjin 2025. Shugaban ya damu matuƙa da cewa amfani da katin banki na dole da...
    Sabbin ‘yan sama-jannatin da aka tura, za su gudanar da gwaje-gwaje da bincike game da yanayin rayuwa a sararin samaniya, da kimiyyar karamar fizgar kasa ko jazibiyya (micro-gravity physics) da sabbin fasahohin sararin samaniya.   Kazalika, za su kuma yi tafiye-tafiye mabambanta a sararin samaniya don kakkafa shingayen kariya daga baraguzai da tarkacen sararin samaniya, da kuma girkewa da dawo da na’urorin da aka makala a wajen tashar.   Ya zuwa yanzu dai, ‘yan sama jannatin kasar Sin 26 ne suka yi nasarar zuwa sararin samaniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere). Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
    Tsoffin kwamishinoni na Jihar Kano kamar su Hon. Diggol, Hon. Abbas Sani da Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Baffa Bichi su ma sun koma APC. Hakazalika, Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada wanda ya tsaya takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar ADP a zaɓen 2023, ya sauya sheƙa zuwa APC. Ana kallon wannan sauya sheƙar a matsayin wani babban tagomashi ga jam’iyyar APC musamman a Jihar Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Bugu da kari, masharhanta da dama na ganin karin harajin fito ba zai warware matsalar da Amurkan ke ciki ba. Ko shakka babu idan Amurka na son ta tunkari wannan kalubale bisa gaskiya, sai ta sauya tsarin ilimi, ta kuma bunkasa fannin kirkire-kirkirenta, da daga martabar masana’antu, da zuba jari na dogon lokaci a fannin, ba wai matakin jeka-na-yika na gajeren lokaci, irin wannan na baiwa kasuwa kariyar cinikayya ba.   A daya hannun kuma baya ga illar da wannan kare-karen haraji ya haifar, matakan kasashen da lamarin ya shafa na ramuwar gayya na iya haifar da hauhawar farashi na gaggawa, da jefa tattalin arzikin sassa daban daban cikin halin komada, a maimakon fatan da gwamnatin Amurkan ke yi na...
    An garzaya da ita asibitin Misau, daga nan aka mayar da ita zuwa Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Azare, inda aka tabbatar da mutuwarta. Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Bauchi, CSP Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis. Ya ce waɗanda aka kama sun amsa laifin kuma sun bayyana sunayen wasu da suka haɗa kai da su. Cikin sauran waɗanda aka kama har da Alkali Kawu, Maule Mai Ride, Mai Tumatir, Danguli, Yakubu da Kura. Wakil ya ce bincike yana guduna a hedikwatar ‘yansanda ta Misau, kuma sun ƙudiri aniyar ganin adalci ya tabbata. Ya ƙara da cewa bayan kammala bincike, za a gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar hukunci daidai da laifin da suka...
    Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi dangane da zagayowar ranar shahadar Imam Ja’afar Assadiq ( a.s) ya bayyana cewa: Tafarkin Imaman Ahlul-Bayti (a.s) ya kasance na gwgawarmaya da jajurcewa, kuma koyarwarsu ta ginu ne akan mandiki da kafa dalili. Jagoran juyin musuluncin na Iran ya ce; rayuwar Imam Ja’afar Assadiq           (  A. S ) ta ginu ne akan tafarkin koyar da ilimin addinin Allah, wacce ta kasace mai cike  da abin mamaki. Jagoran juyin musuluncin na Iran ya siffata mutanen Gaza da Lebanon da cewa suna tafiya ne akan wannan tafarki na Imaman shiriya.
    Kafafen watsa labarun HKi sun amabci cewa daya daga cikin sojojinsu ya halaka a Gaza, yayin da wasu 7 su ka jikkata. Kafafen watsa labarun na HKI sun ce, Harin da aka kai wa sojojin ya kunshi harbi daga kwararren maharbi da kuma harba makamin dake fasa motoci masu sulke. An ga jiragen sojan mamaya suna tsananta hare-hare a yankin da lamarin ya faru, saboda su sami damar dauki gawar sojan nasu da kuma wadanda su ka jikkata. Tashar talabijin ta 12; ta HKI ta ambaci cewa;Ana gwabza fada ne a arewacin Gaza, kuma mazauna yankin suna cewa sun ga jiragen sama masu yawa suna kai da komo.  Jiragen yakin HKI sun kai hare-hare masu yawa a yankin Arewacin Gaza,...
    Jiragen yakin Amurka sun kai jerin hare-haren a kan biranen San,a,Sa’adah da kuma Hudaidah na kasar Yemen. Kamfanin dillancin labarun “Saba’a” na kasar Yemen ya nakalto cewa sojojin na Amurka sun kai hare-hare har sau uku a dutsen Naqam, wanda  yake gabashin birnin San’aa. Kamfanin dillancin labarun na “Saba’a” ya kuma ce, jiragen yakin Amurka din sun kai hare-haren ne a tsakanin marecen jiya Laraba da kuma safiyar yau Alhamis. Daga cikin wuraren da aka kai wa harin jiya da marecen da akwai Sahlin dake karamar hukumar Ali-Salim. Sau 6 Amurkan ta kai wa yankin hare-hare. Da safiyar yau Alhamis kuwa jiragen yakin na Amurka sun kai hare-hare a gundumar Sa’adah. Wasu yankunan da su ka fuskanci hare-haren su ne,...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A daidai lokacin da sabani yake yin tsanani a tsakanin India da Pakistan, bayan wani hari da aka kai a Kashmir da ya yi sanadiyyar mutuwar  mutane 26, ministan tsaron kasar Pakistan Khajah Asif ya ce; matukar India ta keta hurumin kasarsa, to kuwa za ta fuskanci mayar da martani mai tsanani. Minista Khajah Asif ya kuma gargadi kasar ta India da ta guji keta hurumin kasar Pakistan. Asif ya kuma bukaci India da ta gudanar da bincike akan harin da aka yi a ranar Talata a yankin Kashmir, kuma ta nesanci yin wani abu wanda zai jefa yankin cikin yakin da ba a san yadda karshensa zai kare ba. Haka nan kuma ya ce; Tushen matsalar tana nan a...
