2025-04-02@12:32:23 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1132
«Babura»:
Ƙungiyar matasan Arewa ta yi Allah-wadai da jita-jitar da ake yaɗawa cewa an kashe wani ɗan ƙabilar Ibo a Jihar Kano saboda kisan wasu Hausawa mafarauta da ɓatagari suka yi kwanan a Jihar Edo. A wani taron manema labarai da gamayyar ƙungiyoyin matasa na ƙabilu daban-daban, ta ce abin takaici ne kisan da aka yi...
Haka kuma, yana shirin gina masana’antar sarrafa itace da samar da sabbin hanyoyin ruwa domin rage cunkoso a tashoshin jiragen ruwa na Apapa da Lekki. Wannan jari ya zo ne a daidai lokacin da Kamaru ke faɗaɗa tashar jiragen ruwa na Kribi domin ƙara inganta kasuwanci a yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
A wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban hukumar makamashin Nukliya ta duniya Rafael Grossy Abbas Aragchi ministan harkokin wajen kasar Iran ya bukaci hukumar ta bayyana matsayinta dangane da shirin makamashin nukliyar kasar Iran. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto ministan yana fadawa Grossy bayyana matsayin hukumarsa dangane da shirin nukliyar...

Iran: Larijani Ya Ce Iran Zata Fara Kera Makaman Nukliya Idan An Kai Mata Hari Kan Shirin Ta Na Makamashin Nuliya
Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Dr Ali Larijani, ya ce duk tare da cewa jagoran juyi juya halin musulunci ya bada fatawar hana kera makaman nukliya, amma idan an kaiwa kasar Iran hari kan shirinta na makamashin nukliya, wannan yana iya tunzura kasar ta kai ga mallakar makaman Nukliya. Jaridar Tehran time...

Sojojin Yemen Sun Cilla Makamai Masu Linzami Kan Kataparen Jirgin Ruwan Yaki Mai Daukar Jirage Na kasar Amurka
Sojojin kasar Yemen sun yi amfani da makamai masu linzami samfurin cruise a hare-haren da suka kai kan kataparen jirgin yaki mai daukarjiragen saman yaki na kasar Amurka da suke cikin tekun maliya a karo na ukku a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar sojojin...
Rahotanni na cewa Allah Ya yi wa Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sunusi ya rasuwa. Wata sanarwa da ta fito daga cikin iyalansa ta tabbatar da rasuwar, inda ta ce nan gaba za a bayyana lokacin da za a yi masa jana’iza. Alhaji Abbas Sanusi kawu ne ga Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, kuma mahaifi ga...
Tawagogin ma’aikatan ceto na kasar Sin na ci gaba da aiki a yankin da ya fi shan wuya na Mandalay da ke tsakiyar kasar Myanmar, sakamakon girgizar kasar da ta afku mai karfin maki 7.9 a makon da ya gabata, inda zuwa yanzu suka ceci mutum takwas da suka tsira daga ibtila’in, da misalin karfe...
Alƙaluman Asusun Tallafawa Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF ya ce Isra’ila ta kashe ƙananan yaran da yawansu ya kai 322 cikin kwanaki 10 da suka gabata a hare-haren da suke ci gaba da kai wa sassan Gaza. Alƙaluman da UNICEF ta fitar ta ce a jimilla ƙananan yara fiye da dubu 15 ne...
Yakin cinikayya ba zai taba durkusar da kasar Sin ba, sai dai kaikayi ya koma kan mashekiya. Yayin da wasu kasashen ke aiwatar da kariyar cinikayya da kokarin rufe kofarsu ga sauran sassan duniya, kasar Sin ta kara bude kofarta, tana kuma maraba da ’yan kasuwa daga kasa da kasa. Maimakon kawo cikas, kasar Sin...
A jiya Litinin ne kasashen Sin da Zambiya suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya kan fitar da kwarurun macadamia nuts zuwa kasar Sin. Bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar ya samu halarcin mukaddashin jakada na ofishin jakadancin Sin da ke Zambiya Wang Sheng, da ministan noma na kasar Zambiya Mtolo Phiri. Kano Pillars Ta Janye Dakatarwar...
Rundunar ’yan sanda ta nemi da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta jingine shirinta na kai ziyara da zummar hada gangamin bikin Sallah a Jihar Kogi. Wata sanarwa da kakakin ’yan sandan Jihar Kogi, ASP William Aya ya fitar, ta ambato Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP William Ɗantawaye na cewa gangamin ya ci karo da haramcin gudanar...
