Yadda Rashin Ilimi Ke Cutar Da Rayuwar Al’umma
Published: 12th, April 2025 GMT
Ilimi Gishirin Rayuwa
Babu shakka ba tun yanzu ba, dan’adam ya dade da fahimtar muhimmancin ilimi ga cigaban rayuwarsa. Walau ilimin addini ko na cigaban rayuwa. Addinin Musulunci ya koyar da mu muhimmancin bai wa ilimi fifiko, kamar yadda aka rawaito a cikin Hadisi. Ma’aikin Allah (SAWA) yana cewa ‘mu nemi ilimi ko da a Birnin Sin ne’.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya hanyoyin da rashin ilimi ke cutar da al’umma suna da yawa domin shi ilimi jigo ne na rayuwar dan’adam muddun kuwa aka ce babu shi to dole abubuwa da dama ba za su tafi daidai ba, domin shi ilimi dan jagora ne ga duk kanin dan’adam shi ke haskawa mutum hanyar daya kamata ya bi da wacce ya kamata ya kaucewa don matsalolin da rashin ilimi ke haifarwa sun fi gaban kidayawa ko kirdado. To magana ta gaskiya a wannan fannin gwamnati ya kamata ta tashi tsaye wajen inganta fannin ilimin dama samar da shi kyauta ga duk kanin al’ummar kasa, sai kuma iyaye suma su tashi tsaye wajen kulawa da sa ‘ya’yansu a makaranta da kuma kula da zuwan yaran akan lokaci. To magana ta gaskiya kimiyya da fasaha tana bada gagarumar gudunmawa wajen saukaka samun ilimi a wannan zamani da muke ciki shi ya sa za ka ga dukkanin kasashen da suka cigaba ta fannin ilimin kimiyya da fasaha to sun fi samun cigaba a fannin ilimi. To amfanin ilimi ko muhimmancin ilimi ga rayuwar dan’adam ya fi gaban kidayawa ko kirdado domin sai da ilimi ne rayuwar take yin kyau kuma sai da ilimi ne ake samun cigaba a rayuwa. To hakika ya kamata irin wannan iyaye su sake tunani domin fa ilimi shi ne hasken rayuwa wanda duk ya rasa ilimi to ya rasa komai a rayuwarsa don haka ya kamata iyaye su tashi tsaye wajen kulawa da ilimin ‘ya’yansu.
Sunana Fatima Nura Kila A Jihar Jigawa:
Rashin ilimi na haifar da matsaloli musamman a cikin al’umma kamar su sata, fyade, rashin girmama manya duk wadannan rashin ilimi na kawo su. Hanyar daya kamata abi shi ne; Gwamnati ta zage damtse wajen tura yara makarantu da kuma saukaka karatu tun daga matakin firamare, har gaba da sakandare. Ilimin kimiyyya nada matukar amfani ga al’umma ta fuskar tabbatar da sauye-sauye tare da samar da cigaban rayuwa, musamman abin da ya shafi bunkasa tunanin dan’adam wannnan ba karamar taka muhimmiyar rawa yake ba. Ilimi jigo ne sannnan mahadin rayuwa ne, ilimi na da amfani musamman wajen zamantakewa da kuma kasuwancinmu na yau da kullum. Shawarar da zan basu shi ne su bar ‘ya’yansu su je makaranta domin Ilimi shi ne ginshikin rayuwa, mutum mai ilimi ma ya fita daban a cikin al’umma.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Jihar Kano Rano LGA:
Hanyoyin suna da yawa amma daya daga ciki ita ce; aikata ibada ba daidai ba da sabawa Allah kai tsaye. Samar da ilmi ta internet duk da mafiya yawan wasu mutanen tuni sun yi nisa ta wannan fannin. Wajen kirkirar wasu abubuwan da bamu saba ganinsu ba a yankunanmu. Daya daga cikin amfani Ilmi shi ne; aiki da shi a dukkan al’amuranka. Shawarata a garesu ita ce gaskiya su canja tunani kada iyaye su ga wai yanzu idan ka yi karatu ba a samun aikin yi a’a shi ilmi koda irin ‘yan iskan gari ne za ka ga sun bambanta da wadanda ba su yi ba, a saka yara su yi Ilmi ko wanne iri ne domin a can gaba za a ga amfaninsa. Allah ya sa mudace.
Sunana Aisha T Bello Jihar Kaduna:
Rashin ilimi cuta ce gaskiya, saboda ilimi shi ne kishin zaman duniya, yanzu misali; gida babu miji ya rasu in mata na da ilimi za ta nemi aiki dan ta kula da yaranta. Saboda yanzu duniya da zaran ba maigida ba masu kulawa da marayu Allah ne gatansu. Kimiya da fasaha na taka rawa sosai wajen kawo, cigaba ga al’umma bakidaya. Ga iyayen da basu tura yara makaranta gaskiya babbar cutarwa ce, domin kuwa yanzu duniya ta ci gaba, yanzu idan baka da ilimi kana ji kana gani ka zama dan kallo, don haka iyaye su daure su tura yara makaranta don cigaban al’umma bakidaya. Allah ya amfanar damu baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Taskira rashin ilimi Rashin ilimi Rashin Ilimi a makaranta
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Tasirin ’Yan Uwantaka Ga Rayuwar Al’umma
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Irin alaƙar da ke tsakanin wasu abokai na da matuƙar kusanci da kyau, ta yadda a wasu lokutan ma ba a iya banbance dangantakar tsakaninsu ta ’yan uwan na jini ko kuma abota.
Irin wannan dangantaka ya kamata ne a ce ana samun ta a tsakanin ’yan uwa na jini.
Sai dai a yayin da wasu ke samun kyakkyawan dangantaka tsakaninsu da ’yan uwan su na jini, wasu kuwa ba sa ga-maciji da nasu ’yan uwan da suke uwa ɗaya uba ɗaya.
NAJERIYA A YAU: Dabarun Samun Kuɗaɗe Ta Hanyar Amfani Da Wayar Hannu DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan irin tasirin da ’yan uwantaka ke da shi ga rayuwar mutum.
Domin sauke shirin, latsa nan