    Ya ce, “Muddin muna da kwarin gwiwa, da karfin goyon bayan juna da hadin kai, za mu kai ga kawar da manufofi masu illa, da wanzar da daidaito da ci gaba a manufofin jagoranci a fannin kare yanayi da samar da ci gaba. ” (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi ta sallami ɗaya daga cikin malamanta, Dokta Usman Mohammed Aliyu daga jami’ar bisa zargin neman yin lalata da wata ɗaliba matar aure da ke karatun digiri na biyu. Idan dai ba a manta ba, Kamila Rufa’i Aliyu, ɗalibar Sashen koyon aikin injiniya ce, a shekarar bara ta roƙi mahukuntan Jami’ar ta hannun tsangayarsu da su binciki lamarin. Yobe na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya mafi zaman lafiya – Buni An kama mata 2 na ƙoƙarin sayar da ƙananan yara da aka sace Ɗalibar ta kuma zargi Dakta Aliyu da yi mata barazanar rashin samun nasarar karatunta idan har ta ƙi amincewa da biyan buƙatarsa. Malamin da ya samu labarin ƙarar da aka shigar da...
    Ban da haka, yadda gwamnatin Trump ba ta da tabbas a kan manufofinta na haraji yana kuma ba kasashen duniya mamaki. Ba a jima ba da gwamnatin Amurka ta sanar da matakinta na harajin ramuwar gayya a kan kasashen da ke ciniki da ita, sai kuma ga shugaba Trump ya sanar da dage harajin a kan wasu kasashe na kwanaki 90. Kuma kashegari sai aka ji ya yi barazanar cewa, in dai ba a kai ga cimma daidaito a shawarwari ba, to, Amurka za ta maido da harajin. Ban da haka, gwamnatin Amurka ta kuma yi gyara ta ba-zata a kan dokokinta na haraji, inda ta cire harajin ramuwar gayya a kan kayayyakin lataroni da suka hada da wayar salula...
    Ya buƙaci jama’a da su ci gaba da tallafa wa jami’an tsafta domin tabbatar da tsaftar muhalli a jihar. Aikin tsaftar muhalli na wata-wata, wanda ake yi a ƙarshen kowane wata, ana dakatar da zirga-zirgar ababen hawa na wasu awanni domin tsaftace muhalli a faɗin Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya ƙara da cewa IEDs guda biyu da aka gano an birne su ne yankunan ƙaramar hukumar Hong, kuma an fashe su. Morris ya kuma ce ‘yansandan sun ceto wasu da aka sace guda shida tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro. Ya jinjina wa jami’an tsaron da suka taka rawar gani wajen wannan aiki, kuma ya tabbatarwa da jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da ɗaukar matakai don tabbatar da tsaro a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce a yanzu jihar na ɗaya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Najeriya. Ya ce, a matsayinsa na babban jami’in shari’a da tsaro a Jihar Yobe, yana da haƙƙin ganin an bi doka don tabbatar da cewa jihar ta samu zaman lafiya. An kama mata 2 na ƙoƙarin sayar da ƙananan yara da aka sace An fara raba wa almajirai tabarma da gidan sauro a Yobe Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin karɓar lambar karramawa da aka yi masa shi da wasu shugabnnin da Ƙungiyar Inganta zaman lafiya ta “Peace Building Development Consult” (PBDC) ta yi musu. Gwamnan wanda ya samu wakilcin babban lauya kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Imo ta kama wasu mata biyu a lokacin da suke yunƙurin sayar da wani yaro ɗan shekara huɗu da aka yi garkuwa da shi a Owerri kan kuɗi Naira miliyan 2.7. An yi garkuwa da yaron ne a Abuja a lokacin da yake tallan kayan miya, sannan aka kawo shi Owerri a sayar da shi kafin a sa’ar kuɓutar da shi daga masu son sayar da shi. An fara raba wa almajirai tabarma da gidan sauro a Yobe Na ba ku wata 1 ku murƙushe ’yan ta’adda — Olukoyede ga sojoji Waɗanda ake zargin sun haɗa da Joy Ugwu daga garin Idah ta jihar Kogi, da Rosella Michael daga garin  Zamba da ke Abuja, yayin da...
    Hukumar Ilimin Larabci da Musulunci ta Jihar Yobe (AISEB) ta fara rabon tabarmi da gidajen sauro ga almajirai a fadin jihar. Sakataren Zartarwa na hukumar, Malam Umar Abubakar ya cen tabarmi da gidajen sauron tallafi na daga cikin kokarin da gwamnati ke yi na inganta walwala da rayuwar almajiran makarantun tsangaya a fadin jihar. A cewarsa, shirin ya yi daidai da umarnin da gwamnatin jihar ta ba hukumar na tabbatar da kulawa da kuma tallafa wa yara almajirai. Ya bayyana cewa an tsara rabon ga ɗalibai 100 a kowace karamar hukuma cikin kananan hukumomin Jihar 17, wanda za a fara daga makarantun Goni Yahaya da Goni Muhammad Tsangaya da ke Damaturu. Ya ƙara da cewa, kayayyakin za su taimaka wa...
    Hukumar lura da gidajen bashin ma’aikatan gwamnatin tarayya (FGSHLB) ta sanar da cewa ta fara tattara jerin sunayen ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya amma ba su biya bashin gidajen da suka karɓa ba. Shugabar sashin sadarwa da hulɗa da jama’a na FGSHLB, Ngozi Obiechina, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis a Abuja, inda ta ruwaito cewa shugabar hukumar, Salamatu Ahmed, tana cewa wannan matakin yana nufin dawo da dukiyoyin da aka yi rance daga ma’aikatan da suka yi ritaya amma ba su kammala biyan bashin ba. Rashin Tsaro: Gwamnatin Neja Ta Saka Dokar Zama A Gida A Minna Gina Al’umma Mai Kyakkyawar Makomar Bai Daya: Jigon Ziyarar Xi A Kudu Maso Gabashin Asiya Salamatu...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ta bayyana cewa; Kakaba takunkumi kan kasarta ya sabawa ikirarin Amurka na yin shawarwari da ita Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta dauka na kakabawa wasu gungun mutane masu alaka da bangaren makamashi, man fetur da iskar gas da kuma wasu mutane da dama masu fafutuka a shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na lumana takunkumi. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Baqa’i ya bayyana manufar takunkuman da Amurka ta kakabawa al’ummar Iran da cewa; A fili take nuna kyama ga masu yanke shawaran Amurka kan al’ummar Iran da kuma nuna rashin mutunta doka da hakkin dan Adam ne. Ya kara da cewa: Dogaro...
