2025-04-22@00:04:37 GMT
إجمالي نتائج البحث: 38

«kiraye kiraye»:

    Kasashen Masar da Kuwaiti sun fitar da sanarwa a yau Litinin ta yin tir da kiraye-kirayen da wasu yahudawa masu tsattsauran ra’ayi suke yi domin a rusa masallacin kudus, suna masu yin kira ga kungiyoyin kasa da kasa domi a tsayar da tsokanar da Isra’ilawa suke yi. Kasashen biyu dai sun fitar da wannan sanarwar ne bayan da wasu yahudawa su ka watsa wani faifen bidiyo na tarwatsa masallacin Kudus da kuma maye gurbinsa da gina wajen bautar yahudawa. Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta bayyana cewa: “Jamhuriyar Larabawa ta Masar tana yin tir da kakkausar murya akan kiraye-kirayen da masu tsattsauran ra’ayin ‘yan share wuri zauna suke yi na tarwatsa masallacin Kudus. Haka nan kuma Masar din ta yi kira...
    Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya reshen jihar Filato ta gudanar da wata zanga-zangar lumana domin nuna adawa da matsalar tsaro da ke addabar jihar. Zanga-zangar ta gudana ne makonni kaɗan bayan munanan hare-haren da aka kai a wasu ƙauyukan Bokkos da Mangu, waɗanda suka yi sanadiyyar aƙalla rayuka 100. Bikin Ista: Hatsarin mota ya laƙume rayuka 5 a Gombe An jingine wasanni a Italiya saboda mutuwar Fafaroma Francis Waɗanda suka yi zanga-zangar sun haɗa da maza da mata da matasa har da tsofaffi ɗauke da alluna waɗanda aka rubuta wa saƙonni daban-daban. Bayanai sun ce maƙasudin zanga-zangar ita ce kiran gwamnati kan ta ɗauki mataki kan kashe-kashen da ake yi a yankin. Jihar Filato da wasu jihohin Arewa maso tsakiyar Nijeriya...
    Hatsarin mota ya yi ajalin mutum biyar tare da jikkatar wasu takwas a yayin da suke bikin Ista a garin Billiri da ke Jihar Gombe. Hatsarin ya faru ne a safiyar ranar Litinin, lokacin da direban wata babbar mota mai ɗauke da buhunan hatsi daga Jihar Adamawa ya auka kan dandazon jama’a da ke tsaka da shagalin bikin Ista. An jingine wasanni a Italiya saboda mutuwar Fafaroma Francis An kama tsohuwa kan zargin lalata da almajiri a Bauchi A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi gaggawar kai ɗauki, inda suka kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti. Sanarwar ta kuma ce bayan faruwar hatsarin,...
    A nawa raayin hakan ba zai zama lefi ba indai har tsakani da Allah suke son junansu. Lokacin fira daban lokacin ziyara kuwa shi zuwa yake yi babu wani lokaci a yadda na fahimci topic din. Ni dai zan tsara shi ne ranar Alhamis bayan sallar la’asar zuwa sallar magrib idan ma firar ta dauki lokaci sosai kenan ya isa tunda ana waya ko chart. A shawarce hakan sai na ga ba lefi bane duba da an zama daya kuma wannan shi ne zai kara sa nutsuwa a zukatanku na tabbacin kowannenku ya san babu wasu da suke kulawa, sannan zai rage karairayin da ake samu wajen sutura ko gidajenmu ko ababen hawanmu dama abokai ko kawayen da muke kulawa....
