2025-04-23@15:38:31 GMT
إجمالي نتائج البحث: 471
«China da Rasha a»:
Bugu da kari, kasar ta samar da cibiyoyin kula da lafiyar mata da kananan yara 3,081, baya ga likitocin yara da na mata a fadin kasar da yawansu ya kai 373,000. Kana fiye da kashi 90 cikin dari na cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a yanzu sun mallaki kayan aiki da sassan kula da lafiyar yara masu inganci. Ba a cikin kasarta kawai take kokarin inganta kiwon lafiyar mata da kananan yara ba, har ma da kasashen duniya, domin kwararrun likitocin Sin da aka tura don ba da agaji a kasashen waje sun gudanar da ayyukan kula da lafiyar mata da yara a kasashe da yankuna 44, ciki har da wasu kasashen Afirka. A cikin 2024 kadai, tawagogin...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: China da Rasha abokan hulda ne na tushe ga Iran bisa kyakkyawan tsari Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana kasashen China da Rasha a matsayin abokan huldar na tsari a kan tubalin manyan tsare-tsare ga Iran, kuma ya dace kasashen uku su ci gaba da tuntubar juna a fannoni daban daban. A yayin da ya isa birnin Beijing, yayin da yake amsa tambaya game da makasudin ziyararsa a kasar China a jajibirin shawarwarin da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, Araqchi ya bayyana cewa: Kasashen China da Rasha abokan hulda ne na kut-da-kut da Iran. Sun kasance tare da Iran a lokutan wahala, kuma abu ne mai...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wutar lantarki ta zama tamkar gwal a wasu sassan Arewacin Najeriya, inda a wasu yankuna aka ba da rahoton samun ta sa’o’i biyu kawai a rana, wasu kuma ba sa samun ko daidai da dakika ɗaya. Masu ƙananan sana’o’i suna kallon rayuwarsu da kasuwancinsu suna durƙushewa yayin da kayan sana’arsu suke lalacewa saboda rashin wuta. NAJERIYA A YAU: Matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa A Tsarin Mulkin Najeriya? DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan wannan matsala da yadda take taɓa rayuwar al’umma da hanyoyin magance ta. Domin sauke shirin, latsa nan
A ranar 17 ga watan Afrilun da muke ciki ne wakilai ko ministocin noma na kasashen kungiyar BRICS suka taro a Brazilian a kasar Brazil inda suka rantaba hannu kan shelanta shirin namusamman na bunkasa ayukan noma da kuma harkokin samar da abinci da kuma wadatar da shi ga kasashen duniya farko ga kasashen kungiyar. Shirin dai ya hada da na shekara ta 2021-2024 da kuma na 2025-2028, wadanda kungiyar zata aiwatar da su tare. Shirin ya hada da bunkasa ayyukan noma da samar da wuraren ajiye kayakin noma da kuma taimakawa kananan ayyukan noma a kasashen kungiyar saboda smaar da manoma wadanda zasu yi noma mai yawa nan gaba. Sannan rage abubuwan da ke hana ayyukan noma ci gaba...
Majiyar fadar Vatican ta bada sanarwan cewa za’a gudanar da jana’izar paparuma Francis a ranar Asabar mai zuwa 26 ga watan Afrilu a dandalin st. Peter dake birnin Vatican amma za’a ajiye gawarsa don yi mata kallo na karshe a daga gobe Laraba a St. Peter’s Basilica har zuwa ranar Jana’izar. Shafin yanar gizo na labarai “Africa News” ya bayyana cewa paparoma Francis ya mutane a ranar 20 ga watan Afrilu yana dan shekara 88 a duniya, kuma fatansa a cikin jama’a da kuma jawabinda na karshe kwana guda ne kafin rasuwarsa. Labarin ya kara da cewa paparoman ya shahara da son talaka, da kuma wadanda aka zalunta, musamman al-ummar Falasdinu, wadanda yahudawan HKI suke yiwa kissan Gila tun sdhekara...
Iyalan Alhaji Surajo Ilyasu Malumfashi (RADIO NIGERIA KADUNA) dana Alhaji Idris Ahmed Accama na farin cikin sanar da bikin aure na ‘ya’yansu, Muhammad Auwal Idris da Zainab Surajo Malumfashi. Za’a gudanar da bikin auren ranar Asabar, 3 ga Mayu, 2025, a Masallacin Juma’a na Dan Fodio, Dake Anguwan Sunusi, Jihar Kaduna. Za a daura auren da misalin karfe 11:00 na safe, sannan ana sa ran ci gaba da liyafa kai tsaye bayan kammala daurin auren. Iyalan suna gayyatar dangi, abokan arziki da duk masu fatan alkhairi su halarta tare da murnar wannan babban biki, wanda ke nuna sabon babi a rayuwar amarya da ango. Surajo Ilyasu Malumfashi
Gwamnan jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, ya sanya dokar hana fita daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a Minna babban birnin jihar, sakamakon yawaitar hare-hare da kashe-kashen da ake yi a birnin. A cewar gwamnan, an takaita zirga-zirgar babura da masu tuka keke napep a tsakanin karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe. Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane 3, Ta Wanke Gonakin Shinkafa Sama Da Hekta 10,000 A Neja Sojoji Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Tare Da Kwato Makamai A Kano Bago ya bayyana hakan ne a yayin wani muhimmin taron tsaro da masu ruwa da tsaki suka yi da sarakunan gargajiya da shugabannin hukumomin tsaro a gidan gwamnati, ranar Talata....
Wasu shugabannin duniya da suka bayyana niyyarsu ta halartar jana’izar sun haɗa da Donald Trump na Amurka, Emmanuel Macron na Faransa, Luiz Inacio Lula da Silva na Brazil, da Volodymyr Zelensky na Ukraine. Ana sa ran jana’izar za ta samu halartar manyan baƙi daga sassan duniya, tare da girmama rayuwar Fafaroma Francis da ayyukansa da ya yi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jamuhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada matsayinta kan batun tace sinadarin yuraniyo. Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatemeh Mohajerani ta bayyana cewa, Iran na kokarin yin shawarwari ne domin samar da amana da samar da gaskiya game da shirinta na nukiliya domin dage takunkumi kanta. A cikin taron manema labarai na mako-mako da ta gudanar a jiya litinin, Mohajerani ta mayar da martani ga wata tambaya game da tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka, inda ta ce, shin bangarorin biyu sun cimma matsaya dangane da kasar da za a aike da hajojin uranium da Iran ta inganta? Shin Iran ta amince ta mika wadannan haja zuwa Rasha? Ta ce: Ina so in bayyana dangane da kashi na...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarammu na yau za yi magana dangane da “Rage kisasfin kudan ma’aikatar harkokin wajen Amurla da kimani kasha 50% da kuma tasirinsa ga matsayin Amurka a duniya da kuma cikin gida. Wanda ni tahir amin zan karanta. A makon da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan, rahe kasafin kudi na ma’aikatar harkokin wajen kasar da kasha 50%, saboda haka kuma ya rufe wasu daga cikin ofisoshin jakadancin kasar da kananan ofisoshin jakadancin kasar fiye da 30 a yankuna daban daban a duniya amma mafi yawansu a nahiyar Afirka. Dangane da wannan matakin da gwamnatin kasar Amurka masana daga ciki ga wajen kasar ta Amurka masu yawa...
A yau Litinin shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya fitar da sanarwa ta nuna aljinin rasuwar Papa Roma Farancis,sannan kuma ya mika sakon ta’aziyya ga Mabiya darikar Roman Katolika na duniya. Shugaban kasar ta Iran ya rubuta cewa; Daga cikin matsaya da ta kasance fitacciya wacce Papa Roman ya dauka a lokacin rayuwarsa ita ce ta kalubalantar yadda ake take hakkin bil’adama a duniya, musamman mai dai yadda ya yi Allawadai da kisan kiyashin da ‘yan sahayoniya suke yi wa Falasdinawa a Gaza. Haka nan kuma yadda ya rika yin kira da HKI ta kawo karshen kisan kiyashin da take yi, da kashe mata da kananan yara. Fizishkiyan ya kuma kara da cewa; Wadannan matakan da Papa Roman ya dauka...