    Jami’in kasar Yemen ya jaddada cewa: Kwanaki masu zuwa za su aiwatar da abubuwan mamaki da za su ba abokan gabanmu mamaki! Daraktan sashin yada labarai na fadar shugaban kasar Yemen Zaid Al-Gharsi ya jaddada samun gagarumin ci gaba a karfin sojojin kasar Yemen musamman a fannin fasaha da makamai. Ya yi nuni da cewa, kasar Yemen na gab da samar da sabbin makamai da za su bai wa kowa mamaki. A cikin wata hira da tashar talabijin ta Al-Alam, Zaid Al-Gharsi ya yi magana game da irin goyon bayan da kasar Yamen ke ba wa yankin Zirin Gaza, inda ya yi nuni da mahimmancin hare-haren soji kai tsaye kan makiya ‘yan sahayoniyya tare da jaddada fifikon karfin kasar Yemen...
    Munanan azabtarwa kan fursunonin Falasdinawa a gidajen kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila da suka hada da fyade da dangogin azaba Rahoton da Hukumar Kula da Fursunoni Falasdinawa dakungiyar Fursunonin Falasdinawa da aka saka daga gidan kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila sun fiyar da rahoton hadin gwiwa a yau Alhamis, 24 ga watan Afrilun shekara ta 2025, da ya kunshi munanan shaida daga fursunonin Zirin Gaza da ke tsare a gidan yarin Negev da sansanin Ofer na gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila. Rahoton ya bayyana yadda ake ci gaba da yin fyade da cin zarafi ga wadanda ake tsare da su a Gaza. Wanda ake tsare da shi a sansanin Ofer ya bayyana cewa da gangan masu gadin sansanin suke kara radadin yadda wanda...
    Sabuwar gwamnatin Siriya tana kara matsa lamba kan bangarorin ‘yan gwagwarmaya domin Isra’ila ta janye daga wasu yankunan kasarta Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da tura kayayyakin soji zuwa tsaunukan Dutsen Harmon, yayin da suke hanzarta gina abin da suka kira “Katangar tsaro.” Har ila yau, sun karfafa wuraren tsaro da suka kafa a cikin yankunan Siriya, a cikin abin da gwamnatin Isra’ila ta kira “yankin da ke da kariya,” wanda ya hada da mamaye wasu sassan garuruwan Quneitra da Dara’a. Majiyoyin cikin gida a garin Nawa da ke cikin karkarar Dara’a na cewa, mahukuntan kasar Siriya na ci gaba da daukan matakan matsin lamba, ta hanyar shugabannin kabilu da kwamandojin ma’aikatar tsaro a Dara’a, na tilastawa bangarorin da...
    Mutane 47 ne suka rasa rayukansu tare da jikkatan wasu da dama a harin da aka kai da jirgin sama kan birnin El-Fasher na kasar Sudan Runduna ta 6 da ke yankin El- Fasher ta sanar da mutuwar fararen hula 47 tare da jikkata wasu da dama sakamakon kazamin lugudan wuta da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka yi kan birnin El- Fasher, fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa. A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce: Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces na ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula, inda suka yi amfani da harsasai masu yawa a yayin da suka yi ruwan wuta a kan unguwannin birnin El-Fasher a...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, ’yan kasuwa 1,000 za su samu jarin fara aiki na Naira 150,000 kowannensu, da nufin sauya akalar kasuwancin su zuwa sana’o’i na zamani a faɗin Jihar Zamfara.   A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cewa bayan hawansa mulki, gwamnatinsa ta bullo da shirye-shiryen ƙarfafawa da dama tare da samar da damarmaki don cimma manufofinsa na ceto.   “Waɗannan tsare-tsare ba wani kebantaccen abu ba ne, wani ɓangare ne na babban burinmu wajen samar da jihar Zamfara mai albarka don haɗa abokan hulɗa don magance ɗimbim matsalolin zamantakewa da tattalin arziki. “Yawancin tsare-tsare na rage raɗaɗin talauci da wannan gwamnati ta bullo da su sun yi tasiri ga rayuwar dubban ‘yan jihar, ƙudirin...
    Gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da ƴan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda sun amince su dakatar da faɗa a gabashin ƙasar har sai an kammala tattaunawar sulhu da ke gudana a halin yanzu wanda Qatar ke shiga tsakani. Wannan dai ita ce yarjejeniyar sulhu ta baya-bayan nan tun bayan da ƴan tawayen suka ƙara kai farmaki a gabashin ƙasar inda hukumomi suka ce an kashe mutane 7,000 tun daga watan Janairu. A ranar Larabar da ta gabata ce, ɓangarorin biyu suka ba da sanarwar yin aiki tare don samar da zaman lafiya, bayan shafe sama da mako guda suna tattaunawa, wanda suka ce an gudanar cikin aminci tare da mutunta juna. A watan da ya gabata, shugaban ƙasar...
    Ma’aikatar yada labarai ta jihar Kano tare da hadin gwiwar hukumar kula da gidajen Radiyo da Talabijin ta kasa NBC sun shirya taron yini biyu ga masu fafutukar siyasa da masu sharhi kan harkokin yada labarai.       Taron na da nufin tsaftace harkar siyasa da inganta fahimtar juna tsakanin ‘yan siyasa a jihar.   An zabo mahalarta taron ne daga jam’iyyun siyasa daban-daban da gidajen rediyo a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.   A nasa jawabin, kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Waiya, ya bayyana cewa, a karshen taron, mahalarta taron za su fahimci ladubban da suka shafi harkokin siyasa.   Ya yi Allah wadai da karuwar kararrakin batanci da sunan...
