Kasashen Masar da Kuwaiti sun fitar da sanarwa a yau Litinin ta yin tir da kiraye-kirayen da wasu yahudawa masu tsattsauran ra’ayi suke yi domin a rusa masallacin kudus, suna masu yin kira ga kungiyoyin kasa da kasa domi a tsayar da tsokanar da Isra’ilawa suke yi.

Kasashen biyu dai sun fitar da wannan sanarwar ne bayan da wasu yahudawa su ka watsa wani faifen bidiyo na tarwatsa masallacin Kudus da kuma maye gurbinsa da gina wajen bautar yahudawa.

Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta bayyana cewa: “Jamhuriyar Larabawa ta Masar tana yin tir da kakkausar murya akan kiraye-kirayen da masu tsattsauran ra’ayin ‘yan share wuri zauna suke yi na tarwatsa masallacin Kudus.

Haka nan kuma Masar din ta yi kira da a kawo karshen keta hurumin masallacin Kudus wanda yake tsokana ce ga al’ummar musulmi.

Ita ma kasar Kuwaiti ta fitar da bayani da a cikin ta yi tir da kora zuwa ga rusa masallacin Kudus da kungiyoyin ‘yan share wuri zauna suke yi. Ta kuma kara da cewa, kiraye-kiraye irin wadannan tsokana ce ga al’ummar musulmin duniya.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kiraye kiraye

এছাড়াও পড়ুন:

Mene Ne Shirin Nukiliya Na Iran Kuma Me Amurka Ke So Ta Yi?

Ta nanata cewa ba neman hada bam din nukiliya take yi ba, amma wasu kasashe – da kuma hukumar kula da makaman nukiliya ta duniya International Atomic Energy Agency (IAEA) – ba su yarda ba.

An fara zargin Iran ne game da shirin nata bayan an gano wasu boyayyun wuraren binciken nukiliya a 2002.

Hakan ya jawo karyewar wata yarjejeniya da ake kira Nuclear Non-Proliferation Treaty (NPT), wadda Iran ta kulla da wasu kasashe, wadda ta ke hana yaduwar makaman nukiliya a duniya.

NPT kan bai wa kasashe damar yin amfani da fasahar nukiliya wajen ayyukan lafiya, da noma ban da hada makamin nukiliya.

 

Yaya ci gaban shirin nukiliyar Iran yake?

Tun bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar da aka kira Joint Comprehensibe Plan of Action or JCPOA a 2018, Iran ta karya ka’idojinta a matsayin martani, wanda ya sa aka sake kakaba mata takunkumai.

Ta kara zuba dubban na’urorin tace ma’adanin Uranium wanda yarjejeniyar JPCOA ta haramta.

Hada makamin nukiliya na bukatar a inganta ma’adanin uranium zuwa kashi 90 cikin 100. A karkashin yarjejeniyar, an bai wa Iran damar inganta kashi 3.67 ne kawai ko kuma zuwa nauyin kilogiram 300 – wanda zai iya ba da damar ayyukan bincike amma bai kai na hada makami ba.

Amma zuwa watan Maris na 2024, hukumar IAEA ta ce Iran na da uranium kusan kilogiram 275 da ta inganta zuwa kashi 60 cikin 100. Hakan zai iya ba ta damar hada bam kamar shida idan ta kara inganta shi.

Jami’ai a Amurka sun ce sun yi imanin Iran za ta iya mayar da shi zuwa makami daya a cikin mako daya. Amma kuma sun ce Iran sai ta yi kamar shekara daya zuwa wata 18 kafin ta iya samar da cikakken makamin nukiliya.

Amma wasu kwararru na cewa za a iya gina karamin makamin cikin wata shida ko kasa da haka.

 

Me ya sa Trump ya cire Amurka daga yarjejeniyar?

Amurka da Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai sun saka wa Iran takunkuman tattalin arziki daga 2010 saboda zargin cewa tana shrin hada nukiliya.

Sun hana Iran sayar da man fetur dinta a kasuwar duniya da kuma hana ta taba kudinta Dala biliyan 100 da ke kasashen waje. Tattalin arzikinta ya karye, kuma darajar kudinta ya yi ta karyewa, wanda ya jawo hauhawar farashi.