Fadar Vatican ta sanar da mutuwar shugaban majami’ar katolika na duniya, Fafaroma Francis yana da shekaru 88 a duniya. A shekarar 2023 ne cocin ya zaɓi Fafaroman, wanda asalin sunansa shi ne Cardinal Jorge Mario Bergoglio a matsayin wanda zai jagorance ta, bayan saukar Fafaroma Benedict XVI daga kan muƙamin. Da safiyar Litinin ne ɗaya daga cikin jagororin cocin ya sanar cikin jimami game da rasuwar ta Fafaroma Fraincis, inda ya ce: “Ya ku ƴan’uwana, cikin alhini, ina sanar da ku game da rasuwar Babanmu a addini, Francis. Da misalin ƙarfe 7:35 na wannan safiya (Agogon Vatican), Bishop ɗin Roma, Francis ya koma ga mahalicci. Ya sadaukar da rayuwarsa baki ɗaya wajen bauta wa ubangiji da kuma coci.” “Ya koya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ana zargin wani ɗan kasar Indiya mai shekara 20 da tserewa da surukarsa mai shekara 40, kwanaki tara kacal kafin aurensa da ’yarta. Ma’auratan Rahul da Shibani, matasa ne ’yan Aligarh, a Jihar Uttar Pradesh ta Indiya, wadanda suka shirya yin aure a ranar 16 ga Afrilu na watan da muke ciki. Zaɓen 2027: Babu ɗan takarar da zai yi nasara ba tare da goyon bayan Arewa ba — Hakeem NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye cikin littafai ana shirin kaiwa Saudiyya An aika wa dangi katin gayyata domin halartar taron bikin, amma kwanaki tara kafin ranar bikin, sai wani iftila’i ya afku. Angon dan shekara 20 ya lallaba ya bace, amma bai tafi shi kadai ba; ya...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi watsi da barazanar HKI na kaiwa cibiyoyin makamashin nukliyar kasar don hana kasar abinda take kira makaman Nukliya. Ministan ya kara da cewa kasar Iran zata iya kare kanta ko da Amurka ce ta takaleta, kuma Amurka ta san hakan. Sannan ya ce HKI bata taba kaiwa Iran hari a bay aba kuma ba zata taba kai mata hari ba. Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya buga wannan labarin a jiya Asabar ya kuma nakalto ministan yana cewa kasashen Rasha da Iran basu taba karfafa dangantakar tsakaninsu fiye da yanzu ba. Aragchi ya kara da cewa kasashen Iran Rasha da kuma China suna aiki tare don tabbatar da zaman...
Kungiyar Masu Babura Uku ta Najeriya, Jihar Kaduna ta Rantsar da Shugabannin Sassa Goma Sha Biyar da Manyan Jami’ansu don Gudanar da Harkokin Kungiyar a Tsawon Shekaru Hudu Masu Zuwa. Mataimakin Kwamandan Hanya kuma Mataimakin Jami’in Wayar da Kai na Hukumar Kiyaye Haddura ta Tarayya (FRSC), Kaduna, Usman Garba, wanda ya yi magana da manema labarai bayan bikin rantsarwa, ya yaba wa kungiyar, yana mai cewa wannan ci gaba ne mai kyau ga kungiyar. Ya ce Hukumar Kiyaye Haddura na farin ciki da wannan ci gaba saboda sabon tsarin shugabanci zai taimaka wajen magance matsalolin da suka shafi direbobin babura uku (Keke Napep) da hukumar ke fuskanta a jihar. A cewarsa, yanzu hukumar za ta yi...
Gwamnatin Rasha ta sanar da amincewarta da tsagaita bude wuta da Ukraine a wannan karo Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanar da tsagaita bude wuta na kwanaki uku na Ista, inda ya yi kira ga sojojin kasarsa da su kasance cikin shirin ko ta kwana idan Ukraine ta karya yarjejeniyar. Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ba da sanarwar tsagaita wuta na kwanaki uku na Ista, yana mai kira ga sojojin kasarsa da su “ci gaba da kasancewa cikin shiri don yiwuwar keta yarjejeniyar tsagaita wutan daga bangaren Ukraine, a sanarwar da fadar Kremlin na fitar. Putin ya fada a ranar Asabar cewa: “Tsarin tsagaita bude wuta zai nuna a fili gwamnatin Ukraine tana da ikon warware matsalar cikin lumana.”...
Shugaba Vladimir Putin a yau Asabar ya umarci sojojin Rasha da su tsagaita buɗe wuta a Ukraine a wanan ranar ta Ista da kuma gobe Lahadi. Putin ya kuma yi kira ga Kyiv da ta yi hakan, yayin da ake ganin tattaunawar tsagaita buɗe wuta ta ci tura. Kada Kanawa su bari rigingimun siyasa su hana su zaman lafiya — Shettima Shin Mataimakin Gwamnan Bauchi ya ‘mari’ Ministan Tinubu? Haka kuma, Rasha da Ukraine sun yi musayar fursunonin yaƙi na sama da mutum 500 — kuma mafi girma tun bayan fara yaƙi a tsakanin kasashen biyu. Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskiy, ya ce ƙasarsa ta karɓi sojoji fursunonin yaƙi akalla 277 waɗanda ke tsare a gidajen yarin Rasha, kamar yadda ya...
An kuma buƙaci a ci gaba da siyasa cikin fahimta da girmama juna domin amfanin Jihar Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An kuma buƙaci a ci gaba da siyasa cikin fahimta da girmama juna domin amfanin Jihar Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A nawa raayin hakan ba zai zama lefi ba indai har tsakani da Allah suke son junansu. Lokacin fira daban lokacin ziyara kuwa shi zuwa yake yi babu wani lokaci a yadda na fahimci topic din. Ni dai zan tsara shi ne ranar Alhamis bayan sallar la’asar zuwa sallar magrib idan ma firar ta dauki lokaci sosai kenan ya isa tunda ana waya ko chart. A shawarce hakan sai na ga ba lefi bane duba da an zama daya kuma wannan shi ne zai kara sa nutsuwa a zukatanku na tabbacin kowannenku ya san babu wasu da suke kulawa, sannan zai rage karairayin da ake samu wajen sutura ko gidajenmu ko ababen hawanmu dama abokai ko kawayen da muke kulawa....
Fadar Shugaban Ƙasa ta buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da irin waɗannan labaran ƙarya, tare da kira ga kafafen yaɗa labarai su riƙa tabbatar da gaskiya labari kafin wallafawa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

An Fara Bikin Ranar Sojin A Iran 18 Ga Watan Afrilu Tare Da Gudanar da Fareti A Gaban Shugaban Kasar
An fara gudanar da bukukuwan ranar soji a Iran a ranar 18 ga watan Afrilu ta hanyar gudanar da faretin soja a gaban shugaban kasar Mas’ud Pezeshkian An fara faretin soji na sojojin kasar Iran a kusa da hubbaren Imam Khumaini (r.a) da ke kudancin birnin Tehran fadar mulkin kasar a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan ranar sojoji ta 18 ga watan Afrilu. A jiya Juma’a 18 ga watan Afrilu ne sojojin kasar Iran suka fara faretin soji na murnar zagayowar ranarsu da kuma irin bajintar jarumtakar sojojin kasar, a kusa da hubbaren Imam Khumaini (r.a) da ke kudancin babban birnin kasar Tehran. A cewar kamfanin dillancin labaran IRNA na Iran, faretin ya samu halartar shugaban kasar Mas’ud...
Sojojin Sudan sun sanar da kashe mayakan dakarun kai daukin gaggawa 70, ciki har da kwamandojin mayakan a birnin a El Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa A ranar Alhamis ne rundunar sojin Sudan ta sanar da kashe mayakan da jami’an dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces fiye da 70 da suka hada da kwamandojin ‘yan tawaye a shiyar kudu maso gabas da arewa maso gabashin El Fasher. Kamfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) ya watsa rahoton cewa: A ranar Alhamis ne sojojin kasar Sudan tare da hadin da tallafin dakarun hadin gwiwa na kungiyoyin fafutuka, da hukumar leken asiri ta kasar da ‘yan sanda, suka dakile wani mummunan hari da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support...
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bukaci Kiristoci da su yi tunani a kan darussa, muhimmaci, da kuma kyawawan dabi’u na makon Easter. Gwamna AbdulRazaq a wani sako da ya aike a Ilorin, ya taya mabiya addinin kirista a jihar da ma fadin Najeriya murnar bikin Easter. Gwamnan ya ce nasarar da Yesu Kiristi ya samu a fuskantar wahala, wanda bikin Ista ke alamta, ya kamata ya fitar da imani ga Allah da kuma yuwuwar da ba su da iyaka da ke zuwa tare da samun bangaskiya mara girgiza cikin ikonsa. Ya yi addu’ar Allah ya sa lokacin Easter ya kawo farin ciki da jin daɗi mara iyaka ga kowane gida a jihar da kuma bayansa ...
Gao ya kara da cewa, Sin da kasashen Afirka sun zamo misali na bunkasa hadin gwiwar kasashe masu tasowa, suna kuma gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil’adama, kana sun nunawa duniya cewa kasashe masu tasowa na da ikon samar da sabon salon wayewar kan bil’adama na kashin kan su, kuma za su iya bin tafarkin zamanantarwa da ya sabawa na yammacin duniya. A nasa bangare kuwa, daraktan hukumar lura da harkokin waje na kasar Masar Ezzat Saad, cewa ya yi shawarar da Sin ta gabatar ta aiwatar da manufofin zamanantar da duniya, ta samar da karin sassan hadin gwiwarta da kasashen Afirka, tare da yayata kusancin sassan biyu ta fuskar amincewa da juna da hadin gwiwarsu....