    Sakatare-janar na kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya yi Allah wadai da kalaman da kiraye kirayen da ake na “kwance damarar” kungiyar Hizbullah, yana mai kiransa da cewa wani yunkuri ne na raunata kasar Lebanon da kuma ci gaba da fadada manufofin Tel Aviv. Sheikh Naim Qassem ya bayyya hakan ne a wani jawani da ya gabatar da kai tsaye ta talabijin jiya Juma’a. Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a karshen shekarar da ta gabata da nufin kawo karshen kazamin rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 4,000 a kasar Labanon. Sheikh Qassem ya jaddada cewa ci gaba da kokarin da...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Benuwe a ranar Alhamis ta tabbatar da cewa an samu kwanciyar hankali a unguwar Otobi da ke Ƙaramar hukumar Otukpo biyo bayan wani mummunan hari da ya tilastawa mazauna garin barin gidajensu. Kakakin rundunar ’yan sandan, CSP Catherine Anene a wata tattaunawa ta wayar tarho da wakiliyarmu, ta kuma yi watsi da rahoton sabbin hare-haren da aka kai kan unguwannin Emichi, Okpomaju da Odudaje, inda ta bayyana su a matsayin rahoton ƙarya don yawo tsoratar da jama’a. An kashe sojoji, fararen hula da dama a Borno ’Yan Najeriya miliyan 150 sun samu ingantacciyar wutar lantarki – Minista “Unguwar Otobi yanzu akwai kwanciyar hankali, mun bar wasu jami’anmu tun ranar Laraba ana gudanar da bincike,” in ji...
    Masu wannan fahimta sun yi imanin cewa duk lokacin da mutum ya ji baya son wani abu to a wurinshi wannan abin ba mai kyau ba ne. Haka nan kuma duk lokacin da mutum ya ji cewa ga wani abu amma shi ne ya kwanta mashi, toh wannan abin shi ne mai kyau. Babban misalin da wadannan masu ra’ayi suke jaddadawa da nanatawa a kullum shi ne cewa a lokacin da mutum ya yi tsammanin cewa wani abu na da kyau a ra’ayinshi, to idan ya je cikin wata al’ummar zai tarar da cewa wannan abin barna ko wani abin ki. Misali da shan giya, caca da sauransu. Da irin wannan nazari ne aka samar da mafi shaharan nazariyyar nan...
    Wata budurwa ’yar kasar China ta janyo muhawara a shafukan sada zumunta bayan ta nuna masaukinta da ba a saba gani ba — banɗaki mai faɗin ƙafa 6 a wurin aikinta, wanda ta biya kuɗin China Yuan 50 kacal, kwatankwacin Naira dubu 10 da dari 533. Kowa yana ƙoƙari ya tara kudi, amma mutum nawa ne za su yarda su kwana a banɗaki don tara kuɗi? HOTUNA: Zulum ya karɓi baƙuncin Majalisar Sarakunan Arewa a Borno Hauhawar Farashi ya ƙaru a watan Maris — NBS Wannan budurwa ’yar garin Hunan a ƙasar China, ta girgiza duniya kwanan nan, bayan ta wallafa hotunan wajen zamanta da ba a saba gani ba – wani ƙaramin banɗaki da ba a amfani da shi...
    Ilimi Gishirin Rayuwa Babu shakka ba tun yanzu ba, dan’adam ya dade da fahimtar muhimmancin ilimi ga cigaban rayuwarsa. Walau ilimin addini ko na cigaban rayuwa. Addinin Musulunci ya koyar da mu muhimmancin bai wa ilimi fifiko, kamar yadda aka rawaito a cikin Hadisi. Ma’aikin Allah (SAWA) yana cewa ‘mu nemi ilimi ko da a Birnin Sin ne’. Kuma ya gaya mana cewa, “haddar yaro karami kamar rubutu ne akan dutse…” Kenan, wannan yana karfafa mana gwiwa mu koyawa yaranmu Ilimi tun suna kanana, don za su fi rikewa ya zauna a kwakwalensu. Ilimi tamkar fitila take, yana haskakawa mutum abubuwa na rayuwa, yadda zai koyi zaman duniya da gina wa kansa rayuwa mai inganci. Wannan ilimin kuwa ko...
    Rasuwar Sheikh Dakta Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi rasuwa ce da ta jijjiga al’ummar Nijeriya da ma ƙasashen ƙetare, bisa la’akari da irin faɗakarwarsa da karantarwarsa da gwagwarmayarsa. Hakan ya jawo dandazon al’ummar Musulmi suka halarci sallar jana’izarsa kuma fitattun mutane da malamai suka yi ta yin ta’aziyyar rasuwarsa. Lokacin da Malamin yake raye kusan a kulum sai ya gabatar da huɗuba ko darasi na wayar da kan al’umma ko kuma ilmantar da su kan wani abu mai muhimmanci a masallacinsa da makarantarsa. A ’yan shekarun nan Allah Ya jarrabe shi da rashin lafiya, wanda a sanadiyyar haka ya xauki tsawon lokaci ba a ji huɗubarsa ko karantarwarsa ba da suke xaukar hankalin dubban masu sauraro a faɗin Afirka, lamarin...
