Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana China Da Rasha A Matsayin Abokai Na Tushe Ga Iran
Published: 23rd, April 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: China da Rasha abokan hulda ne na tushe ga Iran bisa kyakkyawan tsari
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana kasashen China da Rasha a matsayin abokan huldar na tsari a kan tubalin manyan tsare-tsare ga Iran, kuma ya dace kasashen uku su ci gaba da tuntubar juna a fannoni daban daban.
A yayin da ya isa birnin Beijing, yayin da yake amsa tambaya game da makasudin ziyararsa a kasar China a jajibirin shawarwarin da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, Araqchi ya bayyana cewa: Kasashen China da Rasha abokan hulda ne na kut-da-kut da Iran. Sun kasance tare da Iran a lokutan wahala, kuma abu ne mai kyau cewa Iran suna ci gaba da tuntubar juna tare da su a fagage daban-daban, musamman a yanzu da aka tabo batun tattaunawa da Amurka a fakaice.
Araqchi ya ci gaba da cewa: “Suna bukatar su sanar da abokansu da ke kasar China cikakkun bayanai game da abubuwan da ke faruwa tare da tuntubarsu, kuma sun yi hakan a makon da ya gabata a kasar Rasha.” Inda ahalin yanzu suke kasar China, kuma zai isar da sakon shugaba kasar Iran Mas’ud Pezeshkian, kuma idan Allah ya yarda za su yi tattaunawa mai kyau.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: China da Rasha a
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Manufar Kasarsa Da Shirin Kare Muradunta A Duk Wata Yarjejeniya
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: A shirye suke su cimma yarjejeniya yayin da suke kiyaye muradun kasarsu
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran a shirye take ta cimma matsaya bisa kayyade tsare-tsare tare da kiyaye moriyar kasarta, amma idan ba ta son yin shawarwari da ta daga kan matsayinta, tare da ci gaba a kan tafarkinta. Kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce: Babu kyakykyawan fata kuma ba za a fitar da rai ba.
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da yake jawabi a taron da gwamnonin kasar suka yi a ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar a yau, ya yi jawabi kan shirin tattaunawa ba na kai tsaye ba da Amurka, yana mai cewa: Tun da fari gwamnatin Iran ta jaddada cewa tana kokarin karfafa dangantakar siyasa da tattalin arziki da kimiyya da al’adu da sauran kasashe, musamman ma kasashen musulmi da na makwafta. Iran tana kuma neman kyakkyawar mu’amala da sauran kasashe bisa mutunta juna.