Kakakin sojojin Yemen Janar Yaha Sari ya sanar da cewa, sun harbo jirgin leken asirin Amurka samfurin MQ9 a saman yankin Ma’arib. Janar Sari ya ci gaba da cewa za mu ci gaba da abinda muke yi na hana jiragen ruwa wuce ta tekun “Red Sea” domin zuwa HKI, tare da kara da cewa, ba...
Babban Darakta Muryar Najeriya VON, Malam Jibrin Baba Ndace ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kara kaimi wajen addu’o’in samun nasara ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bisa tsarinta na sabunta fata. Ya yi wannan kiran ne a cikin sakonsa na Sallah ga al’ummar Musulmi da aka rabawa manema labarai a...
Kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Kebbi, NUJ, ta taya gwamnatin jihar da al’ummar musulmin jihar murnar zagayowar ranar Sallah. Majalisar a cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na jiha, Kwamared Bello Sarki Abubakar da Sakatare, Ismail Adebayo, ta yi murna da al’ummar musulmin jihar kan...
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, Dakta Abdul’aziz Yari, ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu na alheri fiye da watan Ramadan. Da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa Talatan Mafara, a wani bangare na...
Mai bai wa jagoran juyin musulunci na Iran shawara Dr. Ali Larijani ya ce, idan har Amurka da Isra’ila su ka fake da batun shirin makamashin Nukiliyar Iran na zaman lafiya, su ka kawo mata hari, to ya zama wajibi a gare ta ta kera makaman Nukiliya. Dr. Ali Larijani wanda tashar talabijin din Iran...
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Arakci ya bayyana cewa, duk wata barazana da za a yi wa Iran za ta sa makiya su yi babbar nadama. A wata hira a tashar talabijin din almasirah ta kasar Yemen ta yi da shi, ministan harkokin wajen na Iran ya ce, farfagandar da ake yi ta cewa, kai...
Da safiyar Yau Talata jiragen yakin HKI sun kai hare-hare akan unguwar Dhahiya dake Beirut tare da bayyana cewa ta kai wa wani kusa ne a kungiyar Hizbullah hari. Harin na yau shi ne irinsa na biyu da HKI ya kai a unguwar Dhahiya tun daga tsagaita wutar yaki a cikin watan Nuwamba na shekarar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi kakkausan gargaɗi kan barazanar Amurka da ƙawayenta na kai wa ƙasarsa hari. Khamenei ya sha alwashin maida mummunar martani idan har Amurka da ƙaddamar da hare-hare a ƙasar ta Iran. Gargaɗin nasa martani ne kan barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa ƙasar cewa...
Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran,Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana cewa yau duniyar musulmi tana bukatar hadin kai fiye da ko wane lokaci. A yayin ganawarsa da jami’an tsare-tsare da jakadun kasashen musulmi yau Litinin ranar karamar sallah a Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya mayar da hankali kan abubuwan...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta gayyaci mai kula da harkokin kasar Switzerland da ke Tehran domin nuna fishi kan irin munanan ayyukan Isra’ila a yankin da kuma barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ke yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Babban daraktan ma’aikatar harkokin wajen Iran Issa Kameli ne ya gayyaci jami’in diflomasiyyar na...
A Gaza fiye da mutane 1,000 ne Isra’ila ta kashe tun daga ranar 18 ga watan Maris, tun bayan sake dawo da yaki a Zirin. Hakan ya sanya adadin falasdinawan da Isra’ila ta kashe tun watan Oktoba ya kai 50,350 tare da raunata 114,400 a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza. Hare-haren da Isra’ila ta kai...
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya bayyana rashin jin daɗinsa dangane da kashe matafiya ’yan Arewa da aka yi a Jihar Edo. Saboda haka Sarkin ya ce suna dakon ganin hukuncin da za a ɗauka dangane da faruwar wannan mummunan lamari. Kisan Mafarauta: Matakan da gwamnatin Edo da ta Kano suke ɗauka Dalilin...

Ofishin Siyasa Na Kwamitin Tsakiyar Jks Ya Kira Taron Nazarin Ayyukan Kiyaye Muhallin Halittu Da Sauransu
Yau Litinin, ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS ya kira wani taro na nazarin ayyukan kiyaye muhallin halittu, da rahoton ayyukan kewaye da kwamitin tsakiyar JKS karo na 20 ya gabatar, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron. Taron ya nuna cewa, sa ido kan aikin kiyaye muhallin halittu wani muhimmin mataki a...
A safiyar yau litinin ce a nan Iran da kuma wasu kasashen duniya da dama suka gudanar da sallar Idi wanda ya kawo karshen watan Ramadan mai al-farma wanda musulmi suka yi azuminsa daga safe zuwa faduwar rana na tsawon kwanaki 29-ko 30. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa a nan...