    “Ka koma gefe – ba wai kabar wa abokan hamayyarka takara ba, amma don sabbin jini matasa ‘yan Nijeriya da za su iya ciyar da al’umma gaba da sabbin kuzari da tunani.” in ji shi.   Ya kara da cewa, ya kamata shugaban kasa ya yi tunani a kan nagartattun abubuwan da yake son bari bayanshi da kuma yadda tarihi zai tuna da shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya ba da umarnin ga rundunar sojin Najeriya da ta fatattaki ‘yan bindigar da ke addabar al’ummar kananan hukumomin Baruten da Kaiama na jihar kwara da Borgu da ke dajin Kainji a jihar Neja cikin wata guda.   A jawabin da ya yi wa dakarun rundunar soji bataliya ta 22  a Sobi Ilorin, Oluyede ya ce sojojin Najeriya ba za su bari tashin hankalin yankin arewa maso gabas ya rikide zuwa arewa ta tsakiya ba.   A cewarsa nauyi ne da ya rataya a wuyan sojojin Najeriya su kare martabar yankunan kasar.   Shugaban hafsan sojin ya ce dole ne a fatattaki ‘yan bindigar daga yankin Najeriya nan da wata guda.  ...
    Kujeru dubu daya da dari hudu da bakwai ne aka ware wa hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Taraba domin maniyyata bana.   Babban Sakataren Hukumar mai barin gado Umar Ahmed Chiroma ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan matakin da ake na shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin bana na 2025 ba tare da tangarda ba.   Aikin Hajji daya ne daga cikin rukunnan Musulunci guda biyar kuma Musulmin muminai na gudanar da aikin Hajji a kowace shekara akalla sau daya a rayuwarsu.   Chiroma ya ce hukumar ta kai wani mataki na ci gaba ta fannin shirye-shirye kamar yadda hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta bayar, inda ya ce sama da maniyyatan jihar...
    A hukumance gwamnatin tarayya ta ayyana filin jirgin saman Bola Ahmed Tinubu dake Minna a matsayin mafita ga jiragen dake sauka Abuja.   Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan a yayin bikin kaddamar da jirgin saman na Overland Airways a filin jirgin sama na BAT dake Minna.   Festus Keyamo ya ce ana shirin daukar matakan da suka wajaba kamar su kwastam, shige da fice, ‘yan sanda, NDLEA da sauran su don sarrafa fasinjoji idan filin jirgin Abuja ya samu matsala.   Gwamnan jihar Neja Mohammed Umar Bago wanda ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa ci gaba da goyon bayan da yake baiwa jihar, ya bayyana cewa wannan nasara wani kokari ne na hadin...
    Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya  ba da umarnin gaggawa da a yi cikakken sauyi ga dabarun tsaron ƙasa, yana mai umartar shugabannin tsaro su ɗauki matakan gaggawa don daƙile ƙaruwar tashin hankali da kashe-kashe jihohin Borno, Filato, Binuwai, da Kwara. Tinubu, wanda ya gana da shugabannin tsaro a Fadar Shugaban Ƙasa, ya ce dole ne a kawo ƙarshen kashe-kashe a jihohin da abin ya shafa. “Ya isa haka,” in ji Shugaba Tinubu yayin da ya sake yin tir da kai hari ga ’yan Najeriya ba tare da wani dalili ba. Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa (NSA), Nuhu Ribadu, ya shaida wa manema labarai cewa shugabannin tsaron sun yi wa shugaban ƙasa cikakken bayani kan halin da...
    Shi dai filin jirgin saman, wanda gwamnatin Umaru Bago ta gina a Jihar Neja, an raɗa masa sunan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.   Jirgin kasuwancin na farko mallakin kamfanin Overland Air mai lamba 5N-CCN ya sauka ne da misalin ƙarfe 1:32 na rana.   Cikin fasinjojin akwai Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, Minista Mohammed Idris, tsohon Gwamnan Neja Dakta Babangida Aliyu, Ƙaramin Ministan Harkokin Noma da Samar da Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, da wasu manyan jami’an gwamnati.   Ministan ya yaba wa Shugaba Tinubu saboda samar da yanayin da ya bai wa filin jirgin damar fara aiki, yana mai cewa hakan na nuna jajircewar Shugaban Ƙasa wajen inganta ababen more rayuwa a faɗin ƙasar.   Haka kuma, Ministan...
    Muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Ambasada Umar Damagum, ya umarci jami’an jam’iyyar da su yi karɓi Arch. Setonji Koshoedo a matsayin mukaddashin sakataren jam’iyya na ƙasa. Gwamnonin PDP, a taron da suka yi a Ibadan, Jihar Oyo, sun amince da Koshoedo a matsayin mukaddashin sakatare har sai lokacin da shugabannin shiyyar Kudu maso Gabas za su zaɓi cikakken sakatare wanda Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar zai amince da shi. Kotun Ƙoli, a hukuncin da ta yanke kan wanda ya cancanci ya riƙe muƙamin tsakanin Sanata Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye, ta ba jam’iyyar ikon yanke shawara kan shugabanninta. Sai dai a wata takarda da Alhaji Gurama Bawa, jami’in gudanarwa na mukaddashin shugaban jam’iyyar ya fitar, ta ce...