    Wakilin kungiyar Hizbullah a majalisar dokokin kasar Labanon ya yi kira ga gwamnatin kasar da ta ba da fifiko wajen dakatar da hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa kasar Labanon. A cewar Al-Mayadeen Hassan Fadlallah mamba a bangaren Hizbullah a majalisar dokokin kasar Labanon ya ce: Dakatar da wuce gona da iri kan kasar Labanon wani muhimmin al’amari ne na kasa da ya zama wajibi a sanya shi cikin ajandar gwamnatin Lebanon. Ya kara da cewa: Al’ummar kasar Labanon suna fuskantar wuce gona da iri na gwamnatin sahyoniyawan tare da yin kira ga gwamnati da ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na dakile wannan ta’addanci. Fadlallah dai ya dauki babbar matsalar...
    Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana gamsuwarta da yadda ake ci gaba da gudanar da ayyukan gina tituna da gyare-gyare a fadin jihar.   Kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa na jihar Alhaji Lawal Barau Bungudu ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau babban birnin jihar.   Alhaji Lawal Barau Bungudu ya bayyana cewa, tun bayan hawan Gwamna Dauda Lawal mulki, gwamnatin ta ba da fifiko wajen samar da ababen more rayuwa, musamman gine-gine da sake gina tituna, a wani bangare na babban shirinta na sabunta birane da nufin kawo sauyi a jihar da kuma saukaka zirga-zirgar ababen hawa.   Ya ce gwamnatin jihar ta dukufa wajen fadada hanyoyin jihar domin ingantawa...
    Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF), ya buƙaci Gwamnatin Najeriya da ta tabbatar da cewa manufofin tattalin arziƙin ƙasar sun kare muradun mutane masu rauni. Daraktar Hulɗa da Jama’a na IMF, Julie Kozack, ta bayyana hakan a yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Washington, D.C. NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16m Ta jaddada muhimmancin bai wa talakawan Najeriya masu fama da ƙuncin rayuwa tallafin kuɗi sakamakon sauye-sauyen tattalin arziƙi. Aminiya ta ruwaito cewa cire tallafin man fetur, wanda IMF ta ba da shawara a kai, ya haifar da tashin farashin man fetur daga kimanin Naira 200 kan kowace lita zuwa...
    Yanzu da ya rasu, Hauwa ta ce ba ta da tabbas kan yadda za ta yi rayuwa da ‘ya’yanta. Lamarin mai tayar da hankali ya faru ne a ranar 27 ga watan Maris, lokacin da wasu matafiya 16 ‘yan asalin Arewacin Nijeriya suka faɗa tarkon wasu ‘yan sa-kai a Uromi, a Jihar Edo, inda suka kashe su. Wani rahoto na musamman da gidan talabijin na News Central TV, ya bayyana halin da Hauwa ke ciki, wanda ya nuna irin tasirin da wannan lamari ya haifar. Yanzu tana fuskantar babban ƙalubale na kula da ‘ya’yanta bakwai, tare da neman mafita game da rayuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau, da dama daga cikin matasan Najeriya na fama da matsaloli masu tarin yawa, musamman wajen ciyar da kansu da biyan buƙatunsu na yau da kullum. Wannan na faruwa ne sakamakon halin da tattalin arziƙin ƙasa ke ciki, rashin aikin yi, da kuma tsadar rayuwa. NAJERIYA A YAU: Yadda Ake Yi Wa ‘Yan Majalisar Ƙasa Kiranye NAJERIYA A YAU: Illar Sare Itatuwa Ga Sauyin Yanayi Da Lafiyarmu Wasu daga cikin matasan sun kammala karatu, wasu kuma suna da sana’o’in hannu, amma duk da haka, rashin samun aikin da zai biya musu buƙatunsu yana ƙara jefa su cikin mawuyacin hali. Wannan matsala na ci gaba da haddasa damuwa ga matasan ƙasar, inda da...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300 a Yobe Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu Ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara, tare da yin kira a gare su da su ci gaba da halaye nagari da suka koya a watan. Haka kuma ya jaddada muhimmancin soyayya, yafiya, da haɗin kai wajen gina al’umma. Tunji-Ojo, ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan...