Kasar Chaina ta musanta zargin shugaban kasar Ukraine ga kasar, dangane da tallafawa kasar Rasha da makamai. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar wajen kasar China Lin Jian yana fadar haka a safiyar yau Jumma’a ya kuma kara da cewa, kasar China bata taba daukar bangaren a yakin na Ukraine ba, kuma ra’ayinta shi ne shiga tsakanin don kawo karshen yakin. Kafin haka dai shugaban kasar Ukraine Volodimir Zelesky ya zargi gwamnatin kasar China da tallafawa kasar Rasha da makamai a yakin da kasarsa take fafatawa da ita. Zelesky ya ce a wannan karon kasar China ta aikawa Rasha makaman Atilari da kuma PorwerGun. A can baya ma gwamnatin kasar ta Ukraine ta zargi kasar...
“Maimakon ya bai wa babban jami’in nasu kudin ya raba wa mutanensa, sai ya zabi rarraba musu shi da kansa”, kamar yadda wata majiya ta shaida wa wannan jarida. Sai dai, wata majiyar ta shaida wa wakilinmu a ranar Larabar da ta gabata cewa, an gayyaci ‘yansandan ne zuwa babban birnin tarayya Abuja, domin ladabtar da su. An gayyaci jami’in da sauran yaransa zuwa hedikwatar ‘yansanda da ke Abuja, domin daukar matakan ladabtarwa, in ji majiyar. Kamar yadda siginal mai dauke da kwanan wata na ranar Talata 15 ga Afrilun 2025, wadda LEADERSHIP ta samu, ya nuna cewa; ‘yansandan da shugaban tawagarsu, DSP Aliyu Adejembi, za su bayyana a hedikwatar ‘yansan da ke Abuja, domin amsa tambayoyi kan rashin da’a...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya mika rubutacciyar wasikar jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ga shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. Araghchi, wanda ya je birnin Moscow a matsayin shugaban tawagar diflomasiyya don ganawa da wasu manyan jami’an Rasha, ya gana da Putin a yammacin ranar Alhamis. Ministan ya gabatar da sakon Jagoran ga shugaban kasar Rasha tare da bayyana ra’ayoyi da matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da batutuwan da suka shafi ajandar huldar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma ci gaban yanki da sauran batutuwa na kasa da kasa. Araghchi ya tabo yarjejjeniyar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare da shugaba Putin da takwaransa na Iran, Masoud Pezeshkian suka rattabawa hannu a birnin Moscow a...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Sakon jagora ga shugaban kasar Rasha yana da alaka da ci gaban kasa da kasa da na yanki Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana hakan ne a yau Alhamis a birnin Moscow na kasar Rasha cewa: Abu ne da ya dace a rubuta sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aikewa shugaban kasar Rasha dangane da ci gaban kasa da kasa da na yanki da kuma batutuwan da suka shafi kasashen biyu. Araqchi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya isa filin tashi da saukar jiragen sama na Vnukovo da ke birnin Moscow a yau, yayin da yake amsa tambayar da wakilin IRNA ya yi masa kan...

Wata Cibiyar Kare Hakkin Bil’Adama Ta Bukaci Kama Jami’in Haramtacciyar Kasar Isra’ila A Kasar Birtaniya
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Hind Rajab ta yi kira ga Birtaniya da ta kama ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Hind Rajab ta gabatar da bukatar fitar da sammacin kame ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila Gideon Sa’ar da yake ziyara a Birtaniya. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa: Cibiyar Hind Rajab Foundation da ta mayar da hankali kan neman gurfanar da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da ake zargi da aikata laifukan yaki, ta mika bukatar kama Gideon Sa’ar a birnin Landan na Birtaniya. Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun jiyo ofishin ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila na cewa babu wata niyyar takaita ziyarar Sa’ar...
Dakarun da ke karkashin sashe na 3 na OPSH, da aka tura wurin da lamarin ya faru, biyo bayan kiran gaggawa da aka yi musu, sun tabbatar da cewa, makiyayan sun riga sun yanka shanun da kansu, domin gudun kar a yi asara da yawa. Binciken da aka yi a yankin ya kai ga gano tumatur da ake zargin guba ne da yalon lambu an warwatsa a filin. Kuma babu gidaje a kusa da wurin, wanda hakan ke haifar da zargin cewa, mai yiwuwa wasu da ba a san ko su waye ba ne suka ajiye abun wanda ake kyautata zaton yana dauke da guba. A martanin da babban jami’in runduna ta 3 kuma kwamandan OPSH, ya jagoranci wata...
Ministan Harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya je kasar Rasha a safiyar yau Alhamis don isar da sakon jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminaei zuwa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan sakon na zuwa ne rana guda da amincewar majalisar dojojin kasar Rasha ta dangantaka ta musamman tsakanin kasashen biyu, mai tsawon shekaru 20. Har’ila yau da kuma kwanaki biyu kafin a gudanar da tattaunawa na biyu tsakanin Iran da Amurka dangane da shirin ta na makamashin Nukliya a birnin Roma na kasar Italiya. Masana dai sun bayyana cewa kasashen Rasha da Iran suna kara dankon zumunci a tsakaninsu ne a dai-dai lokacinda al-amura da dama...
Majalisar kasa ta kasar Rasha ta amince da yarjeniyar dangantaka ta musamman tsakanin kasar da JMI a ranar 8 ga watan Afrilun da muke ciki sannan ana saran shugaban kasa Vladimir Putin zai sanyawa yarjeniyar hannu a nan gaba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa yarjeniyar ta musamman mai kuma dogon zango na shekaru 20 zai bawa kasashen biyu damar tallafawa juna da kuma aiki tare da bangarori daban-daban wadanda suka hada da tsaro makamashi kimiyya da fasaha da sauransu. Labarin ya kara da cewa idan yarjeniyar ya fara aiki kasashen biyu suna da damar kyautata dangantaka a tsakaninsu, wanda zai rage dogaro da suke yi da kasashen yamma a bangarori da dama. Dangantakar Tehran da...
Hukumar UNICEF ta MDD mai kula da yara ta bada sanarwan cewa kimani yara 3,500 suka rasa rayukansu a kokarin ketara tekun Medeteranina a cikin shekaru 10 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran Spunic na kasar Rasha ya nakalto hukumar tana fadar haka a wani rahoton da ta fitar dangane da hakan. Labarin ya kara da cewa, wannan ya nuna cewa akalla yaro guda ne ya ransa ransa a ko wace rana. Kuma kashi 7/10 daga cikinsu sun halaka ko sun bace ne su kai ba ba tare da rakiyar iyayensu ba. Har’ila yau rahoton ya kara da cewa akalla mutane 20,803 suka halaka a tsakiyar tekun na Mediterranean a kokarinsu na tsallakawa zuwa kasashen na turai. Daga karshe hukumar...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakisatan ta kara jaddada matsayinta na rashin amince da HKI a matsayin kasa tana kuma goyon bayan Falasdinawa a gwagwarmayan da suke yi na kwatar yencinsu da kuma kasarsu daga hannun HKI da kuma kasashen yamma musamman Amurka masu goya mata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran wannan sanarwan tazo ne bayan da hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta samar da wani kuduri dangane da rikicin da ke faruwa a gabas ta tsakiya. A dai-dai lokacinda aka kara yawan tashe-tashen hankula a kasar Falasdinu da aka mamaye tsakanin HKI da kuma Falasdinawa masu gwagwarmaya. Kungiyar kasashe masu musulmi mafi rinjaye wato OIC ta yanke shawara kan cewa bai kamata kasashen su samar da huldar...
Mai Magana da yawun kakakin babban magatakardar MDD Steven Dujarric ya nuna damuwa akan sanar da kafa wata gwamnati ta daban da shugaban rundunar daukin gaggawa Hamidati Duklu ya yi a shekaran jiya Laraba. Shugaban rundunar kai daukin gaggawar ta Sudan wanda yake fada da sojojin kasar ya shelanta kafa sabuwar gwamnati wacce ya ce za ta kasance ta zaman lafiya da hadin kai ce. Hamidati wanda ya gabatar da jawabi a lokacin da ake tunawa da zagayowar cikar shekaru 3 da fara yaki a kasar ta Sudan, ya kuma ce; A halin yanzu suna Shirin buga kudaden Sudan na daban, da kuma samar da wasu muhimman takardu na aikin gwamnati. Wannan sanarwar daga shugaban rundunar kai daukin gaggawar ta...