A 2015, Iran da manyan kasashen duniya shida – Amurka, Faransa, Rasha, Jamus, Birtaniya – suka kulla yarjejeniyar JCPOA.

Kasashen sun amince su dage wa Iran takunkumai bisa sharuddan yarjejeniyar.

An tsara yarjejeniyar za ta yi aiki tsawon shekara 15.

Lokacin da Donald Trump ya kama mulki ya fitar da Amurka daga yarjejeniyar a 2018, wadda babbar dirka ce a cikinta.

Ya ce yarjejeniyar ba ta da kyau saboda ba mai dorewa ba ce kuma ba ta yi magana kan shirin Iran na makamai masu linzami ba. Ya kara wa Iran takunkumai saboda ta dawo kan teburin tattaunawa.

Isra’ila ta yi ikirarin cewa Iran ta ci gaba da neman hada nukiliya a boye kuma za ta yi amfani da kudin da ta samu bayan cire tukunkumi wajen karfafa rundunar sojinta.

 

Me Amurka da Isra’ila ke so yanzu?

Da alama sanarwar da Trump ya bayar ta neman fara tattaunawa da Iran ta bai wa Isra’ila mamaki. Ya dade yana cewa zai iya kulla yarjejeniya mafi kyawu sama da JCPOA, amma har yanzu Iran ta yi watsi da bukatar.

Trump ya yi gargadi cewa idan Iran ba ta yarda da sabuwar yarjejeniya ba “zai kai musu hari”.

Mai bai shi shawara kan harkokin tsaro Mike Waltz ya ce Trump na son Iran ta “lalata baki dayan” shirin nukilyar tata, yana cewa: “Kamar ingantawa, ko hada makami, wato shirinta na makamai masu linzami.”

Duk da cewa Trump ya ce tattaunawar ta gaba da gaba ce, ministan harkokin Iran Abbas Araghchi ya ce tattaunawar da za a yi a Oman ba ta gaba da gaba ba ce. Ya ce a shirye suke su tattauna amma dole sai Trump ya amince cewa “babu maganar hari”.

Bayan sanarwar da Trump ya yi, Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce yarjejeniya daya da za su amince da ita ita ce wadda Iran za ta yarda da hakura da shirin nukiliya gaba daya.

Ya ce hakan na nufin: “Mu shiga mu tarwatsa masana’antun, mu lalata komai bisa sa ido da jagorancin Amurka.”

Abin da Isra’ila ke fargaba shi ne Trump zai iya yarda da wani abu kasa da lalata shirin na Iran gaba daya da zai yi kurin cim mawa a matsayin nasarar difilomasiyya.

Isra’ila da ba ta shiga yarjejeniyar NPT ba, ana ganin tana da makaman nukiliya, abin da ba ta taba amsawa ko karyatawa ba.

Isra’ila na ganin idan Iran ta samu nukiliya barazana ce a gare ta saboda har yanzu ba ta amince da ‘yancin Isra’ilar ba a matsayin kasa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sharhin Bayan labarai: Rage Kasafin Kudin Ma’ailatar harkokin wajen Amurka da tasirinsa
  • Kakakin Ma’aikatar Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Babban Abin Da Suke Bukata Shi Ne Daga Takunkumi
  • Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam Ta Amnesty International Ta Ce; Gwamnatin Mamayar Isra’ila Ba Ta Dace Da Bincike Laifukan Sojojinta Ba
  • Wasu Falasdinawa Sun Yi Shahada A Harin Sojojin Mamayar Isra’ila Kan Zirin Gaza
  • Gaza : Red Crescent ta yi watsi da rahoton Isra’ila kan kisan da aka yi wa jami’an agaji
  • Hamas ta yi watsi da shirin kwance damara na Isra’ila
  • Dakarun Gwagwarmayar Yemen Sun Kai Hare-Haren Daukan Fansa Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila
  • Mene Ne Shirin Nukiliya Na Iran Kuma Me Amurka Ke So Ta Yi?
  • Sheikh Naim Qassem ya yi fatali da kiraye-kirayen kwance amarar kungiyar Hezbollah