    “Akwai wasu bincike da ake gudanarwa domin kamar yadda muka sani, an sanar da cire tallafin man fetur ne a ranar 29 ga watan Mayun 2023, amma an dauki lokaci kafin a cimma wannan kudurin. A halin yanzu, wani bangare na biyan basussukan da ake bin NNPC, daga kasafin kudin gwamnati ake tanada”.   Ya kara da cewa, babban aikin da ke gaban NNPCL shi ne bunkasa hako danyen mai da kuma samar da karin kudaden shiga – a takardun Dala zuwa Asusun Tarayya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
    Ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso, ƙarƙashin inuwar Ƙungiyar Ƙasashen Sahel (AES), sun sanar da shirinsu na ƙaddamar da gidan rediyo na haɗin gwiwa. Ƙasashen guda uku, waɗanda duk a halin yanzu suke ƙarƙashin mulkin soja, sun jaddada cewa sun kafa gidan rediyon ne da nufin daƙile farfagandar ƙasashen waje da kuma isar da “ingantattun bayanai na gaskiya” ga ’yan ƙasarsu. Sanarwar tasu ta kasance bayan ƙaddamar da gidan talabijin ɗinsu na intanet na haɗin gwiwa da suka yi a watan Disamba na 2024, wanda suka bayyana a matsayin dandamali da aka samar domin “yaƙi da yaɗa labaran ƙarya.” Baya ga waɗannan ayyukan watsa labarai, a baya ƙungiyar ta nuna sha’awarta ta kafa kamfanin jiragen sama na yankin da...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jinjinawa kasashen Sin da Rasha a matsayin abokan hulda na kut-da-kut da kasar, yayin da ya isa birnin Beijing domin yin shawarwari da manyan jami’an kasar Sin, gabanin yin tattaunawa zagaye ta uku da Amurka kan shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Abbas Araghchi ya shaida wa kafar yada labaran Iran a babban birnin kasar Sin a ranar Laraba cewa, “Sin da Rasha abokan hulda ne na kut da kut da suka tsaya tare da mu a lokutan wahala, don yana da kyau da ma’ana mu ci gaba da tuntubar juna tare da su a bangarori daban-daban, musamman ma yanzu da ake tattaunawa da Amurka.” “Ya zama dole mu sanar da abokanmu a kasar...
    Amurka ta kai wasu sabbin hare-hare ta sama a Yaman, a daidai lokacin da kasar Larabawar ke ci gaba da nuna goyon baya ga Falasdinawa a Gaza. Gwamnonin Sana’a da Sa’ada su ne wuraren da Amurka ta kaddamar da sabbin hare-hare a safiyar Alhamis. A birnin San’a, jiragen yakin Amurka sun kai hare-hare 6 a yankin Barash da ke gabashin Dutsen Nuqum. Har ila yau Amurka ta kai hari a unguwar Al-Jarf da ke gabashin gundumar Sha’ub ta lardin Sana’a. A arewa maso yammacin kasar, an kai wasu hare-hare 6 ta jiragen yakin Amurka a yankin Sahlin da ke gundumar Al Salem a gundumar Sa’ada. Har ila yau, Amurka ta kai wasu jerin hare-hare ta sama kan lardin Al-Hudaidah, inda...
    Aljeriya sun kori fiye da bakin haure 1,100 zuwa Nijar a rana guda, al’amarin da ba a taba ganin irinsa ba. Bakin hauren da hukumomin Aljeriyar suka bayyana da basa bisa ka’ida, an kora su a cikin hamadar sahara a ranar Asabar din da ta gabata, Inda sukayi tattaki zuwa kan iyakar kasar Nijar, kasar da dubban bakin haure ke bi domin zuwa Libya da Aljeriya domin isa Turai. Wannan dai shi ne karo na farko da aka kori bakin haure da dama daga kasar Aljeriya a lokaci guda. A cewar kungiyar ‘Alarme Phone Sahara’ ta Nijar da ke taimakawa bakin haure a cikin hamada, an kori mutane 1,140 a lokaci guda, adadin da ba a taba ganin irinsa ba....
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran,  za ta karbi bakuncin taron farko na kasa da kasa kan kare hakkin bil adama a Gabas ta Tsakiya. Shugaban Hukumar Al’adu da Sadarwa ta Musulunci Mohammad Mehdi Imanipour ya bayyana cewa, za a gudanar da taron farko na kasa da kasa kan batun kare hakkin bil’adama kan Gabas ta Tsakiya a lokaci guda a Tehran, Qom da Isfahan daga ranar 28 ga Afrilu zuwa 2 ga Mayu. Hakkin dan adam na daya daga cikin batutuwan da suka fi muhimmanci a cikin al’ummomi, saidai a baya bayan nan wasu gwamnatoci sun yi watsi da yancin dan adam gaba daya. Mohammad Mehdi Imanipour ya ce “A yau, misali karara na take hakkin bil’adama shi ne kisan kiyashi...
    Sanarwar ta kara da cewa, Shugaban tawagar ‘yan fashin, Baba-Beru ya samu munanan raunuka, wanda daga baya ya rasu a Asibiti.   “An garzaya da dukkan wadanda suka samu raunuka zuwa Asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano, inda Baba-beru ya rasu a lokacin da ake jinyarsa, amma jami’an ‘yansanda an sallame su bayan sun gama jinya,” in ji sanarwar.   Rundunar ‘yansandan ta ce Baba-Beru, mazaunin Kofar Mazugal a karamar hukumar Dala, na cikin jerin sunayen wadanda ake nema ruwa a jallo kafin faruwar lamarin.   Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Ibrahim Bakori, ya yabawa bajintar jami’an da suka dakile yunkurin ‘yan fashin tare da jaddada aniyar rundunar na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar.  ...
    Jami’in ya kara da cewa, kasar Sin ba ta son gwabza yakin kasuwanci da karin harajin kwastam, amma kuma ba za ta rungume hannu ta zuba ido ba idan yakin ya kaure, yana mai nuni da cewa, idan har Amurka ta zabi fafata yakin kasuwanci, Sin za ta sha damarar yakin har sai ta ga abin da ya ture wa buzu nadi. Sai dai kuma duk da haka, ya ce idan Amurka na son a tattauna, Sin za ta bar kofarta a bude domin yin hakan.   Bugu da kari, dangane da batun yadda a baya-bayan nan kafafen yada labarun kasar Panama suka soki Amurka kan yin katsalandan da nuna babakere a kasashen yankin tsakiyar Amurka, musamman a kasar ta...