Rasha ta ce tana ta na sa ido sosai game da tattaunawa karo na biyu tsakanin Amurka da Iran kuma a shirye take ta taimaka wajen warware shirin nukiliyar Iran ta hanyar siyasa da diflomasiyya. Makomar shirin nukiliyar Iran da kuma zaman lafiyar yankin na iya danganta ne kan ko Washington da Tehran za su koma kan teburin shawarwari. Yayin da tattaunawar tsakanin Amurka da Iran ta tsaya cik a baya, manyan kasashen duniya musamman Rasha da China sun yi yunkurin ganin neman farfado da tattaunawar ta diflomasiyya. Tunda farko a makon da ya gabata Majalisar Tarayyar Rasha ta amince da yarjejeniyar hadin gwiwa ta tsawon shekaru 20 a hukumance da Iran, wanda ke karfafa kawancen dogon lokaci tsakanin kasashen...
Ƙarin bayani na tafe… Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Neja ta kaddamar da rabon sutura da jakunkunan hannu masu nauyin kilo 8 ga maniyyatan bana, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen aikin Hajji na shekarar 2025. A lokacin da yake jawabi yayin kaddamar da rabon, Shugaban Hukumar, Sheikh Muhammad Awwal Aliyu, ya bayyana cewa rabon kayayyakin na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da sauƙin tafiya da kuma aikin Hajji ba tare da wata tangarda ba ga maniyyatan jihar. Shugaban wanda Daraktan Gudanarwa, Babani Aliyu Yahaya, ya wakilta a yayin bayar da kayan ga Jami’in Alhazai na Ƙaramar Hukumar Chanchaga, ya ce kayayyakin na maniyyatan da suka kammala biyan kuɗin kujerunsu ne. Daraktan Gudanarwar ya kuma yi kira ga waɗanda har yanzu ba su...
A cewar Ministan, samun wannan ƙwarewar ya zama wajibi a wannan zamani da kowa da kowa – wato daga masana hulɗa da jama’a zuwa shugabannin kamfanoni – yake taka rawa a matsayin mai magana da yawun wani. Idris ya ce: “Yau a wannan zamani da kowa ke zama mai magana da yawu – ko ɗan hulɗa da jama’a ne ko shugaban kamfani a ɓangaren gwamnati da masu zaman kan su – wajabcin samun ilimi kan kafofin watsa labarai ya zama abu mai matuƙar muhimmanci, domin yana ba da damar fahimta, nazari da tantance sahihancin saƙonnin da ke yawo a kafafen watsa labarai, wanda hakan zai ba da damar yanke sahihin hukunci da mu’amala da labarai yadda ya kamata. ...

Rasha Ta Sanar Da Kashe Manyan Kwamandojin Sojin Ukraine Fiye Da 60 A Birnin Sumy Na Kasar Ta Ukraine
Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da yin luguden wuta kan zaman taron shugabannin sojojin Ukraine a birnin Sumy da ke arewa maso gabashin Ukraine Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa, ta kai hari kan wani ofishin rundunar sojojin Ukraine da ke dauke da makamai masu linzami na Iskander a yayin wani zaman taron manyan sojojin kasar a birnin Sumy, inda aka kashe jami’ai sama da 60. Ma’aikatar tsaron Rasha ta kara da cewa sojojin na Ukraine na ci gaba da amfani da fararen hula a matsayin garkuwa gare su, tare da kafa cibiyoyin soji da kuma shirya tarurruka tare da halartar sojoji a tsakiyar birni mai yawan jama’a, tare da yin nuni da cewa; Rasha ta kai harin...
Al’ummar Babura sun shirya gagarumin taron girmamawa domin karrama Dr. Salisu Mu’azu, bayan nada shi a matsayin Daraktan kuma babban likitan asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ke jihar Jigawa, da kuma samun matsayin mamba na Cibiyar Kasa (mni). Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kwamitin Shirye-shirye, Rabiu Umar, ya bayyana cewa an gudanar da taron ne domin nuna godiya ga Allah da kuma murnar manyan nasarorin da Dr. Mu’azu ya samu. Ya yaba da kokarin Daraktan wajen gudanar da aikinsa da kwarewa, da kuma ci gaba da tallafa wa al’umma. A sakon da aka gabatar a madadin Mai Martaba Sarkin Ringim, Alhaji Dr. Sayyadi Abubakar Mahmoud, wanda Mai Girma Alhaji Usman Sayyadi, Babban Hakimin Masarautar, ya wakilta,...
Majiyar Falasdinawa a Gaza sun bada labarin kissan wasu sojojin HKI a unguwar Shuja’iyya kusa da Gaza a jiya Litini, inda wasu kuma suka ji rauni. Kafafen yada labarai da yahudawan da kuma larabawa sun bayyana cewa kungiyar Jihadul Islami a Gaza ta ce nayakanta masu farautar yahudawa daga nesa sun bayyana cewa suk halaka wasu yahudawa wadanda suka boye a wani gida a garin Rafah kudancin Gaza, inda suke halakasu. Sannan a sauran wuraren kuma sojojin yahudawan da dama ne suka ji rauni. Kuma sun ga jiragen yakin masu sauran ungulu na yahudawan sun zo sun tafi da wadanda abin ya shafa. Wannan dai kadan Kenan daga hare-haren maida martanin da dakarun falasdinawan suke mayarwa ga sojojin yahudawan, tun...
Rundunar ‘yansandan ta ce ta fara bincike kan lamarin, kuma ta ja kunnen jama’a da su guji irin wannan aiki da ya ke barazana ga rayuka, tsaro da tattalin arziƙin jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sai dai har yanzu rundunar ‘yansandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa ba kan lamarin, kuma ƙoƙarin da samun martaninsu ya ci tura. A gefe guda kuma, gwamnatin jihar Filato ta nuna damuwa kan hare-haren da ake samu a wasu sassan faɗin jihar, lamarin da ke ƙara haifar da damuwa a zuƙatan jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Shugaban Kasar Iran Ya Mika Ta’aziyyar Ta Rasuwar Wanda Ya Assasa Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Iran
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana alhininsa akan rasuwar Dr. Akbar I’itimadi wanda shi ne na farko da ya kafa hukumar makamashin Nukiliya ta Iran. Wasikar ta’aziyyar da shugaban kasa ta kunsa ta ambaci cewa: Shakka babu hidima mai kima da wannan masanin ya yi, ya share fagen gina da ci gaban fasahar makamashin Nukiliya a Iran da kuma mayar da kasar mai cin gashin kanta a wannan fage. Har ila yau, shugaban kasar ta Iran ya mika sakon ta’aziyyarsa ga masana na Iran, da kuma iyalansa. Ya kuma yi addu’a da rokon Allah madaukin sarki da ya lullube shi da rahamarsa da kuma gafararsa, sannan ya bai wa iyalansa na hakuri.
Kungiyar Kwararrun Masu Fasahar Injiniya ta Ƙasa (NATE) ta rantsar da sabbin shugabannin reshen Jihar Kaduna da za su jagoranci harkokin kungiyar a jihar. Mataimakin Shugaban Yankin Arewa maso Yamma na NATE, Injiniya Bala Muhammad, yayin bikin rantsarwa da aka gudanar a Kaduna, ya bukaci sabbin shugabannin da su fifita haɗin kai da ci gaban ƙungiyar. Sabbin shugabannin da aka rantsar sun hada da: Injiniya Audu John a matsayin Shugaba, AbdulKadir Julde a matsayin Mataimakin Shugaba, sannan Williams Okonkwu a matsayin Sakataren reshen. Sauran su ne Sim Marca Maikege a matsayin Ma’ajin Kuɗi, AbdulGaniu Isah a matsayin Sakataren Kuɗi, da Racheal Ovbiagele a matsayin Sakataren Fasaha. Haka kuma, Engr. Ishaya Buba daga Radio Nigeria Kaduna...

Ukraine na Fuskantar Wata Barazana, Dangane Da Bukatar Amurka Na Kwace Iko Da Cibiyar Gas Na Rasha A cikin Kasar
Labaran da suke fitowa daga kasar Ukraine sun bayyana cewa, gwamnatin kasar tana son karban iko da bututun iskar gas na kasar Rasha wanda yake yammacin kasar da Turai, wanda kuma yake kai iskar gasa zuwa kasashen Turai. An gina bututun tun zamanin tarayyar Soviet kuma kasashen biyu suna samun kudade masu yawa daga wannan bututun. Gwamnatin kasar Amurka dai tana son ta dawo da kudaden da ta kashewa kasar Ukraine na makamai wacce ta karba a likacin shugaban Biden. Daga cikin dai Amurka ta bukaci Ukraine ta bada ma’adinanta na kimani dalar Amurka biliyon $500. Wasu rahotanni sun bayyana cewa jami’an gwanatocin kasashen Amurka da Ukraine sun tattauna wannan batun a ranar jumma’an da ta gabata, don tattauna batun...