Yawan Kayayyakin Da Aka Yi Hada-hadarsu A Tashoshin Jiragen Ruwa Na Sin A 2024 Ya Ci Gaba Da Kasancewa Na Farko A Duniya
Bayanai da ma’aikatar sufuri ta kasar Sin ta fitar a jiya Asabar sun nuna cewa, a shekara ta 2024, yawan kayayyakin da aka yi hada-hadarsu a tashoshin jiragen ruwa na kasar ya kai tan biliyan 17.6, kuma yawan kwantenan da aka yi hada-hadarsu ya kai miliyan 330, hakan ya sa kasar ta ci gaba da...
Watan Ramadan mai alfarma na wannan shekara ya zo ni’imomi masu Yawa wanda matasa da sauran mutanen kasa sun amfani da ayyukan ibada wadanda suka hada da karatun Alkur’ani mai girma, mun yi addu’o’I mun kuma yi magana da All..mun roke shi a cikin watan. Da fatan All..ya karbi ayyukammu. Amma a wani bangare a...
Yan wasan kwallon kafa na kasar Iran sun zama zakara karo na 4 a kwallon kafa na yashin bakin teku a karo na 4 a cikin kasashen Asiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ba bayyana a gasa ta karshe wanda kungiyar kwallon kafa ta yashin bakin take wanda aka gudanar tsakanin JMI da...

Iran Ta Ce Tattaunawa Da Amurka Tare Da Mai Shiga Tsakani Na Gaba, Ya Danganci Matakan Da Ta Dauka Kan Iran
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa gwamnatin JMI ta yi watsi da tattaunawa kai tsaye dangane da shirinta na makamashin Nukliya, sannan ya kara da cewa amma tattaunawa tare da masu shiga tsakani a bude take. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana cewa tuni, mun bawa gwamnatin Amurka...
Wani yaro dan shekara hudu da ya kira wayar salular ’yan sandan yankin Mount Pleasant a Karamar Hukumar Charleston Jihar South Carolina da ke Amurka ya ce, mahaifiyarsa ta shanye masa ‘ice cream’ dinsa kuma yana bukatar a hukunta ta, a kai ta gidan yari saboda aikata hakan. A cewar ’yan sanda yaron dan...
Jiragen yakin Amurka sun kai sabbin hare-hare kan kasar Yemen a daren Lahadi a wasu yankuna a birnin San’aa babban birnin kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bada sanarwan cewa a safiyar yau Litinin ne jiragen yakin Amurkan suka kai hare-hare har 13 a kan wurare daban-daban a kasar, daga ciki har...
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa, Iran ba ta shiga tattaunawa da Amurka kai tsaye ba, yana mai mayar da martini kan wasikar da shugaban Amurka ya aike mata, amma kuma ya bayyana cewa hakan zai bude kofa ga tattaunawar kai tsaye. Da yake magana a wani taron majalisar ministocin a ranar Lahadi, Pezeshkian...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Amurka na da hannu a ayyukan haramtacciyar kasar Isra’ila na yada rashin tsaro da zaman lafiya a yankin. A wata ganawa da ya yi da Hans Grundberg, wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Yemen a birnin Tehran, Araghchi ya yi Allah wadai da ci gaba...
Sabon tsarin sayar da man fetur a Najeriya ya haifar da ƙarin farashi, inda ake sayar da kowace lita a kan Naira 930 a Legas da kuma Naira 960 a Arewa. A ranar 28 ga watan Maris, 2025, sabon tsarin ya fara aiki bayan da aka dakatar da sayar wa matatar Dangote mai a farashin...
Minista mai kula da al’ada da yawon bude ido da kuma sana’o’in hannu na Iran Ridha Salihi wanda ya gana da jakadan Tunisiya a Iran,Imad al-Rahmani ya bayyana bukatar hanyoyin bunkasa alakar yawon bude ido a tsakanin kasashen biyu, yana mai kara da cewa: Yarjejeniyar da aka cimmawa a tsakanin kasashen biyu dangane da yawon...
Kakakin sojan kasar Yemen janar Yahya Sari ya sanar da cewa sau uku su ka yi taho mu gama da sojojin da suke cikin jirgin dakon jirayen yakin Amurka “ Trauman” a cikin sa’oi 24. A wata sanarwa da janar Yahya Sari ya yi a jiya Asabar ya bayyana cewa; Sun kai wa jirgin dakon...
Ƙungiyar Hamas ta ce tana goyon bayan komawa yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin Gaza, tana mai cewa za ta yi amfani da shawarar da masu shiga tsakanin suka bayar wadda za ta kai ga sakin ƙarin fursunonin Isra’ila biyar da kuma tsagaita wuta a Gaza tsawon kwana 50. Babban jami’in Hamas da baya zaune a...
Ƙungiyar Hamas ta ce tana goyon bayan komawa yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin Gaza, tana mai cewa za ta yi amfani da shawarar da masu shiga tsakanin suka bayar wadda za ta kai ga sakin ƙarin fursunonin Isra’ila biyar da kuma tsagaita wuta a Gaza tsawon kwana 50. Babban jami’in Hamas da baya zaune a...
Sheikh Na’im Qasim babban sakatarin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa JMI ce ginshikin goyon bayan al-ummar Falasdinu, kuma itace gaba-gaban a duk wani yunkuri na yentar da falasdinawa da Falasdinu daga hannun HKI da masu goya mata baya. A wani jawabin da ya gabatar a jiya Asabar, shugaban kungiyar ta Hizbullah, ya...
An fara wallafawa ranar 13 ga Mayu, 2022 A halin yanzu al’ummar Musulmi sun yi haramar fara shagulgulan Karamar Sallar bana bayan kammala Azumin Ramadan. A kan haka ne muka rairayo muku abubuwan da malamai suka kwadaitar da Musulmai su yi a irin wannan rana ta farin ciki da godiya ga Allah bisa ni’imominsa da...
Tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana jin daɗin yadda shugaban ƙasar Bola Tinubu yake tafiyar da gwamnatinsa. Buhari ya ce har yanzu Tinubu bai sauya ba daga tsari da manufofin da jam’iyyar APC ta kafa wanda har ya sanya shi kansa ’yan Nijeriya suka zaɓe shi a 2015. An ga watan Sallah...
Hukumomi a kasar Saudiyya sun sanar da hango jinjirin watan Shawwal, wanda ke nufin kawo karshen watan azumin Ramadana. Shafin Haramain ne ya ruwaito hakan, bayan daukar awanni ana neman wata. Wannan ke nufin gobe Lahadi ne 1 ga watan Shawwal, wato ranar karamar Sallah a kasar ta Saudiyya.
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai kan kungiyoyin kare fararen hula da masu aikin ceto Palasdinawa a Rafah da ke kudancin zirin Gaza, tare da bayyana hakan da aikata laifukan yaki. Sojojin Isra’ila sun amince a ranar Asabar 29 ga watan Maris cewa...
Rahotanni daga Najeriya na cewa mutane 20 ne suka mutu sakamakon hatsaniyar da aka samu tsakanin sojoji da masu jerin gwanon ranar Kudus ta duniya a Abuja fadar mukin Najeriya. Hotunan faifan bidiyo sun nuna yadda masu zanga-zangar ke neman mafaka yayin da karar harbe-harbe ke kara kamari a kusa da su. An ce an...
Hukumomi a Myanmar sun ce adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar ya kai 1,644, yayin da wasu 3,408 suka jikkata, ye zuwa ranar Asabar din nan. Tunda farko dai mutane 1,007 ne aka sanar sun mutu sai wasu 2,389 da suka jikkata. Girgizar mai karfi maki 7.7 ta shafi Kasashen Myanmar da Thailand wadanda...
Shahararren masanin tarihin nan na Jihar Kano, Ibrahim Ado Kurawa, ya bayyana cewa soke hawan Sallah da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yi tamkar wani wasan kwaikwayo ne. A makon jiya ne dai Sarki Aminu Ado ya sanar da janye hawan Sallar da ya ce zai jagoranta kan abin da ya kira...
Majalisar Karamar Hukumar Jahun dake Jihar Jigawa ta kaddamar da rabon tallafin kayan noman rani ga manoma 300. A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a Garin Darai, shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Jamilu Muhammad Danmalam yace hakan na daga cikin manufofin Gwamna Umar Namadi na bunkasa noman rani da na damina domin kawar da...
Wadanda suka rasa ‘yan uwa ko suka jikkata sakamakon fashewar tankar mai da ta afku a Majia, Jihar Jigawa, a bara, za su karɓi Naira miliyan huɗu kowanne domin rage radadin halin da suka tsinci kansu a ciki. Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana haka a lokacin da aka fara rabon kuɗin tallafin ga waɗanda...
Hukumar ’Yan Sandan Saudiyya, ta yi magana kan bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta, wanda ya nuna wata mata tana mari wani ɗan sanda bayan ya hana ta wuce wata hanya da aka rufe. A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Asabar, ta ce tana bincike domin tattara dukkanin bayanai kafin...