    Na uku, ba da ra’ayin samun tsaro kafada da kafada, inda aka jaddada cewa, ya dace kasa da kasa su yi fatali da ra’ayin nuna wa juna fito-na-fito, kana, su fuskanci dimbin kalubalen tsaro cikin hadin-gwiwa. Na hudu wato na karshe, tallata ra’ayin tabbatar da tsaro mai dorewa, wato a maida hankali kan dorewar tsaro na wani dogon lokaci. Alal misali, yayin da ake daidaita rikicin wani yanki, bai dace a dogara kan matakan soja kadai ba, ya kamata a nemo mafita tun daga asalin rikicin. Wannan shawarar tsaron da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ta samu amincewa sosai daga mutanen kasa da kasa, inda ya zuwa yanzu, ta riga ta samu goyon-baya daga kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa...
    Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ya gana da babban mai ba da shawara kan tsaron ƙasa, Nuhu Ribadu, da hafsan hafsoshin tsaro na ƙasa, Christopher Musa. Rahotanni dai na nuna sun shiga taron ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja da misalin ƙarfe 3 na rana. Majalisun jihohi sun buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro Gwamna da jiga-jigan siyasa a Delta sun fice daga PDP zuwa APC Wannan dai shi ne karo na farko da Tinubun ke ganawa da jagororin tsaron tun bayan dawowarsa daga Faransa da Birtaniya ranar Litinin. Kafin dawowarsa dai, ‘yan siyasa da dama da sauran al’umma sun koka ka yadda shugaban ya shafe sati biyu a ƙasashen duk da cewa matsalar tsaro na ci gaba da...
    Rashford ya yi watsi da yiwuwar komawa Landan, inda yace ba lallai bane ya cigaba da wasa a karkashin Ruben, inda yake da burin zama a kungiyar da zata buga gasar Zakarun Turai a badi, majiyoyi na kusa da dan wasan sun tabbatar Rashford har yanzu bai tattauna kan makomarsa ba kuma baya shirin yin hakan har zuwa tsakiyar watan Yuni. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa, Abdurrahman Kawu Sumaila ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC. Sumaila ya tabbatar wa Aminiya ficewarsa a wani saƙon kar ta kwana, bayan wallafa wa a shafinsa na Facebook. Majalisun jihohi sun buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro Gwamna da jiga-jigan siyasa a Delta sun fice daga PDP zuwa APC “Gaskiya ne na koma APC. Damuwata a ko yaushe ita ce walwalar al’ummar mazaɓata,” in ji shi. Sanatan ya jaddada cewa matakin da ya ɗauka na sauya sheƙar ya yi shi ne domin inganta rayuwar al’ummar mazaɓarsa, da kuma tabbatar da ci gabansu mai dorewa. Kawu dai ya daɗe da raba gari da tafiyar Kwankwasiyya da NNPP da ya...
    Da yake jawabi a fadar Mai Tangele (Sarkin Billiri), Danladi Sanusi Maiyamba, ya bayyana lamarin da matukar bakin ciki tare da fatan samun makoma mai kyau ga wadanda suka rasu, ya kuma warkar da wadanda suka samu raunuka da gaggawa.   Daga nan sai Gwamna Inuwa ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 2 kowanne ga iyalai biyar da suka rasa rayukan ‘yan uwansu, wanda ya kai adadin zuwa Naira miliyan 10.   Ya kuma yi alkawarin biyan kudaden jinya ga wadanda ke karbar magani a Asibitocin jihar.   A yayin da yake godiya, Sarki Maiyamba ya ce, hatsarin na Easter ya girgiza daukacin masarautar Tangale, amma ya amince da matakin da gwamnatin jihar ta dauka, wanda ya ce hakan...
    A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, yake-yaken karin haraji da kasuwanci ba su haifar da komai illa tauye halastattun hakkoki da muradun dukkan kasashe, tare da kawo cikas ga tsarin ciniki tsakanin bangarori daban-daban, da kuma yin tasiri mara kyau ga tsarin tattalin arzikin duniya.   Yayin ganawarsa da shugaban kasar Azabaijan Ilham Aliyev, shugaba Xi ya yi bayanin cewa, kasar Sin tana da muradin yin hadin gwiwa tare da kasar Azabaijan wajen kiyaye tsarin kasa da kasa a karkashin Majalisar Dinkin Duniya, da tabbatar da tsarin kasa da kasa bisa dokokin da aka amince da su a duniya, da yin tsayuwar daka wajen kare halastattun hakkoki da muradu, da kare daidaito da adalci...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umurni a kwanan baya kan aikin inganta hadin gwiwar jama’a da sojan kasar, inda ya ce, nagartacciyar hulda mai karfi tsakanin jama’a da soja fifiko ne da bangaren siyasar Sin ya jima da shi. Ya ce ya kamata a tsaya tsayin daka kan jagorancin ra’ayin gurguzu mai salon musamman na kasar Sin a sabon zamani, kuma a nace ga jagorantar jam’iyyar JKS a dukkanin fannoni, da zurfafa yin kwaskwarima, da kirkire-kirkire, da ma kyautata tsare-tsare da manufofi, har da raya aikin inganta hadin gwiwar jama’a da soja.   An kira taron rada sunan birane ko gundumomi dake taka rawar gani a wannan bangare a yau Laraba a nan birnin Beijing. Inda...
    Gwamnatin Shugaban kasa John Mahama ta tsige Gertrude Torkornoo daga mukaminta na babbar mai shari’ar kasar, bisa wasu zarge-zarge da ake yi mata, domin bayar da damar gudanar da bincike. Matakin da gwamnatin ta dauka na tsige babbar mai shari’ar ya jawo cece-kuce a tsakanin mutanen kasar. Tsohon mai shigar da kara na kasar Godfrred Yeboah Dame ya yi tir da matakin na gwamnati da ya siffata da farmaki mafi girma akan ma’aikatar shari’a a tarihin kasar.”  Ita kuwa jam’iyyar hamayya ta zargi shugaban kasa da tsoma baki a harkokin shari’ar kasar, domin nada alkalan da za su  zama masu biyayya ga jam’iyyar da take Mulki ta ( NDC). Torkornoo da ta hau mukamin nata a 2023, kuma  ta kasance...