Jiragen yakin HKI HKI sun yi ruwan boma-bomai kan astin Al-Ahli, asbiti tilo da ya rage yake aiki a arewacin zirin Gaza, a safiyar yau Lahadi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jiragen yakin HKI sun wargaza bangaren ’emagencu’ bukatar kula na gaggawa a asbitin da kuma kofar shiga asbitin. Har’ila yau hare-haren sun lalata bangaren Iskar Oxigen na kula da wadanda suke bukatar kula mai tsanani a asbiti. Kuma sanadiyyar haka mutane da dama sun rasa rayukansu awannan bangaren daga ciki har da wani yaro dan shekara 12 wanda ya ji rauni a kai. Razan Al-Nahhas wani likita mai aiki a bangaren kula na gaggawa a asbitin ya fadawa kafafen yada labarai kan cewa wannan...
Isra’ila ta ce ta karbe iko da wata muhimmiyar hanya a zirin Gaza a wani mataki da ya yanke gaba daya yankin kudancin Rafah mai yawan jama’a daga sauran yankunan Falasdinawa da aka yiwa kawanya. A cikin wata sanarwa da Isra’ila ta fitar yau Asabar ta ce dakarunta sun yi wa Rafah kawanya gaba daya tare da samar da “yankin tsaro” a can. Sanarwar da ministan harkokin soji na gwamnatin Isra’ila Katz ya fitar ta ce sojojin sun karbe ikon “Morag axis, wanda ke ratsa Gaza tsakanin Rafah da Khan Yunis.” Katz ya kuma yi kira ga Falasdinawa da su fara kaura zuwa yamma, yana mai gargadin cewa nan ba da jimawa ba za a kara kaimi da fadada ayyukan...
Manufar “ramuwar gayya” ba za ta daidaita gibin cinikin da kasar Amurka take fuskanta ba, illa ta daga farashin kayan da ake shigarwa kasar daga kasashen waje, da haddasa hadarin hauhawar farashin kaya a kasar, da kawo illa ga zaman rayuwar jama’ar kasar. A karshe Amurka ba za ta cimma burinta na zama a matsayin koli a duniya ba. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Za a ci gaba da tunawa da shi a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ‘yan wasan Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ilimi Gishirin Rayuwa Babu shakka ba tun yanzu ba, dan’adam ya dade da fahimtar muhimmancin ilimi ga cigaban rayuwarsa. Walau ilimin addini ko na cigaban rayuwa. Addinin Musulunci ya koyar da mu muhimmancin bai wa ilimi fifiko, kamar yadda aka rawaito a cikin Hadisi. Ma’aikin Allah (SAWA) yana cewa ‘mu nemi ilimi ko da a Birnin Sin ne’. Kuma ya gaya mana cewa, “haddar yaro karami kamar rubutu ne akan dutse…” Kenan, wannan yana karfafa mana gwiwa mu koyawa yaranmu Ilimi tun suna kanana, don za su fi rikewa ya zauna a kwakwalensu. Ilimi tamkar fitila take, yana haskakawa mutum abubuwa na rayuwa, yadda zai koyi zaman duniya da gina wa kansa rayuwa mai inganci. Wannan ilimin kuwa ko...
Ya zamto kowacce rana kina hada salad me yawa ki cinye shi, kar ki cika cin abin da zai birki ta miki ciki don kuwa shifa zai dinga rage miki ruwan jikinki ne, ki dage da cin kayan dadi sosai a wannan watannin. (2b) Abubuwa masu mahimmacin da ya kamata su zama abincinki: Tuffa, Baure, Inibi, musanman sati 4 na karshe. (3). Sinadaran gyaran jiki: To a nan fa matsalar take don gaskiya a wannan yanayin idan har kina so ki ga kyakkyawan sakamako dole sai kin sha supplement na gyaran jiki masu ciko da mace saboda an fi son a ga amarya a cike ba za ki gane da gaske nake ba sai kin zauna nan a waje namiji...
Ministan ya ce maganar da ya faɗa da farko wadda ba a ruwaito ta a daidai ba ita ce: “E, lallai an samu cigaba a harkar tsaro a sassa daban-daban na ƙasar nan, ko da yake ba a kawar da duk wani aikin tashin hankali gaba ɗaya ba. “Hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana don tabbatar da cewa an shawo kan matsalolin da ake da su a wasu sassan Jihar Borno da wasu wurare. “Haɗin gwiwar da muke gani tsakanin hukumomin tsaro, musamman a shekaru biyu da suka wuce, da kuma gagarumin zuba jari a kayan aiki da na’urorin zamani da ake yi, yana nuna yadda Gwamnatin Tarayya take ɗaukar batun tsaro da matuƙar muhimmanci. “Gwamnatin Tinubu tana...
Wannan ya hada da darajar kayayyakin da ake shigowa da su daga waje da kuma fitar da su, wanda ke nuni da irin dimbin alakar kasuwanci da ke tsakanin kasashen biyu. Kayayyakin da Nijeriya ke fitarwa a cikin gida da na waje da jirgin ruwa ya kai dala miliyan 473.6 a watan Fabrairun 2025, kadan ya ragu daga dala miliyan 501 a watan Fabrairun 2024, wanda ke nuna raguwar kashi 5.5 cikin dari. A shekarar zuwa yau, fitar da kayayyaki na FAS ya ragu daga dala miliyan 792.8 a shekarar 2024 zuwa dala miliyan 687.4 a shekarar 2025, wanda ya nuna raguwar kashi 13.3 cikin dari. Amurka ta samu gibin ciniki a kan Nijeriya ne kawai a watan Janairun 2025,...
Wata kungiya mai zaman kanta da ke dauke da sunan Kauru Emirate Consultative Initiative (KECI) ta nisanta da yunkurin da wasu ke yi na saka Masarautar Kauru cikin sabon tsarin Jihar Gurara da ake kokarin kirkira daga Jihar Kaduna. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar, Malam Isah Mukhtar, ya sanya wa hannu, kuma aka raba wa ‘yan jarida a Zariya. A cewar Malam Mukhtar, ikirarin da wasu ke yi musamman daga yankin Kudancin Kaduna na cewa Masarautar Kauru na son shiga cikin Jihar Gurara ba gaskiya ba ne kuma yana bata suna. “Mutanen Masarautar Kauru ba su da hannu a wannan yunkuri. Muna alfahari da kasancewarmu a cikin Jihar Kaduna, musamman saboda alakar tarihi, al’adu...

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (2): Kyawawan Dabi’u Ke Fayyace Tsoron Allah A Musulunci
-Mun lura da ilimomin harkokin zamaninmu a cikin Alkur’ani Cikin godiyar Allah, muna mika ziyara ga Shehu Isma’ila Umar Almadda (Mai Diwani) da kuma ban gajiya da gabatar da Tafsirin Alkur’ani mai girma na Azumin Ramadan na bana. Allah ya kai mu na badi albarkar Annabi (SAW) da Shehu (RTA). Ya Shehi, a Tafsirinka na rana ta bakwai mun ji yadda ka yi bayani na ilimomin kiyaye hadurran hanya da ke kunshe a cikin aya ta 63 ta Suratul Furkan (Sura ta 25), “Wa Ibadur Rahman…”. Mun kara fahimtar cewa, ayar tana nusarwa a kan tafiya cikin tsari walau sufuri ne na titin mota, ko na jirgin sama ko na ruwa ko jirgin kasa, da dukkan alamomin da ake...
Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da dokar albashi na naira 70,000 a ranar 29 ga watan Yuli na 2024, bayan shafe watanni ana muhawara da kungiyoyin kwadago. Sabon mafi karancin albashin na wata-wata ya karu da kaso 133 daga naira 30,000 zuwa naira 70,000, sakamakon matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasar nan. Da yake ba da bayani kan halin da ake ciki, shugaban kungiyar NULGE ya ce, “A zahirin gaskiya muna fuskantar matsaloli da jihohi da dama, kusan jihohi 20 ba su fara aiwatar da mafi karancin albashi ba. “Muna da Jihohi irinsu Sakkwato, Yobe, Gombe, Zamfara, Kaduna, Imo, Ebonyi, Borno, Kurus Ribas, Abuja, da dai sauransu, wasu sun fara biyan ma’aikatan jiharsu albashi sun...