    Kasashen Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun bayyana matukar damuwarsu kan yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sake dawo da yakin kisan kare dangi a zirin Gaza da kuma hare-haren da Amurka ke kaiwa kasar Yemen. A wata tattaunawa ta wayar tarho a wannan Juma’a, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na UAE  Abdullah bin Zayed Al Nahyan, sun tattauna batutuwan da suka shafi yankin, musamman ma ayyukan wuce gona da iri na Isra’ila a Gaza da kuma hare-haren Amurka a Yemen. Araghchi ya yi kakkausar suka kan kisan gillar da gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta yi wa daruruwan Falasdinawa  da ba su ji ba ba su gani ba tun daga ranar Talata, yana mai jaddada cewa yin...
    “Gwamnati gaba daya ta dogara ne kan yadda za ta kyautata rayuwar jama’a, mun dauki lamarin matasa da muhimmanci sosai.” Ya tabbatar wa matasan cewa gwamnatinsa a kowani lokaci a shirye take wajen yin ayyukan tukuru domin kyautata rayuwar matasa da saukaka matsalolin da Nijeriya ke fuskanta. Kan kwamitin da ya kaddamar, Tinubu ya kalubalancesu da su yi aiki tukuru domin ganin rayuwar matasa ya samu tagomashi a kowani lokaci. Shi kuma a jawabinsa, ministan bunkasa harkokin matasa, Ayodele Olawande, ya ce, kwamitin za su yi aiki sosai wajen ganin an samu inganta shigo da matasa cikin sha’anin mulki. Olawande ya lura cewa gwamnatin Shugaba Tinubu gwamnati ce mai saurare da ke shirye ta mai da hankali tare da hada...
    Rahotanni da ke fitowa daga kasar suna nuni da cewa, Yawancin fararen hula da aka kashe a tashe-tashen hankulan da suka faru a wannan Juma’a, dakarun sabuwar gwamnatin kasar ta Syria ne suka kashe su, kamar yadda binciken kungiyar kare hakkin bil Adam ta (SOHR) ya tabbatar. Ayyukan tashe-tashen hankulan sun yi sanadin Kisan mutuwar fararen hula 162 a lardunan gabar tekun Syria, ciki har da mata da kananan yara, in ji rahoton kungiyar ta SOHR. Akasarin wadanda aka kashe dai kamar yadda aka gani a wasu fayafayin bidiyo da aka dauka, jami’an tsaron sabuwar gwamnatin Syria ne da suke da alaka kungiyoyi masu tsatsauran ra’ayi irin su Tahrir Sham da makamantansu da suke da alaka da Alqaida ne suka...
    A wani bincike mai kayatarwa da wani rukuni na masana kimiyya na kasar Sin ya gudanar, ya gano wasu tsare-tsaren gudanar da rayuwa, a muhallin halittu mafi zurfi cikin kwarin teku da ake cewa “Mariana Trench”. Wurin da ake ganin shi ne mafi zurfi a sassan tekunan duniyar nan. Sakamakon binciken da aka wallafa a mujallar “journal Cell”, cikin wasu takardun bincike 3, ya bayyana cewa, ta amfani da na’urar nutso a karkashin teku mallakin kasar Sin mai suna Fendouzhe, masu nazarin kimiyyar sun gano tsare-tsaren gudanar rayuwa na musamman, da ma albarkatun dake tattare da kananan halittu dake rayuwa a wurin mai tsananin zurfi, da halittu dangin kaguwa, da dangin kifaye dake wurin. Kazalika, sakamakon binciken ya baiwa bil...