    Asusun bayar da lamuni na duniya ( IMF) ya yi gargadin cewa rashin tabbataci da Karin kudin harajin Amurka ya haddasa zai iya kawo tsaiko a cikin harkokin cinikiyya ta duniya. Sanarwar wacce babban jami’in ttatalin arziki na Asusun bayar da lamunin na duniya Pierre -Oliver-Gourinchas, ya bayyana ta kara da cewa; Za a iya samun karuwar hargitsi a cikin harkokin tattalin arzikin na duniya da dama yake fama da matsala. Jami’in ya yi bayani ne  bayan sake yin hasashe akan ci gaban tattalin arzikin duniya, wanda aka fitar a cikin rahoto a ranar Talatar nan. Asusun bayar da lamunin ya yi hasashen cewa tattalin arzikin duniyar zai bunkasa da kaso 2.8 % a cikin 2025, da hakan yake nuni...
    Kungiyar da take wakiltar Iran a wasannin Taekwondo na duniya a kasar Sin, ta sami lambobin yabo 8 a ranar farko da bude gasar ta kasa da kasa. An  fara wasannin na Tikondu a garin Tayan dake kasar China wanda shi ne karo na 7 da kuma ‘yan wasa 491 daga duniya suke gasa. Daga cikin lambobin yabon din da tawagar ta Iran ta lashe da akwai gwala-gwalai 4, azurfa 3 da kuma tagulla.
    Ministan harkokin wajen Iran wanda ya ziyarci kasar China, ya bayyana cewa, tattaunawa da mahukunta wannan kasa ta yi kyau, kuma ba da jimawa ba, shugaban kasar Iran zai kai Ziyara can kasar. Ministan harkokin wajen na Iran Abbas Arakci bayan ganawa da takwaransa na China ya ce; Na yi doguwar ganawa da ministan harkokin wajen China, wacce take mai muhimmanci, kuma kusan dukkanin bangarorin da suka shafi alakar tsakanin kasashenmu biyu mu ka tattauna, haka nan kuma batutuwa da su ka shafi siyasar kasa da kasa.” Arakci ya kara da cewa; Da akwai fahimtar juna a tsakaninmu, musamman abinda ya shafi batun makamashin Nukiliyar Iran na zaman lafiya, da tataunawar da ake yi da Amurka.” Haka nan kuma ya...
    Hukumar lafiya ta duniya  (W.H.O ) ta sanar da cewa rashin magani da na’urorin wanke koda a Gaza, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 400 masu fama da wannan cutar. Hukumar lafiyar ta duniya ( w.h.o) ta kuma yi ishara da yadda ‘yan mamaya su ka lalata bangarorin da suke kula da cutuka na musamman a cikin asibitoci. Ita ma hukumar lafiya ta Gaza ta bayyana cewa; masu fama da cutar koda a yankin suna fama da matsaloli na rashin Magani, kuma daruruwa daga cikinsu sun mutu saboda hakan. Haka nan kuma ta  yi ishara da yadda mutane 400 daga cikinsu su ka rasu, da hakan yake nufin kaso 40% na adadin masu wannan cutar. A gefe daya, ma’aikatar kiwon lafiyar...
    Ƙungiyar shugabannin majalisun jihohin Nijeriya ta yi tur da matsalolin tsaron da suka addabi jihohin Filato, Borno, Binuwai, Neja, da kuma Kwara a baya-bayan nan. Ƙungiyar ta buƙaci gwamnatocin jihohi da na tarayya da su ɗauki matakan gaggawa domin daƙile bala’in da jihohin a kwanan nan suka tsinci kansu a ciki.  Abin da ya sa na bi sahun mahaifiyata a Kannywood — Maryam Intete Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta ɓulla a Nijeriya Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a Ibadan da ke Oyo mai dauke da sa hannun shugabanta, Adebo Ogundoyin. Ya bayyana cewa kashe-kashen dubunnan al’ummar da ba su ji ba, ba su gani ba ya janyo musu asarar gidajensu, da dukiyoyinsu, yana haifar...
    Matsalar tsaro ta kara tabarbare a jihohin Filato da Benuwai, inda rahotanni ke cewa, wasu da ake zargin makiyaya ne daga kasashen waje ne ke kai hare-haren kashe rayuka da kuma raba al’umma da matsugunansu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa na jihar sun sun sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Daga cikin jiga-jigan da suka sauya sheƙa har da tsohon gwamna Ifeanyi Okowa, shugaban jam’iyya, da sauran masu ruwa da tsakin jam’iyyar reshen jihar. Abin da ya sa na bi sahun mahaifiyata a Kannywood — Maryam Intete Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta ɓulla a Nijeriya Sanarwar ficewar ta su ta zo ne bayan kammala taron sa’o’i shida da suka gudanar a gidan gwamnatin jihar, kamar yadda sanarwar da Sanata daga jam’iyyar, James Manager, ya bayyana. “Duk wani dan PDP na jihar har da gwamna, da tsohon gwamna Okowa, da shugaban majalisa, da shugaban jam’iyyar, da duk ciyamomin ƙanannan hukumomi...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Bugu da kari, kasar ta samar da cibiyoyin kula da lafiyar mata da kananan yara 3,081, baya ga likitocin yara da na mata a fadin kasar da yawansu ya kai 373,000. Kana fiye da kashi 90 cikin dari na cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a yanzu sun mallaki kayan aiki da sassan kula da lafiyar yara masu inganci.   Ba a cikin kasarta kawai take kokarin inganta kiwon lafiyar mata da kananan yara ba, har ma da kasashen duniya, domin kwararrun likitocin Sin da aka tura don ba da agaji a kasashen waje sun gudanar da ayyukan kula da lafiyar mata da yara a kasashe da yankuna 44, ciki har da wasu kasashen Afirka. A cikin 2024 kadai, tawagogin...
    Ba wannan ne karon farko da ake zargin wasu ‘yan ƙasashen waje da kai hare-hare a Nijeriya ba. A baya an yi zargin cewa ƙungiyoyi kamar Lakurawa da ke kai hare-hare a jihohin Sakkwato da Zamfara, sun samo asali ne daga ƙasashen waje. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    113-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissiso da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin dastane rastan, ko kum littafin mathnawi na maulana Jalaluddeen rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau. ///… Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-hassan limami na biyu daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s), kuma da na farko ga Fatimah diyar manzon All..(s), sannan jikansa na farko. A cikin shirimmu da ya...