Asusun ba da lamuni na ilimi na Najeriya ya yi barazanar daukar matakin shari’a a kan cibiyoyin da ke boye bayanai kan yadda ake biyan dalibai rancen kudi yayin da suke neman biyan kudaden makarantun daga hannun daliban. Sanarwar da Manajin Darakta na NELFUND, Mista Akintunde Sawyerr ya fitar ta bayyana cewa, sakamakon binciken da aka gudanar a baya-bayan nan ya nuna cewa wasu cibiyoyi bayan karbar lamunin dalibai kai tsaye a cikin asusunsu, sun kasa sanar da daliban da abin ya shafa ko kuma nuna kudaden da aka biya a cikin takardun kudin makarantarsu, wanda hakan ya haifar da rudani da bai kamata ba. Mista Sawyerr wanda ya bayyana lamarin a matsayin rashin da’a, ya kuma gargade...

Babban Taron LEADERSHIP Karo Na 17: Tinubu Ya Kare Yadda Gwamnatinsa Ke Tafiyar Da Tsarin Rabon Arzikin Kasa
Mataimakin shugaban kasar wanda ya samu wakilcin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Na Musamman Kan Ayyuka Na Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Aliyu Modibbo Umar ya ce, “Kalubalan Nijeriya ya ta’allaka a tsarin tarayyarmu,” in ji Shettima. “Ba batu ne na wai nawa ne kowace rukunin tarayya ke samu ba, magana ce ta yadda ake amfani da irin wadannan albarkatun.” “Ba kuma batu ne na cewa nawa ne kowace bangare ke samu ba, sai dai a yi batun yadda ake amfani da irin wadannan kayan.” Ya yaba wa LEADERSHIP bisa samar da wani dandali wanda “ba a samar da shi kadai don musayar ra’ayi ba sai don tsara manufofi masu ma’ana.” Ya kuma bayyana sauye-sauyen da ake yi a karkashin gwamnatin...
Daga nan sai ya ce, kasar Sin na aiwatar da matakan ramuwar gayya na wajibi game da cin zalin Amurka, ba kawai don kare ikon mulkin kanta, da kare tsaro da muradun ci gabanta ba ne, har ma da tabbatar da gaskiya da adalci tsakanin sassan kasa da kasa, da wanzar da tsarin cinikayyar sassa daban daban na duniya, da kuma moriyar bai daya ta dukkanin al’ummun duniya. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kamfanin Media Trust Limited na farin cikin sanar da al’umma cewa daga ranar Juma’a 11 ga watan Afrilun 2025, Rediyonta na Tusts Radio zai fara shirye-shiryen gwaji. Tashar za ta fara yaɗa shirye-shiryenta a kan mita 92.7 a zangon FM a birnin tarayya Abuja da kewaye, kuma wannan na daga cikin tsare-tsaren da kamfanin ke bi na faɗaɗa aikin watsa labarai sama da shekaru 27 a Nijeriya. An kama masu garkuwa da mutane biyu a Yobe Gwamnatin Kano ta tura tawaga zuwa Edo kan kisan mafarauta Kamfanin Media Trust shi ne mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya a Nijeriya kuma mamallakin Trust TV da kuma Trust Radio a yanzu. Ga waxanda ba su a birnin tarayya Abuja ko kuma...
Wata sanarwa da Ma’aikatar Kuɗi ta fitar ta ce: “Wannan tsari ba na wucin gadi ba ne. Tsarin sayar da ɗanyen mai a farashin Naira wata dabara ce ta bunƙasa tace mai a cikin gida da kuma bunƙasa tsaron makamashi a Nijeriya.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya nuna kaɗuwar sa bisa rashin da aka yi na ɗan Majalisar Dokokin jihar, Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji, ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Ƙauran Namoda ta Kudu. Iyalai sun bayyana cewa Hon. Aminu Kasuwar Daji ya rasu ne a cikin barcin sa da asubahin ranar Larabar nan a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa gwamnan ya miƙa ta’aziyyar sa ga Majalisar Dokokin jihar da Iyalan mamacin. Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta aika da tawaga ta musamman, ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Mallam Mani Mummuni a yayin jana’izar ta marigayi Aminu K/Daji in...
“Ina rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, ya sa ya huta har abada.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Ina rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, ya sa ya huta har abada.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Dokar bunkasa ci gaban Afirka da samar da dama ga yankin (AGOA), wacce ta bai wa kasashen yankin damar fitar da kayayyaki zuwa Amurka ba tare da haraji ba, ta shiga gararamba bisa yadda karin harajin zai kassara masana’antu kamar su masaku, da na karafa, da kuma noma. Nijeriya da Afirka ta Kudu da suka fi karfin tattalin arziki a yankin, Amurka ta kakaba musu haraji na kaso 14% da 30% bi-da-bi, saboda rashin imani kuma karamar kasa kamar Lesotho wacce du-du-du karfin tattalin arzikinta na GDP bai wuce dala biliyan 2 ba, aka dankara mata karin harajin da kashi 50%. Galibin tattalin arzikin kasashen Afirka ya fi dogaro ne da fitar da kayayyaki zuwa ketare don dorewar...
Majalissar Dokokin Rasha ta amince da yerjejeniyar huldar ta shakaru 20 tsakanin kasar da Iran. Wannan na nuna muhimmin mataki na zurfafa dangantakar siyasa, soja da tattalin arziki tsakanin Moscow da Tehran. Yarjejeniyar ta tsawon shekaru 20, wakilan majalisar sun amince da ita ne a kuri’ar da aka kada a ranar Talata ta yadda kasashen biyu za su iya yin hadin gwiwa cikin tsari da inganci. Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na kasar Iran Massoud Pezeshkian ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a cikin watan Janairu, da nufin karfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban da suka hada da tsaro, makamashi, kudi, sufuri, masana’antu, noma, al’adu, da kimiyya da fasaha. Yarjejeniyar ta kuma bada damar zuba jari a...
Amurka za ta iya janye sojoji 10,000 daga Gabashin Turai, kamar yadda rahoton NBC News ya bayyana. A shekarar 2022, tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya tura karin sojoji 20,000 zuwa yankin bayan Rasha ta kai hari Ukraine. A ranar Talata, NBC ta ruwaito cewa jami’ai shida daga Amurka da Turai sun tabbatar da tattaunawa kan rage yawan sojojin da aka tura, inda aka fi mayar da hankali kan rage adadin a Romania da Poland. Shugaba Donald Trump yana kokarin kawo karshen yakin Ukraine da aka shafe fiye da shekaru uku anayi tun bayan hawansa mulki, amma har yanzu bai cimma nasarar warware matsalar ba. Ya sha sukar NATO, yana mai jaddada cewa ya kamata Turai ta dauki karin nauyi...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne sun kashe masunta uku a wani hari da suka kai ƙauyen Sanyinna da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato. Wata majiyar a ƙauyen ta ce ’yan bindigar sun kashe mutanen ne a lokacin da suka kawo hari da safiyar Talata yayin da mutanen suka fita sana’arsu ta su. Kazalika, majiyar ta ce ko a ranar Litinin da ta gabata ’yan bindigar sun kai hari garin Sutti da Takkau duk a karamar hukumar inda sun jikkata mutum biyu. Mataimaki na musamman ga shugaban Ƙaramar Hukumar Tangaza kan tsaro, Alhaji Gazali Raka ya tabbatar da faruwar lamarin. Alhaji Raka ya bayyana cewa ’yan bindigar sun sace dabbobi da suka haɗa da Shanu...
Duk da wannan zullumi da ake ciki, a kwanakin baya, kasar Sin ta tattauna da wasu kamfanonin Amurka sama da 20 cikinsu har da Tesla, inda ta kara ba su tabbacin cewa, za ta ci gaba da bude kofarta ga kamfanonin kasashen waje da aiwatar da gyare-gyare a gida. Wannan shi ake nufi da babbar kasa mai sanin ya kamata, mai kuma la’akari da moriyar sauran kasashe maimakon moriyarta ita kadai. Idan Amurka na ganin matakanta za su danne ci gaban wasu kasashe, su kuma bata fifiko a duniya, to ta yi kuskure, domin yanzu ta budewa duniya ido, kuma kasashe da ma kamfanoninsu, za su koma ne ga inda suka tabbatar da cewa za su samu moriya, kuma...
Ya ce karin wa’adin na baya-bayan nan ya biyo bayan cikar wa’adin farko na ranar 1 ga Afrilu, 2025, wanda aka sanya tun da farko a ranar 24 ga watan Janairu. Umar ya kara da cewa, duk da wannan karin wa’adin, amma an ci gaba da samun karancin fitowar masu filaye domin sabunta takardunsu. Domin tabbatar da bin ka’ida, kwamishinan ya yi gargadin cewa, nan ba da jimawa ba, za a buga sunayen wadanda ba su bi ka’ida ba a jaridun kasar nan da kuma nuna su a allunan sanarwa a muhimman wuraren gwamnati da suka hada da dakin karatu na jihar Kano, Sakatariyar Audu Bako, Gidan Murtala, da kuma babbar kotun jihar. Daga kanmu, magana ta...