    Ƙamshi abin so ne a wurin kowa. Mata su kasance suna saka turaren wuta a kullum. Su mayar da shi dole kamar yin wanke-wanke. Ko kun san cewa, wannan turaren wutar za a iya amfani da shi da kabbasa domin turara zanin gado da rigar sawa? An horas da masu unguwannin Katsina kan sasanta jama’a Ramadan: Gwamnatin Jigawa ta rage lokacin aiki Bayan haka, akwai turaren humra wadda za a iya shafa shi a gashin kai. Akwai na hammata daban sannan akwai na shafawa kamar mai, wanda aka fi sani da kulacca da kuma na riga. Lallai duk macen da ta kasance cikin ƙamshi, za ta sami girmamamwa a cikin al’umma da kuma mai gidanta. Kuma akwai turaren kanti kamar...
    Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Nasarawa da Toto daga Jihar Nasarawa, Honorabul Abdulmumin Ari ya ba da cekin Naira miliyan 45 don biyan kuɗin jarabawar WAEC ga daliban sakandare a mazaɓarsa. Da yake jawabi a wajen taron a garin Keffi, Abdulmumin Ari ya bayyana cewa kimanin shekara biyar ke nan yake aikin agaza wa daliban mazaɓar a duka matakai don cika alkawura da ya yi a baya. Ya ce ya yanke shawarar yin haka ne don tallafa wa iyayen ɗalibai marasa galihu don ba su damar cimma burinsu na samar wa ’ya’yansu ilimin zamani dana addini. Ya ce kawo yanzu ya kashe sama da Naira miliyan 500 a cikin shekara biyar da duka gabata a kan irin wannan aiki....
    Rashin kishin wani mutum ya zama abin mamaki bayan ya bayyana cewa, yana zaune lafiya tare da matarsa da suka yi shekara uku da wani saurayinta har ma sun shigo da shi cikin gidansu. Prince Soy, matashi mai dafa abinci a kasar Japan kuma mai amfani da intanet, wanda ke tallatawa da siyar da abincin gargajiya na kasar na okara granola a intanet, kwanan nan hankali ya koma kansa. Ya rasu a yayin buɗa-baki a Abuja Ramadan: Coci ya ciyar da Musulmi 1,000 a Kaduna A ranar 8 ga Yuli, ya sanar a shafin sa na sada zumunta na kafar X cewa, matarsa Seira za ta dawo gida bayan ta shafe wata shida tana karatu a kasashen waje kuma za...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wutar lantarki a Najeriya ta zama ginshiƙin rayuwa da al’umma ba sa iya rayuwa ba tare da ita ba. A duk lokacin da aka ɗauke ta al’umma kan shiga matsanancin hali. Mutane da dama sun dogara ne da wutar lantarki wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum, kai har ma da na kasuwanci. A kwanakin baya ne jihohin Kaduna, Sakkwato, Zamfara da kuma Kebbi suka fuskanci ɗaukewar wutar lantarki na tsawon kwanaki, wanda ya jefa al’ummar jihohi cikin halin ni-’yasu. NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi? DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wutar lantarki a Najeriya ta zama ginshiƙin rayuwa da al’umma ba sa iya rayuwa ba tare da ita ba. A duk lokacin da aka ɗauke ta al’umma kan shiga matsanancin hali. Mutane da dama sun dogara ne da wutar lantarki wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum, kai har ma da na kasuwanci. A kwanakin baya ne jihohin Kaduna, Sakkwato, Zamfara da kuma Kebbi suka fuskanci ɗaukewar wutar lantarki na tsawon kwanaki, wanda ya jefa al’ummar jihohi cikin halin ni-’yasu. NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi? DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na...
    Fiye da mutane 7,000 da yawancinsu fararen hula ne aka kashe a yankin gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango tun daga watan Janairu, in ji Firaminista Judith Suminwa Tuluka a ranar Litinin. Mambobin kungiyar M23 da ke samun goyon bayan kasar Rwanda sun kwace iko da yankunan gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo masu arzikin ma’adinai da suka hada da manyan biranen Goma da Bukavu da ke gabashin kasar. Firayim Minista Judith Suminwa Tuluka ta yi gargadin cewa, halin da ake ciki na tsaro a gabashin DRC ya kai matsayi mai daukar hankali, yayin da take jawabi ga kwamitin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya a Geneva. Ta ce mutanen da suka mutu sun hada da “fiye da gawarwaki 2,500 da aka binne...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa matukar aka samu mamaya to za a samu manyan mutane irin shahid Sayyeed Hasan Nasrallah da za su tsaya tsayin daka kan yaki da hakan, kuma ba za su bari ‘yan mamaya su cimma manufarsu ba. Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa, Hizbullah tana nan a raye kuma tana ci gaba da bin tafarkinta mai daraja fiye da kowane lokaci a baya. A yayin zaman majalisar ministocin kasar Iran, Pezeshkian ya bayyana cewa, matukar dai abin ake yi na zalunci da danniya a kan masu rauni zai ci gaba, to kuwa tabbas ba za a rasa mutane irin Nasrallah ba, masu tsayin daka da jajircewa wajen tunkarar zalunci da...
    Aƙalla mutum 12 — ciki har da mata huɗu da maza takwas — sun riga mu gidan gaskiya a sanadiyyar wani mummunan haɗarin mota da ya auku a kan hanyar Lapai zuwa Agaie da ke Jihar Neja. Wani da lamarin na safiyar wannan Asabar ɗin ya faru a kan idonsa, ya shaida wa Aminiya cewa uku daga cikin matan da suka rasu ’yan gida ɗaya ne. Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Kano ta raba kayan tallafi Ɗan Abacha ya kare mahaifinsa bayan ƙaddamar da littafin IBB Sai dai wasu fasinjoji uku da suka haɗa da mata biyu da direban motar sun tsallake rijiya da baya, inda a yanzu suke samun kulawa a Babban Asibitin Lapai. Bayanai sun ce haɗarin ya auku ne...
    Hukumomin Jami’ar Tarayya da ke Lokoja a Jihar Kogi, sun rufe jami’ar har zuwa wani lokaci domin daƙile ci gaba da asarar rayuka da dukiya. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun magatakarda kuma sakatariyar majalisar Jami’ar, Dokta Rebecca Aimiohu Okojie, a ranar Alhamis kuma ta bayyanawa manema labarai a Lokoja. Jihar Gombe na ƙarfafa haƙƙoƙin yara masu nakasa — Ƙungiyar JONAPWD NNPP ta rasa Ɗan Majalisa na farko da ya koma APC Hukumar Jami’ar ta yi zargin cewa, ɗaliban sun tare babbar ƙofar shiga jami’ar ne tun bayan haɗarin da ya yi sanadin mutuwar ɗaliban jami’ar biyar a ranar Litinin, wanda ya sa shiga harabar jami’ar ke da wuya. “Rufewar jami’ar ya biyo...
    Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan zanga-zangar yunwa, ya gano cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum bakwai suka samu munanan raunuka. Rahoton ya kuma bayyana cewa an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11, sakamakon ƙone-ƙone, sace-sace, da lalata kadarorin gwamnati da na ’yan kasuwa a faɗin jihar. Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram Da yake jawabi a taron majalisar zartaswar ta jihar karo na 25 a ranar Talata, Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi rahoton daga shugaban hannun kwamitin, Mai shari’a Lawan Wada (ritaya). Ya tabbatar da cewa za a fitar...
    Gwamna Umar Namadi  ya kaddamar da aikin gina titin Kanya Babba (Kwanar Duzau) zuwa Kankare zuwa Ballada zuwa Duzau zuwa Danhill zuwa Kyambo zuwa Mundu zuwa Goron Maje. Aikin wanda aka bayar da shi kan kudi naira biliyan 6 da miliyan 300, wani muhimmin mataki ne a yunkurin gwamnatin jihar na inganta ababen more rayuwa da  hanyoyin sada yankuna. Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Namadi ya jaddada muhimmancin hanyoyin, wajen samar da ci gaban tattalin arziki, da inganta hanyoyin samar da ababen more rayuwa, da inganta rayuwar al’ummar yankin. Ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na samar da ingantattun ababen more rayuwa da za a dade ana amfana da su. Ya kuma bayyana cewa,  ana sa ran ...