    Maryam Abubakar, ɗaya ce daga cikin jaruman masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood ’yan ƙalilan da suka yi nasarar bin sahun iyayensu a harkar fim. Matashiyar jarumar, wadda aka fi sanin ta da Maryam Intete a masana’antar, ta yi bayani a kan matsayinta na wadda iyayenta suka suka a cikin cikin harkar fim. Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta ɓulla a Nijeriya DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa A wannan tattaunawar, jarumar ta yi bayani game da gogewarta da yadda ake samun daukaka a Kannywood, da wasu abubuwa game da ita kanta da iyayenta, da kuma sana’ar fim da dai sauransu. Wace ce Maryam Abubakar? An haife ni ne a Kano kuma a nan na girma....
    Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Iran ba za ta taba gudanar da shawarwari kan tsaronta ba A cikin jawabinsa na shirye-shiryen shirin zaman taron Carnegie kan manufofin nukiliya na kasa da kasa da aka soke a yanzu, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa kamfanonin Amurka za su iya cin gajiyar damar dala tiriliyan da tattalin arzikin Iran ke samarwa kuma kasuwar Iran za ta iya farfado da masana’antar nukiliyar Amurka da ta tsaya cak. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana ta shafinsa na Twitter a takaitaccen jawabin da aka shirya yi a taron manufofin nukiliya na kasa da kasa na Carnegie, yana mai jaddada cewa, “Iran sam ba ta da niyyar yin...
    Garuruwan da aka fi tsananta wa harajin sun haɗa da Gijinzama da aka tilasta musu biyan Naira miliyan 8.5, Dakolo da aka karɓi Naira miliyan 5 da buhun wake 20, sai Kibari da Kunchin Kalgo da suka biya Naira miliyan 20, Sungawa da Naira miliyan 15, da kuma Yalwa da aka tilasta su biyan Naira miliyan 2.7. Bayan rasuwar Isuhu Yellow, wani ƙasurgumin jagoran ‘yan bindiga mai suna Dogo Gide ya sa harajin Naira miliyan 100 a kan ƙauyuka 23 da ke ƙaramar hukumar Tsafe. A ƙarshen makon da ya gabata kuma, mazauna ƙauyen Dankurmi a ƙaramar hukumar Maru sun fuskanci sabon harajin Naira miliyan 60. Wani mazaunin ƙauyen Dan Jibga, Muhammad Dogo, ya bayyana cewa bayan kashe mutane biyu...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: China da Rasha abokan hulda ne na tushe ga Iran bisa kyakkyawan tsari Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana kasashen China da Rasha a matsayin abokan huldar na tsari a kan tubalin manyan tsare-tsare ga Iran, kuma ya dace kasashen uku su ci gaba da tuntubar juna a fannoni daban daban. A yayin da ya isa birnin Beijing, yayin da yake amsa tambaya game da makasudin ziyararsa a kasar China a jajibirin shawarwarin da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, Araqchi ya bayyana cewa: Kasashen China da Rasha abokan hulda ne na kut-da-kut da Iran. Sun kasance tare da Iran a lokutan wahala, kuma abu ne mai...
    Al’ummar Gaza sun bukaci kasashen duniya da su tilasta daukan matakin shigar da kayan agaji cikinsu Al’ummar Falasdinawa a Zirin Gaza sun yi kira ga hukumomin kasa da kasa da na Larabawa da su tilasta shigar da kayan agaji cikin yankin, duba da munanan bala’in jin kai da al’ummar yankin ke fuskanta. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Akif al-Masri, kwamishinan hukumar koli ta al’amuran da suka shafi Falasdiwa a Gaza, ya ce: “Matsalar yunwa tana barazana ga rayuwar dubban daruruwan mutanen Gaza,  yana mai cewa: Mafi yawan gidaje kusan babu kayan abinci, kuma iyalai ba za su iya samun abincinsu na yau da kullum ba.” Al-Masry ya tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun ketare dukkan iyakokin kasa...
    Adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da irin sojojin mamayar Isra’ila kan Gaza ya kai shahidai 51,266 Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa: An isar da gawawwakin shahidai 26 da kuma wasu 60 da suka jikkata a asibitocin zirin Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata. Ma’aikatar ta bayyana a cikin wata sanarwa a jiya Talata cewa adadin wadanda suka yi shahada da wadanda suka jikkata tun ranar 18 ga Maris, shekara ta 2025 ya kai shahidai 1,890 da kuma jikkata wasu 4,950 na daban. An tabbatar da cewa adadin wadanda suka yi shahada a sakamakon harin ta’addancin ‘yan sahayoniyya ya karu zuwa shahidai 51,266 da jikkatan wasu 116,991 tun daga ranar 7 ga...
    Wani rahoton kare hakkin bil adama ya tabbatar da aikata manyan laifuka a gabar tekun Siriya tare da yin kira da a kare fararen hula Kwamitin da ke bin diddigin kare hakkin bil adama a kasar Siriya karkashin jagorancin dan gwagwarmaya Haitham Al-Manna, ya fitar da wani cikakken rahoton take hakkin dan Adam mai shafuka 72 da ke kunshe da jerin munanan laifukan da aka yi wa fararen hula a gabar tekun Siriya, yana mai bayyana shi a matsayin “neman shafe wata al’ummar daga kan doron kasa a kan tubalin sabanin Mazhaba”. Rahoton wanda masu fafutuka 12 suka shirya, ya zo ne bayan kisan kiyashin da aka fara a ranar 6 ga Maris. Rahoton ya yi nuni da wani tsari...
    “Yaron ya kuma ce akwai lokacin da ta ba shi wani lemun tsami da yake zaton an saka wani abu a ciki kafin abin ya faru. Ya bayyana cewa ta sha maimaita wannan aika-aikar a kansa,” Wakil ya ƙara da bayani. Wakil ya ce a yayin bincike, wadda ake zargin ta amsa laifin da ake zarginta da shi. Ya ce za a ci gaba da tantance bayananta, sannan a gurfanar da ita a gaban kotu bayan kammala bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp