Al’ummar Babura sun shirya gagarumin taron girmamawa domin karrama Dr. Salisu Mu’azu, bayan nada shi a matsayin Daraktan kuma babban likitan asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ke jihar Jigawa, da kuma samun matsayin mamba na Cibiyar Kasa (mni).

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kwamitin Shirye-shirye, Rabiu Umar, ya bayyana cewa an gudanar da taron ne domin nuna godiya ga Allah da kuma murnar manyan nasarorin da Dr.

Mu’azu ya samu.

Ya yaba da kokarin Daraktan wajen gudanar da aikinsa da kwarewa, da kuma ci gaba da tallafa wa al’umma.

A sakon da aka gabatar a madadin Mai Martaba Sarkin Ringim, Alhaji Dr. Sayyadi Abubakar Mahmoud, wanda Mai Girma Alhaji Usman Sayyadi, Babban Hakimin Masarautar, ya wakilta, ya nuna godiya ga masu shirya taron.

Ya bayyana karramawar a matsayin abin da ya dace da Dr. Mu’azu, yana mai jaddada jajircewarsa, da tausayi da himma wajen yi wa al’umma hidima.

Haka zalika, Shugaban Karamar Hukumar Babura, Alhaji Hamisu Muhammad Garu, ya taya Dr. Mu’azu murna bisa nasarorin da ya samu a fannin aikin likitanci, inda ya danganta hakan da jajircewa da  amana.

Ya tabbatar masa da cikakken goyon bayan al’umma tare da addu’ar samun karin nasarori.

A nasa bangaren, Dr. Salisu Mu’azu ya bayyana godiya sosai bisa girmamawa da karramawar da al’ummarsa ta masa.

Ya kuma nuna godiya ga Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, bisa damar da ya ba shi zuwa makarantar NIPSS da ke jihar Filato.

A yayin taron, mutane da kungiyoyi daban-daban sun mika kyaututtuka da lambobin yabo ga Daraktan, ciki har da reshen kungiyar likitoci ta Najeriya na jihar Jigawa, J Health Beneficiaries, kungiyar Nas nas da Ungozoma ta kasa, da kuma kungiyar masu kula da lafiyar hakora ta Babura da sauransu.

 

Usman Muhammad Zaria 

 

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Babura Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun kashe mutane 40 a sabon hari a Filato

’Yan bindiga sun kashe mutane arba’in a wani hari suka kai a ƙauyen Zike, a yankin Kwall da ke Ƙaramar Hukumar Bassa a Jihar Filato.

Wani shugaban al’ummar Kwall, Wakili Tongwe, ya ce maharan sun shiga ƙauyen ne da sanyin safiyar ranar Litinin suna harbi kan mai uwa da wabi, lamarin da ya sa mazauna gujegujen neman tsira.

Ya shaida wa wa kafar talabijin ta Channels cewa wata tawagar ’yan banga, da shi kansa da wasu jami’an tsaro, suna sintiri a wani ƙauye ne lokacin da maharan suka kai harin.

Ko da yake jami’an tsaron sun yi artabu da maharan kuma sun yi nasarar fatattakar su, amma an riga an riga an kashe mutane talatin da shida nan take, wasu huɗu kuma suka mutu daga baya.

Boko Haram ta kashe mutum 300 ta kwace ƙananan hukumomi 3 a Borno — Ndume NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar Borno

Wasu mazauna garin kuma sun samu raunukan harbin bindiga kuma suna samun kulawa a asibiti.

Hukumomin tsaro a jihar ba su yi wani sharhi ba game da harin, wanda ya zo ƙasa da makonni biyu bayan an kashe mutane hamsin da biyu a wasu ƙauyukan Karamar Hukumar Bokkos ta Jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hajj 2025: Hukumar Alhazai Ta Shirya Taron Bita Ga Mahajjata a Jihar Kwara
  • Gazawar Gwamnati Kan Kiyaye Rayuka Da Dukiyoyi: Gwamnan Filato Ya Nemi Yafiyar Al’ummar Jihar
  • Sabon Shugaban Kasar Gabon Ya Bayyana Shiransa Na Kawo Sauyi Mai Kyau A kasar
  • ’Yan bindiga sun kashe mutane 40 a sabon hari a Filato
  • An Karrama Shugaban Qausain TV, Kanar Sani Bello Da Lambar Yabo
  • Jiragen Saman Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Luguden Wuta Kan Asibitin Baptist Da Ke Gaza
  • Al’ummar Mauritaniya Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Nuna Adawa Da Yakin Gaza
  • Inganta Rayuwar Al’umma: Amurka Da Ƙungiyar Kasuwanci Ta Nijeriya Sun Karrama Gwamna Lawal
  • Gaza: Sojojin HKI Sun Sake Kai Wa Asibitin “Ma’amadani Hari