    Bayan bincike ta hanyar fasaha, an gano inda wayarta take, wanda hakan ya kai ga kama Abdulrahman Bello. Lokacin da aka kama shi, ya amince da laifin kisan Hafsoh da nufin yin sihirin kudi (oshole/ajoo owo). A binciken da aka yi a gidansa, an samu: Wayoyi biyu da takalmin mamaciyar Hannaye da aka sare daga jikin gawarta roba mai dauke da jininta Adda, wuka, gatari, da akwatin sihiri Buhun tsafi da tebur da aka yi amfani da shi wajen aikata kisan An tura Abdulrahman zuwa sashen binciken manyan laifuka (SCID) Ilorin, domin zurfafa bincike da gurfanar da shi a gaban kotu. Mai martaba Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya bayyana takaici kan wannan ɗanyen aiki, yana mai cewa “abin baƙin...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ta sanar da kiran taron kasahen larabawa a karshen wannan watan na Febrairu da ake ciki domin tattauna batun tilasta wa Falasdinawa yin hijira daga Gaza a karkashin shirin Amurka da Isra’ila. Da safiyar yau Lahadi ne dai ma’aikatar harkokin wajen ta Masar ta bayyana cewa za ta karbi bakuncin taron kungiyar kasashen Larabawa a ranar 27 ga watan nan na Febrairu,domin tattauna sabbin batutuwan da su ka taso dangane da Falasdinu. Har ila yau sanarwar ta ce, Masar din ta yi wannan gayyatar ne bayan tattaunawa da kasar Bahrain wacce a halin yanzu take rike da shugabancin kungiyar kasashen Larabawan, haka nan kuma tuntubar babbar shalkwatar kungiyar. Bugu da kari Masar din ta sanar...
    Wani matashi ɗan kasar Argentina mai shekara 23 ya rasa ransa a sakamakon daɓa masa wuƙa da budurwarsa ta yi saboda kawai ya gaisa da wata mata a kan titi. Kishi madaidaici zai iya zama abu mai masu alaka da juna, amma mafi yawanci na iya wuce kima! Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano Shigo da hatsi daga ƙetare ya karya farashinsa a Neja Idan aka dubi labarin Mariano Grinspun, ɗan shekara 23 daga González Catán, wani birni a lardin Buenos Aires na Argentina, wanda budurwarsa mai tsananin kishi ta caka masa wuka wanda ya yi sanadiyya mutuwarsa bayan ya gaisa da wata tsohuwar abokiyar karatunsa a titi, za a ga abin akwai ban mamaki. Abin ya faru ne...
    Shugaban Majalisar Wakilai Dr Abbas Tajuddeen, ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar fitaccen dan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, Alhaji Bala Abdulwahab da ke Zariya, wanda aka fi sani da Albabello. A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Malam Musa Abdullahi Krishi ya fitar, Dakta Abbas Tajuddeen, ya ce masarautar Zazzau da jihar Kaduna sun yi rashin babban dan kasuwa wanda ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen yi wa al’umma hidima. Shugaban majalisar ya jaddada cewa, Albabello, ta hanyar sahihancinsa na kasuwanci, ya samar da ayyukan yi ga dubban jama’a a Zariya da ma fadin kasar nan, ta hanyar amfani da rassan kamfaninsa daban-daban. Ya ci gaba da cewa Albabello, ya kuma...
    11-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da war haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na Aya. Shahida Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin rumi. Ko kuma cikin wasu littafan. Da fatan masu sauraro zasu kasan ce tare da mu. ///..Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a shikin shirimmu da ya gabata, mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Hassan (a) jikan manzon All..(s) kuma limami na biyu daga cikin limamai masu tsarki daga cikin iyalan gidan manzon All..(s), sannan dan Fatimah(a) diyar manzon All..(s) na...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta kashe sama da naira miliyan dubu dari da sittin da hudu wajen tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu a jihar. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da rabon katin cire kudi na ATM ga wadanda suka ci gajiyar shirin inganta rayuwar al’umma na gwamnatin tarayya da aka gudanar a sakatariyar karamar hukumar Dutse. Malam Umar Namadi ya bayyana cewar, hukumar bunkasa tattalin arziki ta jihar ce ta fitar da ta hannun shirin farfadowa daga annobar cutar corona. A cewar sa, kusan mutane dubu ashirin da uku ne za su amfana da tallafin naira dubu saba’in da biyar a jihar. Yana mai cewar, hakan na daga cikin kudirin shugaban kasa na Renewed Hope agenda...
۱