Hukumar Kula da Jin DDaɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta ayyana ranar Juma’a 11 ga Afirilun 2025 a matsayin ranar ƙarshe da za a kammala biyan kuɗin aikin hajjin bana ga dukkan maniyyatan jihar. Shugaban hukumar, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam ne ya bayyana hakan a yayin wata hira da manema labarai a Ilori. Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa jimillar kuɗin aikin hajjin bana ya kai naira miliyan 8,459,000. Ya yi kira ga dukkan maniyyatan da suka fara biyan kuɗi da su tabbatar sun kammala ragowar kuɗin kafin ranar ƙarshe, wato 11 ga Afrilu, domin ba za a ƙara lokaci ba. Alhaji Abdulsalam ya kuma buƙaci maniyyatan da su gaggauta miƙa fasfo ɗin su na tafiya ƙasashen waje ga jami’ansu domin fara...
Wasu daga cikin maharan sun tsere zuwa dajin Sambisa, bayan da sojoji, mafarauta da mazauna garin suka yi musu kaca-kaca. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kasashen Uku Suna Yin Taron ne dai a matsayin kwararru domin tattauna batutuwa da dama daga cikinsu da akwai na shirin Nukiliya na Iran. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’ila Baka’i ne ya sanar da cewa za a yi wannan taron ne a birnin Moscow wanda kuma ya kuma kunshi wakilai daga kasashen Iran, China da kuma mai masaukin baki Rasha. Buku da kari Baka’i, ya kuma bayyana cewa za a yi wata tattaunawar a tsakanin Iran da tarayyar turai a matakin masana shari’a. A can kasar Rasha mai Magana da yawun harkokin wajen Rasha Maria Zakharova ta fada wa kafafen watsa labarun kasar ta Rasha cewa, a gobe Talata ne za a yi tattaunawar a tsakanin kwararru daga kasashen...
Gwamna Caleb Mutfwang ya bayyana hare-haren baya-bayan nan da kashe-kashen da aka yi a wasu sassan jihar a matsayin shirin masu nufin tada zaune tsaye da kawo cikas ga zaman lafiyar jihar ne a maimakon a alakanta harin da rikicin manoma da makiyaya. Da yake karin haske kan lamarin, Mista Aradong ya ce ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da kayan abinci da sauran kayayyaki. Mista Aradong, wanda ya yabawa gwamnatin jihar da jami’an tsaro bisa fara gudanar da binciken gaggawa da suka yi, ya kuma bukaci a kara tura jami’an tsaro a yankunan da lamarin ya shafa. Da yake jawabi yayin ziyarar, Mista Jatau, wanda ya jajanta wa iyalan da suka rasa ‘yan uwansu yayin...
A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, a yayin bikin ranar yara kanana ta duniya a Falasdinu, cibiyoyi masu fafutuka kan harkokin fursunoni sun sanar da cewa: Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila tana ci gaba da tsare kananan yara Palastinawa sama da 350 a gidajen yari da wuraren da ake tsare da fursunoni. Sanarwar hadin gwiwa da hukumar kula da harkokin tsare-tsare, da “Kungiyar Fursunonin palasdinu”, da kuma “Cibiyar Kare Hakkokin Bil Adama ta Al-Dameer” suka fitar, ta bayyana cewa, yaran na fuskantar matsaloli Ciki har da azabtarwa, yunwa da gangan, da rashin kulawar likita. Wadannan cibiyoyi sun jaddada cewa yaran Palasdinawa su ma suna fuskantar tauye hakkinsu, wanda irin wannan hali ne ya yi sanadin shahadar wani yaro a cikin makon...
Gwamnatin Kasar Iran ta bada sanarwan samun sabbin ci gaba a fagen fasaha da kuma kayakin da suka shafi makamashin Nukliya, wanda za’a baje kolinsa a ranar 9 ga watan Afrilu na wannan shekarar , wato ranar makamashin Nukliya ta kasa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto mataimakin shugaban kasa kuma shugaban hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran Mohammad Eslami yana fadar haka a yau Lahadi. Ya kuma kara da cewa, masana fasahar nukliya ta kasar sun samar da sabbin ci gaba a fagen makamashin nukliya wadanda suka hada da magungun wadanda suka yi amfani da sinadarin Nkliya don samar da su, da kuma ci gaba a fannin ilmi da dama, duk tare da fasaha da kuma...
Ya kuma bukaci jama’a musamman mazauna Damaturu da su kwantar da hankulan su, su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba. Abdulsalamu ya bada tabbacin aniyar gwamnati na wanzar da zaman lafiya da tsaro, yayin da ya yi gargadi kan yada labaran karya da ka iya haifar da firgici a tsakanin ‘yan kasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Olunloyo ya jagoranci jihar Oyo tsakanin 1 ga Oktoba, 1983 zuwa 31 ga Disambar 1983. Rasuwar marigayi dan siyasar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da tsohon Editan jaridar Nigerian Tribune, Barista Oladapo Ogunwusi ya fitar a ranar Lahadi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin kasar Sin ta yi kakkausar suka da bayyana adawarta ga matakin Amurka na kakaba “harajin fito na ramuwar gayya.” A cikin wata sanarwar da ta fitar, ta yi Allah-wadai da matakin na Amurka, wanda ya kasance daukar mataki bisa radin kai, da kuma kariyar cinikayya da cin zarafin tattalin arziki. Sanarwar ta kara da cewa, ta hanyar fakewa da abin da take kira “ramuwar gayya” da “adalci,” a zahiri dai Amurka ta tsunduma a aiwatar da dabarun danniya da babakere, tana neman cimma manufarta ta “Amurka na gaba da komai” da kuma “Amurka ta fi kowace kasa.” Har ila yau, Amurka na amfani da harajin fito don kawo cikas ga tsarin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa,...
A yayin hirar Abdullahi Shuaibu ya ce “Ni dai suna na Abdullahi Shuaibu, amma al’uma na kirana da Karkuzu, ko kuma Abdullahi Kano, yanzu shekaru 43 kenan ina wannan harka ta fina finan Hausa, amma yanzu wasu lokutan sai in kwana ba ni da abin da za a ci a gida na, kuma wani abin tausayi, ni Karkuzu a yanzu zancen da na ke, wannan gida da nake ciki an sa shi a kasuwa, ba gida na ba ne, haya nake yi. Ya ci gaba da cewa, yanzu a cikin wannan al’amari da na ke yi, in an ce na mallaki gida mai dimbin yawa, wadansu da za su ke kallo na sai su ce gaskiya ne, amma wallahi tallahi,...
Ministan harkokin wajen kasar Nijar ya sanar da cewa nan ba da jimawa ba za a Rasha za ta aika tawagar diflomasiyya a Nijar. Nijar ta tabbatar da aniyar ta na karbar bakuncin ofishin jakadancin Rasha a karon farko cikin sama da shekaru talatin, in ji ministan harkokin wajen kasar ta yammacin Afirka, Bakari Yaou Sangare a ranar Alhamis. Bayanin ya fito ne yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa a birnin Moscow bayan tattaunawa tsakanin ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov da takwarorinsa na kasashen Nijar, Mali, da Burkina Faso. M. Sangare ya bayyana cewa, a halin yanzu Nijar na neman wurin da ya dace domin gina ofishin jakadanci na tawagar diflomasiyyar Rasha a kasar, ya kara da...
Alhamdulillah, a makon jiya ne muka fara gabatar da wannan rubutu wanda fahimtar malaman Mazhabar Malikiyya ce a kan azumin Sitta Shawwal a wani yunkuri na warware shubuhar da ake samu a tsakanin mabiya mazhabar a nan Najeriya. Yayin da wadansu ke kokarin haramta azumin wadansu kuma nema suke yi su mayar da shi wajibi. Muna fata da wannan dan rubutu da muka ciro daga shafin Cibiyar Imam Malik ta Intanet (Markazu Imam Malik) za a kawar da wannan takaddama. Mene ne matsayin azumin Sitta Shawwal a Mazhabar Malikiyya Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan 1. Na ce ya dace a gabatar da biyan azumi ban ce ya wajaba daga farko ba. Ya inganta a yi Sitta Shawwal...
Gwamnatin Jihar Borno ta nuna matuƙar damuwarta kan yadda wasu matasa ke amfani da kafafen sada zumunta na yanar gizo wajen yin kalamai masu nuna barazana da al’adunmu na rashin ɗa’a da rashin sanin ya kamata. A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar yaɗa labarai da tsaron cikin gida ta jihar Borno ƙarƙashin Kwamishinanta Farfesa Usman A. Tar ta fitar, gwamnatin ta yi Allah-wadai da irin munanan kalamam da suke yi da kan iya haifar da barazana. An kai wa motar haya hari an kashe mutum 2 da sace wasu a Benuwe ’Yan sanda sun gayyaci Sarki Sanusi domin amsa tambayoyi Inda ta yi nuni da cewa, waɗannan kalaman sun saɓawa al’adunmu da tsarin rayuwarmu, musamman a shafukan sada zumunta na...

Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Amurka Da Jakadan Sin A Burtaniya Sun Nuna Adawa Da Matakin Harajin Fito Na Ramuwar Gayya Da Amurka Ta Dauka
A ranar Alhamis ne, ofishin jakadancin kasar Sin da ke Amurka da jakadan Sin a Burtaniya Zheng Zeguang, suka bayyana matukar kin amincewa da harajin fito “na ramuwar gayya” da Amurka ta kakaba. Suna masu nuni da cewa, Amurka ta sanar da karin harajin fito kan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashe da dama ciki har da kasar Sin, ta hanyar fakewa da abin da take kira ramuwar gayya, ofishin jakadancin Sin da ke Amurka ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, matakin ya saba wa ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kuma ya saba wa ka’idojin tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban. Kana, ya bukaci Amurka da ta gyara kurakurenta, tare da warware sabanin cinikayya tsakaninta da kasar Sin...
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang ya ce hare-hare da kashe-kashen da ake yi a wasu sassan jihar wasu ne ke ɗaukar nauyinsu ba rikicin manoma da makiyaya ba ne. Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin bikin baje kolin kayayyaki da fasaha da ƙungiyar Tincity Fashion Week ta shirya a daren Juma’a a Abuja. An ceto fasinjoji 14 a hannun ’yan bindiga, 3 sun rasu a Benuwe Sabon harajin Trump zai jefa tattalin arziƙin duniya cikin matsala — WTO Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN ya bayar da rahoton cewa, a ranar 2 ga watan Afrilu, wasu ’yan bindiga sun kai hari a ƙauyukan Manguno, Daffo da Josho na ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar. Maharan sun kashe mutane da dama tare...
Kasar ta sha alwashin ci gaba da taimakawa kasashen nan guda uku na kawancen sahel da suka hada da Mali, Burkina faso da kuma Nijar a fannin tsaro. Ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ne ya bayyana haka ranar Alhamis bayan ya gana da takwarorinsa na ƙasashen Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar a birnin Moscow, yana mai cewa a shirye suke su taimaka domin bunƙasa alaƙar soji da ƙasashen. “Ina jaddada aniyar Moscow ta taimakawa domin samar da gamayyar rundunar soji ta yankin Sahel, tare da ƙarfafa dakarun soji da sauran jami’an tsaro na waɗannan ƙasashe uku ta hanyar ba su horo da makamai,” in ji Lavrov. Wannan bayanin ya fito ne a yayin taron manema labarai da bangarorin...
SShugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana alhininsa bisa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Bauchi, Dr Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, wanda ya rasu a daren Juma’a yana mau shekaru 68 a duniya. Mai ba Shugaban ƙasa shawara na musamman kan Harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ne ya fitar da sanarwar, inda ya jaddada muhimmancin gudummawar Dr. Abdulaziz wajen koyar da addinin Musulunci da kuma ci gaban matasa. Shugaba Tinubu ya yabawa ƙoƙarin marigayin wajen yaki da tsattsauran ra’ayi da rikicin Boko Haram tun farkon bayyanar kungiyar. Ya ce al’ummar Musulmi sun yi babban rashi bisa mutuwar Dr. Abdulaziz wanda kan jajirce kan gaskiya da ɗa’a. Shugaban ya kuma yi addu’a ga Allah Ya jikansa, tare da...
Shugaba Tinubu ya zanta da manema labarai bayan kammala Sallar Idi na karshen watan Ramadan a filin da aka gabatar da Sallar Idi na kasa a Abuja ranar Lahadi. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, shugaban ya bukaci ‘yan Nijeriya da kada su koma kan aikata abubuwan da su ba ta dace ba, a maimakon haka, ya bukace su da su dage wajen aiwatar da kyawawan dabi’un game da darusan da suka koya a watan Ramadan. A cikin hudubar da babban limamin masallacin kasa dake Abuja, Dakta Abdulkadir Salman Sholagberu, wanda ya jagoranci Sallar ya gabatar, ya jaddada bukatar Musulmi su ci gaba da gudanar da ibadar da suka koya a Azumin watan Ramadan,...
Matakan harajin fito na Amurka na haifar da koma-bayan tsarin cinikayyar duniya. Game da wannan batu, kafar CGTN ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, ta gudanar da wani binciken jin ra’ayin al’umma ga masu amfani da intanet na sassan kasa da kasa, inda suka yi tir da irin wannan abun da Amurka ta yi, al’amarin da a cewarsu, ka iya janyo ramuwar gayya daga kasashe daban-daban, har ma zai iya ta’azzara yakin harajin fito a duniya, da kawo babbar illa ga tattalin arzikin duniya. Kashi 82.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyinsu sun nuna cewa, yayin da ake fuskantar rashin daidaiton ci gaba da karfin tattalin arziki tsakanin kasa da kasa, neman cike gibin cinikayya da...
Ya roƙi Allah da Ya ji ƙansa, tare da bai wa iyalansa da almajiransa haƙurin rashinsa. Hakazalika, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana kaɗuwarsa game da fitaccen malamin. Ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukan sada zumunta. “Ina miƙa ta’aziyya ta ga iyalai da almajiran Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi. “Dokts Dutsen Tanshi ya kasance abin tunawa saboda jajircewarsa wajen yaɗa ilimin addinin Musulunci. “Allah Ya jikansa da rahama, Ya sanya shi a Aljannatul Firdausi,” in ji Kwankwaso. Dokta Abdulaziz ya kasance mashahurin malami wanda aka san shi wajen faɗar gaskiya, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da tsattsauran ra’ayi da ƙarfafa zaman...
Na ji dadi da yadda ka yi kira ga sauran Malamai da su zama masu kwadaitar da neman Ilimi a kowanne fanni, sannan su kaurace wa furta haramci a kan abubuwan da Shari’a ba ta yi haramci a kai ba. Tabbas, ayoyin Alkur’ani suna nan kamar yadda aka saukar kuma ba za su sauya ba har duniya ta nade, amma fahimtarsu tana sauyawa daidai da zamani, don haka, bai dace a yi watsi da kimiyya da fasahar zamanin nan ba da ake ganin na turawa ne kawai, matukar ba a samu fiye da tasu ba. Akramakallah, gaskiya ne, ya dace Malamai su rika ba da fatawa da ta yi daidai da zamaninsu da kuma fahimtar da al’ummar Musulmai Isharori na...
Yayin gabatar da rahoton an raba lambar yabo ga Hakiman da aka fi samun gudunmawar Zakkar daga gundumominsu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jamhuriyar Musulinci ta Iran ta yi kira ga kasashe mambobi kungiyar hadin guiwa ta Shanghai da ta yi Allah wadai da barazanar Trump ta baya baya nan kan kasar. A taron ministocin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da aka gudanar a birnin Moscow a ranar Alhamis, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht Ravanchi, ya yi kira ga mambobin kungiyar SCO da su yi Allah wadai da kalaman da shugaban na Amurka Donald Trump ya yi a baya-bayan nan kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, lamarin da ya ce yana da hadari. Majid Takht Ravanchi ya yi kakkausar suka ga barazanar harin bam da Trump ya yi a wata hira da tashar NBC News, inda ya ce, hakan ya keta...
Ministocin harkokin wajen kasashen kawacen sahel na AES da ya hada Mali da Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar, na wata ziyarar aiki a kasar Rasha. Ana sa ran ministocin za su kasance a birnin Moscow a yau Alhamis da gobe Juma’a, don tattaunawa, da zurfafa hulda tsakanin bangarorin biyu, kamar dai yadda aka bayyana cikin wata sanarwar hadin gwiwarsu. Sanarwar, ta ce shawarwarin da ministocin kasashen kungiyar ta AES za su yi tare da ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov, wani bangare ne na burin shugabannin kasashen uku na yankin sahel da sojoji ke mulki da kasar Rasha, na fadada hadin gwiwa a fannonin siyasa, tattalin arziki da kuma tsaro. Har ila yau, sassan biyu za su zanta game...
Ana yi wa Shehin Malamin laƙabi da Dr. Tauhidi saboda da’awarsa ta ƙarfafa ne akan Tauhidi da kuma riƙo da Sunnar Annabi (S.A.W.) da kuma yaƙi da fararrun al’amura a cikin addinin Islama. Za a yi sallah jana’izar Babban Limamin da misalin ƙarfe 10 na safe a Masallacin Idi na Games Village, Jihar Bauchi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp